Showing 30001 words to 33000 words out of 61932 words

Chapter 11 - DAN HAKIN DAKA RAINA Zuciyar Uwa BY UMMUH FATEEMAH

10 Jul 2026

124

'karawa, babu mai lallashi


   Dan Anas ana fad'a masa yajuya yatafi dan siyo musu kayan da za'asa musu, yayi musu siyayya sosai yakawo aka shirya yaran cikin kayan sanyi green ☘ da white sunyi kyau acikin kayan


Ita kuma yasaka Jazuli agaba sukaje aka d'auko mata kayan sawa, dan ko takan Balaraba Bai biba bare tasaran zai bata hakuri, dan gani yake abunda suke aikatawane yake dawo musu


Saida Hapsatu ta kwashi tsawon sati 5 kafun ta warware sosai jikinta yayi kyau tayi lumi mi abunta sbd Anas yana bata kulawa ita da yaranta

   Amman tun daga wannan lokacin data haihu har kawo yanzu basa magana da Mama Balaraba dan ita tsoronsa takeji sbd yadda yake had'erai inya shigo


Shima Jazuli sosai yake kulawa da iyalansa dan yanasan yaran sosai

    Yau Fauziyya tayi sati na 6 a asibiti amman dinkin nata bai warkeba dan haka doctor faruq yace abari ta 'kara sati biyu in sha Allah zai warke



Haka kuwa akai kafun sati biyun ma yawarke, aikuwa ana sallamar su suka wuce gidan su Mama Balaraba acan tayi wanka tayi dukkan jegonta inda jarabar "yan unguwa ma ta ishe su, kullum ba'a rasa mai zuwa ya'kare musu zagi


   Saida Anas yatashi tsaye sannan suka samu sukuni, kusan kullum cikin kuka Balaraba take na wannan haihuwar da Fauziyya tai


    Yau tun wurwuri tagama komai aka yankawa yaran hakika akan barsu da sunan su hasan da usaina
    Ad'an dafa abunci aka raba, sunyi taro amman ba sosai ba, dan komai rabun abun ma Anas ne yayi matashi




Kullum baya gajiyawa dayi musu hidima, in kagansa kamar bashi da damuwa

     Amman a'kasan ransa kuma tunanin inda zaiga hapsatune da 'kaninta kullum yake damunsa dan duk inda zaije cigiya yaje, har gidan redio da TV duk yake amman shiru, yana damuwa sosai dan duk Jazuli yabasa labarin komai daya faru


   Bayan an kammala suna ba'a watse ba saida aka kusa dambe da'kar aka shawo kan abun aka samu sauki

  Alhaji kuwa baban su Hapsatu yadamu sosai da wannan d'ibar albarkar da ake masa agidan sa kullum


   Hakadai yake hakuri dan babu yadda zaiyi


Yau tun safe Balaraba ke shiri ita da Fauziyya suka goya yaran suka kama hanyar gidan Boka



Babu 6ata lokaci suka isa wannan 'kasurgumun jejin suna isa cikin bukkarsa

   Yafara she'ka Dariya yana shewa harda tafawa hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh  😁😁😀😀😀😂😂😂😂😂

   Kun 'Kara so alokacin daya dace sosai ma kuwa, kuzauna kuzauna
   Zama sukai nan yafara labarta musu cewa, ai anan Jazuli yazo ya amshi maganin mallaka wanda shida Fauziyya mutu ka raba, kuma yace kar'abashi mai la'kanin dazai karye


   Kunyi sakaci dan bazata iya auren likitan nanba kuda nace muku tana haihuwa kuzo ko kuma ke kizo


Ai mlm babu natsuwane dan batai haihuwar kwanciyar hankali ba

     Mun sani ai dan mu muka rin'ka jaa mata rai dankarta haihu da wuri sbd tasa6a mana umarnin mu


  Toh yanzu boka menene abunyi
Hhhhh😀 ai abunyi d'ayane saidai ahaukata Jazuli saitayi wani auren amman idan ba haka ba tofa wannan auren bazai mutuba


Amman meyasa kai masa wannan aiki
    Hhhhh😀 Hhhhh😀 Hhhhh😀 kud'ifa zai bamu da jini tayaya bazamuyi masa aikiba
   Jini kuma?
Ey jinin haihuwarta yakwaso mana wanda kukace yazubar toshiyakawo mana mukuwa mukai aiki mai kyau



Toh gaskiya ahaukatashi sannan kuma akarkato da hankalin likitan nan yadawo kan Fauziyya sbd ayi ai auren nan muhuta

Zanyi aiki amman saidai kubari aure saita yaye yaran nan nanda wata 14  ai ayi aure


Aa mudai ayi auren in yaso komai ayishi daga baya
   To zanyi amman kuma saikinje kin kwanta da d'an tsito
    Dan me?
Abunda kunnen ki yajiye miki, inba hakaba kuma, kutashi kuban guru
   Zanyi ranka yadad'e duk yadda kace haka za'ai babu matsala


Toh tashi kishiga yana jiranki, saiku tafi daga baya, tashi tai tashiga d'ayar rumfar, tana ta sauri sbd ayi awuce gurin


   Dagataje sai tagansa yana zaune haihuwar uwarsa ba komai acikin jikin sa yana jiranta
   Tunowa tai dawahalar datasha rannan babu yadda ta iya haka ta 'karasa dan tasan idan tajuya sai yayi sau uku

    Tana zuwa tacire nata kayan, babu wani wasa ko wani abu, kawai far mata yay aikuwa ihuuu kawai kake jiyowa



  Fauziyya ce ta mi'ke zata shiga d'akin, Boka yatareta yace kina shiga kema saina kwanta dake kuma shima haka, dan bayasan yana aiki ashiga wannan yasa6awa dokar mu


Gaba tai abun....................... ✍🏻✍🏻✍🏻



Keep waiting my fan's 🤗🤗🤔🤔
Hallmarth ce💕💖💕

  
[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔*
_Story and written by_

*SADIYA •A• UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}




🅿---5⃣1⃣&5⃣2⃣


............... Gaba tai abunta harta kusa 'karasawa kuma saita fasa tajuyo,  sbd tasan mahaifiyarta jarababbiya ce amman kuma tana kuka dawa wannan d'an tsiton to ina kuma gani da bankaita jaraba ba

   Dawowa tai tazauna, Boka yafara dariyar mugunta Hhhhh😀 Hhhhh😀 Hhhhh😀 Ashe kinajin tsoro shegiya dakin je ai dayanzu munyi maganinki babu 6ata lokaci


Hhhhh😀 Hhhhh😀 Hhhhh😀 Hhhhh😀 dariyar ce tacika gurin sosai har tana yi mata amsa kuwa akunnen ta, haka ta hakura amman badan tana soba saidan babu yadda zatai tana jiyo ihun mahaifiyarta


   Saida Balaraba takwashi kusan awa 1h sannan yakammala, saida ta huta sannan da'kar takamo hanya tana jan 'Kafa ta futo, tanata sharar kwallah



Magun gunan su aka had'a musu sannan suka kama hanya suka tafi gida da'kar suka isa gidan


   Babu 6ata lokaci suka fara aikin da nakan dutse yasakasu, sunyi komai kamar yadda yace sannan suka koma suka sanar dashi, yace toh su jira nanda kwana 7 komai zaiyi yadda sukeso
    Sannan yabasu wani magani yace suyiwa likitan farfesu susaka masa aciki, idan yazo, yanaci shikenan zance ya'kare dan kuwa baza'ai wata ba zai turo


Haka kuwa akai dan bayan kwana 7 komai yayi inda Jazuli yafara hauka harda bin mutane da bololi


Nanfa mama Balaraba tayi tsalle ta dire akan saiya saketa, aikam da dance masa kasaki Fauziyya saiduka baya bada amsa saidai duka kawai


    Haka dai tarinka shiga tana futa har aka raba auren nan, ba'adad'e da raba aurenba dan watanta biyu aikam sai ga doctor faruq nan

   Yasamu Alhaji yace yanasan auren "yarsa Fauziyya, yakuma gaya masa bayasan ad'auki lokaci
    Amsa masa yay ace amman yabari ta gama iddah kafun nan sai ayi maganar auren


  Ahaka suka rabu inda aka yi masa farfesu kamar yadda Boka nakan dutse yalabarta musu


Yaci kuwa sosai, aikam sunji dad'i ba kad'an ba
     dan suna ganin burin su yakusa cika akan sa

    Bayan wata d'aya da tafiyar doctor yadawo su Mm Balaraba ma anzata aiki baiyiba


     Saigashi da manyan ledoji da kud'i yakawowa Fauziyya, itakam sai yau'ki take tana wani rangwad'a alamar ta isa d'in nan
     Saida tagama yau'kin sannan taje, doctor faruq kuwa kamar zai haukace sanda yaganta haka yayta zuba yana yaba kyan ta(wanda nikam dana ganta kamar nayi kuka dan rashin had'uwa😙😙)

     Wasa² soyayya mai 'karfice tashiga tsakaninsu inda take samun kud'i yadda take so tayi mai ta'kara fari, gashi tasha, shaka fashe tayi wata irin 'kiba sosai

    Anas kuwa tun abun nabashi mamaki har yadaina, yazuba musu ido kawai dan dai yasan wannan abun bana Allah bane
   Babu abun da yake damunsa kamar rashin jin labarin Hapsatu dabaiyiba


     Yau tun safe su Mm Balaraba ke shiri ita da Fauziyya dan yaune za'a saka ranar auren su akuma kawo lefe dakud'in nagani inaso


  Sai wajen 12:09pm sannan suka iso Alhaji da kakah hajja sai gyaran gida ake anata gwalli za'a "yarsu zata auri mai kud'i
    Shidai Alhaji sbd kar kaka hajja tace zata tsine masa yasa yakeyin wasu abubuwan amman badan ransa yanasoba
    Kuma abunda yafi d'aga masa hankalinsa shine yanasan yatambayi ina su Hapsatu suke amman saiya kasa kwata²


    Koda family 'n su faruq sukazo sun raina wannan gidan da faruq yaketa rawar 'kafa akansu
    Saida sukaga amaryar ma sannan sukai dana sanin zuwan dasukai, dan waye baisan family d'insuba wajen bin bokaye da malamai har la'kabi ake musu da "ya"yan Allah bani sbd dukkan su halinsu d'aya



   Hakadai sukai duk abunda yakamata inda suka kawo lefe akwati 8 da bakko guda 2 anzuba kaya sosai
      Nan aka saka sati biyu dan haka faruq yace kuma yace kar akawota da komai yasaka komai acikin gidan sa



In kukaga Fauziyya abun saiya baku mamaki sosai dan babu kunya tazo tanata dudduba kayan tunkan ba'kin sutafi



Haka aka tafi da ita abaki anata zaginsu
    Itakam ko ajikinta saima shewa take da bud'a



   yarone yayi sallama, aka amsa yace kawu Anas yana nan
   Akace ey
Yace ana sallama dashi awaje
   Toh, kace waye
Futa yay, bai dad'eba yadawo
   Ance wai ansamu labarin wanda yagansu zasu hau mota subar gari
    Suwa fa inji Mm Balaraba
Anas ne yafuto dasauri yace A'a wannan zance nane
   Muje ko tasa yaron yay suka futa daga gidan ashirin yabashi yace ngd kaji yaron kirki

  Amsa yay yana ta murna yace angode kawu

    Yana futa yaga wani mutum abakin kofa dasauri ya'karasa suka gaisa

    Mutumun ne yace yawwa wannan yarinyar daka bamu cigiya anganta amman kuma wanda yaganta yace ansaidasune gawasu mutane
    Masu siyan yara a garin Abujah

Mekace wannan yarinyar fa tacikin wayata
   Tabbas ita nake nufi dan har hotunan su yanunamun suna cikin adai-daita za'asiyar dasu kuma dama mai adai-daitar Saida yara suke shida mahaifiyar sa, suna zaune ne atashar kaduna, kuma sunyi hatsari sun mutu gaba d'aya
   Shine nazo in gaya maka maka dan kar ka cigaba da neman su
   Tunda antabbatar da duk yaran da suka d'auka yankasu akeyi

    Wata juwace tad'auki Anas yayi baya luuuuuuuuu..................... ✍🏻✍🏻✍🏻



Keep waiting my fan's🤔🤔🤗🤗🤗
Hallmarth 💕💖💕
[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔*
_Story and written by_

*SADIYA •A• UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}

🅿---5⃣3⃣&5⃣4⃣



...............luuuu yay yafad'i 'kasa sumamme mutanen gurin da kuma d'an sandan ne suka taimaka aka saka masa ruwa yafarfad'o bayan sun yayyafa masa



   Sosai Anas yaji wannan batun danji yay kamar yagama samun farin ciki dajin dad'i kenan arayuwarsa taduniya dan yana matu'kar san Hapsatu amman kuma yakasa fad'a mata sbd gudun karya ja mata masifa

    Sai yau yake daya sanin dabai auretaba yabar garin da itaba, dayanzu tana tare dashi


Hakadai akai ta ban baki anata yi musu jaje, su Mm Balaraba kuwa kamar mutuniyar kirki harda kukan munafurci itada Fauziyya

    Alhaji kuwa jiyay kamar ancire masa wata laka daga jikinsa, duk jiyay yarasa duk wata nutsuwar sa da kwanciyar hankalin sa 


   Balaraba kam da Fauziyya ji sukai wannan labarin yafimusu ko wane albishir dad'i dan ji suke kamar yau sallah, sai juyi suke suna shewa abunsu, kamar ba gobe




Wasa² saida aka had'awa kawu Anas da addu'oin samun nutsuwa sannan yadawo hayyacinsa

    Sosai yarame yayi ba'ki gaba d'aya yacanja kamar ba kawu Anas d'an gayu da kwalliyaba



Abu kamar wasa bikin Fauziyya sai 'kara sowa yake inda Jazuli babu alamar lpy atare dashi sam kullum haukar tasa cigaba take, daga ''karshema gidan mahaukata aka kaishi, dan zaifi samun kulawa acan



Tun saura sati biyu aka kai Fauziyya gidan gyaran jiki anata gwalli, duk,  'kauyen su babu wadda ta auri mai kud'i kamar ta intabiyo hanya kokai waye saika caya ta wuce sannan kawuce



" ya"yan gidan Alhaji Hamisu d'an kakah hajja sune suka dawo 'kawayen ta, dan sune suke da kud'i suma a 'kauyen




Yau ce takama ranar d'aurin aure kamar yadda yakama alissafi
   Ansha faty anci DJ angaji sosai tun jiya yau kuma za'ad'aura aurene da kuma kai amarya


   Ahanyar su ta zuwa d'aurin aure su sani 'kannen Fauziyya  suka had'u da wan mijinta b......................


**************

A6angaren su Hapsatu kuwa saida ta kammala aikin komai sannan tasallami kowa sannan tazauna akan tabarma dan jiran "Baba mlm idi"

      Yajuma sannan yafuto wajen gaf da magriba dan haka saida yaje sallar Isha'i sannan takai masa wani abuncin da ruwa yaci yasha


    Sannan tai musu shimfid'a atsakar gida dayake akwai wutar nefa dan haka suka zama idan yaranta suna nan


Saida yakammala, sannan ta bashi gurin zama yazauna, suka 'kara gaisawa sannan, yace mata Rabi'atu maiya kawoki nan garin ne keda kike aure agarin kano,  can 'kauyen rano


   Baba mlm ba rabi'tu bace  "yar tace Hapsatu wadda suke kawo muku kunu ko fura idan Ummerh ta dama


A'a dai A'a dai A'a dai, karki ce mun Hapsatu ce, itace baba

    Kuka yasaka yana tafa hannuwa yace kuma kinyi kama da ita sak dan wlh baku da maraba, keda RABI'ATU


Allah kenan mai yadda yaso da bawan sa
     Ina ita innar taki tak?
Aurene yakawoki nan?
Ina sirikin namu yake?
Tunda nazo bangan saba


    Sunkuyar da kanta tai 'kasa taji wata kwallah tacika mata idan ta, tace baba, ai Ummerh na ta dad'e da mutuwa


    Mekikace Hapsatu ban fahimce kiba , Rabi'atu d'ince tarasu, kuka ya'kara sakawa harda shar6ar majina



     Kayi ha'kuri baba haka Allah yaso, Tooo yaushe akai aurenki Hapsatu
    Baba ba aure nayi ba, zaro ido yayi yace ba aure kikai ba, mekikeyi agidan nan zaman kanki kike yi Hapsatu

   Ey, baba
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Hapsatu inashi Alhajin yake da Kakah hajja menene amfanin su dazasu barki kina zaman kanki bazasu ri'ke kiba


    Kuka tasaka tana yinsa da'karfin ta kanaji kasan tun daga 'kar'kashin zuciyarta yake zuwa, abdad'e ana danneshi, na zallar ba'kin ciki ne da 6acin rai, duk wanda yake sauraron sautin kukan ta saiyajishi acikin jikinsa sbd rad'ad'i dazafin da sautin ke futarwa


   Baba malam idii ne yace Hapsatu daina kuka kinji gaya mun meyake faruwa inji



    Babah dan Allah suwaye dangina kuma a ina suke inasan zuwa cikin su nima inji dad'in da mutane sukeji idan suna tare da 'yan uwansu


      Zan fad'a miki Hapsatu amman dafari dai kidaina kukan kifad'amun meyake damun ki inji
     Nima sai in baki labarin 'yan uwanki yanzunnan


    Rage sautin kukan tai tad'ago idanunta dasukai jaaa jaajirrr tace baba, nidai tunda nataso naganni tare da ummerh ta acikin Wannan gidan kuma ban waye dakuba sosai lokaci d'aya muka rasa BAFFA tun banda wayau daga baya kuma muka rasaka, kullum natambayi  Ummerh sai tace mun inyi hakuri zataban labarin inda kukaje, kuma BAFFANA yana kawo mana sa'ko dan yana samun labarin mu daga baya kuma yadaina kawo mana komai


     Tiryan tiryan Hapsatu tabashi labarin komai daya faru arayuwarsu bata 6oye masa komai ba har wahalar dasuka sha da kuma shekarun da suka d'auka acikin garin kaduna



    Sosai Baba mlm idiii yatausaya musu wani gurin ma saida yay kuka yace meyasa ya'auro wad'an nan ahalin, wanda ake musu take kala²,   "kwar kwasa fidda na kogo" ai indai sukai shiga saisun fitar dana ciki, in kuma babu to baka isa kashigoba


    Baba Kakah Hajja ce tasashi yay auren ai, kakah Hajja ita awa kuma
    Baba ai ita kakar muce
Inji wa yace miki
Inji Abban mu


  Hmmm 🤔 murmushi yay yace a'a wannan batun ba haka yake ba Hapsatu


   Yaya yake Baba ban gane ba sam
Zan baki labari komai yanzu Hapsatu


    gyara zaman ta tai ta maida nutsuwarta kansa dan tanasan taji labarin Ahalinta itama


      ALHAJI IBRAHIM MAI SHADDAH
shine kakan Ummerh ki
   An haifesane agarin kano acikin unguwar yakasai alayin 'kofar mata anan ne gidan su yake


  Susu biyu iyayen su suka haifa inda suka basu ilimi da tarbiya dai² misali kakan Ummerh ki yayi makarantar primary dashi da 'kanin sa musa wanda daga nan suka tsaya sai suka kama kasuwanci sosai



     Sana'ar shadda shine kasuwancin gidan kakan nin ummerh ki susu biyu suka taso Ibrahim da kuma Musa suna san junan su sosai dan idan babu d'aya to d'aya bazai iya koda zaman kasuwa bane


    Sun ginu akan sana'ar saida shadda sosai sannan Allah yay wa iyayen su rasuwa wanda hatsarin mota yakashesu ahanyarsu tadawowa daga YAMAI sunkaiwa danginsu ziyara


    Sosai mutuwar iyayen su ta gigitasu wanda kakan JAURO mahaifina kenan  yaso yad'aukesu amman sukace abarsu suci gaba da harkar kasuwancin su anan kawai


   Babu yadda suka iya dole suka barsu inda kakan JAURO yadawo kano da zama badan yana soba
   Saidan yakula da yaran d'an uwansa tunda iyayensu d'aya

   Kakan Ummerh ki shiya sha nono yabawa kakan JAURO


Yataho da JAURO lokacin shima baifi sa'an suba  inda suka cigaba da kasuwanci tare sosai suke girmama junan su wanda daga 'karshema kakan JAURO yayi aure ya auri HAJIYA TABAWA


    HAJIYA TABAWA macece mai hkrn gaske wadda bata da saka ido ko kuma ba'kin ciki akan abun wani


    Kuma duk iya abunda zaka mata bazata ta6a nuna kayi mata laifiba tsakaninta dakai addu'a kawai da kuma nasiha akan ka gyara
   Haka ta kwashi shekaru amman bata ta6a haihuwa ba har su IBRAHIM  da MUSA da JAURO sukai aure


   Basu dad'e dayin aure ba tasamu ciki inda wannan ciki shine yazama ajalinta dan tunda tasamu cikin nan kullum cikin ciwo take yau da lpy gobe babu lpy


   Randa ta haihu kuwa ranar tarasu inda tahaifi d'anta namiji aka saka masa suna NAZIRU



  Sosai su IBRAHIM suke kula da yaron nan wanda kakan Jauro badan yasoba ya'kara aure inda ya auri Kaka Hajjah


   Hjy mashid'a kenan iyayenta 'yan kano tu jiddane shiyasa idanunta suke abud'e zam²


       Bata ganin kowa da arzi'ki shigowarta wannan gida yafara haddasa bala'i wanda kakan Jauro yasha yi mata fad'a da kuma takara amman bata gani


    Matar Ibrahim da musa sun haihu rana d'aya inda matar Ibrahim tahaifi namiji, matar musa kuma ta haifi mace



   Namijin aka saka masa suna Hashim, macen kuma fauxiya wadda akeceda Mamie, Hashim kuma ake ce masa Baffan
    

      Matar jauro bata samu cikiba saida aka yaye yaran Ibrahim da musa


    Sannan tasamu ciki sunyi murna sosai inda tacigaba da renon cikin ta harta haihu d'anta namiji aka saka masa idiris



   Bayan ta haihune babu dad'ewa Allah yay wa kakan Jauro rasuwa
   Inda wannan rasuwa ta girgiza wannan family sosai

    Sunyi kukan rashin baban su sosai da kuna kewarsa


   Kakan Jauro bai dad'e da rasuwaba kaka Hajjah tace tanada ciki wanda wannan cikin nata ma ba'asan dashiba yakai kusan wata 4



    Alokacin ne kuma IBRAHIN mai shadda shida 'yan uwan sa suka gida makeken ESTATE acikin garin RANO


    Wanda gidane nagani nafad'a acan suka tare suda matansu da iyalinsu baki d'aya inda suka baje gidan su nagado suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login