Showing 24001 words to 27000 words out of 39414 words
wajan isha'i su Iman su basu dawoba, Suna dakinsu ya kalli barrister yagashi Ko ajikinsa ma aiki
yake a computer, bai dacewa yarinyar Nan tadawo Ko batada dawoba
Ahankali yatashi yadubi Imran din yace Ina Zuwa Bros
Kawai Daga masa Kai yayi batare daya kalleshi ba
Aliyu na fita, yaje bakin gate Daga gefe inda hankalin mutane bazai kawo kansa ba yanemi waje yazauna
Be Dade da zamaba suka shigo
Itace tafara futowa Daga motar, sai Farhan, kwalin fizza ne ahannunsa yayi ciki, Itama ta biyoshi Abaya
tana chtting da yusy tana Bata labarin Yanda abubuwa suke wakana
Bamata Kallan gabanta kanta aqasa Taji anfizge wayar Anja hannunta, ihu zatayi yayi saurin saka tafin
hannunsa Yarufe mata baki
Tsoro ne yakamata lokaci daya, idanunta suka furfuto waje, kallansa take babu damar magana saboda
yayi Mata mugun ruqo
Inda yazauna dazu nan yakoma yatsaya sannan yacire hannunsa abakinta yace "dama jira nake kidawo,
Wai in tambayeki, mekike taqama dashi ne? Mekikeji dashi dakikemin barazana da rayuwata?
Kallansa take, Yanda Yarufe ido yana yi mata fada, yayi Mata kwarjini, Amma haka ta dake, murya na
rawa alamar kuka tace," Kaine kakemin barazana da rayuwata, bantaba kwanciya jinya ba sai akanka,
kanaso kakasheni kanamin maganar inama barazana da rayuwa..... Dakata Dan Allah, Aliyu yayi saurin
katseta
Karki sake cemin akaina kin kwanta jinya, aidama Sansa kike shiyasa kike biyeshi Kuna Zuwa yawon
banza, sannan kizo kina kukan munafurci kice kina sona
Wannan Karon Kam Iman Bata Iya tsaida hawayen idonta ba, cikin kuka tace edin Ina sonsa, koma
menene ai Kaine kajawo, jinake Cewa kayi kafi sonsa akaina, tonima nasoshi, Kuma wallahi yanzu nafara
nuna masa so
Gefen da Zuciyar sa take yadafe, yace saboda Ke, saboda soyaiyar danake Miki nakamu da hawan jini,
still kina fadamin kina sonsa,
Idanunsa jajir, cikin Daga murya yace waike wacce irin marar Imani cene? Agabana kina Cewa Zaki Bawa
wani qato tea, Agabana kindau ice cream kin bashi yasha, wato inmutu konai rai bakida asara.... Ke..
Ke... Nunata yake da hannu Amma yakasa qarasa maganar da zaiyi dalilin kukan dayazo masa
Tashin hankali ne qarara ya baiyyana afuskarta, namiji babba baitaba kuka agabanta ba inde ba mutuwa
ba, sai yau
Ita kanta hawayen datake yaqi tsayawa, cikin kuka tace nakiraka awaya nayima magana akansa Jace
zansoka inqishi, Wai Yaya kukeso nayi ne? Hauka kukesan sakani?
Dago kansa yayi yana kallanta
Adede wannan lokacin Alhaji daya dawo Daga sallar ishsha'i yagansu
Da mamaki afuskarsa yace wannan yaran me yake faruwa suka tsaya anan? Sake kallansu yayi to ai
wannan Fatima ce da Aliyu Bama Imran ba
Tsayawa yayi yaqare musu kallo, nan take yagane Cewa kuka suke gaba dayansu biyun
Su kuwa masifa ta rufe musu ido basusan dashi Bama
(tofa team din Aliyu yau ruwa yaqarewa Dan kada 🤔🤔kawai kuyi tagumi Dan Baku da ta Cewa)
Sharhi please 🙏🏻
Mrs Usman Ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
17
Lalle akwai matsala, dole yaran nan akwai abinda yake faruwa atsakaninsu, lalle yakamata Zuwa wannan
lokacin yasaka ido Akan iyalansa, Kuma yazama dole ya bincika yaji menene yake faruwa
Alhaji nagama maganar zucinsa yajuyo yasake kallansu gamida girgiza Kai yayi cikin gidan
Yana shiga falon nasu yaga babu kowa, sai Farhan dayasa fizza agaba yanaci
Alhaji ya kalleshi yace turomin Hajiya, sannan yayi cikin dakinsa, dasauri Farhan yayi dakin Hajiya domin
bin umarnin Alhaji
*** *** ***
Kallanta yake da idanunsa jajir, yace bazamu saki hauka ba, Amma aike kina neman sakamu hauka a
kanki, a dalilin soyaiyar ki, kinsa inajin kishin dan'uwana
Cikin kuka tace ni ban zama silar da zaisa kuyi kishi da junnanku akainaba, bazaku nunamin Kuna son
junnanku ba, saikun Rabu Dani gaba dayanku
OK haka kikace?
Still cikin kukan tace eh haka nace, nace kurabu Dani gaba dayanku
Yana huci yace za'a Rabu dake kuwa
Itama cikin bacin rai tace fine, tayi gaba, Shima rai babu dadi yayi hanyar part dinsu
Yana Zuwa part dinsu, ya janyo qaramar trolly yafara zuba kayansa aciki, aransa yanata masifa, zan
nunawa yarinyar Nan qarshan zuciya, bade tace murabu da itaba, zantafi Saudia inyi Addu'ah Allah
yayayemin wannan masifar
Saida yagama shirya komai, sannan yaje wajan barrister yace Bros gobe zan wuce Abuja, akwai aikin
danake so nayi acan
Kallansa yayi jiki asanyaye yace Amma Bros idan likitanka yazofa, kana ganin Alhaji zai barka katafi
kuwa?
Kafadarsa yadafa yace karka damu, bazan wuce 1week ba zan dawo insha Allah, idan nayi masa bayani
insha Allah zai barni
Amma Bros tafiya haka Rana daya babu shiri,
Aliyu yace yanzu suka kirani ne, akwai sababbin sojojin da aka dauka ake basu horo, inaso Nakai musu
ziyara
Jin haka yasa barrister yace to shikkenan Allah yakaimu
Dahaka haka Aliyu yasamu ya lallaba dan'uwan nasa
*** *** ***
Tana shigowa falon, Farhan yaganta ido jajir alamar Tasha kuka
Da mamaki afuskarsa yace sister lafiya kuwa?
Tace abune yafadamin cikin idona, shiyasa
Cikin alhini yace sorry
Kawai Daga Masa Kai tayi ta wuce cikin dakinta, tana Zuwa wanka tayi, tayi sallah, sannan ta kwanta,
hawaye yana tsiyaya ta gefen idonta, Zuciyar ta banda quna babu abinda take, banda ma renin wayo
Kace in Rabu dakai, Kace zan soka inqi dan'uwanka, sannan kazo kanamin fada Akan nasoshi, koma
menene ai banda laifi anan,Tunda Kaine kabani dama naci gaba da kulashi, shi na tambayeshi wayafiso
tsakaninmu yace badan yana sonaba zai Iya sadaukar Maka Dani, Kai kacemin kana sonsa fiye Dani
Sai garani kuke saikace wata qwallo
Juyi tayi Akan gadon afili tace garama ku Rabu Dani gaba dayanku, Nima nahuta, Bata gama tunanin ba
zazzafan zazzabi yarufeta
*** *** ***
Yana Kwance Akan gadonsa Hajiya tashigo dakin tareda sallama
Akusa dashi ta zauna tace Alhaji sannu da Zuwa, ai Bansan gashigo ba, sai yanzu Farhan yake cemin kana
nemana
Tashi yayi zaune yace Hajiya dama nakiraki ne Akan maganar yaran nan
Wanne Yara Alhaji?
Ina nufin babu abinda kika fuskanta wanda yake faruwa tsakanin Aliyu da Imran da Fatima?
"a a Alhaji, gaskiya ban fahinci komai ba, shi Aliyu kasan baya shiga Harkar Yara bare nace Ko tayi masa
wani Abu ne
Shikuma Imran kaga ni Tunda nake dashi banga abinda yataba shiga tsakaninsu ba, Amma Alhaji meyasa
kayimin wannan tambayar?
Girgiza kansa yayi yace "a a babu komai Hajiya, kawai de Ina tsoron ace zamansu da Fatima waje daya
yasa kusanci a tsakanin su Har suji wani Abu aransu, kinsan zuciya hajiya
Daria tayi tace Alhaji Wai soyaiya?
Daga mata Kai yayi alamar eh
Haba Alhaji, aisu ba qananun Yara bane da zasuso Abu daya, gaskiya Bana tunanin haka Alhaji
Ajiyar zuciya yasauke, badan zuciyarsa ta gamsu da bayanin nataba, yace to shikkenan, Zaki Iya tafiya,
idan Zaki dawo ki shigomin da coffee
Tace to Alhaji, sannan tafice
Bayanta yabi da kallo, aransa yace lalle su Hajiya ma basusan abinda yake faruwa ba, shi Dan yau kawai
kazuba masa ido kaganshi kawai, Amma karma kafara shaida akansa, dole ne yatashi tsaye Akan sanin
dalilin kukan su, yasan Aliyu da juriya Akan Abu, zai wahala kaga kukansa, dole akwai abinda yake faruwa
*** *** ***
Washe gari Aliyu baisha wahala ba wajan tsara Alhaji da mamy, babu Bata lokaci suka yarda yatafi Abuja
Yana Zuwa Abuja yasa akayi Masa duk abinda yakamata da yamma ya wuce Saudia
Iman kuwa tana daki, kasancewar tana Fama da zazzabi
Babu wanda tafadawa, haka tawuni a daki, sai wajan azahar ta futo
Harabar gidan ta leqa ta window bataga soja Ko dayaba
Abakin zeey auta takejin labarin Cewa ya Aliyu yatafi Abuja
Tabe baki tayi, cikin ranta tace kafi ruwa gudu
Al'amarin Yan Saudia kuwa shida yaje domin yayi Addu'ah Allah yayaye masa son wannan marar kunyar,
sai gashi ya bige da Addu'ah Akan Allah yakawo musu mafita
Yagama komai Amma haka yaqi dawowa gida, yayi zamansa acan, Ko mamy batasan Cewa baya qasar
ba, Tunda da Sim card dinsa yake amfani
Wasa wasa tun Iman tana sharewa harde tazo tana zancen zuci Akan yaushe wannan mutumin zai dawo,
tafiya kusan 1week Shiru babu labarinsa
*** *** ***
Suna zaune a falo Dukansu, zainab tana warware mata kalbar dake kanta
Hajiya tace yanzu Iman banda lalaci irin naki yaushe Zaki bawa auta kanki ta nayi Miki tsifa,? Ta kalli
zainab tace auta bakida homework ne?
Allah Ina dashi Hajiya, Saida nace ba zanyi ba tace sainayi kotamin duka
Dasauri Hajiya tace tashi tashi, kiyi ai kinki, tamaida kallanta ga Iman tace ki qarasa da kanki, kizo Kuma
girki yana jiranki, Dan yau kece zakiyi bamasu aiki ba
Iman Kamar zatai kuka tafara tsefe kalbarta da kanta, mamy dake gefe tayi Daria tace haba Hajiya, duk
ita kadai, munada yawa a gidan fa
Hajiya tace ai Hajiya fati idan bayi takeba Saida sangarce, kina ganifa babu abinda take a gidan nan sai de
in anzo cin abinci tazubawa kowa, in Kinga Iman tayi girki to tabbatar baqi Zamu yi, ai Gara tafara tun
yanzu, Tunda gidan Aure zata tafi
Cikin shagwaba tace Allah Hajiya ba inda zani, Hajiya tace aikwa saikin tafi, bazansaku agaba ina kallo ba,
Daga Ke Har Imran din nayafe
Mamy tayi Murmushi tace Fatima taso na tsefe Miki kinji, babu musu Iman tatafi
Mamy tafara warware mata kalbar gwanin sha'awa
Hajiya tace andaiji kunya wallahi
Suna zaune Imran yashigo yace Hajiya zanje court
To Allah yadawo dakai lafiya,
Yadubi iman yayi qasa da murya yace akwai bikin abokina da akeyi, anjima Zamu shopping musiyo kayan
dazamu saka ranar dinner
Ahankali tace to Yaya
Mamy nagama mata tsifar, tashige kitchen tahada abinci me rai da lafiya, jallof din kuskus dataji Nama d
kayan lambu, sai dambun shinkafa dayaji su carrots, sai zobo tahada dashi
Yamma nayi suka shirya suka tafi wajan shopping, Kaya yasiya musu latest masu kyau, shi suit yasiya ja
me shegen kyau, sai rigar cikin fara
Ita Kuma yasiya mata wata doguwar Riga ja, Mai sirkin fari ajiki, da mayafin rigar nayin rolling Shima ja
Kowa yaga kayan yasan ankone akayi, sosai yakashe mata kudi, suka taho
Karfe biyar da rabi suka dawo gida, Suna shiga gidan sukayi tozali da sojoji a harabar gidan
Gabantane yafadi, wannan mutumin yadawo Kenan, ai kuwa Suna qarasawa cikin falon taganshi a zaune
akafet yanacin abinci, girkin datayi Kamar danshi, Yanda yazauna yanaci Kamar ba gobe hakanne zaisa
kagane yadade rabon dayaci irinshi
Hannu Imran yabashi suka tafa, ita kuwa Ko kallansa batayi ba tanufi wajan Hajiya ta nuna Mata kayan
dasuka siyo
Hajiya tana hankalce dasu Tunda Alhaji yayi Mata magana akansu
Tana lura da ita Ko gaida Aliyu batayi ba, anan tasan Cewa lalle akwai abinda yake wakana
Zama Imran yayi awajan sukaci gaba dacin abincin, Suna gamawa Hajiya tace Iman tashi ki kwashe
abubuwan da yayanki yaci abinci kikai kitchen
Tsam tatashi tanufi wajan nasu, tana Zuwa fuska atamke tafara hada kwanukan sai kwala flet din take da
junansu daniyya
Fuska tamke yace Kinga barshi, Bari Nakai dakaina
Imran yace haba Bros yaza'ai Kaje kitchen, kabarta taje wannan ai aikin mutane
Batace musu komai ba, tagama qwala flet din tadauka fuuuu tayi kitchen
Duk Akan idon Hajiya
Dawowa tayi ta zauna a falon, wayarta tadauki qara, tana dauka tace yusy yakike? Bayan sungaisa yusra
tace mata ansa bikin wata qawarsu, harma anfidda anko, taduba whatspp zataga pictures din ankon
tatura mata
Kai wallahi yusy naji dadi, namata murna, Allah yabasu Zaman lafiya, kice dole mushiga kasuwa muyi
siyaiyar kayan biki
Yusy tace to amara
Bawani amara, kede Bari saima Billy tashigo wani abun
Dahaka sukai sallama, ta kalli hajiya tace Hajiya Wai kinji za'ai bikin wata qawarmu, Dan Allah Hajiya kiyi
mana ankon nida Bilkisu kinji Hajiya
Ke qyaleni da wannan ankon naku, ku bikinku baya qarewa, da biki yatashi zaku Daga hankalinku, ni
wallahi kekika koyawa Bilkisu ma, nasan da bahaka takeba, anemi takalmi anemi jaka, anemi wacece
Iman tace Kai Hajiya, Dan Allah mude kiyi mana, tana fadar haka tadau jakar kayan dasuka zo dashi tayi
cikin daki
Mezai faru,? Tana shiga cikin daki ta kwanta agado danta huta Taji qaran shigowan text wayarta, tana
dubawa taga anyi mata transfer na kudi Har dubu Dari biyu , dasauri tatashi zaune tace Kai wannan
mistek akayi, wannan kudin ai saide wani, ni Iman inani Ina wannan kudin, qasan text din taduba anan
taga sunan wanda ya turo kudin Aliyu Sa'ad Bilal
Kai!!! Wannan Ina yasamu account number na? Innalillahi kawai dagajin zancen anko saiya turomin
kudi? Ina zan samu account number dinsa namaida masa abinsa?
Tana wannan tunanin Taji wani massage din yashigo, tana dubawa taga shine ya turo mata text "kuyi
amfani dashi wajan bikin,"
Cikin Jin Haushi tayi jifa da wayar Akan gado, gayen nan yagama Dani wallahi, komai nawa yasani Kamar
aljani, Ko waye yabashi number account Dina?(nikwa nace tambayeshi😏)
*** *** ***
Next day
Zaune take agaban mirror tana shiryawa,Karfe takwas da rabi na dare, kwalliya take ta kece raini Tunda
Yaya Imran yace mata za'aje dinner dinnan take tunanin Yanda zatai wanka na kece raini Dan bakasan
wazaka hadu dashiba
Wayarta ce tayi qara, tana dubawa taga shine me Kiran, tana dagawa yace muradina nagama shiryawa
kifuto mu wuce, Ina compound
Janbaki ta zizara alips dinta sannan tace to Yaya gani nan, tareda kashe wayar
Tana futowa Daga dakin ta, taganshi cikin qananun Kaya yana waya zai shiga dakin mamy, cak yaqame
awajan da waya ahannunsa, yazuba mata ido yana kallanta, tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qera
wannan halitta, Ahankali yace Mustapha kajirani gani nan Zuwa, insha Allah komin dare zanzo, yana
fadar haka yakashe wayar
Yatunkareta, jatafarayi da baya da baya, Allah Yarufa asiri babu kowa awajan, Kallan tuhuma take binsa
dashi Ahankali tace lafiya?
Kallanta yasakeyi Daga Sama Har qasa, yace "Ina Zaki fita ahaka? Wato kinyi wanka zakije ki nunawa
maza awaje Ko?
Cikin bacin rai tace bangane in nunawa mazaba, nida muradina zamu fita, Dan Allah matsa kaban hanya
Babu inda zan matsa, Kuma kema babu inda zakije
Malam kaifa ba mijina bane dazaka hanani shigar danayi niyya, Kuma bakada damar dazaka hanani fita
Tana fadar haka ta matsa Daga inda yatare mata hanya zata wuce
Dasauri yariqo hannunta, yasake matsowa dab da ita, Har tanajin hucin numfashinsa, Ahankali Kuma
cikin rada yace please Fatima, Dan Allah kirufamin asiri karki fita ahaka, naroqeki karki fita ahaka wasu
mazan su kalleki, Fatima zuciya ta zafi takemin, inasonki Fatima, Dan Allah kisoni Ko Rabin son danake
mikine kohakan zaisa kiji tausayi nah
Wallahi kika fita ahaka kikaje wasu suka kalleki na tabbatar sainayi zazzabi
Bata kulashiba tafara kokarin qwace hannunta, murya na rawa tace karabu dani, kaida baka sona, baka
kaunata, kafison dan'uwanka akaina
Sake riqe mata hannun yayi yace kiyi hakuri mana, naji nayi laifi kiyafemin
Hawaye ne masu dumi suka zubo mata, ita kanta tarasa na menene, na farin ciki Ko akasin haka
Ganin hawaye a idonta yasa hankalinsa tashi, Ahankali yasa hannunsa ya share mata hawayen, fuskarsa
dab da Tata yace kin hakura? Ahankali ta Daga masa kanta alamar eh tahakura
Baiyi wata wataba yahade bakinsu waje daya,cikin nutsuwa yake kissing Dan qaramin lips dinta
Zaro ido Iman tayi, domin kuwa batayi tunanin abinda zaiyi mata Kenan ba
Agogon hannunsa yaduba yaga lokaci yaja, Har yanzu Bata futoba, Dan haka yabiyo bayanta domin yaga
meya tsada ta
Yana Zuwa hanyar dakinta yagansu awannan halin, Gabansa ne yayi muguwar faduwa, nan take yaji jiri
yana neman dibarsa
(tab da alama gidan Alhaji zai kama da wuta, yasin na fece )
Sharhi please 🙏🏻
Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
18
Idanunsa ne suka ciko da qwallah, daqyar ya motsa Fatar bakinsa Ahankali yafurta kalmar Bros....
Babu Bata lokaci hawaye yasakko a idanunsa, dan'uwansa dayake so fiye da komai, shine yake kissing
matar dayake mutuqar so ya aura
Yana kallansu awannan halin ya juya yashige dakin Hajiya, domin kuwa ayanda yakejin qafafunsa Suna
rawa, bayajin zasu Iya daukarsa
Yana shiga dakin yacire suit din jikinsa yayi jifa da ita, Zuwa wannan lokacin kuka yake wiwi
Duk abinda yadauka adakin Hajiya jifa yake dashi, gaba daya ya haukata mata daki, kuka yake sosai
banda wani irin daci da yakeji a maqogwaronsa
Dakarfi yace Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, bros... Why bros... Menayima dazaka min haka bros....
Awajan ya tsugunna yahada Kai da gwiwa yana sheshshekar kuka
*** *** ***
Ganin bashida niyyar daina abinda yake ne yasa Ahankali tazare bakinta Daga cikin nasa
Wai dama haka yake? Gaba daya yayi Mata kwarjini, takasa hada ido dashi, Koda yake ai dama yataba
fada mata Cewa shi idan yanason Abu to zai nunama ne abaiyane
Idanu yazuba mata yanajin wani irin yanayi atare dashi, wannan ne Karo nafarko daya taba hada jikinsa
Dana wata yarinya harma yayi wani Abu waishi kiss
Ahankali ta Bude baki tace Naga kudi nagode, Amma Kuma ai sunyi yawa... Bata qarasa maganar datake
yi ba ya katseta
Baiyi yawaba, kisai muku ankon dashi, idan Bai isaba kawai ki sanar Dani
Kanta aqasa tace mungode
Babu godia tsakaninmu, kidauka Cewa wannan shine gift na farko Dana taba Bawa wata mace
arayuwata, da sunan Ina sonta
Zanje wajan Mustapha abokina yashigo kano, akwai aikin danakeso muyi dashi, may be saikinyi bacci zan
dawo
To saika dawo
OK kikulamin da kanki, yana fadar haka yajuya ya fita harabar gidan, yana Zuwa yashiga Mota shida
sojoji mutum biyu suka fita
Itama Iman daki Takoma, tana shiga tafada Kan gado tasaki Murmushi, lips dinta ta shafa da hannunta,
ashe haka akeji?
Dasauri tatashi data tuna da barrister yana jiranta, wani janbakin tasake shafawa sannan ta futo harabar
gidan, gani tayi bayanan Bayan Kuma yace mata yana wajan yana jiranta
Wayarta ta dauko cikin fos din hannunta, takirashi Amma Bai dagaba, tasake Kira still Bai dagaba, Bai fiya
shiga dakin Hajiya ba Saida dalili, danhaka Bata kawo Cewa yana canba
Part dinsu taje, taduba ko'ina baya nan, haka tagama dubanta Bata ganshi ba, harda qwanqwasa toilet
Ko yana ciki
Afili tace to Yaya lafiya?
Kafada ta Daga sannan tafice Daga part din nasu, cikin gidan Takoma, ganin babu kowa yau a falon yasa
ta wuce dakinta ta zauna Agefen gado, afili tace may be Yaya yafita ne, Bari najirashi Ko Zuwa anjima zai
dawo
, Amma Kuma Saida nagama shiryawa zai fita? Girgiza kanta tayi tare da kwanciya
*** *** ***
Next day
Haka Iman tagama jiran Imran Har bacci ya dauketa, Amma babu Imran babu alamar kiransa
Da asuba ma haka taita gwada kiransa Amma yaqi dauka, hankalinta duk yatashi, haka taita zarya a falo
Ko Hajiya zata futo Daga dakin Alhaji tasanar da ita halin da ake ciki, Amma Shiru Hajiyanma yau Bata
futo da wuri ba
Hakade Takoma dakinta Amma duk hankalinta atashe
Al'amarin Imran kuwa yana gama kuka anan zazzabi Mai mutuqar zafi yarufeshi, Kuma Har Zuwa lokacin
kansa yana kan gwiwarsa yaqi dago da kansa, Shiru babu magana, daya rufe idonsa su