Showing 12001 words to 15000 words out of 39414 words

Chapter 5 - WAZAN ZABA by Amnah El Yaqoub

14 May 2026

110

Amma Baisan lokacin daya tashi zaune ba, gabansa ne yake wata irin faduwa,
hannunsa ma kansa rawa yake Kamar bazai Iya riqe wayar ba



Komawa yayi yakirata, Zuciyar ta daya tadaga tace kaganshi?



"naganshi, Amma kin tabbatar wannan gayen dakika turomin pic dinsa shine Saurayinki?
Babu tunanin komai tace "yes shine MURADINA"



Idanunsa ne suka kada sukai jajir lokaci daya, Bai nuna mata komai ba yace mata to shikkenan zan Dan
kwanta sai anjima



Wayar ta takallah afili tace to lafiya irin wannan sallamar? Kafada ta Daga taci gaba da sabgar gabanta



Wayar hannunsa ya wullar gefe daya, kadan yarage wayar ta Fado Daga Kan gadon dayake Kai

Lallausar sumar kansa ya hargitsa, Nan take yafara maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihirraji'un



Adede wannan lokacin mamy tashigo dakin nasa, ganin yau tajishi Shiru Bai shigo wajantaba

Hankalinta atashe taqarasa wajansa tace baby me yake damunka?



Be Iya Bata amsaba, saide wayarsa daya nuna mata



Wayar ta dauka taduba, photon data gani a screen din wayar Bai tsoratata ba, tasake dubansa tace
menene Wai



Kansa ya dafe da hannunsa duka biyu, idanunsa jajir yace Mamy....Shine....shine saurayin Iman



Da tsananin mamaki tace Iman Kuma?

Waye yafada ma Hakan?



Hawaye ne suka cika idanunsa, yace Mamy yanzu take fadamin Imran saurayinta ne
Yana gama fada mata hawaye suka sauko a idanunsa



Sai yau Mamy ta tabbatar dacewa ba qaramin so Haidar yake yiwa yarinyar nanba, kuka! Yau Haidar
dinta ne da kuka Akan mace



Ajiyar zuciya tasauke, Amma abin yabata mamaki, gudun kada yagane halin datake ciki, saita dake tace
ALIYU



dausari yadago manyan idanunsa ya kalleta, yau ba baby, ba Haidar, Kai tsaye Aliyu



Be Iya Bata amsaba, saide kallanta dayake



Tace Aliyu amatsayina na mahaifiyarka, Ina baka umarnin karabu da yarinyar Nan "



(tofa wata sabuwa, Nima nace Ko meyasa? 😏😏)



Sharhi

Sharhi

Sharhi please



Mrs Usman Ce WAZAN
✍🏻 ZABA?πŸ’–



Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem
10



Saida ya goge hawayen idonsa sannan yace but mamy...



Cikin sauri ta dakatar dashi, "dakata Aliyu, sokake nabaka goyon baya Akan Kaci gaba da neman yarinyar
da Imran yake so? Kafi kowa sanin Yanda nakeso kayi Aure, Amma Hakan bazaisa na amince kaso abinda
Imran yake soba, kayi Hakuri, Allah ya musanya ma da mafi alkhairi



Cikin dakiya yace "to shikkenan mamy,"



"yauwa Allah yayi Maka albarka "Tana gama fadar haka tatashi tabar dakin



Shima miqewa yayi Ahankali yashige toilet



*** *** ***



Computer ce agabansa yana aikin wasu takardu, sau biyu yanayin mistek awaje daban daban



Tsaki yasaki yature computer Daga gabansa, meyasa komai zaiyi saiya tunata? Dole ne yabi umarnin
mahaifiyarsa kodan yagama da Dunia lafiya, yayi kokarin Raba kansa da tunaninta Amma yakasa jurewa



Idan ya kwanta bacci yayi mafarkinta, ido Bude yayita aikin tunaninta



Yarasa Yaya zaiyi da ransa, saboda ya nisanta kansa agareta yasa yau kusan 1week Kenan Bai sake
neman ta ba, Amma abin yaqi dadi
Yana wannan tunanin musty yashigo gidan, afalo yasameshi, Bayan sun gaisa yace banga su mamy ba
kobasa Nan ne?

Ahankali Kamar wani marar lafiya yace "sun fita sunje shopping"



Computer yaturawa musty, ka qarasa wannan aikin, bazan iyaba



Da mamaki Mustapha ya kalleshi yace meyasa? Meyake damunkane?



Batare daya kalleshi ba yace "Fatima, girlfriend din Barrister Imran ce"



Arazane Mustapha ya dubeshi yace tayaya? Kasan me kake fada kuwa?



Kansa ya girgiza yace itace ta sanar Dani Hakan da kanta, nafadawa mamy komai tace tabani umarnin
narabu da ita



Jikin musty yayi sanyi

Kafin yayi magana Aliyu yace Bama wannan ne damuwar ba, Yanda na dauketa nasata araina shine
damuwar, yanzu haka nakasa Dena tunaninta, wannan aikin tun safe nake Abu daya, Amma nakasa
qarasawa sai mistek nake, Kuma tunaninta ne ya haifar min da Hakan



Ajiyar zuciya yasauke yace, kayi hakuri abokina, maganar mamy itace ta gaskiya, bazai iyu ba Hakan,
Allah yasa hakane yafi alkhairi, Amma kayi kokarin rage tunanin kada Hakan yataba lafiyarka



Insha Allah zan kiyaye musty



*** *** ***

Next day
Tun Daga wannan lokacin Aliyu yahana

Kansa neman Iman, duk da yanasan Hakan, wannan satin dayan dayayi Batare daya nemetaba jiyake
Kamar Akan qaya yake, yasha gwada kiranta Amma saiya katse, idan yatuna da umarnin mamy



Yanzu ma yana harabar gidan yana motsa jiki abinda yazame masa qa'ida duk safiya kokuma da yamma
sai yayi



Tunanin ta yake, wannan jaraba ta isheshi Dan haka ya yanke wa kansa hukuncin kiranta



Yana Kira cikin sauri ta Daga, atare sukai Ajiyar zuciya,

"yanmatana ya kike? "



Cikin shagwaba tace" Bayan ka manta Dani, Baka kirana, gaba daya kazubani a kondon sharah



Waneni na manta dake, ai Har abada bazan Iya mantawa dakeba



Taji dadin wannan maganar tasa

Tace "to meyasa Baka kirana?



Qanwata kawai ayyukane sukamin yawa, kinsan mu Bama zama, yau mune can gobe mune can



Qanwata? Ta maimaita kalmar acikin ranta, yau Aliyu ne yake kiranta da Qanwata? Tunanin ta baikai
wani wajenba tace to shikkenan Allah ya temaka



Toki kulamin da kanki, saimun sake magana latter,
Dahaka sukai sallama



*** *** ***



Yaya Iman, yakamata ki rage wannan tunanin fa, kema kinsan semester mu tayi Nisa, Gara muyi karatu,
Amma wannan tunanin babu inda zai kaiki



"Nima ai bani nadorawa kaina tunanin ba, kema kanki kinsan da inada damar careshi araina da tuninayi,
Amma yariga daya shiga Raina, dole Hakan zan barshi



"to Yaya Iman, kibarshi aranki, Tunda Kinga Zaki iyada iyayenmu ai shikkenan, Tunda haka kika zabawa
kanki "



Itama Iman cikin dakiya tace" haka nazaba, Kuma haka zanci gaba, sannan Kuma kitashi kibarmin wajan
Nan kafin naci Miki mutunci



"a a Yaya Iman, abin baikai nanba, Billy tasa hannu tadauki handout dinta, tadubi yar'uwar tace Toni nayi
library



"Daga Nan Bayan kin gama karatun ki hada harda takardar ki cinye "

Cewar Iman



Daria ce takesan qwacewa Billy Saida danne tareda ficewa Daga dakin



Tana ganin fitar Billy, tayi wulli da fillos din dake Kan gadon nata, wannan jaraba Dame tayi kama? Iman
meya kaiki kula wannan bawan Allah? Yanzu gashinan saboda Bai nemekiba kina Fama da tunaninsa



Haka taita magana ita kadai Kamar marar lafiya
Batasan Cewa Shima awajansa hakane ba, kawai yana daurewa ne domin yin biyaiya ga mamynsa



*** *** ***

Nifa abokina banga amfanin boye matan dakake ba, kawai kafuto fili kafada mata gaskiya, rashin baiyana
gaskiyarka agareta hakanma matsala zai janyo, Tunda kaika fadamin da kanka Cewa tafara qaunarka
yarinyar Nan



Hakane musty, wallahi idan zan fada mata maganar mamy agareta jinake nakasa, Har yanzu gani nake
Kamar zan Aure ta



Murmushi musty yayi, yace hakane Matar mutum kabarinsa, Amma inaso a duk lokacin daka tuna da ita,
toka tunada barrister Imran



Hakane musty insha Allah zan fada mata, muyi hakuri, Dan ba ita kadai ce zatayi hakuri ba, dukanmu ne



Daria Mustapha yayi sannan yace yauwa kokaifa,yanzu zanje inci gaba da aikin daka bani, yayi masa
sallama yatafi



Musty na tafiya, yadauko wayarsa yakirata, a lokacin tana zaune ita kadai adaki, computer ce agefenta
tana kallo



Yusy da Billy sun fita kasuwa domin yi musu cefane



Tana kallan Kiran nasa taqi dagawa Wai irin Jan ajinnan, afili tace wato sai yau kayi niyyar kira



Tana gama yin mitar Tata, tadaga Kiran nasa saura kadan Kiran ya katse
Abinda tafara Cewa shine, haba Sojana kasan Yanda nake jiran kiranka kuwa? Bakasan ahalin danake
cikiba adalilin rashin kiranka Ko?

Pls kadena, zuciya ta bazata Iya jurar hakanba



Banasan na dameka da kira saboda nasan Cewa kana wajan seminar, Amma badan hakaba saika gaji da
ganin kirana



Idanunsa ne sukai jajir, akwai matsala Kenan, inde Itama tanajin irin abinda yakeji, Bayan Kuma dole su
Rabu kodan barrister Imran



To yanzu shida yakirata domin yayi Mata zancen rabuwa, Yaya zaiyi yasanar mata?

Wata Zuciyar ce tace Aliyu kadaure, kadaure Aliyu

Haka cikin sanyin jiki yace da ita "kiyi hakuri, akwai dalilin dayasa Bana nemanki, Abaya nasa araina Cewa
zan Aure ki, Amma yanzu babu Hakan araina, nayi kokari nacire soyaiyarki Daga cikin zuciya ta, kema Ina
fatan Hakan Daga gareki



Iman, wannan gayen dakika nunamin amatsayin saurayinki, inasonsa fiye da kaina, Ina sonsa fiye da ke,
bazan Iya qwace masa abinda yake soba, kiyi hakuri idan nabaka Miki rai ataraiyyata dake



Tun kafin yagama magana hawaye ya wanke mata fuska, cikin kuka tace Amma Ina sonka Aliyu



Kirjinsa ya danne dayakejin Kamar Ana zuba masa barkono aciki, cikin dauriya yace kiyi Hakuri Fatima,
sannan yakashe wayar



Yana Kashe wayar, ya zauna awajan, zazzafan zazzabi yana neman rufeshi



Wayar dake hannunta tasaki, Nan take wayar tafadi qasa Har screen guard dinta yafashe, kanta tadora
Akan gwiwarta tasaki wani irin kuka
Wallahi Yanda take jinsa aranta, Ko Yaya Imran batajin Hakan akansa, to waye shidin? Meya hadashi da
Yaya Imran da zaice yafi sonsa akanta?



Tana wannan kukan suka shigo cikin dakin kowacce da Kaya ahannunta niqi niqi



Gabon Billy ne yafadi, Don tayi zatan kowanine ya mutu a gida

Ledar hannunta ta zubar taqarasa wajanta da gudu tace Yaya Iman lafiya? Menene yake faruwa a gida?



Banza tayi mata, Ko dago kanta batayiba



Yusy ce tazauna jikinta asanyaye tace, Besty Meyake faruwa Dan Allah?



Sai a sannan tadago da kanta idanunta jajir da kuka tace, Baya sona, Wai baya sona, bazai Iya Aure naba,
Aliyu baya sona "



Ajiyar zuciya Billy tasauke tace alhamdulillah, wallahi ni jinake ma wanine ya mutu a gida



Cikin kuka Iman tace Yanda nake jinsa araina, Har Gara wani Abu yasameni Akan narasashi



Me Billy zatayi inba Daria ba, wayyo Allah Yaya Iman, yanzu duk wannan haqilon dakike akansa, da
wannan gayu irin naki, shine yace baya sonki?



Wayyo Allah cikina, Kai wannan Abu Yamin dadi wallahi, soja soja, Yaya Iman ta sojanta



Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?πŸ’–



Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem



11



Batare da tacewa yar'uwar Tata komai ba Akan dariyar datake mata tajuya baya tareda kwanciya

Ba'a dauki tsawon lokaci ba zazzabi Yarufeta



Yusy ta kalli bilkisu tace dr. Kinga muna ta neman mafitar Yanda zamu Rabu da wannan gayen gashinan
shida kansa ma yabamu hakuri



"hmm damafa rikici ne irin na Yaya Iman, inba hakaba mutimin Nan baki sanshi ba, ba ganinsa kikai
azahiri ba, kawai magana ta chatting shikkenan Har kije kidorawa kanki damuwa akansa?

Cewar Billy



Yusy tace aikinsan Zuciyar mata daban take data maza, inda munsan za'a yi hakanma Ina ita Ina sauraron
shi



Hakane Kam, to Allah yaqara kiyayewa de



Amin "inji yusy



Tashi sukai suka tafi kitchen domin yin girki



Iman kuwa Daga wannan kwanciyar batama San inda kanta yakeba, zazzabi yayi Mata mugun kamu



Saida suka gama hada komai, zasuci abincin yusy tace Teemah taso muci abinci, taji Shiru
Besty na, kohar yanzu fishin ake damu ne?

Nanma taji Shiru, Dan haka tatashi taje takama hannunta zata jata"



Jitayi jikinta zafi rau, tace subhanallah, da karfi tace Besty!!



Billy tataso dasauri tace Yaya Iman menene? Tana tambayar tana tattaba jikin Iman din



Innalillahi Yaya Iman ai zazzabi ne yakamaki, Daga nanfa jikin Billy yayi sanyi

Lalle wannan al'amarin na Yaya Iman ba qarami bane, ita wannan Aliyun Allah yasa de ba aljani bane
yar'uwar ta tayi Gamo dashi

Yanzu gashi memakon su qureshi Kamar Yanda suka fada su ya quresu



Kamata sukai, suka tafi clinic, abincin da basu ciba Kenan



*** *** ***

Awajan daya ke motsa jikin anan ya zauna, dafe kansa yayi dayake ji Kamar zai Rabe gida biyu

Ya tsani kukan mace, Kuma dagaji yasan Cewa kuka take yakashe wayar Nan, yau Wai shine fatimansa
take kuka bashida damar dazai rarrasheta



Dan qaramin towel yaja yagoge face dinsa, sannan yajuya yanufi dakinsa



Ruwa ya watsa yafuto, Daga shi sai singlet da gajeren wando yafada Kan gado ya kwanta, kansa nayi
masa mugun ciwo



*** *** ***
Tun Daga wannan Rana Iman tashiga damuwa, tun Billy najin Haushi harta dawo tana tausayin yayar
Tata

Sonsa yana Nan daram acikin ranta, Har Zuwa yanzu dayace baya Santa bataji kaunarsa taragu ba acikin
ranta



Sunata shirin rubuta exam dinsu na qarshe, haka Billy da yusy suka dage Akan Iman wajan Bata
shawarwari masu kyau, to shine ma ta kwantar da hankalinta take karatun exam din



Yauma Suna dakin Dukansu Suna fira, wayarta ce ahannunta, ba komai take ganiba sai pictures dinsa



Bilkisu ta kalleta tace Yaya Iman kirage tunanin nanfa,



Itama kallan bilkinsun tayi sannan tace keba tunani bakeba, kawai pic din Aliyu nake gani



Hannu Billy ta miqa mata tace muga pic din Aliyun naki yau de Yaya Iman



Babu musu tamiqa mata wayar, Billy na karba tace wow yayi kyau gaskiya



Dadi yakama Iman, sosai, Har Billy ta lura da Hakan, Dan ta qara kwantarwa da yar'uwar ta hankali
saitace gayen yahadu sosai, baida makusa, sai waje daya tak



Da mamaki Iman ta kalleta tace Ina Kenan? Billy tace makusarsa daya awajena shine dayace yadena son
Yaya Iman dina



Dukansu sukasa Daria, Iman tace emana, waishi banza, ai yaban Haushi wallahi,



Wayar ta karba awajan Billy ta kalli pic din Nasa sannan taci gaba da Cewa Kaiko hmm saina Rama
abinda Kamin wallahi
Dukansu kallanta suke Kamar wata me aljannu inba aljannu ba Ina zata ganshi ma bare Har aje ga
ramuwa



Ammafa Yaya Imran yafishi doguwan fuska, Kuma Daga gani ma Yaya Imran dinmu zai fishi fara'ah

Ko a photo Zaki Gane haka

Cewar Billy



Iman tace ni Bilkisu Ko Imran dinnan zan barmiki ne? Kinwani dameni Yaya Imran Yaya Imran ha'a



Sakare Bilkisu tayi tana kallanta tace ke kanki kinsan da ace banda Haroon babu abinda zai hanani
Aurensa Tunda ke gudunsa kike

Ni inada halacci bazan Iya Qin jinin Hajiya ba



Cikin masifa ta hayaiyaqo tace to saiki fadamin waye yake Qin jinin hajiyan?



Gashi kuwa kinason wani bare, kinqi dan'uwanki

Inji Bilkisu



Daga kwanciyar datake tatashi zaune, tace to Wai in tambayeki Bilkisu, jinake da din ninace Ina Sonsa,
Kuma na dawo nace banaso



Cikin Daria Bilkisu tace ai bazaki birgeniba Yaya Iman saikin kalli idan Yaya Imran kince Bana sanka Imran



Cikin bacin rai tace Wallahi zan Iya Bata Miki rai yanzu Bilkisu, kinfa rainani, kin kaini bango



Kunnanta takama tace sorry Yaya Iman, Ala barmana ke
Kude Allah ya shiryeku wallahi, adinga maimaita magana dayade, Tunda yanzu komai ya wuce ba
shikkenan sai ayi hakuri ba



Iman tace ai ita Naga farin ciki take da rabuwar Tamu, namutu konai rai babu ruwanta



Jin furucin Iman yasa jikin Billy yayi sanyi, tace kiyi Hakuri Yaya Iman, insha Allah ma bazaki mutu ki barni
ba



*** *** ***

One week later



Waya take da qawarta Daga Nigeria, tana lura da yanayinsa, Tunda yazauna yake juya tea din dake
gabansa

Tagama lura dashima kwata Kwata tunaninsa baya wajan



Miqawa yayi, yayi cikin dakinsa, atika dake zaune tana kallo tabishi da kallo, a ranta tace yau Kuma waya
taba babyn mamy



Yana Zuwa daki, yafada Kan gado tareda jawo blanket Yarufe duka jikinsa dashi

Zazzabi yakeji da ciwon Kai sosai, Kuma bayasan ya kwanta mamy tagane, Gara yadawo daki may be idan
yahuta zaiji normal



Tana gama wayar datake ta miqe, Bata zarce ko'inaba sai dakinsa



Dasauri ta qarasa Kan gadon, bargon daya rufa dashi ta janye, wani irin zafi ne ya bigeta

Tace subhanallah baby, zazzabi ne ajikinka Amma bazaka Iya fadamin Akira doctor ba
Narasa Gane wanne irin miskilin mutum ne Kai wani lokacin wallahi



Cikin runtse ido, yadafe kansa dake masa ciwo yace mamy..... Kaina... Ciwo mamy



Janyoshi tayi jikinta tana Jijjiga jikinsa tace sannu baby, yi hakuri Bari nakira Mustapha Yazo da likita ya
dubaka



Wayarsa ta dauka tanemi musty, tana shiga tasanar dashi halin da ake ciki



Tareda doctor suka dawo, doctor na ganin situation din dayake ciki, yace dole suje asbiti domin ayi masa
Dan gwaje gwaje



Mustapha ne yakamashi, suka fita, sai sojoji guda uku dasuke take musu baya, Suna Zuwa asbiti aka
bashi gado, likita yayi gwaje gwajensa yadawo

Ya samu mamy da Mustapha yace Hajiya gaskiya yakama ta adinga kula dashi sosai, saboda yasa
damuwa aransa, tunani yayi masa yawa

Gashi yanzu Hakan harda haifar masa da Hawan jini



Mamy da Mustapha ne suka hada baki wajan fadin Hawan jini doctor



(kuyi hakuri da wannan nayi busy ne,πŸ˜’)



(Daga yau nadena posting WAZAN ZABA a Facebook, duk me buqata Iya mata, ta turomin number dinta
zan sakata a group na whatspp, wannan group din saboda sharhi na budeshi, please idan kinsan bazakiyi
magana a karki turomin phone number naki, Iya mata plsπŸ™πŸ™



Mrs Usman Ce WAZAN
✍🏻 ZABA?πŸ’–
Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem



12



Sosai makuwa hajiya, hawan jini yayi masa mugun kamu, yakamata adena barinsa shi kadai, yana
kebewa bare Har Hakan ya haifar masa da damuwa

Duk wata kulawa zan dinga Zuwa Har gida Ina bashi, idan time din shan maganinsa yayi zanzo nabashi, ki
kwantar da hankalinki insha Allah inde kunyi amfani da shawarar Dana Baku, zai warware Kamar da



Cikeda damuwa mamy tace to shikkenan likita mungode

Tashi tayi takoma dakin da Aliyu yake, bacci yake, harma ruwan da aka daura masa yakusa qarewa

Agefen gadon dayake ta zauna, tazuba uban tagumi tana kallansa



Cikin sanyin jiki Mustapha yashigo dakin, yana kallan mamy yaji duk tabashi tausayi, gaba daya
hankalinta atashe yake,

Ahankali yaqaraso cikin dakin, yazauna akujera ya fuskanci mamy sannan yace mamy kiyi hakuri, ki
kwantar da hankalinki insha Allah zai samu sauqi



Kamar zatayi kuka tace ta Yaya zan kwantar da hankalina Mustapha, Aliyu shi kadai gareni, shi nake kalla
inji dadi, yau gashi akwance asanadin soyaiya, ni DANA SANI ban matsa masa Akan yasamo yarinyar
dazai auraba, da duk haka Bata faruba



A a mamy kidena fadar haka, Aure ai dole zaiyi Aure dama, Kuma dakin yi masa magana da bakiyiba dole
Tunda Allah yatsara Hakan, to dole zai gamu da abin
Wannan Karon mamy hawaye ne suka zubo mata, tasa hannu ta share, tace Mustapha idan ban Hana
Aliyu yadena kula yarinyar nanba, nan gaba idan magana tayi Nisa kunya zamuji Kai kanka kasan komai



Jijjiga kansa yayi Cikeda gamsuwa yace hakane mamy, Allah de yabashi lafiya



Bata Iya Cewa komai ba, sai sharar hawaye datake



*** *** ***

Kwanansa daya suka sallameshi yakoma gida, saide doctor yana Zuwa gida yana duba shi akai akai,
Kamar Yanda yace



Mamy tayi masa fada sosai Akan rashin lafiyar sa, sannan taqara da nasiha da Kuma lallashin yadena
tunanin Iman, ya hakura yacireta aransa



Tundaga wannan lokacin, tadena barinsa yazauna shi kadai, bare ma yayi tunani



Saide abinda mamy takasa sani shine, yana nuna mata ne ya hakura da Iman, Amma acikin Zuciyar sa,
kaunarta sake nunkuwa take, inda ace akwai inda zaije acire masa soyaiyar ta, da tuni yaje, Kodan Imran



*** *** ***



Wallahi zazzabi nakeji Bilkisu



Billy ta kalleta Cikeda da tausayi tace Yaya Iman kisawa Zuciyar Ki salama Akan wannan bawan Allanfa



Ke kanki kinsan abinda kika dauko, bamai dorewa bane Ko awajan iyayenmu
Sannan Kinga Koda yaushe kina Fama da zazzabi, Ina tsoron Kar wani Abu yasameki Yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login