Showing 21001 words to 24000 words out of 39414 words

Chapter 8 - WAZAN ZABA by Amnah El Yaqoub

14 May 2026

109

yayi yana nazari shin yashiga dakin
yagani tadanji sauqi kokuma kawai yajuya? Karfa yashiga yaje ba ita kadai bace adakin mezece idan
yashiga?

Yana wannan tunanin mamy tafuto falo dauke da jug ahannunta zatakai kitchen

Da tsananin mamaki afuskarta tace Baby me kakeyi anan?



Arazane ya juyo, baiyi zatan ganin mamy ba a yanzu

Cikin damuwa yace mamy...



Kama hannunsa tayi taduba gabas da yamma babu kowa sannan tajashi cikin dakinta

Tace mekakeyi a wannan lokacin bakai bacci ba?



Kamar zaiyi kuka yace mamy Iman batada lafiya, nakasa baccin mamy...... Yaqarasa maganar muryarsa
na rawa, nan take hawaye suka zubo acikin idanunsa



Cikin ranta tace yau nashiga uku, wanne irin so Yarannan sukema junansu?

Afili tace to menene abin kuka Kuma Dan batada lafiya? Ai zataji sauqi
Kansa yadora acinyarta yace to mamy naje Naga halin datake ciki? Dan Allah mamy karki hanani kibarni,
Wlhy tun dazu zuciyata zafi takemin, mamy Ina sonta.... Inasonta mamy bazan Iya cireta araina ba...



Innalillahi.. Mamy take maimaitawa acikin ranta, tofa wannan al'amarin yafara daure mata Kai, ta
saddaqar kawai tabarwa Allah komai dangane da wannan Yara, zata musu Addu'ah kawai shine mafita



Afili tace nasan kana sonta Aliyu, ka kwantar da hankalinka, insha Allah zataji sauqi, Amma karma kaje
dakinta, Aliyu idan kaje dakinta Garin futowa wani a gidannan yaganka mezamuce dasu? Kayi hakuri kaji
baby insha Allah zata warke



Ajiyar zuciya yasauke yace to mamy Dan Allah kijanye maganar dakikai tsakanina da Bilkisu, mamy bazan
Iya auranta ba, idan kuwa na Aure ta to zan Aure tane dason yayarta acikin zuciyata, mamy kada na
zalinceta, nayi Miki alqawarin zan Kwantar da hankalina Allah yayayemin yakwomin wata matar



Shiru mamy tayi, itakam Zuwa yanzu ai babu abinda zata Iya Cewa game da wannan al'amari

Tace to Aliyu Allah yayima albarka, jeka kwanta

Tashi yayi jiki asanyaye yakoma part dinsu



*** *** ***

Next day



Dasafe Suna zaune a falo, game suke bugawa a TV kowa ya nutsu yanaso yaga yaci, Daga Aliyun Har
Imran wando ne ajikinsu three quarter

Na Imran fari sai farar Riga marar hannu



Na Aliyu Kuma Daga wandonsa Har rigar duk kalar kakin soja ne, Farhan yana zaune agefe anci manyan
Kaya farare hardasu agogo
Yana kallansu, Aliyu yace Bros yakamata muje wajefa mudan buga qwallo kadan, Shima Imran din
hankalinsa yana kan game din dasuke bugawa yace Ok Bros



Dan Murmushi Farhan yayi harda Sosa qeya yace Yaya Ina tuni de



Murmushi Aliyu yayi yace Farhan karka damu wayarka tana hanya



Jijjiga Kai Imran yayi yace wannan Yaron zaka siyawa waya? Sau uku Ina siya masa Yana Bawa yanmata,
yanzu haka nan daka ganshi da manyan Kaya wajan yanmata zaije



Murmushi Aliyu yayi kafin yayi magana Alhaji yashigo cikin falon, basuji shigowar saba, saboda game din
daya dauke musu hankali, Imran Cewa yake yess nine first

Aliyu yace inaaa Bros nine zancinye



Hajiya da mamy Suna Daga can gefe Hajiya tace Alhaji sannu da Zuwa, mamy ma tace Sannu da Zuwa
yaya



Lokaci daya suka kalli kofa, Alhaji suka gani atsaye, kowa kansa ya sunkuyar Kamar marasa gaskiya

Baqin ciki yakama Alhaji, dubesu Dan Allah azaune da wannan kayan, sun girma harsun gaji Amma babu
me maganar Aure acikinsu, Ko ajikinsu Suna zaune sunyi biris da maganar Aure



Aliyu ne yace sannu da Zuwa Alhaji, Imran ma yace sannu da Zuwa



Be amsa musu sannun tasuba yace wato ku ba'a Isa dakuba, anyi muku maganar Aure kunyi Shiru, yanzu
ku duba kuga kayan dayake jikinku Baku da maraba da arna



Da hannu yanuna musu Farhan yace kuduba kuga qaninku yayi shigar mutunci Amma ku kokunya
bakwaji
Dasauri Imran yace Alhaji wallahi Shima Farhan din wajan.... Bai qarasa maganar ba Alhaji yace kowa
nabashi nanda wata daya acikinku yakawomin matar Aure



Imran yasosa kansa ya kalli hajiya, nan take tagane nufinsa tace Alhaji ai Imran yadade dayimin magana,
nice de namanta banyima zancenba, Wai Tunda su Iman sungama school yanaso Asa ranar bikinsu



Adede lokacin Iman tafuto Daga daki, da wata doguwar rigar bacci ajikinta medan kauri, wannan
maganar ta Hajiya ce tasauka adodon kunanta

Ahankali tajuya Takoma cikin dakinta gabanta na mugun faduwa



A falo kuwa Alhaji Murmushi yayi sannan ya kalli Aliyu yace to kaima Aliyu kakawomin yarinyar dakakeso
sai ahada gaba daya Asa muku ranar



Jikinsa asanyaye yace to Alhaji insha Allah



Alhaji yayi ciki, Adede lokacin wayar Aliyu tayi qara, abin mamaki yana duba me Kiran nasa yaga number
Iman ce



Kirjinsa ne yake masa zafi, yadubi barrister yace Bros Bari na amsa waya, yayi waje

Yana fita harabar gida yafara Tari, jiyake abin nasa naqare ne, yasa hannu zai Daga Kiran nata yaji Tari
yaqi qarewa, haka Kiran nata yakatse Bai dagaba



Direct part dinsu yanufa dasauri yanaso yasha ruwa kozai daina tarin



Yana Zuwa yanufi fridge yasha ruwa kadan, Amma still tarin yakeyi, amai yafara ji, dasauri yanufi toilet,
yana shiga yaji amai yataho masa, danhaka yanufi sink yayi aciki

Abinda yaganine yabashi mamaki matuqa
Ahankali ya tambayi kansa "jini"?



Sharhi please πŸ™πŸ»



Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?πŸ’–



Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem



16



Shiru yayi yana maida numfashi, yana gama Aman jinin sai tarin yatsaya, wanke bakinsa yayi sannan yayi
brush yafuto Daga toilet din



Agefen gado yazauna, yadafe kansa da hannunsa, yanzu Yaya zaiyi yasamu yarinya cikin 1month?
Shiyasa yafadawa mamy tun farko zamansa agidannan wata matsalar zata haifar masa

Ya tabbatar wannan Aman jinin yanada nasaba da Zuciyar sa



Afili yace Innalillahi...



Tunawa yayi da Kiran ta, cikin sauri yadauki wayar yakirata, ringing biyu wayar tayi Iman ta dauka



Kukanta ne yadaki dodon kunnansa, rintse idanunsa yayi yanajin kukan nata nataba masa zuciya

Daqyar yace "meyasa kike kuka?"
Shiru tayi takasa magana sai shashshekar kuka datake

Ahankali cikin rada yace Fatima banasan kukan nan, me akayi Miki Wai?



Cikin kuka tace "kanajin abinda Alhaji yacefa, Wai zaisa min Rana da Yaya Imran, Allah banasan sa, ni Kai
nakeso"



"meyasa zakice bakya sonsa? Kenan bakyason Bros Dina nikuma kice kinasona nayarda, me Imran din
yayi Miki? Yanasonki Fatima,



"OK haka zakace? "



" mekikeso nace Miki? Kisoni kiqi dan'uwana?



Cikin takaici tace Masa shikkenan, tareda kashe wayar



Wayar yabi da kallo, yanzu banda yanasan yarinyar Nan Yama za'ai takashe masa waya afuska? Yaya
takeso yayi ne?

Gaba daya jiyake yatsani kansa dakuma wannan rayuwar

Wayar doctor din dake dubashi yakira yace masa basai yazoba yau, babu abinda yakeji na rashin lafiya
atare dashi



Yana kashe wayar, yayi wulli da ita agadon hadi da tagumi hannu bibbiyu



*** *** ***



Acan cikin gida kuwa Iman kuka take sosai Kamar ranta zai fita, hannu tasa ta share hawayen idonta,
p.o.p din dakin tazubawa ido tana nemawa kanta mafita
Iman Kinga wannan mutumin baya kaunarki, bayason mu'amularsa dake, qarara yadade da baiyana Miki
abinda yake cikin Zuciyar sa, naci da jaraba irin taki ne yasa kika liqe masa, kin zubar da qima da darajarki
ta ya mace kin nuna masa so, Amma shi yana Miki maganar Imran, wato da gaske Kenan yafison Yaya
Imran akaina

Juyi tayi Akan gadon sannan taci gaba da zancen zuci ita kadai



Iman Barrister yana sonki, yana baki duk wata kulawar data dace, bazaki Iya cire son Aliyu acikin ranki
ba, Amma haka zakiyi hakuri kici gaba da sauraron muradinki

Saida tagama zancen zucinta sannan afili tace "insha Allah Nima nadena wahalar dakaina abanza,
nadena wahalar da kaina Akan mutumin dabaisan darajar soba, bayace Ina sonsa naqi dan'uwansa ba?
To yanzu zanso dan'uwan nasa Tunda haka yakeso



Daga nan tatashi tashiga wanka, tana futowa ta zauna ta tsara kwalliya, atamfa ta saka Mai launin green
dinkin Riga da sket, sosai kayan yayi Mata kyau, tafuto falo



Hajiya da mamy Suna zaune a falo, sai Imran dayake jiran Aliyu suyi ball, tana futowa mamy cikin ranta
tace masha Allah, dole Aliyu na ya rikice

Aqasan kujera ta zauna, tana gaida su, gaba dayansu suka hada baki wajan amsawa, banda barrister
daya Kafeta da ido



Ahankali tatashi tayi wajansa, tace Yaya Dan Allah anjima muje shopping kaji, Wlhy kayan make up Dina
duk sun qare

Yana kallanta yace to shikkenan karki damu, Dama ai munjima bamu je yawoba, da yamma saimu tafi,

Cikin murna tace to Yaya ngd

Sannan ta maida hankalinta Kan Kallan dasu hajiya sukeyi



Kusan minti talatin da zamanta, saiga Aliyu yashigo cikin falon,kallo daya tayi masa tadauke kanta, Shima
anasa bangaren fuskarsa ahade yadauke kansa

Barrister na ganinsa yace dama Kai nake jira, muje
Dasauri ta tsaida shi, domin Aliyu yaji Haushi tace Muradina Dan Allah tsaya kasha Ko ruwane sai kuje

Bata jira amsarsa ba, tajuya tayi kitchen da sauri, saigata da gorar ruwa da cup

Tsabar iyayi irin nata data zuba masa ruwan Saida ta rissina sannan tace gashi kasha kaji sanyi aranka



Dadi sosai barrister yaji, yasa hannu yakarbi ruwan da niyya yahada da hannunta yariqe

Ahankali ta janye hannunta



Duk abinda suke Akan idonsa, dasauri yakawar da kansa



Harabar gidan suka fita, Daga can bakin gate sojoji ne wanda suka zo tareda Aliyu

Dan haka sukai baya, suka fara buga ball dinsu



*** *** ***



Da yamma wani wankan tasakeyi, doguwar Riga tasaka baqa, sai fulawa ajikinta fara, rolling tayi da
dankwalin rigar, sai zuba qamshi take



Falo tafuto, Hajiya tace Ina zakije? Hajiya da Yaya zamu fita



Hajiya tace Adawo lafiya, tayi kitchen



Zama tayi a falo tana selfie a wayarta, ahaka yashigo yasameta, yayi kyau sosai cikin suit baqa

Tana ganinsa tasaki Murmushi tace Yaya kayi kyau sosai

Shima Murmushi yayi yace ai kinfini kyau Muradina
Kofa ya nuna mata yace muje Ko? Babu musu tatashi suka futo

Kowa yagansu saisun birgeshi, Yanda sukai kyau babu qarya

Suna Zuwa wajan Mota yabude mata, Bata shiga ba Saida ta juyo tace Yaya Bari inyi mata pic

Matsowa yayi dab da ita tayi musu selfie sannan tashige cikin motor, shikuma Yarufe yazagaya yajasu
suka fice Daga gidan



Suna fita yasaki labulen window din dakinsu, Ina zasuje haka? Kuma yanzu ahaka zasu fice maza suyita
kallanta? Meyasa ma becewa Bros baida lafiya ba Dan su fasa fita? Harda yimusu photo, shi kuwa Tunda
yake da ita Bata taba tunanin yin pic dashiba, may be bekai matsayin dazatayi dashi dinbane



Da wannan tunanin danake garama natafi wajan mamy kozan danji sauqi, yana gama magana da Zuciyar
sa yayi cikin gidan



*** *** ***

Suna tafiya ahanya yace Bansan meyake damun Bros dinaba, nace masa yashirya muje unguwa yaqi
yarda, Amma inaga Dan yaga dake zamu fitane, kinsan shi bayason raini, yanzu sai yace mun dauki
yarinya muna Abu agabanta, karta rainamu, abinda yasa ban matsa masa mutaho tareda kinsan shi idan
zai fita dole Saida wannan sojojin, ranar da muka kaiki asbiti ma saboda darene shiyasa yataho shi kadai,
Amma badan haka ba bazasu barshi yafita shi kadai ba, shiyasa yanzun ma na qyaleshi, banason tafiya
da wannan jiniyar wallahi



Murmushi tayi tace nikam Yaya in tambayeka



Inajinki Muradina



Naga kunason junanku sosai kaidashi, yanzu misali wani Abu yasameni, Shima Kuma wani Abu
yasameshi, wazaka fara temakawa acikinmu?



Daria yayi yace Kai Muradina, kincika rigima, mekuma yakawo wannan maganar
Cikin shagwaba tace Dan Allah Yaya ka amsa min



Hankalinsa yana kan driving din dayake yace, Fatima inason Aliyu fiye da Yanda nakeson kaina, zan iyayi
masa komai danjin dadinsa, Kinga yanzu da Alhaji yasa masa wannan dokar ta fidda matar da zai aura
cikin wata daya? To wallahi jinake araina dazan Iya cireki araina Dana cire nahakura nabashi Ke, nikuma
nadau hukuncin da Alhaji zaiyi masa

Dannasan bazai samu mace cikin wata dayaba, to matsalar shine inasonki



Aliyu yana sona, tun bamusan kanmu ba ansha siya masa Abu yace ya hakura yabani, Mota tare muke
bada order su idan zamu siya, Ke hatta waya yanzu ne muka daina siya tare

, zan iyayi Masa komai Fatima, Kamar Yanda Shima na tabbatar zai iyamin fiye da haka



Tanajin karshan maganar tasa tashareshi ta kalli window tana ganin gefen titi

Wato kowannensu zai iyayin komai Akan dan'uwansa, kowa yanason dan'uwansa fiye Dani, ai sai kuje
kuyi tayi, Naga Yan biyu ma, Kuma ta tabbatar da gaske yake, Tunda Har Taji yakirata da Fatima abinda
saita Dade rabon dataji yakirata Da wannan sunan sai Abu me muhinmanci



Jintayi Shiru ne yasa yace dafatan ban Bata ranki ba?



Ahankali tace a a Yaya



Shopping din sukayi, duk inda sukayi sai ankallesu, Daga nan suka wuce yawonsu



*** *** ***



Agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yaduba, Ina suka tsaya basu dawo gidaba Har yanzu Karfe Tara
da kwata?
Harabar gidan yake zagayewa



Wayarsa yadauko Har zai Kira Bros, kawai saiya fasa yakira Mustapha

Yanayin wayar yana duba Agogon hannunsa



Har suka gama wayar baiga sun dawoba, lokacin Tara da rabi na dare

Cikin gidan yashiga, yana shiga sai Hajiya da Zeey a falo, yace Hajiya mamy nafa?

Daria tayi tace to Dan mamy gatacan a kitchen



Daria yayi yana sosa kansa yayi kitchen din



Mamy mekikeyi a kitchen da kanki? Batare data kalleshi ba tace baby tea nake hadawa



Yauwa mamy hada Dani, zansha Nima



Tace to baby



Yana zaune yana Kallan Yanda take hada tea din, Amma tunanin sa yana can wata duniyar, kome suke
basu dawoba? Wata yar qaramar wuqa ce a ajiye agefe yadauka yana wasa da ita, yana tunanin irin
wulaqancin dazai yiwa yarinyar Nan Tunda Har tafice Daga gida, ta zauna awaje Har tsawon wannan
lokacin



(jama'ah kunji karfin haliπŸ€”)



Mamy na juyowa da karfi tace Aliyu!!!



Arazane ya kalleta
Cikin fada tace Wai yaushe zaka Dena wannan tunanin Naka marar bullewa? Sau uku Ina kiranka kayimin
banza, yanzu duba Yanda kajiwa kanka ciwo da wuqa



Sai a lokacin ya kalli hannun nasa, jini ne yake disa awajan, shi bemasan yaji ciwonba, Ahankali yace
mamy Bansan naji ciwonba



Harara tazuba masa, cikin tashin hankali tace muje muje mutafi asbiti ayi treatment din wajan



Kamar qaramin yaro haka tajawoshi suka futo falo

Adede lokacin su Iman suka dawo da ledoji a hannunta



Imran ne yasaki tasa ledar yayi wajan sa yace Bros, meyasami hannunka? Subhanallah ai ciwo kaji

Hajiya ma tace Toya kuka tsaya asaka masa tissue awajan mana



Haushi ne yakama Iman, ganin duk sun wani rikice saikace wanda akace wani mummunan hatsari
yasamu



Mamy tace Imran gashinan kawai ku wuce asbiti



Imran yace no mamy , ai Iman tana nan Bari ta wanke masa wajan zata Iya



Sai a lokacin suka Kai kallansu gareta tana tsaye awaje daya



Shima gogan kallanta yayi cikeda takaici, shibama ciwon hannunsa ne yadameshi ba, sai Yanda taje ta
zauna awaje da wannan yar iskar shigar



Hajiya tace kinaji Ana Miki magana Amma kin zubawa mutane ido
Cikin ranta tace Hajiya Kenan bakisan halin wannan me baqar Zuciyar ba

Ahankali taqaraso falon tace Bari nadauko kayan, tayi cikin dakinta da sauri



Saida tahado komai sannan ta futo falon, Hajiya na zaune agefe da Zeey, sai Imran da Aliyu dasuke can
gefe Suma, wajan su ta nufa ta zauna aqasa, su Kuma Suna Kan kujera, Imran yace please muradina kiyi
masa Ahankali kinji



Ahankali tace to muradina



Tadubi Aliyu datakejin Haushin abinda yayi Mata da safe tace kawo hannun



Shima fuska atamke yakawar dakai tare d miqo mata hannun



Saida ta kalli hannun nasa fari tas Kamar nata, gashi kwance abayan hannun, sannan tariqe tafara wanke
masa wajan

Da niyya take dannawa da karfi, duk Dan yaji zafi, Amma Ko a fuska bataga ya nuna yanajin zafin ba



Shima yanajinta, yasan Sarai da niyya take masa Hakan, kawai yana tunanin irin hukuncin dazai mata ne

Mamy ce takawo musu tea harda Imran din tana ajiye musu tace ga tea nan kusha, ta kalli Iman tace
sannu takwarata kinji, anhadaki da aiki, ashe dama kin Iya



Imran ne yace A'i medicine sukayi Daga ita Har Bilkisu



Masha Allah, to Allah yatemaka, cikin Murmushi Iman tace amin mamy
Mamy na tafiya wajan Hajiya Imran yace sannu Bros, aide bakajin zafi Ko? Kafada yadaga yace no babu
zafi kokadan Bros



Imran yace OK, yadauki tea dinsa zaisha

Dasauri tace muradina Dan Allah karka wahalar da kanka kabari naqarasa saina baka



Cikin mamakinta Imran yace iyee babyn nan Kin dagefa da bani kulawa, Naga alama kinaso ayi akaiki
gidan barrister



Tace sosaima yaya



Murmushi yayi yace ai kuwa a ranar dakikazo gidana zakiga Yanda zan baki kulawa Nima, da kanki Zaki
bani dama inyi bake-bake acikin Zuciyar Ki



Murmushi tayi batace komai ba



Duban ta yayi cikin bacin rai yace Wai baki gama bane? Dagoda kanta tayi ta kalleshi cikin bacin rai Itama
tace nakusa



Sai a lokacin ta maida hankali tadaure masa hannun, dama ta nayi Ahankali ne Dan tayi fira da Imran
agabansa yaji Haushi, Kuma yajin



Tana gamawa ta tattara abin gabanta tayi cikin daki



Akan gado ta zauna tace nasan kaji Haushi, ai tukunnama, Dani kake zancen

Bata sake futowa falonba, haka Suma su Imran suka tafi part dinsu, Allah Allah Aliyu yake yagamu da
yarinyar Nan, zata sani ne
*** *** ***

Next day

Da yamma Suna zaune itada Farhan a harabar gidan Akan kujerun roba



Ice Cream ne ahannunta, gakuma wani agabansu, tace Farhan kadau ice cream din mana,

Ajiyar zuciya yasauke yace Bari sister yaubata ice cream nakeba



Wallahi wata yarinya nahadu da ita me zafi, Kuma da alama konayi mata magana ba za'a daceba, Dan
Naga alama ustaziya ce

Daria yabawa Iman, tace haba Farhan, kaida kake da yanmata, karka bani kunya mana Akan mutum
daya, yarinya guda daya tak



Kansa yashafa da hannunsa yace wallahi inason yarinyar Nan sosai

Dazaki shirya Dana kaiki unguwarsu kinganta yau, Zaki ganta da hijabin ta, Amma saide kiganta Daga
nesa saimu dawo gida mu tattauna akanta, idan tayi saina koma gobe



Tace to shikkenan Farhan, Allah yakaimu yamman saimuje



Daga bayansu sukaji ance yauba fada Kenan Ana fira



Juyawa sukai sukaga Barrister da Aliyu da alama zasu shiga cikin part din Hajiya ne



Murmushi tayi gamida miqewa tsaye tace Yaya sannun ku da futowa

Cikin kulawa yace Yauwa muradina



Kan Aliyu na qasa yana duba wayar hannunsa
Ice Cream din hannunta tabashi tace Yaya ga ice cream, jiya damuka dawo dashi Naga baka shaba



No muradina, Kisha abinki, bazan Iya shaba Bros Dina bayajin dadi saboda hannunsa



Batare data nuna damuwarta Akan maganar saba tace a a muradina dansha kaji akwai dadi

Ta debo a spoon tatura masa bakinsa, babu Yanda ya Iya haka ya shanye



Haushi, takaici, kishi, duk suka taso acikin Zuciyar Aliyu, ya kalli barrister yace muje Bros

Hannu Imran ya kadawa Iman sukayi cikin gidan



Itama wajan Farhan Takoma sukaci gaba da tsara Yanda zasu fita anjima da yamma



*** *** ***

Dayamma tashirya cikin atamfa dinkin Riga da sket, Dan qaramin mayafi tayafa Iya kafadarta daya,
tariqo fos dinta ahannunta sai wayarta

Already Farhan na jiranta amota, tana futowa tashige motar suka tafi



Basket ball su Aliyu da Imran suke bugawa, Dan haka Akan idonsu suka fita, Imran Bai kawo komai
aransa ba, yasan Cewa yanzu haka yawonsu zasu fita



Shikuwa Aliyu ransa abace yake, yagaji da wannan renin hankalin da yarinyar Nan take masa, zai jira
harta dawo ayita taqare



Har dare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login