Showing 33001 words to 36000 words out of 39414 words

Chapter 12 - WAZAN ZABA by Amnah El Yaqoub

14 May 2026

105

masu kula dakai, insha Allah gobe da wuri
zanzo



Badan yasoba, murya ciki ciki yace shikkenan



Murmushi tayi tareda ficewa



Tana fita ya runtse idonsa, meyake damun sane kwana biyun nan?
Meyasa yakeji aransa bayaso tatafi gida tabarshi?



Tana Zuwa gida Hajiya tace Bilkisu Shiru Har dare yayi bamu ganki ba sai yanzu?

Agogon hannunta me kyau ta kalla tace laa Hajiya Karfe Tara nefa yanzu, shine Daren yayi?



Hajiya ta girgiza kanta Cikeda mamaki tace um um dare beyiba



Batareda talura da yanayin hajiyaba tayi cikin daki abinta



Washe gari Tunda sassafe tashirya, abaya tasaka tayi rolling da dankwalin, Kamar wata balarabiya haka
tazama



Su Hajiya Suna futowa domin yin break suka ganta sai zagaya falon take, Itama tana ganin su tagaidasu
tace Hajiya natafi, nasan Yaya yanacan shi kadai Shiru, saina dawo



Gaba dayansu sukabi bayanta da kallo, mamy tace Bilkisu fa andage, Yanda take magana serious dinnan
irin itace Likitan datake dubashi



Hajiya tace um ai Hajiya fati tun jiya nake ganin iyayi iri iri, Wai jiya nace mata Bata dawo da wuri ba,
Amma yarinyar Nan sai cemin tayi ai darenma baiyi ba



Mamy tace gsky ne Bilkisu fira tayi dadi, ni wancan Tunda yatafi ma Ko nemana baiyi ba, yasan zanyi
masa tas shiyasa



Hajiya na Daria tace, anjima de maje musake gano jikin Imran din, sukuma Yan India idan sun gama
rashin kunyar magani Ko zasu nememu, Nima Iman Ko Kira, Bayan Alhaji yayi waya da doctor jabir yace
tafarka jiki yafara kyau
*** *** ***



Tunda ta zauna yaketa aikin kallanta, sai yanzu yake Ganin tsananin kyanda take dashi, wanda Abaya
soyaiyar Iman tasa Bai Gane hskanba, Ahankali yace kinsan me?



Girgiza kanta tayi tace um um Yaya saika fada



Kinyi kyau sosai



Gabanta ne yafadi, Yaya Imran dayake son yar'uwar ta, meyasa zai dinga yimata Abu haka?



Murmushi tasaki tace ngd Yaya, Bari in shiga toilet, tashi tayi tashige toilet

Yana ganin shigarta toilet yadauki wani memo dake gefen gadon dayake yayi Dan rubutu aciki yasaka
acikin handbag dinta



Tana futowa suka ci gaba da firar su

Bilkisu tace Yaya yanzu Kam kaji sauqi, likita zai Iya sallamarmu Kwana kusa nasan



Yatsina fuska yayi yace no, Har yanzu Ina danjin ciwon Kai gaskiya, yafadi hakanne Dan Baisan kulawar
dayake samu awajanta taqare



Ita kuwa zuciya daya tace to Allah yabaka lafiya Yaya



Yace amin, yau bazaki bani labarin naki ba?



Murmushi tasaki sannan tafara bashi labari, Shikuwa gaba daya ya tattara nutsuwarsa akanta, bawai
labarin yake jiba, a a kawai kallanta yake San ransa
Suna wannan halin su Hajiya suka shigo dakin, da mamy dakuma Alhaji



Saida suka sake yimasa sannu sannan Alhaji yace su zasu koma gida



Bilkisu tana zaune babu alamar zata tashi tayi musu rakiya tace to hajiya Allah yakiyaye



Mamaki yagama kashe Alhaji, harsunje kofar fita Daga dakin Alhaji yadawo yace dama akwai maganar
danakeso muyi dakai



Ahankali yace to Alhaji



Alhaji yace akwai wata yarinyar abokina danakeso idan ansallameku Daga asbiti kaje ka ganta Ko
zatayima, inyaso ita Fatima saika barma dan'uwanka ita



(wata sabuwa 🤔, Ko Imran zai yarda? Kome yasakawa Bilkisu acikin jaka? To nide fatana aci gaba da
bibiyata)



Sharhi please 🙏🏻



Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖



Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem



23
Lokaci daya yayi Kicin Kicin da fuska

Kuma de Tunda ance yarabu da fatiman menene sai an liqa masa wata

Kansa aqasa yace a a Alhaji ai babu damuwa kawai abar wannan maganar Allah yakawo mafita



Alhaji yace to shikkenan Allah yakawo mafitar

Suka fita gaba dayansu, Suna cikin Mota Alhaji shi kadai yana Murmushi dama ya gwadashi ne yaga Yaya
zaiyi



Acan asbiti kuwa Bayan tafiyar su Alhaji barrister yayi Shiru sai bacin rai yake shi kadai



Bilkisu ta kalleshi nan take yabata tausayi, yana kwance a gadon asbiti ma Amma ba'a qyaleshi ba,
Ahankali tace kayi hakuri Yaya,kayiwa Alhaji biyaiya shine zakaga daidai

Hannu kawai yadaga mata alamar tayi Shiru, Bata barshi d abinda yakejiba shine zata qara masa wata
damuwar



Awannan Rana haka suka wuni Shiru, shi yana tunanin mafita, ita kuwa tana tausaya masa ne, awani
bangaren na Zuciyar ta Kuma tana Cewa Wai meyasa ma su Alhajin nan suka zone? Tasamu Suna Dan
Zaman su rimi rimi Amma yanzu sunzo sun lalata komai

Har dare haka takasa Gane kansa, domin kuwa shi yana tunanin Kamar zasu kawo masa wata yarinyar ne



Haka Billy Takoma gida sukuku da ita




*** *** ***

Washe gari da wuri tazo asbitin Kamar Yanda tasaba, fruit yakesha Suna firarsu Sama Sama, yaude taga
yadan ware ba Kamar jiyaba, jakar hannunta ya kalla yace Ina handbag din dakikazo da ita jiya?

Tace tana gida mana Yaya, meya faru?
No babu komai kawai de jakar ta nayi miki kyaune



Murmushi tayi tace Allah Ko Yaya?



Sosai makuwa jakar tanada kyau, Amma bakiga wani Abu aciki ba?



Girgiza kanta tayi tace a a banga komai ba Yaya



Jikinsa ne yayi sanyi, karfa tarasa wannan takardar Kuma azo asamu matsala



Yanayinsa kadai ta Kallah tagane akwai wani Abu daban dayake boye mata

Dan haka tasa aranta Cewa tana Zuwa gida zata duba jakar taga menene aciki



Kafin tayi magana doctor Yazo yadubashi, yana Murmushi yace gaske jiki yayi kyau, yauma zaku Iya
komawa gida,

Cikin murna Billy tace yeee, alhmdlh



Kallanta Imran yayi, wato murna take zata koma gida, shikuma baya murna asalima jiyake aransa dama
su tabbata ahaka



Dakanta tayi driving dinsu Zuwa gida, ahanya sai fira take masa Shikuwa yayi Shiru, Suna Zuwa gida suka
zube a falo, anhadu a falo kowa sai murna yake, saboda dawowarsu gida



Jikinsa a sanyaye yatashi yace Hajiya zanje part dinmu zan Dan kwanta na huta kadan



Hajiya tace to Imran
Yana Zuwa part dinsa ya kwanta, yazubawa Saman dakin ido, karfa ace yarinyar Nan tarasa wannan
takarda, runtse idonsa yayi afili yace oh ya Allah, nikam inaga banida sa'ah Akan komai



Bilkisu kuwa tana ganin yanayinsa ayanda yatashi yayi part dinsa tasan tabbas yana cikin damuwa,
lokaci daya jikinta yayi sanyi, tashi tayi Ahankali tashige dakinsu, Hajiya na lura dasu gaba dayansu



Tana shiga dakinsu tafada duniyar tunani, meyasa Yaya Imran ya sauya mata? Toma menene abin
damuwa danya sauya matan? Ba saurayin yayarta neba? Maganar jakar dayayi mata dazu ne yafado
mata Arai

Dasauri tatashi tanufi inda suke ajiye handbags dinsu, wadda tasaka jiya tadauko ta zauna Akan gadon ta
zazzageta bataga komai ba



Hannu tasa ta laluba cikin nanma bataga komaiba, ziff din jakar ta zuge Aikuwa saiga yar qaramar
takarda tafado



Ahankali take Bude takardar harta warware ta dukanta, abinda da taganine acikin takardar yasa gabanta
faduwa



Hannunta tadora Akan kirjinta dayake wani irin lugude Ahankali ta sake karanta abinda yake rubuce a
takardar da manyan baqi (BILKISU DO YOU MARRY ME?)



Innalillahi... Yaya Imran nefa, saurayin yayarta, a duniya Bata taba kawowa aranta Cewa Wai zata Iya
soyaiya dashiba, bare aje ga rayuwar Aure

Kuma ai yasan Ina tare da Haroon , but meyasa zaimin wannan maganar?

Lalle maza basuda kunya, inba hakaba Yanda take tsananin bashi girma meyasa zaiyi mata
makamanciyar wannan maganar ma?



Har dare Billy tana daki taqi futowa falon, zeey auta ce tashigo da gudu tace anty Bilkisu kizo muyi dinner
inji Hajiya
Tashi tayi zaune, takama hannun zeey tace Yaya yana nan?



Zeey tace Yaya Farhan?



No Yaya Imran



Eh yana nan yana danna waya, kowa Yazo Ke ake jira



Ahankali tace to gani nan Zuwa



Zainab na fita tace ni yanzu da wanne ido zan kalleshi ma?

Haka de ta futo falon, tun kafin ta zauna ya kafeta da ido yana kallanta, shi sai yanzu nema yake Ganin
kyau da sura irinna Bilkisu



Kujera taja ta zauna, Kuma sai akai sa'ah tana facing dinsa, Bata yarda tadago idonta taganshi ba,
Shikuwa duk abincin dazaikai bakinsa idonsa akanta



Hajiya na kallansu, aranta tace oh Imran babu kunya, Ko yar Kara ma babu



Tace Bilkisu yanaga bakya cin abincinne sosai?

Dago kanta tayi tace Hajiya inaci

Dan satar kallansa tayi, ai kuwa karaf idonsu yahadu, dasauri ta maida kanta qasa



Murmushi yasaki, aransa yace da alama taga komai
Bayan sun gama cin abincin falon suka koma suka fara fira, Ana kallo, tashi tayi zata tafi daki Hajiya tace
Ina zakije ki zauna Ke kadai? Salan kije kina tunani, zauna anan



Haka de Billy ta zauna, Amma duk atakure take, Shikuwa Imran waya yake dannawa Amma hankalinsa
yana kanta



Har wajan Karfe goma na dare kowa ya watse yatafi dakinsa, Bilkisu dadi Taji dama tagaji da wannan
Zaman



Shima Imran yana futowa harabar gidan yayi dialing number ta, harta katse Bata daukaba

Saida yasake Kira sannan ta Daga daqyar,



Kisameni a falo yanzu



Abinda yace mata Kenan, ya kashe wayar



Gabanta yana faduwa ta futo falon, babu kowa, sai shi dayake zaune



Kanta aqasa tatako tazo Har inda yake, aqasa ta zauna, shikuma yana kan kujera



Yace taso ki zauna anan Bilkisu, ya nuna mata waje akusa dashi



Zama tayi, Amma kanta aqasa tana murza zoben hannunta

Qasa qasa yayi da murya, ita kanta badan tayi kusanci dashiba bazataji abinda yake fada ba



Cikin rada yace Bilkisu
Yanda yafadi sunan kadai ya Isa ya birgeka



Ahankali tace na'am



Kinga Yanda Allah yake hukuncinsa Ko? Bilkisu

Arayuwa ban taba tunanin zan Iya auran wata yarinya Bayan Iman ba, sai gashi Daga baya abubuwa da
dama sun faru, ciki kuwa harda hakuri danayi da ita nabarwa dan'uwa na, yanzu haka Ina fishi dashi ne
Akan meyasa tun farko Bai sanar Dani gaskiya ba, yabar abin acikin ransa Har Hakan ya haifar Masa d
mugun ciwo, a yanzu banida zabin daya wuce nasoki, azamana dake a asbiti nayaba da kyawawan
halayen ki Bilkisu, please Ina neman alfarma awajanki ki daure ki aureni Kodan Hajiya (😃😃)



Kanta na qasa Ahankali tace Amma Yaya kasan Haroon...



Haroon Haroon, kede kullum maganarki Haroon, Bilkisu Haroon Bai sonki, kema bakya sonshi

Meyasa bazamu hada kanmu ba, muyi Addu'ah Allah yakawo mafita?



Shiru tayi masa takasa bashi amsa, sake matsowa yayi dab da ita, yakama hannayenta duka biyun ya
riqe, wani irin taushi yaji hannun nata nayi



Innalillahi take maimaitawa aranta, banda wani irin yanayi daya ziyarceta lokaci daya, ita Tunda take
wani babban namiji Bai taba riqe hannunta ba sai yau, Kuma Wai yau dinma Yaya Imran, wanda take
ganinsa Kamar yayansu dasuke ciki daya



Adede wannan lokacin Hajiya ta futo Daga dakin Alhaji domin tahada masa coffee

Cak taja tatsaya batare data qaraso cikin falon ba,

Ahankali ta juya cikin dakin, tace Alhaji zo kaga abinda idona yagani



Alhaji na tasowa Hajiya takama hannunsa tajashi Har setin indasu Imran suke
Shima ganinsu yayi, yasaki Murmushi



Dukansu suka juya cikin dakin suka fasa futowa falon, Alhaji yace lalle Imran da rigima yake, yanzu Hajiya
Yaya yake so muyi da shu'aibu?domin kuwa Zaman da yaran nan sukai kadai zai tabbatar mana da Cewa
akwai wani Abu a tsakaninsu, Kinsan de yarinyar Nan akwai maganar wani akanta

Hajiya tace hakane Alhaji, Amma gaskiya Nima Ina Bayan Dana, gaskiya Alhaji asan Yanda za'a shawo Kan
matsalar nan



Murmushinsu na manya yayi, yadauki wayarsa yakira doctor jabir



Bayan sun gaisa yake tambayar sa Yaya yanayin jikin Fatima?



Jabir yace jiki da sauqi sosai, anasa ran sallamarta ma nanda sati daya

Godia Alhaji yayi masa ya kashe wayar



Hajiya tace to ai Gara tadawo domin mufara shirin biki



Cikin Daria Alhaji yace mata Kenan, Ana maganar mahaifin yaran kina maganar biki



Afalo kuwa, Imran ya tsara Bilkisu da magiya

Akan ta amince



Hannunta dake cikin nasa take kokarin qwacewa Amma Kuma yaqi Bata damar Hakan



Ahankali yasake Cewa please Bilkisu



(Nima nace please Billy 🙏🏻)
Sharhi please 🙏🏻



Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖



Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem



24



Batace masa komai ba yasake Cewa "kin amince?"



Ahankali ta Daga masa kanta, tareda qwace hannunta tashige dakinsu da gudu



Bayanta yabi da kallo yanayin wani irin Murmushi, Ahankali yace Alhmdlh, sannan Shima yatashi yayi
part dinsa



*** *** ***

Next day



Hajiya na zaune asallaya tana lazimi, Bilkisu tashigo da sallamarta ta zauna agefe

Hajiya na kallanta tasan Cewa akwai magana abakin ta, Amma Sai tayi Shiru batace mata komai ba tana
jira taga gudun ruwanta



Kanta aqasa tana wasa da yatsun hannunta tace Hajiya
Na'am Bilkisu, inji hajiya



Am Hajiya dama... Dama Yaya ne jiya.. Saita Kasa qarasawa



Hajiya tasaki Murmushi tace meyake faruwa Bilkisu? Me yayan naku yayi?



Hajiya shine jiya yace Wai yana sona, Kuma ni Hajiya Ina tsoron baba yaji



Hajiya na Murmushin tace toke Kuma me kika cemasa? Ko bakya sonsa?



Kunya ce takama Billy, yau ne Rana ta farko data tabajin kunyar Hajiya

Cikin kunya tace wayyo Hajiya



To Bilkisu me kikeso nafara tambayar ki? Kinsan de duk da Nina haifi Imran bazanso nayi muku auran
dole ba, dole sai Kuna da ra'ayin juna



Hajiya ni dama Ina tsoron baba ne



To karki damu kinji Bilkisu, inde wannan ne ai akwai Allah, babu abinda yafi karfin Addu'ah, kuje kuyita
Addu'ah Allah yashige gaba



Ahankali tace amin Hajiya



Tundaga wannan lokacin soyaiya Mai karfi tashiga tashiga tsakanin Bilkisu da Imran

Ayanzu Kam yariga daya koya mata Yanda zata soshi, abin Har mamaki yake bata, Bata cikakken minti
talatin batare datayi tunaninsa ba
Bata fatan wani Abu yashiga tsakanin su bare Har aje ga zancen rabuwa, Abu daya take tunani da
fargaba shin Yaya zata Iya Zaman Aure dashi? Tana ganin girmansa sosai, Kuma tasan Cewa dole akwai
ranar dazatazo ta kauda wannan kunyar atsakanin su

Abinda take fargaba Kenan



*** *** ***



Kowa na zaune a dining Suna cin abinci cikin walwala, Alhaji ya kalli family din nasa cikin ransa wani irin
dadi yakeji, saide Aliyu da Iman ne kadai babu awajan

Kwanan wata yasake dubawa ya jinjina kansa yasan Zuwa yanzu ansallami Fatima ya Kamata ace sun
dawo gida haka

Yaga alama yaran nan idan ba sune suka nemesuba tofa saisu shekara ahaka

Danhaka yadauki waya yakira Aliyu saide harta gama ringing dinta Bai dagaba, haka Alhaji yasa wayarsa
a aljihun sa yace Allah ya kyauta



*** *** ***



Suna zaune Afalo cikin luntsima luntsiman kujerun dasuka kewaye falon launin farare, firarsu suke cikin
Jin dadi, basa tuna kowa sai kansu, Cikeda so da kauna ya dube ta yace



Matar Aliyu



Cikin nishadi da Jin dadi tace hmm Kamar gaske Wai matar Aliyu, Bayan kagama ban wahala



Ji yarinyar Nan, kebance kin bani wahala ba, agabana fa kika Bawa bros ice cream, gefenda Zuciyar sa
take yasa hannunsa awajan, yaci gaba da Cewa a lokacin dakinsan Yanda naji araina dabakiyi ba

Fatima Ina Miki wani irin so Mai wuyar fassaruwa, bantaba soyaiya ba, Amma ansha kawo min mata Kala
Kala na Aure su, Amma nace Ina Nifa Sam sai diyar Hajiya
Murmushi tayi tace Aikuwa nabashi ne dannaga da gaske kake kadena sona baka kishina kokuma Har
yanzu kana sona



Hararar wasa yayi Mata yace um wato dama da niyya kikeson kashe Dan bawan Allah, duk abinda kike
Ina gani ai, nasan da niyya kikeyi



Wayarsa ce tayi qara, cikin nutsuwa yadaga Daga wajan aikinsu ne, Ahankali yake Bata order Kamar yana
wajan, Saida yagama dasu sannan hankalinsa yakai Kan Kiran da Alhaji yayi masa



Zaro ido yayi yace Innalillahi



Tace lafiya Yaya? Meyake faruwa?



Saida yashafa kansa yace wallahi Alhaji ne yakirani, kinsan sai yanzu natuna banma Kira mamy ba
tsawon wannan lokacin? Kuma duk laifinki ne ai



Cikin tashin hankali tace nashiga uku, wallahi Nima ban Kira Hajiya ba, wayyo Allah da wanne ido zan
kalleta?



Da wanne ido Zaki kalleta Koda wanne ido zan kalli mamy da bros? Ga Yan gida agefe da basu San
nataho wajan ki ba sai saqo na bayar afada musu



Yanzu Yaya Zamu yi Yaya?



Cikin dakiya yace karki damu tsaya nakirashi nasashi a hands free kiji Yanda zamuyi

Haka akayi kuwa, yana Kiran Alhaji ya ajiye wayar atsakanin su



Cikin ladabi ya gaida Alhaji yace Alhaji wallahi wayar Bata tare danine lokacin daka Kira
Alhaji yace eh ai Tunda Fatima tana tare dakai aiba saika nemi kowaba



Hada ido sukai da Iman Kamar wasu munafukai



Yace a a Alhaji wallahi bahaka....



Kafin yaqara sa maganar da zaiyi Alhaji yace nasan kun gama komai yanzu to inaso kukamo hanya
kudawo gida, in Kuma Kuna nan din za'a daura auren to



Cikin kuskurin kunya yace to Alhaji insha Allah, tareda kashe wayar



Duban Iman yayi yace Kinga abinda kika janyo mana Ko?



Tace kaji Yaya zaka doramin laifi, kajanyo mana de, ba Kaine ka biyoniba



Yace naji, yanzu de tashi tashi muhada yanamu yanamu wallahi tun kafin su biyo sawunmu, mutafi gobe
mubasu hakuri



Haka suka tashi suka fara shiri



*** *** ***



Tsaye suke a filin jirgin Malam aminu

Yayi kyau sosai acikin suit dinsa ruwan toka, yayinda ita Kuma tasa atamfarta Riga da sket dinkin yahau
jikinta yazauna Kamar Dan ita akai
Basufi minti talatin da tsayawa ba jirgin su yasauka, Suna futowa kuwa sukagansu, da gudu Bilkisu taje ta
rungume yar'uwar Tata

Oyoyo Yaya Iman



Cikin murna Itama tace Bilkisu nayi missing dinki, inasu Hajiya?



Uhm Hajiya tana gida, tun safe tahana kowa sukuni a gidan nan tana ta murna Zaki dawo, Ke baba mafa
Yazo



Cikin mamaki Iman tace baban? Yaushe Yazo?



Wlhy tun sassafe Yazo, bakiga Yanda hankalinsa yatashi ba dayaji bakida lafiya, Aikuwa yau Alhaji yana
masa waya yace zakizo, saiga baba da kansa akano



Jinjina Kai Iman tayi tace um lalle baba yafara saukowa

Cikin Mota suka shiga sunata firarsu sunma manta da Aliyu da Imran



Shikuwa Aliyu cikin kunya ya Bawa Imran hannu da nufin su gaisa, gaba daya kunyar bros din nasa yake



Shima Imran din anasa bangaren fishi yake da dan'uwan nasa



Yana ta shan qamshi batare daya kalleshi ba yamiqa masa hannun suka gaisa Sama Sama



Amota ma Iman Da Bilkisu Suna baya, Aliyu na zaune adaya gefen, yayinda Imran yake driving



Hankalinsa yana kan driving din dayake yace "yajikin naki?"
Iman tanajin tambayar tasan da ita yake, dole tasan dama zaiyi fishi, to Amma Yaya zatayi

Ahankali tace jiki da sauqi, yasu Hajiya?



Agajarce yace mata lafiya



Har sukaje gida babu wanda yasake magana acikinsu, shi Imran yana fishi, shikuma Aliyu kunyar sa
yakeji, gani yake Kamar yayi wa dan'uwan nasa qwace ne



Yanayin parking su Bilkisu suka shiga cikin gidan, Imran ma Yarufe motor zai shiga Daga ciki, ba tareda
daya sake Kallan Aliyu ba



Abin nasa ne yafara damun Aliyu, Bai sababa, sannan Kuma basu sabarwa kansu da hakanba, cikin sauri
yariqe hannunsa Ahankali yace bros...



Imran ya kalleshi baice komai ba



Yasake Cewa bros... Kayi hakuri



Cikin fishi Imran yace kaga Dan Allah Malam kasakeni,zan shiga ciki ne



Bazan sakekaba,saikayimin hukunci daidai da laifin Dana aikatama



Cikin Jin Haushi yace haba! Haba!! Haba bros, mezaka fadamin Dan Allah? Yanzu ashe Har akwai abinda
zaka boyemin azamana dakai? Kai wanne irin mutum ne bros? Saboda kanasan Fatima Ina Santa ka
gwammata kakashe kanka Akan kafuto fili kasanar Dani gaskiya?

Yanzu Bayan rashin lafiyar daka kamu dashi dakasa mun rasaka wakayiwa asara Sama dani?
Aliyu yace kayi hakuri bros insha Allah bazan sakeba, hade hannayensa yayi waje daya yasake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login