Showing 3001 words to 6000 words out of 39414 words

Chapter 2 - WAZAN ZABA by Amnah El Yaqoub

14 May 2026

119

Gama, shine yayi
training din Iman tun kafin tasan kanta, yakoya mata ado da daukan wanka, basai nafadaba kowa yasan
Yanda barristers suke da Daukan wanka, haka yake ma awajan Imran,shide burinsa kawai yaganta Tasha
wanka na kece raini sufita yawonsu, bawai Dan baya Santa ba, a a kawai shi mutum ne maisan ace yau
gashi da fitacciyar mace Mai kyau da aji Kamar Iman



Daga kanta tayi ta kalli Saman falon, photonsu ne amanne shida ita, yazuba mata ido yana kallanta itama
haka, babu wanda zaice basu birgeshi ba, indai yagansu
Tana kallan pic din batasan yafutoba, Shima tsayawa yayi yana Kare mata kallo, tayi kyau cikin Riga da
wando qirar fakistan, sai mayafin kayan tayi rolling dashi,



"kona ciro Miki kitafi dashi "



Maganarsa ce tasata Juyawa da sauri, babu kunya ta Zuba masa ido tana kallansa, gaskiya babu qarya
Yaya Imran yahadu, ita kuwa wacce sa'a gareta dahar wannan gayen daya gaji dayin kyau yake kaunarta



Qasa tayi da Idanunta, Bayan tagama kallan nasa, takowa yayi ahankali Saida Yazo dab da ita, Har
sunajin hucin juna, ahankali yasa hannunsa yakama hannayenta, yayi Qasa da murya yace "kingama
kallan nawa Ko Kuma na tsaya ki kalli abinki San ranki?"



Bata Iya bashi amsa ba, domin kuwa gaba daya yakashe mata jiki da wannan maganar dayake mata me
kama da rada



Ahankali ta Bude bakinta tace am Yaya dama jiranka muke yi zamu tafi, Kar muyi missing flight



Kamar wani gaula haka ya zubawa lips dinta ido wanda yakeji Kamar yakamasu ya tsotsa



Dago Zara zaran gashin idonta tayi ta kalleshi, anan taga inda hankalinsa yafi karkata wato lips dinta



Cikin sigar shagwabar da batasan tanada itaba tace "Yaya fa!"



Sai asannan yadawo nutsuwarsa, hannayenta daya kama yariqe su ya murza ahankali, Kasa kallansa tayi
saboda Yanda takejin wani irin baqon yanayi atare da ita, batasan Cewa yafita shiga cikin yanayin ba,
ahankali yace "MURADINA please ki kulamin da kanki kinji, kada kibari wani da namiji ya rabeki dasunan
soyaiya, idan Hakan yafaru bazan yafewa kainaba, please kada kibari Hakan yafaru kinji"



Bata Iya bashi amsaba, wayarsa tadau qara, yana dagawa Hajiya tace Imran mekuke jirane? "
cikin kunya yace Hajiya gamunan, tareda kashe wayar



Kamo hannunta yayi suka futo harabar gidan, baisaki hannun nataba haka sukazo Har wajansu Billy da
Zeey, sai Kuma Farhan, Mota suka shiga dukansu, inda Farhan yayi driving dinsu Zuwa AMINU KANO
INTERNATIONAL AIRPORT



*** *** ***

GHANAH



Teemah kin zauna silent dake, Ko Har yanzu tunanin muradin naki kike? Ajiyar zuciya tasauke sannan
tace "kede bari besty nasan yanzu yanacan yana missing dina Wlhy , fari tayi da Dara daran idanuwanta
taci gaba da Cewa babu me kula dashi, Koda yake ai ga hajiyata Nan, nasan inde tana Nan banda wata
damuwa"



Billy ce ta yatsina fuska ta dubi wadda aka Kira da besty tace "kinjita Ko? Saiki rantse Akan irin wata
muguwar kulawa take bashi, Bayan Ko Iya kallansa batayi, yana fara yimata magana zakiga kanta aqasa
Kamar wani sirikinta"

Tana gama maganar ta miqe tsaye zatabar wajan, harara Iman tasakar mata, tace "Ina Kuma zakije kibar
wannan kayan, ki tsaya ki shirya mana su"



Besty ce tace haba Teemah kofa hutawa bakuyi ba, duban Billy tayi tace Kinga jeki Billy, zan shirya komai



Kallan Iman Billy tayi batace mata komai ba, kawai de ta girgiza kanta tashige toilet domin ta watsa ruwa



Itama Iman miqewa tayi tafara cire kayan jikinta, wandone gajere ajikinta iyakarsa gwiwarta, sai best yar
qarama, Riga da wandon Pakistan din data cire ta ajiyesu agefe, yusra ce ta Kalleta tace um lalle muradin
wata zai huta dayawa, irin wannan abubuwa haka
Sai a lokacin na qarewa hallitar jikinta kallo, cikinta ashafe yake, tanada manyan boobs tsayaiyu, hips
dinta abaje yake, wanda idan tana tafiya saika rantse da niyya take kadasu, Kuma Ko daya bahaka bane,
kawai hallitar ta ce haka



Murmushi tasaki tace Allah sarki muradina

Wlhy Besty Ina kaunar Yaya Imran, Har so nake muyi mugama school dinnan ayi mana aurenmu wallahi



Teemah Kenan, yanzu fa Billy tagama Cewa bawani kulawa kike bashi ba, Kinga fa karkiyi Sanya, mazan
yanzu kana basu kulawa ma Yaya aka qare, bare Kuma keda kika mallaki namiji Kamar barrister



Wlhy yusy kinsan me, sainayi niyyar inyi masa wani Abu daya shafi soyaiya sainaji nakasa, kinsanni da
karatun novel, to idan natuna abinda yake faruwa a novel shine zai faru tsakaninmu sainaji kunyarsa
wallahi, yusy tace ai kuwa Gara ma kidena, Dan shikam Kinga wayaiyan mutum ne dayakesan wayaiyar
mace



Suna wannan firar Billy ta futo Daga wanka Daga ita sai towel, Itama Iman ta miqe tashige toilet din



*** *** ***



Azaune take afalo ita kadai, less ne ajikinta launin ja, sosai yayi Mata kyau, dinkin yakarbi jikinta Kamar
ba wata me shekaru ba

Daga ganta kasan cikakkiyar bafulatana ce basai anfadaba



Wayar tace tadauki qara, tasa hannu tayi picking call din

Cikeda fara'ah tace" Hajiya maimuna yagida ya mutanan Nigeria? "



Itama Daga dayan bangaren tace" Hajiya Fatima wallahi lafiya kalau, ya Switzerland? "
Mamy da fara'arta tace Alhmdlh, ya yata Basma,



Hajiya maimuna Bata amsa mataba tace" Hajiya wallahi dama wani me maganin gargajiya ne naji yana
tallar maganin jinnu, shine nace Bari nafada Miki Ko Zaki siya ku gwada Ko za'a dace,"



Cikeda mamaki mamy tace "to yanzu Hajiya maimuna nikuma meya hadani da maganin jinnu?"



Cikeda izza tace, a a Wai Hajiya Fati kina nufin Dan wajan ki Aliyu ba aljana ce ta Aure Shiba?



Mamy tace Hajiya wacce irin magana kikeyi haka? Aliyu na Kuma?



Daga dayan bangaren Hajiya maimuna tace to Hajiya fati kekuwa idan ba aljana ce ta aureshi ba, wazaiga
mace Kamar Basma yaqita, aisaide inba me cikakkiyar lafiya ba, "



Sai yanzu mamy tagano bakin zaren, wato magana ce take fada mata saboda Aliyu yace bayasan yarta
Basma



Cikeda fishi Itama mamy tace" Hajiya aljana Bata auri Haidar dinaba, ai Aure lokaci ne, Shima wataran
zaiyi "



Hajiya maimuna batayi shiru ba tace a a Hajiya kide bincika, kinsan halin Dan yau



Mamy batace komai ba takashe wayarta, dafe kanta tayi da hannunta, koma me aka fada mata Aliyu ne
sila, wannan Yaron kode sadakarsa zata bayar ne



Ahankali yake ja dabaya yana komawa cikin kitchen, bayaso mamy tajuyo taganshi bare ma tasancewa
yaji wayar Daga gama
(bincika son thanks dinnanba, kawai inkunason injidadi Kuma kuga posting Akan lokaci kazuba min
sharhi nafijin dadinsa fiye da godia)



Har yanzu muna Kan shinfida ne, bamu nutsa cikin labarin ba



Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖



Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem



5



Kamar kullum yauma uniform ne ajikinsa saide nayau kalar blue ne, sosai kayan yakarbi jikinsa, wata yar
qaramar bindinga ce asoke ajikin aljihun wandonsa na baya

Shiru yayi yana nazarin kitchen din Kamar wanda yake neman wani Abu daban

Yanzu akansa Har abin yakai Ana Kiran mamynsa awaya Ana fada mata magana? Shikuwa wanne irin
yarone?

Ajiyar zuciya yasauke Mai karfin gaske, Daga bisani yafara magana shi kadai acikin ransa

Insha Allah nasaka araina Cewa Daga yau zansa adubamin yarinyar data dace in aura, basai naganta ba,
inde anganta Kuma halin ta yayi, to zan Aure ta domin mamy



Yana gama maganar yafuto Daga kitchen din cikin fara'ah yayi wajan mamy wadda ta rafka tagumi tana
tunanin halin da Aliyu yasata



Ta Bayan kujerar da take Kai yazagaya, yadora kansa Akan kafadarta, tanajin qamshin turarensa ta share
shi, Murmushi yasaki shi kadai

Cikin Murmushin yace mamy nah kinsan wani Abu?
Batayi masa maganaba kawai de ta girgiza kanta



Wayarsa yadauko Daga aljihun sa, data yabude yashiga Google, Bansan meya bincikaba, naga yazagayo
yazauna kusa da ita

Wayar tashi yamiqa mata, yace "mamy Kinga wannan materials din Kamar zasuyiwa qawayenta kyau
ranar dinner Ko?"



Asheqe ta dubeshi tace "wa Kenan?"



Shima Sarai yagane a kusa take, Yanda tayi kicin kicin da rai ne Daria taso kamashi

Bai Iya boyewaba Saida ya murmusa

Sannan yace "mamy matata mana, wadda nake San aura"



Tanajin Hakan tasaki ranta, harda qara matsowa kusa dashi tana kallan material din, tace "Kai Amma
yayi kyau gaskiya"



Wani irin dadi yaji acikin ransa, ganin mamyn nasa tasaki ranta



Wani less yanuna mata, yace wannan Kuma Kinga zaiyi muku kyau, keda mutananki



Wannan Karon mamy karbe wayar tayi, tace wow, gaskiya baby ka Iya zaben Kaya, Kamar kashiga Raina,
Amma de kungama dedetawa da yarinyar Ko?



Hannunsa yadora akansa yana Sosa qeyarsa yace "a a mamy Wai idan Allah yakawo"



Haidar tashi kafice kabani waje
Mamy yanzu idan akai ordering dinsu tun yanzu ba shikkenan anhutaba idan bikin Yazo



Saboda bacin rai Kasa yi masa magana tayi, kawai hanyar kofar fita Daga falon ta nuna masa



Yana shafa Lallausar sumar kansa ta fulani, yace to mamy, ankirani meeting na gaggawa yanzu, saina
dawo "



Shiru tayi ta qyaleshi



Beyi Shiru ba, yasake Cewa" kinji "



Nanma Bata kulashiba



" kinji mamy na tafi "



Dan tausayi yabata Dan haka tace" naji Haidar Ala kaika lafiya "



Daria yasaka sannan yafice Daga falon cikin takunsa na qasaita



*** *** ***



Shiru dakin nasu Kamar babu kowa aciki, kowa yariqe waya yana abin gabansa, Iman ce tasaki tsaki, yusy
tadubeta



" me akayiwa Besty nane? "

Wlhy wata shegiyace Naga tasa pic din barrister a Instagram, wallahi na tsani yarinyar Nan"
Besty tace "wacce yarinya Kuma?"



Ke babba cefa ba yarinya ce irinmu ba, kullum batada aiki saide takirashi awaya, kiji tawani maqe murya,
hello babban barrister ya gida "



Cewar Billy



Daria ce takama yusy Saida ta Dara sannan tace" Kuma Ke Iman kina gani kika qyaleta? "



Iman tace Toya zanyi yusy, yanzun nasan inda tasamu pic dinsa, bashi yabata ba



Billy tace a a Yaya Iman karkiyiwa Yaya sharri, dagake harshi takanas kuke Zuwa wajan photo ayi muku,
kawai na dorawa a dp ne, Kinga kwa aikonice tunda Naga Ana sakawa dole nadauka, ni wallahi innice
Itama Bayan nasa pic din saina rubuta my fiance to be



Dallah malama kiyiwa mutane Shiru, Kamar antambayeki sai wani zuba kike

Cewar Iman



Yusra ce takatse musu zancen dacewa, Kai Kai Iman Billy kunga wani video danagani yanzu a net

Wallahi wasu sojojine suke karya kafar kidnappers

Suko Imani ma basu dashi ne Besty

Tafadi maganar tana duban Iman



Billy ce tace Kai Kai bani nagani yusy, tasa hannu ta karbe wayar Daga hannun yusy



Cikin Jin Haushi da bacin rai Iman tace yusy, Dan Allah idan zakuyi haukanku kudena sani aciki
Ke waye yafada Miki sojoji mutane ne?



Billy tace to Yaya Iman sudin aljannu ne?



"ni bance Miki aljannu bane, kawai de ni arayuwata Bana qaunar soja, kokadan basa birgeni "



Yusy tace Toda Imran dinki soja ne Yaya zakiyi?



Bana fatan haka Besty, wataran kana zaune acikin gida za'ayi sallama dakai amiqama takarda, kana
budewa zakaga sunan mijinka yafada cikin wadanda suka mutu awajan yaqi"



Yusy tace tab wallahi kuwa hakane



Billy tace ni dama Haroon daba wani kulawa yake bani ba, inda ace soja ne ai nabani



Ai wannan Haroon din naki sai aslow, Cewar yusy



Wallahi ni na matsu ma exam dinnan ta qare nakoma gida kusa da anty na

Wallahi nayi missing dinta, inji Billy



Iman tace eh dole kiyi fada da Haroon, wato shi bakiyi missing dinsa ba,



Billy tace share shi Yaya Iman



"ai Nima sonake mugama aranar nakeso mugudu 9ja, tadubi yusy tace Besty ai Kema zakije Ko?
Yusy tace Anya kuwa zani, one week nefa zamiyi mukoma wata semester kawai zan zauna, basai najeba
"



To Allah yakaimu Cewar Billy



*** *** ***



Dakin taron nasu ya tsaru matuqar tsaruwa, dukanninsu kaki ne ajikinsu , gaban kowa akwai lasifika
wadda aka rubuta NTA ajikinta, da alama duk abinda suka tattauna awajan kai tsaye yana tafiya ne
akafar sadarwa ta nta, daga saman aljihun rigar kowa naga anrubuta sunan kowa ajikin tasa rigar, shine
kawai yake zaune akan babbar kujerar dake nuni dacewa shine shugaba awajan,shima gaban rigar sa
ansa ALIYU SA'AD bayan qaddamar da bayanai dasuka gama , aka miqo masa wata takarda , umarni
yabayar abude takardar akaranta



Wanda yagama karantawa ne yayi bayani akan takardar , takarda ce qasar ghanah taturo musu , suna
gayyatarsu meeting na kwana daya akan dedeto dakuma zaman lafiya tsakanin Nigeria da Ghana



Goshinsa ya dafe da hannunsa

"Yazasu turo mana wannan takardar bayan sunsan bama qasar, yanzu haka muna wajan seminar ne?"



Wanda ya karanta dinne de , yace"Sir ai 1week suka nema muyi da farko, bayan anyi musu bayani ne
suka rage yakoma 1day saboda ansanar musu muna bakin aiki"



"Ok toba damuwa "



na gefensa yaduba sannan yace"jiragenmu sun zama ready ne?"



Eh sir
Toshikkenan, ashirya mana tafiya zuwa next week insha Allah"



Dahaka meeting din nasu yaqare



*** **** ***



Azaune take afalo remote ne ahannunta , Atika ce azaune aqasanta tana matsa mata qafafu

Hankalinta yana kan tv tace "kai Atika nagaji da zaman wannan qasa wallahi"

Dariya atika tasa tace Tab ai mamy nikam bangaji ba wallahi , kofa sati biyu bamuyiba, ai banqi ace muyi
zamanmu anan ba"



Mamy tace lalle atika bakisan dadin gidaba, atika kowa yabar gida ai gida yabarshi"

Banda ma jaraba irinta haidar ai da yabarmu agida



Atika tace a a mamy wallahi gara da mukazo , ai ko yanzu nikam nahau jirgi



Dariya tabawa mamy , danhaka tayi mata murmushi kawai



Lemo ne ahannunsa na gwangwani , rigar jikinsa amless ce sai wando gajere iyakarsa gwiwarsa, sai yau
naganshi cikin qananun kaya, kullum cikin kaki yake



Farar fatarsa saita haska acikin kayan, kamar ba hausa fulani ba, yana zuwa ya ajiye lemon hannunsa
aqasa ya kwanta akan kujerar tareda dora kansa akan cinyar mamy



Atikace ta kalleshi ta qasan idonta

Aranta tace shide wannan kullum kamar qaramin yaro, garama yayi aure ko mamy ta huta da wannan
shagwabar
Shafa kansa tayi tace baby ya akayi, kallanta yayi yana daga kwancen yace mamy tafiya takamamu zuwa
ghana



Murmushi tasaki tace kamar kasan kuwa yanzu nake cewa nagaji da zaman wannan qasar, kaga
shikkenan daga nan saimu wuce nigeria



Murmushi yasaki wanda yasa gefen kumatunsa suka lotsa (dimple)



Yace mamy ai yanzu kuka fara zama kuwa, kwana dayafa zamuyi aghana mudawo , bawani daukan lokaci
zamuyi ba"



Kiyi hakuri mamy banasan abinda zaisa kiyi nesa danine shiyasa



Aikuwa dole kayi nesa dani baby tunda zakayi aure,



Kuma dan zanyi aure mamy shikkenan saina rabu dake

Haba mamy aiko nayi aure ina tare dake



Murmushi tayi tace to Allah yasa baby



Amin mamy nah, amma mamy yunwa nakeji



Tashi kaje kazuba da kanka kaci,



Cikin shagwaba yace haba mamy , haba mamy
To haidar idan kaji haushi kayi aure mana



Baice mata komai ba, yadubi atika fuska babu alamun wasa yace"ke tashi kibamu waje"



Tunma kafin yarufe bakinsa atika tabar wajan, saboda tasan shi da mugunta tsaf zai iya maketa



*** *** ***



Wow teemah gaskiya kinyi kyau ba qarya, rabonda ki tsatso wannan kyan kin dade



Manyan idanuwanta ta juya tace "kekuwa yusy ba gara inyi kwalliyaba, zanje naga MURADINA



Billy tace nikam gaskya katsina zan wuce , bazan shiga kanoba



Iman tace ki gaida anty da baba , amma nikam sainaga Hajiya hankalina zai kwanta



Yusy ce ta yafa mayafinta, tace kutashi mutafi



Sunyi kyau gaba dayansu , billy abaya tasaka tayi rolling da dankwalin abayar



Iman kuwa riga da wando tasaka , kayan sun amshi jikinta, hips dinnan suncika fam acikin wandon jeans
din data saka, sai riga data saka fara me adon Dark blue agaban rigar, dukiyar fulanin masha Allah
gasunan



Sai doguwar riga data dora akai after dress me kalar dark blue itama, zare ne agefen rigar , hannun rigar
kuma baza gareshi , sai stone da aka diga ajikin hannun rigar
Zaren rigar takama tadaureshi acikinta, sai wani shegen takalmi data saka me tsini, batayi kitso ba, kawai
kama dogon gashin kanta tayi tadaure, batayi rollinga kawai dankwalin after dress din ta yafa, jakarta
takama tanaja suka fita daga hostel din nasu



Suna fita mota suka tare direct takaisu Airport



Suna shiga cikin Air port din suka gama abinda zasuyi , suka zauna awasu kujeru agefe sunata firarsu
tareda yusra datace bazata tafi ba saitaga tashinsu



Iman ce tatashi tsaye tace bari inje can insiyo ruwa nadawo



Bata dade da tafiya ba tadawo hannunta dauke da ruwa da chesee



Ruwan tabasu , itakuma tabude chesee din tafaraci tana daga tsayen



Adede wannan lokacin shikuma yashigo cikin Airport din tareda rundinarsa



Yayi masifar kyau cikin kakinsu na sojoji

Yau harda hular yasaka akansa



Already sunada jirginsu , so babu abinda zai jira kawai tafiya zasuyi sukoma Switzerland tunda sungama
meeting din daya kawosu



Wayarsa ce tayi qara, yatsaya yana magana cikeda aji



Juyowar dazaiyi yahangeta atsaye tanacin chesee
Daskarewa yayi atsaye , ga waya ahannunsa yana magana amma yayi shiru



Danqaramin bakinta yake kalla yanda take juyashi



Kamar wani abin arziqi take ci



Yusy ce tace kai teemah kinga wasu sojoji can, inama zani gida kuma ace jirgi daya zamu hau, yasin dasai
munyi selfie indora a Facebook yanzu zakiga anaban girma



Hararar yusy tayi , tace kesuka dama, nikan basa gabana can dayawarsu



Billy ce tadagakai ta hangesu , itama daga kallan farko bata sake yimusu na biyu ba



Sir ga waya ana kira daga nigeria



Sir!

Sir!!



sai alokacin ya kalli musty dayake bashi wata wayar



Dayar wayar datake hannunsa yakatse batare daya gama maganar dayakeba



Qasa qasa yayi da murya yace Musty katse wayar nan in nunama abinda nagani



Kallansa mustapha yayi da mamaki, yace meke faruwa ne?
Da hannunsa yanuna masa iman datake tsaye, yace"kai kaga wata sura"



Masha Allah kawai mustapha yace, sannan yaci gaba dacewa

Gaskya tayi, ba qarya tahadu, kuma abinda zaka duba shine komai yaji, musanman breast dinta, kana
son mace maishi



Cikin kishi ya dakatar da musty da fadin"kuma menene abin maimaitawa, sai wani zancen breast kake,
matar dazan aura cefa insha Allah



Dariyace takama musty , kawai daga ganin yarinya shikkenan harta zama matar dazai aura



Dariyarsa ya gintse, gudun laifi awajan abokin nasa



"Idanunsa yana kanta yace amma kuma musty meyasa zatasa wannan kayan tafuto waje, dubafa dan
Allah mutane sai wani kallanta suke, aida saitasa hijab ko?



shide musty dayake dariya qasa qasa yace inaga ba halinta bane hakan, yanzu ne kawai tasaka



Qasa yasakeyi da muryarsa yace kafadawa daya daga cikin sojojin nigeria dasuke zaune anan ayimin
bincike akan yarinyar nan, akawomin komai nata nanda jibi



Cikin serious mustapha yace angama sir

Ga wayar taka, yabawa Aliyu wayar , shikuma yajuya yana fadawa wani soja dayamusu rakiya zuwa
Airport saqon Aliyu, tareda nuna musu su iman dasuke tsaye



Murmushi yasaki, dayaga me kiran nasa daga nigeria, yana dagawa yace tuba nake bros , inadan wani
uzuri ne shiyasa nayi rejecting call din naka, dakatawa yayi da magana yana sauraron dayan bangaren
Bansan meyace masaba naji haidar yace a a karka damu ai ABIN BROS NA BROS NE



Yana wayar yajuya yasake kallan iman da batasan dashiba, sannan yatafi sojoji suna take masa baya



Suna tafiya, iman tajuya takalli inda yusy tace mata ga sojoji nan hankalinta ne yakai kansu, saide
alokacin sunbasu baya sun riga dasun tafi, sai bayansu tagani



Juyawa tayi taci gaba dacin chesee dinta



(Tofa yanzu chakwakiyar tafara,😱

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login