Showing 39001 words to 39414 words out of 39414 words

Chapter 14 - WAZAN ZABA by Amnah El Yaqoub

14 May 2026

118

ka kashe yar mutane Ko?



Kunya ce takama shi, tuni ya sunkuyar da kansa, yace mamy kiyi hakuri



Tace a a bani zaka Bawa hakuri ba, idan tatashi a baccin akwai abinci da paracetamol kabata tasha,
Amma nafadama karka sake irin wannan gangancin



Kansa aqasa yace to mamy



Tana tafiya yashiga cikin dakin na Iman, tana bacci, Idanunta sun kumbura, alamar tasha kuka, yasan
Cewa tabbas yabata wahala,

Amma Yaya zaiyi? Shima ba'ason ransa Hakan ya kasan ce ba



Zuba mata ido yayi yanashi mata albarka cikin ransa



Yana zaune harta farka, dasauri yatashi yace matar Aliyu me kikeso?



Saida ta yatsima fuska tace Yaya ciwo nakeji Har yanzu awajan



Cikin tausayawa yace kiyi hakuri insha Allah zai daina Ahankali kinji? Daga masa Kai tayi



Key ne yabata yace gashi Fatima



Kallansa tayi tace key ne fa Yaya na menene?
Sabuwar motor Dana sake Miki ce, Itama Bilkisu nasa antura mata Tata kano dazu



Cikin murna tasakar masa kiss akumatu tace wayyo Yaya Mungo de sosai



No nine d godia ai, abinda kika bani Daren jiya yafimin komai, Allah yayi Miki albarka



Cikin kunya tace amin Yaya



Muje kiga motor Ko? Gatanan a waje



dingisa kafarta tafara zasu fita, yace nahutar dake, yasa hannu ya dauketa cimak suka futo taga motor
sannan suka dawo ciki



*** *** ***

After 4 year's



Momy yaushe zamu tafi gidan su Haidar?



Iman t kalli yar Tata yar shekara hudu tace Bilkisu gobe zamu tafi dukanmu harda mamy ma



Cikin murna tace yeeee tafice da gudu



Aliyu dake aiki a computer yadago kansa yace Suma dazu dazu suka kirani Wai yaushe zamuje nace
musu gobe de muna nan Kan hanya insha Allah, nafadawa Bros ma kowa yazama cikin Shiri da munzo
next week zamu wuce Saudia gaba dayanmu
Kanta ta Dora akafadarsa tace to mijin Fatima, Allah yakaimu, Mungo de Allah yaqara budi, kissing dinta
yayi yace amin matar Aliyu



Gidan Aliyu Kenan, inda suke gudanar da rayuwar su shida mamy da Iman, sai babbar yarsu yar shekara
hudu Mai sunan Bilkisu, da Kuma qanin ta Mai sunan Imran Suna kiransa da Lil Imran



Suma akano haka abin yake, Bilkisu nada Yara biyu maza, daya sunan Aliyu anace masa Haidar, sai qanin
sa Kuma maisunan mahaifin Aliyu Sa'ad Ana kiransa da boy



Haka rayuwar su take gudana cikin kwanciyar hankali da kaunar juna



Tammat bi hamdullah



Anan nakawo karshan wannan littafin nawa Dan karami Mai Dan Karan dadi😂😃😂



Mutara asabon novel Dina Mai Zuwa insha Allah, Allah kabamu ikon yin amfani da abinda yake Mai kyau
acikinsa, kuskuren danayi aciki, Allah kayafemin🙏🏻



Taku Har kullum



Mrs Usman ce
✍🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login