Showing 6001 words to 9000 words out of 39414 words
anya kuwa Haidar bai debo sama da zafi ba😱😱 ????
(Waima wacece iman ne?nasan mai karatu yanaso yaji wacece wannan iman din da ake magana akanta,
to kubiyoni danjin wacece iman)
Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
6
Lokaci Nacika sukai sallama da yusy suka tafi
Zuciyar yusra daya tafita tatare taxi saide abinda Bata saniba shine akwai masu bibiyarta Abaya, Saida
sukaga shigarta hostel din sannan suka tsaya wajan masu gadi
*** *** ***
Karfe biyu nadare flight dinsu yasauka, direct Daga Airport Mota ce ta daukesu tamaidasu masauqinsu
Shima gida aka wuce dashi
Yana shiga Shiru gidan kowa yayi bacci, baiyi gigin tashin mamy ba, dakinsa ya wuce yafada Kan gadonsa
Saman dakin yazubawa ido yana kallo, saide azahiri idonsa ne awajan, ruhinsa da tunaninsa Suna gareta
Gaskiya Allah yayi baiwar komai da komai awajan
Ashe a wannan zamanin zaka samu mace haka, wata Zuciyar tace dashi Har fin hakama Ana samu
Tokodan baya shiga sabgar yanmata ne shiyasa Bai hadu da irinta dinba
Kozata Soni? Yake tambayar kansa
Wani bangare na Zuciyar sane yarinjayeshi Akan Cewa ai bashida aibun dazata qishi
Harya matsu lokacin daya Diba su cika domin yaje ya tunkareta gameda abinda yakeji acikin ransa
"To Allah yasa de tasoni"
yafadi Hakan afili cikeda Alhini
Tashi yayi cikin nutsuwa yacire takalmin sa tareda kakin jikinsa yashiga wanka
*** *** ***
Zeey yakamata Musa Yaya yakaimu saloon Ko?
Kanta yana kan cinyar Iman, tace "Eh anty Daga Nanma saiki kaini wajan wasa, ki siyamin Ice Cream, da
sweet"
"a a Zeey, abin Yamin yawa, bazan iyaba, Daga zancen saloon saiki ta jeromin wannan abubuwa haka "
Fizge kanta tayi Daga hannun Iman tayi wajan Hajiya dake zaune tana kallansu
" hajiya Kinga anty Wai bazata saikin sweet ba "
Cikin fada Iman tace yes fadi da ihu yarinya bazan siyaba
Itama cikin hawaye tace dama bakizo ba anty Bilkisu kawai tazo, kekwa ki zauna a school, dog ya cinyeki
Ba Iman kadaiba hatta Hajiya ma Saida tayi Daria, ta janyo zainab jikinta tace Rabu da anty Iman, yanzun
Nan zankira Miki Bilkisu awaya tataho Daga katsina takaiki duk inda kikeso
Washe bakinta tayi, tayi cikin daki dagudu tana murna
Falon yashigo yayi masifar kyau cikin qananun Kaya, agogon dake hannunsa, Yazo dab da ita yazauna
Akan hannun kujerar datake Kai, Kasa yayi da murya yace "muradina zan fita Ko akwai abinda kikeso?"
Hajiya tana kallansu ta gefen idonta, wannan rashin kunya tafara isarta, garama Iman tayi tagama school
dinnan ayi musu Aure Ko sa huta
Itama Ahankali tace masa Saloon suke San Zuwa itada Zeey
Sai a lokacin yadago Daga sunkuyawar dayayi yanayi mata magana
Daga murya yayi yakira Zeey, ai kuwa aguje tataho ta rungumeshi
Yace yanmatana jeki futo muje wajan saloon keda anty Ko?
Saida tayiwa Iman gwalo sannan tajuya ciki da gudu
Tana futowa sukai wa Hajiya sallama data nuna Kamar Bata ganin su
Suna fita tabisu da kallan birgewa, hannu ta Daga tace Allah ka qara hademin Kan yarana Amin
*** *** ***
A dinning suke zaune mamy nacin abinci taga sai juya abincin yake, kallansa tayi da mamaki tace Baby
me yake damunka ne?
Babu tunanin komai yace "mamy akwai aikin Dana bayar ne Bansan asamu matsala aciki"
Spoon din hannunta ta ajiye tace "to menene abin damuwa, kayi hakuri insha Allah babu matsala kaji?"
Cikin sakin fuska yace to mamy
Yauwa baby nah ci abincin ka
Nan take ya ware yana cin abincin, Amma cikin ransa adduah yake Allah yasa angama binciken da za'ayi
Akan yarinyar Nan
Suna gamawa yace mamy zanje nadan motsa jikina, yafice Daga falon
Yana harabar gidan yana motsa jiki Amma tunani yahanashi yin abin kirki
Towel din dake gefen sa yadauka ya share zuffar dake zubomasa
Huci yayi, tare da firzar da iska Mai zafi Daga bakinsa, yajuya yadanna wayarsa Ko zaiga Kiran musty,
nanma Shiru
Haka ya hakura yayi dakinsa tareda shigewa wanka
Har dare yakasa fita Ko Ina yana zaune a daki yana aikin tunani, Wai wannan wacce irin masifa cene?
Dama haka masoya sukeji? To ai Har Gara masoya ma sunsan sun furtawa junansu so, to Amma shifa Ko
yarinyar ma batasan yanayi ba
Kasa hakuri yayi yadau wayar sa yakira Mustapha, bugun farko Mustapha yadauka yace sorry sir gani
Nan a hanyar Zuwa gidan
Batare dayace komai ba yakashe wayar, yafada Kan gadonsa tareda runtse idanunsa
Ba'a dauki lokaci Mai tsawoba musty yashigo gidan, Saida suka gaisa da mamy sannan yayi dakin Aliyu
Yana shiga qamshi hadeda sanyin esi suka bigeshi, qarasawa yayi Kan gadon yazauna yace" Sir gashi
angama komai"
Yanajin haka ya Bude idonsa yace "musty kadameni da wannan sir din wallahi, Dan Allah ya Isa haka,
haba!
Saida yagama mitar tasa sannan yace" bani"
Takarda yamiqa masa yace Nima sai dazu suka turomin ta email Dina, to da zan turoma ta Email din
saina fasa naje aka ciro ta yanzu
Yana gama magana yamiqe Yace "to abokina saina dawo latter naji bayani, Dan yanzu aiki nake nataso"
Batare daya kalleshi ba yace kaide kawai Kace guduwa zakayi babu wani aiki
Da gaske nake, madam tayi kirana, zan dawo Zuwa gobe
Kansa kawai yakada masa Batare daya yarda da maganar ta Mustapha ba, kawai de yasan Cewa yabashi
dama ne yakaranta abinda yakawo masa
Mustapha nafita ya gyara zamansa a Saman gadon yabude takardar tareda karantawa cikin ransa
Wacece Iman?
Sudin cikakkun shuwa Arab ne dasuka Tashi agarin maiduguri, mahaifiyarta da dangin mahaifiyarta
dukkansu maiduguri ne tushan su
Asalin Sunanta shine FATIMA SHU'AIB Amma Ana Kiran ta da (Iman)
Tanada yar'uwa Bilkisu wadda ta kasan ce Shiru Shiru marar magana, komai nasu daya ake musu,
kasancewar su Kamar wasu twince, tare suka fara makaranta tun Suna Yara, Bilkisu nayiwa yar'uwarta
biyaiya,hakane yasanya take Kiran ta da Sunan YAYA IMAN, saide Iman akwai ta da tsiwa, Tanada San
girma, akomai tanaso taga qanwarta Bilkisu tabata girma
mahaifinsu cikakkan bahaushe ne Dan asalin jihar Katsina Garin Funtua
Yanzu Iman tana matakin gama degree dinta na farko ne Aqasar Ghana itada yar'uwarta Bilkisu, saura
Semester daya su kammalla karatun su
Inda suke Karatun bangaren likitanci Ajami'ar KWAME NKRUMAH UNIVERSITY OF SCIENCE AND
TECHNOLOGY
saide abinda ba'a saniba shine Bilkisu tana hannun mahaifinsu ne a katsina, ita Kuma Iman tana hannun
Mahaifiyarsu ne agarin kano
Anyi musu hutun semester ne na one week shine suka shirya tafiya gida hutu
___________
Ajiyar zuciya yasauke daya gama karantawa, idanunsa yakai kasan takardar yaga number wayarta
dakuma sunayen datake amfani dasu ashafukanta na yanar gizo
Baiyi qasa agwiwaba ya adana komai nata acikin wayar ta hanyar saving
Yana saving number ta yaga dashi take whatspp sannan ya tafi shafinta na Facebook da Instagram, anan
yaga ruwan pictures dinta, domin kuwa Iman takanas barrister yake daukanta suje ayi musu pic, da
Hakan take amfani wajan Dora Iya nata ayanar gizo
Afili yace "wannan yarinyar me yake damunta ne take dorawa Dunia pictures dinta?"
Dan qaramin tsaki yasaki yasake Cewa yanzu haka kowa yadauka "
Saving din pictures din nata yayi dayawa, sannan yakashe datar sa
Bama wannan ne damuwar ba, menene yasa sister nata take zaune ahannun babansu?
Dole ne gobe yanemi Mustapha domin qarin haske Akan Hakan
Photunan ta yaci gaba da kalla, dazaran yaga wannan zai koma Kan wani yayita kallah,
Bai Tashi ganin lokaci ba sai gani yayi dare yayi sosai, Dan haka yayi adduah ya kwanta domin yanaso
gobe da sassafe mamy taji daddadan labari
*** *** ***
Next day
Yana Tashi Daga bacci yashiga wanka, Kamar kullum wando yasaka three quarter
Sai rigar jikinsa wadda ta kasance marar hannu
Shi kansa jinsa yake cikin nishadi, Kuma yasan Hakan baya rasa nasaba ne da wannan yarinyar
Wai a hakama Bata fara bashi kulawa ba, to inaga sunyi Aure Kuma, Ko menene zai kasance?
Kiran musty yayi awaya yana dagawa yace "kazo gida ka sameni, akwai sauran abinda ban ganeba game
da yarinyar Nan"
Daga dayan bangaren Mustapha yace eh dama Ina Kan hanya gani Nan Zuwa "
Yana kashe wayar, cikin galary dinsa yashiga, yafara duba pictures dinta, fridge yanufa yadauki lemo
yariqe ahannun sa Batare daya fara shaba yaci gaba da aikin kallan ta
Anya kuwa dayasan yarinyar Nan bazaice ba kalau tabarshi ba? Daga ganin ta yashiga irin wannan
yanayi?
Yana wannan tunanin Mustapha yashigo dakin, yana zama Haidar yabashi labarin komai, yaci gaba da
fadin
Amma abinda bansaniba shine meyasa basa zama waje daya itada yar'uwarta?
Mustapha yace ni aganina kawai ashare wannan maganar Daga baya idan kun dedeta zaka San komai
"eh hakane Musty, Amma gaskiya inasan yarinyar Nan, banajin zan Iya rabuwa da ita, bantaba tunanin
zanso wata yarinya Har hakaba
Murmushi Mustapha yasaki yace ai kaima ba bayaba abokina, nasan insha Allah za'a dace
"to shikkenan Musty, saimun sake waya, zan shiga wajan mamy, Dan Ko break fast banyiba
Hannu musty ya miqa masa suka sake gaisawa sannan ya tafi
Sai wani walwala yake shi kadai, yanata fara'ah, atika ce tafara ganinsa, a ranta tace to yau Kuma me
akayi masa
Kamar qaramin yaro yana Zuwa yazuba ajikin mamy,
Kai Haidar narasa yaushe zaka girma, wannan ai saika karyani
Atika dake gefe tace cikin ranta uhm yaushe zai girma kuwa kullum Ana ce masa baby
Cikin farin ciki yace "mamy albishir"
"goro fari Haidar "
Yaune Karo na farko dayaji nauyin fada mata magana, kodan maganar Tanada alaqa da Zuciyar sane
Qasa yayi da kansa yace" mamy yaude kinsamu in law"
Baby idan wasan daka saba minne, please kadena "
" mamy da gaske nake, inasonta, Kuma so na Aure, gaskiya mamy idan ban sametaba akwai matsala,
meeting din danaje Ghana acan naganta, Amma Har yanzu banyi magana da itaba, sonake sai kinganta
tayi Miki tukunnah "
Wayarsa yadauko yashiga cikin pictures dinta, yabawa mamy wayar yaci gaba da fadin" mamy
Kingantafa "
Tana ganin photon gabanta yafadi, meyasa yarinyar take mata kama da ZAINAB? babu banbanci sak
photo copy din zainab ce
Amma saitayi tunanin may be kama ce kawai
Haidar yanajinta tayi Shiru yace mamy yakika ganta, tayi Ko batayiba, idan Bata Miki ba asake wata
Jijjiga kanta tafara sannan tace Gaskiya Baby wannan maqiyinka ne kawai zaice ma batayiba, but
tanamin kama da wata mata
, ita wannan yarinyar a'ina take?
"mamy akano take wajan mahaifiyarta, "
Jin wannan amsar da Aliyu yabata yasa Zuciyar ta yarda Cewa ba wadda take nufi bace"
Daga murya mamy tayi tace atika zonan
Atika nazuwa mamy ta nuna mata pictures din Iman tace Kinga budurwar baby, yaude gori yaqare "
Atika nagani tace Kai masha Allah, wallahi mamy saikace balarabiya
Dukansu Daria sukayi
Yau Atika saboda anga waje, taganshi yana farin ciki, akace, Kuma ya sunanta?
Kai tsaye yace sunan mamy nah gareta, Fatima, Amma Iman ake cemata
Mamy tace masha Allah, gaskiya yarinyar tayimin, Allah ya tabbatar da alkhairi, kafada mata da Aure
kakesanta bakasan abin yadau lokaci idan tana sanka
Sunkuyar da kansa yayi yace to mamy
Mamy am hungry
Atika ta kallah da sauri tace maza atika kawowa baby abinci nabashi
Shikuwa saboda farin ciki harda Dora kafa daya Kan daya, yau Mamy zata bashi abinci da kanta, yaushe
rabo
Dakanta taciyar dashi, yanaji yaqoshi yayi dakinsa domin Kiran Iman awaya
(waishin wacece wannan zainab din? 😏😏
Anya kuwa Kuna ganin Iman zata amince da Haidar? 🙉🙉🙉🙉
To kubiyoni de fatana ku nishadantu da wannan labari
(Ayau Ina farin cikin sanar da fan's Dina Cewa zaku dinga Jina kullum, Kamar Yanda nasaba yi muku
Abaya, dama nadan samu matsalar waya ne)
Mrs Usman Ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
7
Tunda yakoma dakinsa yakasa zaune yakasa tsaye, saiya dauki wayarsa zai kirata saiya fasa, yayi Hakan
yakai sau biyar, to idan yakirata me zai fada mata?
Gyaran murya yayi, yafara gwadawa shi kadai agaban mirror yana kallan kansa
Sunana Aliyu Sa'ad Bilal Ina sonki
Girgiza kansa yayi, "no Hakan baiyi ba"
Salamu alaikum, Am Sunana Aliyu Haidar, dama naganki ne a airport shine nake sanki
Tokuma idan tace nikuma Bana sanka fa, girgiza kansa yayi, Allah ma yakiyaye
Qara gyara tsayuwarsa yayi, harda gyara wuyan Rigarsa, sannan yace "Ni Sunana Haidar, ni soja ne,
nadade Ina neman matar Aure bansamu ba, Saida naganki shine kawai Nima naji Ina sonki
Wata Zuciyar ce tace dashi, wato kace mata kadade bakayi Aure ba, Daga Nan Kuma sai tace dama
kwantai kayi shiyasa ni kazo wajena
Dayawan mata ba'a cika birgesu ba idan kahadu da ita gani na farko ka baiyyana mata sirrin dake ranka,
wasu matan sunfi son saikun fahinci Juna tukunna kafin ka baiyyana musu sonka atare dasu
Ajiyar zuciya yasauke, yanemi waje yazauna
Afili yace gaba dayama bazan fadi Ko dayaba, kawai zanbi shawarar mamy, datace nafada mata Cewa da
Aure nake Santa
May be Tunda Nabi shawarar mahaifiya saina dace
Da wannan shawarar yayi amfani wajan dauko wayarsa yabude data, Kai tsaye whatspp yahau
Yaduba number dinta, yatura mata da "hi"
Kuma sai akai dace adede lokacin tana chatting ne da yusy
Ganin sabuwar number taturo mata da hi, Kuma gashi batasan number dinba, hakanne yaja hankalinta
wajan Bude saqon
Yana ganin alamun an Bude saqon yazuba tagumi yace to Allah gamu gareka
Kai tsaye tatura masa tambaya "waye?"
"Sunana Aliyu Sa'ad "
Afili ta furta Aliyu Sa'ad Kuma?
Waye Hakan?
Tambayarsa tayi Cewa" waye?
Kuma wakake nema?
Yace "ke nake nema"
"kasan dawa kake magana kuwa? "
Shima anasa bangaren yatura mata Cewa" da Yaya Iman "
Mamaki ne yakamata, to wannan duk Yanda akai may be yasanta sosai, Tunda Har yasan ta da wannan
sunan
" me yake faruwa?
Abinda tatura masa Kenan
Shima yace "inasan nakiraki idan kin bani damar Hakan"
"no, kafadamin menene, Bana buqatar Kira "
Afili yafurta" tofa"
Achat din saiya tura mata Cewa, "Sunana Ali Sa'ad Bilal, Kamar Yanda nafada Miki, Ina aiki ne tareda
Rundunar sojan Sama ta Nigeria, naganki ne aghana, inason na Aure ki"
Daria maganar ta Bata, Saida Tasha dariyarta, Afili tace wannan wanne irin mutum ne? Kuma ma Wai
soja, Anya kuwa yasan Yanda ta tsani sojoji, kwata Kwata basa birgeta
Amma acht saita ce masa 'thank you "
Shikuma yarasa me zai fada mata, Kenan Bata sanshi ne kokuma tana sanshi, me wannan thank you take
nufi
Tambayarta yayi, Zaki Iya Aure na?
Itama tatura masa Cewa bansankaba, bantaba ganinkaba, kawai Daga haduwa a cht sai in amince inyima
alqawarin Aure?
Kansa yashafa, zuciyarsa tafara daukar zafi, gabansa na faduwa yace mata, ga pic Dina Nan a dp, ki duba
Abangaren Iman kuwa mamaki ne yake sake kasheta a zaune, wannan wanne irin mutum ne? Kana
neman Abu a wajena Amma aji za'ace kokuma girman Kai yahanaka yin biyaiya
Wato pic dinma bazai Iya turo mataba, saide ita tabude, inta matsu
Shikuma anasa bangaren Bai fadi Hakan dawata manufa ba, shide na farko Bai saba hulda da yanmata
ba, bare yasan abinda suke so Ko abinda basa so, sannan shi aganinsa atsaya Ana wani kece farin cikina,
kace kaza Dina, duk ba abin birgewa bane, shi yafi San idan kana San Abu, toka nuna abaiyane Kuma
agaban kowa
Abinda yasani shine Allah yadasa masa soyaiyarta acikin Zuciyar sa Yanda baya zato
Iman batayi qasa agwiwaba tabude pic din Naka
Photo ne dayayi shi acikin jirgi, yana gefen window, da farin kaki ajikinsa na sojan Sama
Saving pic din tayi a wayarta, sannan tace masa Amma Kai fulani ne Ko?
Sai a sannan yayi dariya harda gyara zama ganin tafara kulashi, yace no, babu wani fulani, ni bahaushene
dan'uwanki
Itama tatura masa Cewa ai ni ba bahaushiya bace
Yace sorry namanta, ashe fa ke Shuwah ce
Afili tace Wai wannan mutumin ya akai yasan abubuwana dayawa ne?
Bata bashi amsaba yace nabaki dama kiyi bincike akaina, Kuma kiyi tunani idan Zaki Iya Aure nah, Ki
gaida Bilkisu Bye
Yana gama tura mata yasauka online
Gaba dayama tarasa tunanin mezatayi, wakuma zata fara tunkara da wannan magana? Billy batanan
tana katsina, Amma ga yusra Nan ai Suna chatting Bari tabata labari
Ta chat din takira yusy tace Besty akwai labari, yusy tace Kai Teemah saboda tsabar gulma Akan ki
turomin saikin kirani
Iman tace inaa ai babban labari ne yafi karfin chat
Yusy tace to qawata bani Nasha
Iman ta kwashe komai tafada mata, harda pic dinsa ma duk tatura mata
Yusy tace 'Besty Anya kuwa ba qarya yake Miki ba? Ba irin samarin unguwa bane Yan renin sense?
"Nima abinda nayi tunani dafarko Kenan Besty, but abinda zai baki mamaki shine harfa Bilkisu yasani,
Wai harda Cewa Yaya Iman, sannan Wai ni Shuwah ce
Yusy tace to yanzu yaza'ayi?
Nikam yusra ai ban Isa in saurari waniba, Bayan ga Yaya Imran, Kinga wannan pic din nasama Ina turo
Miki nagogeshi a wayata, gudun matsala, Wai harda Cewa aghana yaganni, inba qaryar mazaba aghana
a'ina? Muda ba yawo mukeba
Yusy tace a a karkice komai, Tunda yafadi Hakan nasan ba zaiyi qaryaba, Tunda naganshi babba ne,
yanzu abinda za'ayi shine Tunda yace kiyi bincike akansa, kiyi din mugani waye shi
Nifa ba zanyi wani bincikeba yusy, kawai zan bashi hakuri in fada masa inada wanda zan aura
Yusy tace karkiyi haka Iman, bahaushene fa yace so Mai sonka, ke zakiji dadi idan Allah yadora Miki son
wani daban, ki tunkareshi kifada masa Amma aqarshe irin wannan amsar tabiyo baya?
Ki lallabashi ku Rabu lafiya, ni aganina hakanne mafita, Kinga kun Rabu lafiya, Shima beji haushinki yaje
ya dirka Miki wani asirin ba
Tanajin zancen asiri tace na shiga ukuna
Yusy tace a a bafa Cewa nayi zaiyi Miki asiri ba, kawai de nafada Miki abubuwan dasuke faruwa ne
gameda wasu samarin idan kace Baka kaunarsu
Cikin sanyin jiki Iman tace to yanzu Yaya zanyi?
Yusy tace menene sunansa?
Kai tsaye Iman tace yacemin sunansa Aliyu Sa'ad, Kuma shidin sojan samane na Nigeria
Yauwa Kinga saimu bincike mugani inma qarya yake ai zamu gani, inji yusy
Iman tace to tayaya zamu bincika?
Yusy tace kadaa ki kashe wayar Bari naduba sunayen sojojin Sama a Google nagani, inma babushi ai
zamu gani
Iman tace toyi sauri Ina jiranki
Yusy batafi minti biyar ba tasaki ihu ta cikin wayar
Iman tace Besty karki kashen kunne, yusy tace Iman wallahi Ina searching sunansa naganshi, shine
shugaban sojojin Sama na Nigeria baki daya
Sunansa kawai nasaka, Amma anturomin harda pic dinsa, Kuma shine de wannan wanda kika turomin
ajikin pic din
Shikkenan Besty keda bakyason soja, gashinan kin kwaso shugaban su
Ajiyar zuciya Iman tayi, sannan tace zan fada masa gaskiya Besty, bazan boye masa komai ba, karma
yaga narabu dashi yayi zatan na yaudareshi
(Yaya kuke ganin Aliyu zaiji idan Iman tafada masa gaskiya?)
Duk wanda yaga banturo masa WAZAN ZABA a group dinsaba, to banga sharhi bane
Idan anjini Shiru, tokada anemeni, Nima najika Shiru ne
Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA? 💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
8
Da wannan shawarar ta yusy Iman tayi amfani, wajan kawar da maganar Aliyu Daga cikin ranta, tama
manta dashi taci gaba da sabgogin gabanta
***