Showing 27001 words to 30000 words out of 39414 words

Chapter 10 - WAZAN ZABA by Amnah El Yaqoub

14 May 2026

117

yake gani ahalin
daya gansu jiya



Sai wajan Karfe Tara Hajiya tafuto Daga dakin Alhaji, tasan Cewa Iman Da mamy Suna nan zasu gudanar
da abinda yakamata ayi break fast dashi
Dining ta kalla taga komai yana nan anshirya, Amma Kuma babu kowa, cikin ranta tace to lafiya?



Kai tsaye tayi cikin dakinta, tuntube tafara yi da kayan da Imran ya hargitsa mata, da mamaki ta sake
Kallan dakin nata

Komai a hargitse, idontane yakai kansa, atsugunne taganshi, dasauri ta qarasa wajansa tafara tattabashi,
tace Imran lafiya? Shiru yayi babu magana



Gabanta na faduwa tasake Cewa Imran nashiga uku me yake damunka, nanma Shiru Imran babu
magana



To itade tasan Cewa Imran bashida aljannu, Amma gashi yau yanayin Abu Kamar na masu aljannu



Daqyar tadago masa kansa tace Imran me yake damunka? Fadamin menene yasameka? Duk ta rude
tanata tambayarsa



Ahankali yace Hajiya zuciya ta zafi takemin, inajin kaina Yana barazanar tarwatsewa



Batace dashi komai ba, tafice dasauri tayi dakin Alhaji, domin tasanar dashi halin da ake ciki



Tare suka dawo dakin itada Alhaji, Alhaji yana kallansa yasan Cewa babu lafiya, fuska babu alamar wasa
yace Kai taso kazo nan, yafadi haka tareda Juyawa



Ahankali yatashi yana dafe da kansa dake masa ciwo yabi Bayan Hajiya d Alhaji suka futo falo



Adede lokacin mamy ma tafuto, tashin hankali qarara ya baiyyana a fuskarta tace subhanallah Hajiya
meyasa meshi?
Hajiya tace wallahi Hajiya fati Nima bansaniba, kin ganshi nande



Zama sukai gaba dayansu a falon, Kan Imran aqasa, idonsa jajir alamar yaci kuka yagaji



Alhaji ya debeshi yace Imran



Ahankali yadago da kansa ya kalli Alhaji, nan take hawaye suka zubo Masa, saboda yasan Cewa dole zasu
so Jin dalilin dayasashi kuka



Alhaji yasake Cewa menene yake faruwa Imran? Fadamin menene yasaka kuka?



Batare daya goge hawayen idonsa ba yace bros ne.... Ya.. Ya... Alhaji bros.. Ne, kuka ne yaci karfinsa,
kuka wiwi Kamar mace yakasa qarasa maganar dayake son fada



Mamy najin ance bros ne gabanta yafadi, yau tashiga uku me baby yajawo musu a gidan nan?



Alhaji yace me bros din yayi?



Adede lokacin Bilkisu tayi sallama tashigo cikin falon tana janye da trolley dinta

Gaba dayansu suka zuba mata ido, Hajiya ce tace Bilkisu sannu da Zuwa, Ahankali taqaraso cikin falon
jikinta asanyaye ganin duk sun zubawa Yaya Imran ido



Aqasa ta tsugunna ta gaida su, miqewa tayi zatayi ciki Alhaji ya dakatar da ita da hannu



Yasake Kallan Imran yace inajinka me dan'uwan Naka yayi?



Hawaye ya share yayi Shiru baice komai ba, ai abinma da nauyin fada
Alhaji ya Jijjiga kansa yace owk yayi ma kyau, sannan yadubi Bilkisu yace Bilkisu Gara da Allah yakawoki
Adede wannan lokacin, dama Koda bakizo yauba, inada niyyar nemanki, inaso inyi Miki tambaya ta farko
Kuma ta qarshe, inaso ki sanar Dani gaskiya



Idontane ya fur futo alamar tsoro, itakam dama batazoba



Alhaji yana ganin yanayinta yasan Cewa akwai wani abun aqasa, yace Bilkisu menene yake faruwa
tsakanin Aliyu da Imran da yayarki Fatima? Tare kuke da ita, kinsan komai nata tasan komai naki,
danhaka Ina so kisanar Dani abinda kika sani dangane dasu



Daqyar tadago idonta, ta kallesu Yaya Iman tajawo mata masifa yau, cikin in-ina tace Alhaji... Alhaji
gaskiya akwai abinda yake faruwa wanda Baku saniba



Sunkuyar dakai mamy tayi, domin kuwa abinda take kokarin boyewa yau yagama tonuwa,



Bilkisu taci gaba da Cewa, Yaya Iman Da yayi Aliyu Suna soyaiya tun muna Ghana, maganar gaskiya itace
yayi Aliyu Baisan Cewa budurwar Yaya Imran bace,...... Tas takwshe komai tasanar dasu



Tana gamawa Alhaji yasaki nannauyar Ajiyar zuciya



Hawaye suka sake tsinkewa afuskar Imran



Alhaji yacewa Bilkisu jeki kiramin yar'uwarki, Bilkisu na tafiya, Alhaji yadau waya yakira Aliyu



Kana inane?



Alhaji Ina tareda abokan aikina ne
To kazo gida kasameni yanzu yanzu



Aliyu Bai kawo komai aransa ba yace to Alhaji gani nan



Iman najin bayanin Bilkisu ta Dora hannunta akanta tace nashiga uku



Haka suka futo gaba dayansu Zuwa falo, kansu aqasa suka nemi waje suka zauna



Shiru falon yayi, kowa yana jiran yaji hukuncin da Alhaji zai yanke



Bai wuce minti ashirin ba Aliyu yashigo falon, da mamy yafara hada ido

Ta wurga Masa harara



Akusa da Imran yazauna, Ahankali yace Alhaji gani



Shiru Alhaji yayi yazuba musu ido yana kallansu, Hajiya tasaki Ajiyar zuciya tace Alhaji kayi Shiru bakace
komai ba



Alhaji yace to hajiya me zance musu? Ai abin nasu abaiyane yake, AI ABIN BROS NA BROS NE ( 😂😂)



Yadubesu yace bahaka kuke fadaba?



Barrister yayi Shiru tareda goge hawaye



Aliyu najin haka aransa yace shikkenan Mai faruwa tafaru, nasan Bros yasan komai yanzu
Ganin duk sunyi Shiru ne ya Alhaji yadubi Iman tace Fatima



Ahankali tadago da kanta tace na'am



Alhaji yace Fatima kifadamin wa kike so tsakanin Aliyu da Imran?



Sai lokacin takai kallanta garesu, kowa yana zaune kansa aqasa babu me kallanta acikin su, zancen zuci
tafara,



Yaya Imran me sona me kaunata, me bani dama inyi duk abinda nakeso, Dan Hajiya, matar data riqeni
tasomu fiye da yayan cikin ta



Aliyu me sona Mai kishi na, wanda a dalilin soyaiyar dayakemin yakamu da cuta, yazabi yayi jinya Akan
dan'uwansa yasan Cewa yana sona



Innalillahi ni Iman WAZAN ZABA???



(fan's Iman tana neman amsa, nide nace... um Bari nayi shiru🤭🤭de)



Kuyi hakuri da wannan bayawa, da ba zanyi typing din Bama to nasan dole wasu jirani shiyasa nayi
wannan, fatana ku kasan ce Dani, Ina yinki sosai my fans💃💃



Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖



Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem



19



(Agurguje pls wlh nagaji da typing dinnan😔😔😔)



Dukansu su biyun ne suka dago kansu kowa yazuba mata ido yanaso yaji wazata zaba acikinsu



Tashin hankali ne qarara Akan fuskarta, yaufa ake yinta, Ayau Kan tayi DANA SANI (my first novel) Akan
Yin soyaiya ma baki dayanta



Cikin kuka tatashi tayi cikin dakinta aguje



Kowa ido yazuba mata, babu wanda yayi yunqurin kiranta, mamy ce tace Ai Yaya daka janye wannan
tambayar ma, rikici ne kawai irinna Aliyu, domin kuwa tun farko muna Switzerland dayazomin da
maganar Naja masa kunne, Kuma nayi masa gargadi akanta, kallanta takai Kan Aliyu taci gaba da Cewa
yaro ne kahaifeshi Amma baka haifi halinsa ba



Hajiya tace ai Hajiya ni duk banga laifinsu ba, gaba daya laifin yanakan Iman, meyasa tasan da haka tun
farko bazata futo tayi bayaniba bare asan ta inda za'a warware matsalar



Billy da kanta yake qasa Ahankali tace wallahi Hajiya Yaya Iman batasan sunada alaqa ba, kawai
gwadash...



Rufemin baki, aiduk bakinku daya, Hajiya tatare mata zancen kafin taqarasa fadar abinda yake faruwa



Alhaji yace komai de ya lalace
Hajiya tadubi su Aliyu tace toku yanzu sai daya yahakura yabarwa daya, Tunda bazaku Iya auranta ku
biyu ba



Alhaji yace babu wanda zai hakura acikinsu, ita fatiman data kulasu duka su biyun ai dole cikin ranta
akwai wanda takeso, danhaka dole itace zata fidda kanta Daga wannan sarqaqiyar

, ba kukaba kome zatayi saide tayi"



Ya kalli Bilkisu yace tashi kibita dakin kutaho tare



Ahankali Bilkisu ta miqe tayi cikin dakin na Iman, ita kanta yau ta tausayawa yar'uwar Tata, wannan
masifa Dame tayi kama



Tana Zuwa dakin taganta Akan gado ta kifa kanta Akan Fillo



Ahankali ta qarasa kusa da ita tace Yaya Iman, al'amarin nanfa yayi tsamari, Alhaji yace kitashi muje



Shiru Taji



Tasake Cewa Yaya Iman fa, kinajina kinyi Shiru



Still shirun Tasake ji



Dasauri Takai hannunta jikin Iman tafara kokarin dagota

Yanda ta dagota haka Iman ta koma Kan gadon ta zube yaraf



Jijjigata tafara yi tana fadin Yaya Iman! Yaya Iman!!

Amma Shiru Iman babu alamar numfashi atare da ita
Gaban Bilkisu yabada dam

Ido ta zazzaro tayi falo aguje tace Hajiya! Hajiya!! Hajiya!!!

Yaya Iman ta mutu

Wallahi Bata motsi



Gaba daya ta rikice Kamar ma Bata cikin haiyyacinta, kawai dakin take nunawa da hannunta



Ai sunajin haka gaba dayansu sukai cikin dakin harda Alhaji



Hajiya da mamy duk sun rikice, Bilkisu kuwa kuka take wiwi



Qirjin sane yake masa ciwo, nan take Tari yake shirin Zuwa masa, yasan Cewa idan yabari yayi tarin
abinda zai biyo Bayan tarin zai sake sakasu cikin wani halin, danhaka ya danne yaqi yarda yayi



Barrister kuwa kawai kallanta yake, tabbas idan ya rasata to ya tabbatar yarasa farin ciki Har abada



Alhaji ne ya tsugunna dede inda take kwance ya duddubata yace kubani ruwa Suma tayi



Dasauri Billy ta Bude fridge din dake cikin dakin nata ta dauko gorar ruwa faro, tabashi



Ahannunsa ya zuba ruwan sannan yashafa mata afuska, Amma Shiru kakeji Ko motsi batayi ba

Haka Hajiya da mamy ma suka Matso kowa yayi Yan dabarunsa Amma Bata farfadoba



Bilkisu na ganin haka Tasake fashewa da kuka tace nashiga uku shikkenan Yaya Iman
Hajiya da gabanta yake faduwa tajuyo cikin tashin hankali tace Wai Bilkisu Zaki mana Shiru Ko saina
dokeki



Hannu tasa abakin ta, Amma hawaye ne yake tsiyaya a idonta



Alhaji kansa yashiga tashin hankali, Amma Bai nuna ba, gudun sake shiga tashin hankalinsu



Duban zaratan samarin nasa yayi yace ku dauko ta muje asbiti



Ai Kamar jira suke atare suka Kai hannu zasu dauketa

Hannunsu ne ya bigi na juna, nan take ran Barrister yabaci ganin karfin Hali irinna Bros dinsa

Shima Aliyun Haushi yaji, Yama za'ai yarinyar yakesan auranta, yake kishinta fiye da komai Amma Bros
yataba jikinta



Kowa fuska atamke, Kuma sunqi Kallan junansu



Hajiya tace Alhaji da daukarta kayi muka tafi, su idan sun gama quncin sa biyo mu Daga baya



Duk halin da ake ciki Bai Hana Alhaji murmusawa ba, ganin kishi qarara a idan 'ya'yan nasa



Jin haka yasa Aliyu matsawa gefe sai kumburi yake



Shima barrister cikin bacin rai ya dauketa suka tafi asbitin



Motoci biyu sukayi, daya Hajiya da Bilkisu Abaya, sai Alhaji dakuma Aliyu dayakejan motar
Dayar Kuma mamy ce Abaya ta Dora Kan Iman Akan cinyarta, sai barrister dayake driving



Kai tsaye suka nufi private hospital na khadija memorial



Suna faka motar, Imran ya dauketa, gaba dayansu suka shiga cikin asbitin, kowa yagansu yasan Cewa
lalle wannan marar lafiyar tanada mutuqar muhinmanci awajan su



Likitoci na karbarta aka kaita shiga da ita wani daki, mamy tace doctor bazamu Iya shiga ba?



Kuyi hakuri Hajiya kubamu Minti ashirin, insha Allah zata samu lafiya, ku kwantar da hankalinku



Zama Bilkisu tayi ta rafka uban tagumi, Aliyu kuwa zagayawa yake awajan, gaba daya hankalinsa atashe
yake



Imran ma zama yayi Daga can gefen Bilkisu, yariqe kansa dake yi Masa masifar ciwo da tafin hannunsa



Suna zaune babu me Cewa dan'uwansa uffan, likita ya futo yace zaku Iya shiga ku ganta, zanje office na
dawo



Zuwa wannan lokacin hakurin Aliyu yagama qarewa, yamatsu yaga halin datake ciki

Danhaka doctor na wannan maganar yasa kansa cikin dakin



Suma sauran suka rufa masa baya



Oxygen ne amanne ahancinta, shine yake temaka mata wajan janyo mata numfashi
Dede kanta Aliyu yatsaya, yazaba mata ido, Wai fatimansa ce wannan halin, yarinyar da Ko zazzabi take
baya samun isasshen bacci



Bacci take tana numfashi Ahankali, gashin idonta dasuka hadu sai sukai kyau, fuskarta tayi fayau lokaci
daya



Ahankali Alhaji yace Allah Yarufa asiri



Dukansu suka ce amin



Turo dakin doctor yayi, yashigo da file Ahannunsa ya kalli Alhaji yace Alhaji Kaine mahaifin yarinyar Nan?



Eh nine, inji Alhaji



Glass din idonsa yacire yace haba Alhaji, Yaya zakuyi sakaci da rayuwar yarinyar ku, kun Barta tana
Yawan tunani



Gashi yanzu Har Hakan yataba Zuciyar ta



Gaba dayansu suka razana dajin furucin doctor, atare suka ce zuciya likita!!!!!



Jijjiga kansa yayi yace qwarai ma kuwa, Zuciyar ta ta kumbura, Kuma idan bakuyi gaggawar nema mata
magani ba gaskiya zaku Iya rasata



Hawaye ne suka wankewa Bilkisu fuska, sai yau taqara tabbatar wa tana son yar'uwar ta, Allah yasa
karta tafi Kamar Yanda umma tatafi tabarsu
Ahankali Aliyu ya Dora hannunsa Akan Zuciyar sa, wani irin radadi yakeji awajan



Idanun barrister jajir alamar tashin hankali atare dashi



Gumi Alhaji ya share yace yanzu doctor Yaya za'a yi? Konawane zan Iya kashewa inde yarinyar Nan zata
samu lafiya



Doctor yace Alhaji abinda zan Iya fadama shine a fita da ita qasar waje, India sunada qwararrun likitoci,
inde ankaita insha Allah za'a samu abinda akeso



Tunani Alhaji yafara, yana Kallan dakin, afili yace India India, alhmdlh ai kuwa akwai wani babban doctor
dayake aiki a India Dan Bauchi state, inaga kawai Gara aturata wajansa



Doctor yace to Alhmdlh, Allah yasawaqe, duk Yanda kukai dashi kusanar Dani Ina office, yajuya yafita



Alhaji ya dubi Aliyu yace kiramin tsohon gwamnan bauchi daddy (BURINAH my second novel)

Kafada masa ya turo ma number abokinsa jabir zamu tura masa da Fatima



Wayarsa yadauka ya kirashi, Saida Kiran ya kusa katsewa sannan aka Daga, Daga dayan bangaren

Aka Daga, the chief of air staff katafi Switzerland kazauna, Kuma Daga dawo Nigeria dinma kabuya



Ahankali Aliyu yace daddy share wannan mgnr, yanzu de muna buqatar number jabir, zamu tura Masa
da marar lafiya ne asbitin su



OK Bari naturoma
Aliyu na kashe wayar, daddy ya turo masa da number, Kiran jb sukayi nan da nan yafada musu Yanda
zasuyi tsare tsaren tafiyar



Zama sukai Dukansu a dakin kowa yayi Shiru yana Kallan Iman datake kwance



Na'urar datake kusa da gadon Iman ce tayi qara, nan da nan numfashinta yafara Sama Sama



Gaba daya hankalinsu yasake tashi, dasauri Aliyu yayi waje yana Kiran doctor... Doctor....



Kan Imran yasara, ganin halin datake ciki, kansa yariqe yana ganin dakin yana juya masa, bayasan yarasa
Iman, jiri ne yadebeshi nan take yazube awajan



Salati su Hajiya suka fara , Dukansu sukayi kansa, ga Iman datake wani irin numfashi



Alokacin Aliyu yashigo tareda doctor, Gabansa ne yafadi, ya kalli Iman yaga abinda take, ya kalli Bros
dinsa akwance aqasa Ko motsi bayayi



Tashin hankali ya ziyarceshi na nan take, yayi dibi dibi Yama rasa wajan wa zaije

Kawai saiyayi wajan Imran yafara Jijjiga shi, bros... Pls katashi, zata warke please bros.... Katashi...

Yana Jijjiga shi yafara Tari, Alhaji ya janye shi, yana buga masa bayansa, yace Aliyu jeka Sha ruwa kadena
wannan tarin



Kafin yatashi yasha ruwan yafara Aman jini



Tashin hankali,Zuwa wannan lokacin Alhaji da kansa jikinsa yafara sanyi dangane da al'amarin yaran
Nasa
Yana Tari jini yana fita Daga bakinsa, yadanne kirjinsa da hannunsa guda daya, Kuma still Jijjiga Imran
yake da dayan hannun nasa, Bai damu da halin dashi kansa yake cikiba



Mamy kuka, Hajiya kuka, Bilkisu kuka

Dakin duk ya kaure da kuka Kamar wanda akai musu mutuwa



Likitan dayaje Kan Iman ne yakira wasu doctor's din akai Kai Aliyu da Imran wani dakin



Haka yazauna yana basu baki Akan suyi hakuri, Tunda anyi sa'ah abin nasu yafaru ne Suna asbiti



Haka su mamy suka wuni a asbitin nan jugum jugum

Farhan ma Yazo yakawo musu abinci Amma babu wanda yakula abincin Har dare



*** *** ***



Washe gari Hajiya ce awajan Aliyu tareda Farhan, mamy Kuma tatafi dakinda Imran yake itada Bilkisu



Alhaji ne kawai yake zirga zirga domin tura Iman India

Dayake abin nasune na manya a ranar aka turata babban asbitin India APOLLO HOSPITAL



Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖



Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem
20



Alhaji Saida yayi waya da jabir, jabir din ya tabbatar masa Cewa zasuje airport sujira Zuwan su Iman
sannan sannan hankalinsa ya kwanta yace su kula da ita dakyau, ayi mata duk abinda ya Kamata inde
kudi ne babu damuwa, Suma zasu taho Daga baya, saboda yanzun hankalin gida ba'a kwance yakeba



Asbitin yakoma domin yaga halin dasuke ciki



Dakin da aka kwantar da Aliyu yashiga, yana kwance yana bacci Amma Leda ce ajikinsa anayi masa qarin
jini



Hajiya idanu sunyi fari fat saboda kuka, tariqe carbi ahannunta tace Alhaji sannu da dawowa



Waje yanema yazauna sannan yace Yauwa Hajiya, Yaya jikin nasu?



Jiki dasauqi, ai Aliyu ma Naga yana daurewa, saboda yana cikin hankalinsa Likitan yadaura masa jinin,
yace idan kadawo ma musameshi a office



To Alhmdlh, Allah yaqara afwa, Itama Fatima sun tafi, angama komai insha Allah za'a dace, Daga baya
saimu bita idan wadannan din sukaji sauqi, Hajiya Kinga abinda nake fada Miki Ko? Shiyasa nake Cewa
kisa ido sosai Akan yaran nan, yanzu Kinga bamusan me yake faruwa atsakaninsu ba inda Allah yayi abin
Yazo da qarar kwana haka duk zamu rasasu



Hakane Kam Alhaji, ai abin nasu da mutuqar daure Kai yake, bazaka taba Cewa akwai wani Abu
atsakaninsu ba



Miqewa yayi yace muje muga jikin Imran din Daga nan saimu qarasa wajan doctor din

Binsa tayi Abaya suka fita, akabar Farhan da Aliyu a dakin
Dakinsu Imran sukaje, anan suka tarar da mamy da Bilkisu, Alhaji yace yajikin dannaki Fatima



Cikin jimami tace jiki da sauqi Yaya, yanzu doctor dinma yagama dubashi, yace dazaran yafarka ayi saurin
bashi abinci da wannan magungunan, sannan Kuma kada abarshi yayi tunani



To Allah de yabasu lafiya,



Amin Yaya



Yakamata muje muga Likitan nan



To Yaya



Bilkisu suka Bari a dakin su Kuma suka tafi wajan doctor



Suna Zuwa office din yabasu waje suka zauna, sannan yadago da kansa yace wato Alhaji abinda yake
bani mamaki dakuma daure min Kai dangane da yaranka shine Dukansu cuta dayace take damunsu



Shi Imran Abubakar Bilal shine me hawan jini, but Aliyu Sa'ad Bilal am sorry to say yanada daukeda
ciwon zuciya



Gaban mamy ne yafadi, nan take kuka Yazo mata, dama tasan dole za'a Rina, tun farko Saida baby yace
mata tayaya zai samu lafiya Bayan yarinyar dayake rashin lafiya akanta tana zaune a gidan?

A lokacin batayi tunanin cuta zata kama mata dannata qwaya daya tal a duniya ba, da Washe gari zasu
hada nasu yanasu su tafi Abuja



Hajiya ma hawaye take sharewa tace Innalillahi mukan munga ta kanmu, Allah kabamu ikon cinye
wannan qaddara
Likitan yace Hajiya ba kuka zakuyi ba, Addu'ah suke buqata, ni kaina nayi mamakin abin, ita yarinyar tana
gab da kamuwa da ciwon zuciya, shi wannan hawan jini, shikuma dayan already yanada rashin lafiyar,
saboda abinciken danayi Nagano ciwon yadade ajikinsa, Tunda Har abin nasa yakai limit din dayake tarin
jini

Amma insha Allah zamuyi Iya bakin kokarinmu muga sun samu lafiya

Yadubi Alhaji yaci gaba da Cewa Alhaji ka kwantar da hankalinka yaranka duka zasu samu lafiya, saide
shawarar dazan Baku zatasa lafiyar su tayi saurin samuwa idan kunbi



Gumi Alhaji ya share, yana ganin yatura Iman India, matsalar sa zata Ragu, ashe ba'a Rabu d bukar ba
anhaifi Abubakar

Yace likita Ina jinka menene shawarar taka?



Yauwa shi Imran adena barinsa yana tunani, kome zai faru kada abarshi shi kadai yana tunani, shi Yawan
tunani shine tushe na hawan jini

Sannan akula da bashi magungunan sa



Shikuma Aliyu already yanada ciwon zuciya, dole za'a kiyaye abinda zai Bata Masa rai, a dinga yi masa
abinda yakeso, insha Allah za'a dace, muma Kuma zamuyi bakin kokarinmu, sannan Kuma zaku Iya barin
mutum daidai awajan su ku koma gida, zamu basu sauran kulawar data dace dasu



Daga mamy Har Hajiya babu me Bawa dan'uwansa hakuri, to kowa share hawaye yake, haka suka futo
Daga office din



Alhaji yace Wai Hajiya Dame kukeso naji ne? Kunsani agaba kunamin kuka, yanzu fisabilillahi idan sauran
yaran suka ganku su Kuma saisu fara hauka Kenan? Haba

, fuuuuu yakada babbar Riga yayi dakin da Imran yake



Ganin Alhaji yayi musu fada ne yasa suka daina kukan, suka bishi dakin Suma
Alhaji yana Zuwa dakin Yadubi Bilkisu yace kikula dashi, zamuje gida muyi wanka



Ahankali tace to Alhaji Allah yakiyaye



Dakinda Aliyu yake suka koma, nanma suka ce Farhan yakula dashi, zasuje gida su shirya



Haka suka futo Daga asbitin sukayi gida, wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login