Showing 30001 words to 33000 words out of 39414 words
Karon Kam, Alhaji ne da kansa yajasu amotar
*** *** ***
Yaya kakejin jikin Naka?
Jiki da sauqi doctor, nifa banajin komai, saide kawai inajin Tari yanadan tasomin kadan
Eh gaskiya ne soja, wato nanma de sai an nuna jarumtar, to kadaure karkayi tarin Koda kanaji din,
sannan karkayi wasa dashan maganinka
Cikin Murmushinsa Mai tsada yace babu damuwa doctor, Bayan tarin babu abinda nakeji
, zan Iya Zuwa Naga jikin Bros Dina?
Farhan dake gefe yayi sauri yace haba Yaya Dan Allah kabari kasake Jin sauqi saikaje
Murmushi doctor yayi yace eh gsky de Hakan zaifi sannan yafita
Doctor na fita me aikin su Hajiya tazo driver yakawo ta, takawo musu abinci da abubuwan buqata
*** *** ***
Tana zaune akujerar dakin tafada duniyar tunanin yar'uwar ta, Ko tana wanne Hali yanzu oho
Allah de yabasu lafiya baki dayansu
Tana wannan tunanin taga yabude idonsa, Ahankali dasauri taqarasa bakin gadon nasa tace sannu Yaya,
mekake buqata yanzu? Babu inda yakema ciwo?
Haka taita jero Masa wannan tambayoyin
Kansa yadafe da hannunsa cikin rintse ido yace kaina kemin ciwo sosai
To Bari nakira likita, tafice da gudu Daga dakin
Tare tadawo da doctor yaduba shi yace a bashi abinci yaci da magungunan sa, zai dawo yayi masa allurai
Doctor na fita, dakin yasake yin Shiru, ita Bilkisu ba gwanar rawar Kai bace irin Iman, sannan ita bawani
sabawa tayi dashi ba Kamar Yanda Iman tasaba dashi duk taga yayi kwarjini, tarasa me zata Masa, wayyo
Allah itakam meyasa Alhaji yace ta zauna da Yaya yau, Allah yadawo dasu gaskiya Suna Zuwa zan koma
gida
Tunawa tayi da maganar doctor, Ahankali tatashi tazuba masa abincin, jallop din taliya ce da tsokar
Nama aciki manya, sai turiri abincin yake, tazuba acikin flet tasa spoon
Agefen sa ta zauna tace Yaya ga abincin Kaci, kaji doctor yace zai dawo yayima allura
Ahankali yadauki spoon yafara cin abincin, cokali biyu yayi yace naqoshi
Haba Yaya, Dan Allah kaqara Ko kadan ne
Kansa yakawar gefe fuska babu alamar fara'ah yace naqoshi nace
Kallan abincin tayi, Yama za'ai yace yaqoshi, kawai de damuwa ce tasa Baisan cin abincin
Diba tayi cikin nutsuwa tanufi bakinsa d abincin
Kallan ta yayi, yaushe yafara wasa d Bilkisu dazatai kokarin bashi abinci abaki? Kota manta Cewa shi
ganin qanwarsa yake mata? Koda yaushe gani yake batada banbanci da Farhan da zainab auta
Shiyasa ma Bai wani saki jikinsa da itaba bare harta Raina shi
Kawar da kansa yayi,
Jikinta ne yayi sanyi Ahankali tace please Yaya
Haka yadaure take bashi abincin, sai wani Bata fuska yake Kamar tana bashi magani
, Saida ta tabbatar ya qoshi sannan tadau tissue ta goge masa bakinsa, tafice Daga dakin
Shide Binta yake da kallo kawai, yana aikin Bata fuska
*** *** ***
Washe gari Bilkisu tahada yanata yanata tatafi gida, itakam bazata Iya wannan Zaman jinyar ba, duk
mutum atakure, shikkenan saide ta zauna tayi dunkum itaba kurma ba, Bayan ance yadena tunani,
Amma bazai yimata magana ba saide ya shareta yana aikin tunani, wallahi Gara Hajiya Ko mamy sudawo
su zauna dashi, bazata iyaba
Ko Farhan dayake kula da Aliyu batayiwa sallama ba tayi gida
Shi kuwa Farhan kalau suke fira da Aliyu, Kamar ma ba marar lafiya ba, sosai yake Daurewa Akan komai
Duban Farhan yayi yace jeka ganomin jikin Bros kaji Farhan
Zuciya daya Farhan yatafi dakin Imran, yatarar dashi Ana qara masa ruwa Amma bacci yake
Danhaka yajuya dakin dasuke, yana Zuwa yaga wayam babu Aliyu babu labarinsa
Hankalinsa ne yatashi, nan take yadinga nemansa daki daki, yafuto harabar hospital din nanma babu
Aliyu babu labarinsa, kusan minti talatin yana dube dube
Wata dabara ce tafado masa nan take yadauko wayarsa ya kirashi, bugun farko yadaga, cikin tashin
hankali Farhan yace, Yaya Aliyu kana Ina ne sai nemanka nake?
Murmushi yasaki Mai aji yace Farhan natafi India, idan kahada kayanmu kakoma gida kasanar dasu Alhaji
Cewa Nina wuce India
Sharhi please ππ»
Mrs Usman ce WAZAN
βπ» ZABA?π
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
21
Daria ce takama Farhan, yace to Yaya, tareda kashe wayar
Dakinda suke yakoma yahada komai, yaje Har office din doctor yace to likita nizan wuce gida, mun
sallami kanmu
Doctor yace ban ganeba, kamarya kun sallami kanku?
To likita majinyacin ya wuce India wajan budurwar sa
Murmushi doctor yayi, Zuwa yanzu Kam yagama Gane Cewa duk saboda soyaiya ne suka shiga wannan
halin
Toshikkenan, idan kaje kagaida Alhajin
Farhan nafita ya wuce dakin da Imran yake, yana Zuwa yaganshi yana bacci, Amma Kuma dakin babu
kowa, tunani yayi Cewa may be Bilkisu tana toilet, danhaka yaja dakin Yarufe tareda fita
*** *** ***
Hajiya na zaune a dakinta tayi Nisa cikin tunani, yanzu saboda soyaiya yaransu Har uku Suna kwance a
asbiti, saboda soyaiyar mutum daya
Babban danta datake ji dashi, yaro me kazar kazar, marassa damuwa Arai, shine kwance a asbiti harda su
hawan jini, Bata fatan ace Ko zazzabi ne yasamu Imran dinta, Amma yau gashi akwance asanadin soyaiya
Shiru tayi tana neman mafita
Wani tunani ne yafado mata, idan Dukansu maza biyun Akan mutum daya ne suke wannan jinyar, Tome
zai Hana tasamowa wannan family nasu mafita ta wata hanyar?
Bilkisu yar'uwar Iman ce, tare suka tashi, tanada nutsuwa da hankali, babu abinda Iman zata fadawa
Bilkisu ta fannin diri na hallita kokuma sura
Inda halinsu ya banbanta kawai waje dayane, Iman akwai daukar wanka, tana saka kayaiyaki na kece
raini, sannan ta kasan ce mutum ce mai nuna kyanta afili, wanda Hakan yasamo asali ne ta wajan Imran
daya dorata Akan wannan turbar
Sabanin Bilkisu datake shiga ta mutunci, gakuma sanyin Hali, kwata Kwata batasan damuwa shiyasa ma
Bata cika shiga sabgar Yan gidan ba, itade Barta da zeey auta
Bilkisu tayi ta Ko wanne fanni, saide Kuma Kash Shu'aibu yayi musu katanga da ita, saboda wani dalilin sa
can marar tushe
Tashi tayi tana zagaye dakin, afili tace wannan Karon Kam Shu'aibu saide kayi hakuri, inaji Ina gani bazan
rasa yarona ba, domin kuwa idan aka biya ta Alhaji dasunan Wai Iman saita zabi daya acikinsu, tofa Iman
batada niyyar zaba, saide Daga qarshe Alhaji yace kowa ya hakura d ita
Da wannan tunanin ta futo falo, turus ta tsaya ganin Bilkisu kwance akujera tana danna waya
Tace a a yaushe kika shigo gidan bansaniba?
Dago kanta tayi tareda ajiye wayar tace Hajiya wallahi na Dade da Zuwa, gajiya nayi da Zaman Shiru haka
ba dadi
A a kamarya gajiya kikai?
Cikin shagwaba tace Hajiya Allah nikam nagaji, Wani yaje kawai
Sallamar Farhan ce ta tsaida musu maganar dasuke
Hajiya tace a a, kaikuma yanaganka da Kaya ahannu? Wai meyake damun kune? Duk kun baro marasa
lafiya a asbiti kun iyo gida
Zama yayi Akan kujera yace Hajiya ai ni mun sallami kanmu, yayi ya fece India wajan Iman, to dawa zan
zauna? Shiyasa Nima nayo gida, Kuma yace afada muku shiya wuce India
Murmushi Hajiya tasaki, ta kwalawa mamy Kira, futowa tayi tana daura dankwali tace Hajiya ya akayi?
Wai Daga kwanciya bacci ya daukeni, kinsan jiya bamu rintsa ba
Hajiya tace kinji Wai Aliyu yatafi India, shine Farhan yadawo gida da kayansu, Wai afada mana shiya tafi,
ita Kuma wannan tagaji ne shine saboda tsabar sakarci tabarshi a asbitin ita Kuma tayo gida
Tafa hannu mamy tafara tana Cewa, la'ilaha illallahu, yanzu shi Haidar dinne yakama hanya yatafi, wato
Bai duba rashin lafiyar dayake ba
Hajiya tace to yaza'amusu, ai sai hakuri
Farhan ne yace nikam nagaji, Bari inje daki nakwanta na huta, ya kalli Bilkisu yace ainaje dakin naku
bangankiba, sai Yaya ne kawai yake bacci, jinakema kina toilet ashe kina nan
Wallahi gajiya nayi nataho gida, inji Billy
Mamy tace to yanzu waye zai zauna da Imran din Bilkisu?
Dasauri Hajiya tace nice zanje mana Hajiya fati, Tunda ita bazata Iya zamanba aini saina dauki mayafina
inje in zauna dashi
Murmushi mamy tayi data Gane gatse ne Hajiya takama Bilkisu
Tana zama akujera Itama, tace a a Hajiya, zata Koma itama, duban Billy tayi tace Bilkisu yata tashi ki
shirya, kikoma kinji, karya tashi Kuma yanemi wani Abu gashi bakya nan, Bari insa Mai aiki tayi muku
abinci, saiki tafi muku dashi
Kamar zatai kuka tace to mamy, tareda tashi tayi dakin Iman, domin shiryawa
*** *** ***
Kai tsaye Abuja ya wuce, Saida yagama abinda zaiyi sannan yatafi India
Baisha wahala ba wajan Zuwa asbitin, Kai tsaye wajan jabir yanufa, Saida suka sake gaisawa sannan suka
nufi Dakinda take ciki
Tana kwance tana bacci, qarin ruwane ajikinta, Zuwa yanzu babu oxygen Din ancire mata shi, saide tana
numfashi ne Ahankali, fuskarta fayau
Dakin babba ne, da kujera 2seater sai qaramin fridge, da gadon datake kwance, komai na dakin kalar
light blue ne Har kujerar, sai wata qaramar kofa agefe da alama toilet ne
Har gaban gadon sukaje, ya sunkuya ya zuba mata ido, Kamar wanda yakeson gano wani Abu
Sannan yadago ya dubi jabir yace, Zuwa yaushe ne zata farka ne?
Aita farka dazu, Bayan ankaita tayi wanka ne, akayi mata allurar bacci, sai nanda awa shida zata tashi,
insha Allah
OK to shikkenan babu damuwa, Nima yakama ta muje Naga likita, ayimin abinda yadace inyaso saina
dawo latter
OK ba damuwa muje
Fita sukai Daga dakin nikuma na iyo Nigeria
*** *** ***
Tsaf ta shirya laffaya, ta futo falon zata tafi asbiti
Hajiya ta kalleta tace yanzu keda zakiyi Zaman jinya, yaushe Zaki saka Kaya masu nauyi, maza koma daki
ki sake shiryawa
Kamar zata fashe haka Takoma dakin, tana cire kayan tana mita, Tunda nadawo Daga katsina ban
zaunaba, Daga wannan matsalar sai wannan, haka tasaka doguwar Riga ta atamfa, Daga Sama dinkin
yakama kirjinta, Daga qasa Kuma abude take
Dan qaramin mayafi tadauka tayafa, tana Kallan kanta amadubi tace Tunda nasaka babban Kaya ance
incire, yanzu Kuma nasaka qarami nasan Shima Hajiya dawo Dani zatayi tace Ina tafe tsirara Kamar Yaya
Iman
Hakade ta futo falon, tadauki kwandon abincin tace Hajiya natafi
ga mamakinta saitaga Hajiya tayi mata Shiru, batayi mata fada Akan shigar datayi ba, Tunda tasan
bahaka tasaba fitaba, Dade Iman ce
Saima Cewa datayi, Wai miye kike ta Bata raine? Ko asbitin ne bakya son Zuwa?
Kamar tasan Bilkisu Dama jiran qiris take, nan take tace to hajiya shi yayan ne saiyayi banza ya qyaleni,
dazu da safe abincin Dana bashi ma daqyar yaci, sai hararata yake, ni wallahi Hajiya dande kince saina
koma ne
Murmushi Hajiya tayi tace, haba Bilkisu, keda dan'uwanki? Lallabashi zakiyi, idan yaqi ci saiki lallasheshi
kibashi, idan Kuma kin gwada lallashin yaqi saiki zare masa ido ki Bata fuska, idan bazai ciba, saiki
qyaleshi
Cikin Zaro ido tace Hajiya yayan zan zarewa ido? Um Hajiya sai anjima
Tadauki kwandon tayi gaba, cikin ranta tana mita ita kadai
taga alama Hajiya sotake taja mata fada awajan Yaya Imran, inba hakaba harda Cewa in lallabashi, in
rarrasheshi, saikace wani jariri
Hajiya kuwa Daria ce takamata, da niyya tabarta tafita da wannan kayan, saboda Hakan yana daya Daga
cikin abinda Imran yakeso, wato daukar wanka, afili tace kuje de can ku qarata
*** *** ***
Ga magungunan Naka, Amma inaga da kazo munje gida gobe da safe idan Allah yakaimu saimu dawo
kafin lokacin ma tafarka
Cikin Murmushi yace no doctor jabir karka damu, zanjira harta tashin insha Allah, zan taho gidan Daga
baya
ok to saimun yi waya, inji jabir tareda fita Daga dakin
Ajiyar zuciya yasauke Bayan fitar jabir, ya ajiye magungunan sa, sannan yanufi fridge din dakin yabude,
acike yaganshi da kayan marmari da ruwa sai lemuka, yasan wannan duka aikin doctor jabir ne
Lemon kwali yadauko guda daya, yadau cup yakoma Kan kujerar dakin yazauna, idonsa akanta yafara
ballar maganin sa yanasha
Saida yagama Sha sannan yatashi yakoma Kan gadon datake yazauna Agefen gadon, idanu yazuba mata
yana jiran tafarka
Haka yayita zama Shiru shi kadai, da lokacin sallah yayi yatashi yayi sallah yakoma, yana zaune harya fara
gyangyadi, Amma Bata farka ba, kansa yadan Dora danyaji dadin gyangyadin, nan kuwa bacci ya
daukeshi
Can cikin dare tafarka, Ahankali take Bude idonta harta Bude gaba daya, kansa dayake dab danata
hakanne yasa numfashinsu haduwa, da tsananin mamaki take kallansa, yaushe Yazo? Kode gizo yake
mata? Anya kuwa soyaiyar Aliyu Batasa yafara yi mata gizo ba?
Domin ta tabbatar da ba mafarki takeba yasa Ahankali takai hannunta Kan Lallausar sumar kansa tashafa
Jin Ana shafa kansa ne yasa yabude lumsassun idonsa dake cike da bacci, yazuba mata ido
Itanma kallansa take domin ganin Cewa tabbas shine ba mafarki takeba
(um jiyakam kunjini Shiru sakamakon wani babban uzuri daya riqeni, π±nasan mutane dayawa sun jirani,
Amma inaso kuyi hakuri please ππ»ππ»)
Mrs Usman Ce WAZAN
βπ» ZABA?π
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
22
Hannunta dake kansa yadauke, ya damqe hannun nata cikin nasa yace "kin tashi?"
Daga masa Kai tayi alamar eh, itade duk mamaki yacikata
Tashi yayi Ahankali yasa hannu yadauketa cak, yanufi toilet da ita
Duk da batada kuzari Saida tayi kokarin sauka Ahankali tace zan Iya tafiya, kasaukeni
Kallanta yayi baice mata komai ba, Saida yakaita cikin toilet din, yabata brush da toothpaste, sannan ya
fita tareda rufe mata kofar
Yana fita ta jingina da bangon toilet din, sai Murmushi take ita kadai
Shikuwa fridge din yanufa yahada mata fruit yakai mata gaban gadon, yahada mata magungunan ta
Bude kofar toilet din tayi Dan kadan tace Yaya hijabina
Dube dube yafara shine baiga wani hijab ba, sai wani mayafi, danhaka yadauki mayafin yameqa mata
Kallan mayafin tayi, sai yau tayi Dana sanin rashin yawo da hijab
Towel din jikin ta ta kalla Dan qarami, da kadan ya wuce Rabin cinyarta, haka tayafa mayafin Har kanta,
ta futo Daga toilet din tana Jan towel din qasa
Yana ganin futowarta yakalleta, cak ya qame a zaune yana Kallan ta
Ganin taqi miqewa ne yasa yagane Cewa atakure take
Shiyasa ya miqe yace Bari nafadawa doctor kin tashi, kiyi sauri ki shirya, yafice daka dakin
Yana fita tasaki Ajiyar zuciya, dasauri kuwa ta zira kayanta, tatada kabbarar sallah
*** *** ***
Ahankali ta turo kofar Dakin tashiga tareda sallama, yana kwance idonsa biyu, Amma yadafe kansa da
hannunsa guda daya,dasauri ta qarasa wajansa tazauna dab dashi, tace sannu Yaya, yajikin Naka?
Bece mata komai ba sai rintse idonsa dayake danyi kadan kadan
Hannunta tasa tajanye hannunsa Daga Kan goshin, sannan tadora hannunta awajan
Dasauri ta dauke hannunta Jin zafi sosai
Tashi tayi tace Bari nakira doctor Yaya, Ahankali yace Yazo yanzu yafita, yace zai dawo nanda 30minutes
Dawowa tayi tazauna, tace to Yaya tashi Kaci abinci kafin yadawo
Ahankali yatashi zaune, still hannunsa na dafe da goshinsa
Zuba masa abincin tayi, tadawo kusa dashi tazauna
Dakanta take bashi abincin, duk ta damu, tadebo a spoon takai bakinsa
Babu musu yafara ci, goshinsa tasake tabawa tace sannu Yaya
Zuba mata ido yayi yana Kallan ta, ganin da gaske take komai duk ta damu
Lumshe idanunsa yayi alamar amsaba
Abincin taci gaba da bashi, wayarta tadau qara, Kallan wayar tayi Amma Bata daukaba, Saida ta tabbatar
ya qoshi sannan ta qyaleshi
Dan qaramin handkerchief ta dauko a handbag dinta, taje toilet din dakin tajiqashi da ruwan sanyi,
sannan tadawo tace kwanta Yaya, babu musu kuwa ya kwanta, shi Har yanzu mamakinta yake, Kamar ba
Bilkisun daya saniba
Yana kwanciya ta linka handkerchief din gida biyu, ta Dora masa Akan goshinsa, sannan ta dubeshi tace
Hakan zai taimakama wajan rage Jin zafin Yaya
Ahankali yace thanks
Kujerar dake gefen gadon taja ta zauna, sannan tadau wayarta takira number data kirata dazu
Hello ya Haroon kakirani Ina busy shiyasa ban samu dama nayi picking ba
Shima Daga nasa bangaren yace wanne irin aiki ne wannan dazai Hana kidauki wayata?
Yayanmu ne baida lafiya, aika ganeshima Yaya Imran, shine nake kula dashi
Cikin bacin rai da nuna kishin sa afili yace, OK kina kula dashi shiyasa ni kika qyaleni, to menene amfanin
Iman, aida saita zauna dashi
To yanzu ya Haroon idan Yaya Iman din tana nan harna zauna anan? Batada lafiya Itama, an fitar da ita
India ma
Cikin nuna ko'in kula yace ok, sai anjima, yakashe wayarsa
Wayar Tata tabi da kallo, ikon Allah, wato shi kawai maslahar kansa yasani, nafada masa yar'uwata
batada lafiya Amma Ko Allah yasawaqe baiyi mataba
Tsaki tasaki ita kadai, Imran dake kwance Baisan Sanda yayi Murmushi ba, Ahankali yace keda saurayinki
Bilkisu, menene abin fishi
Cikin shagwabar da batama San tayiba tace haba Yaya kanajin fa abinda Yamin, shine ya kashe min waya
Murmushi yayi baice mata komai ba, Baisan dalili ba kawai de yaji aransa Yanda tayi shagwabar ta
birgeshi
Harma baiso ta daina ba, domin tasakeyi yace bani labari
Kallansa tayi qasa qasa, tace labari Yaya
Shima yace eh
To wanne irin labari zan baka?
Na samarinki
Yaya ni banda samari sai Haroon, saide nabaka labarinsa
No banaso
To ai Kai kace na samari na,
Tona fasa kibani wani labarin daban
Toshikkenan Yaya Bari nabaka labarin soyaiya
Babu Bata lokaci Billy tafara bashi labarai na soyaiya, tun yanaji yana gyada Kai harya dawo yana Daria,
kawai aikin kallanta yake, Dan qaramin bakinta dake motsawa shiya zubawa ido yana kalla, yana ta
mamaki aransa dama Bilkisu tana da surutu haka? Meyasa da baisaniba?
Ita kuwa batasan ma yanayi ba, Zuciyar ta daya, kawai labari take bashi, Bata tunanin komai
*** *** ***
Yanzu saboda wannan yar allurar kike kuka?
Dazai Gane dayadan matsa Daga kusa da ita, kusancin nasu yayi kusa da yawa, gashi yanayi mata
magana qasa qasa Kamar Baisan wani yaji shi
Wajan allurar da doctor yayi Mata yanzu yafita tashafa tace Allah Yaya akwai zafi
Shikkenan naji, zauna nabaki fruit
Babu musu ta zauna, dakansa yake Bata tanasha, tace inasu Hajiya? Ya akai suka yarda kataho?
Waye yafadamiki sun sanma nataho? Basu saniba, nadai fadawa Farhan yasanar dasu Cewa natafi India
Zaro ido tayi tace yanzu fa sunsan wajena kataho
Kafadarsa yadaga yace so what, inasanki ne, bazan Iya ganin kinyimin nisaba, Bayan nasaba kullum saina
ganki a gida
Kuma kawai yanzu saisu dauke minke in zauna?
Dadi takeji acikin ranta Wai yau Aliyu ne yake fada mata wannan maganganun
Ahankali tace nagode da nuna soyaiyar ku agareni
Um kekuma kin Kasa nuna manaba
Da mamaki ta kalleshi tace kamarya? Bangane ba
Emana gashinan Alhaji yace ki zabi daya acikinmu kin Kasa, kawai Daga yar wannan tambayar kin kwanta
jinya
Cikin shagwaba tace Kai Yaya Aliyu Dan Allah, Niba wata jinya
Kawai kifito fili kice Alhaji Aliyu nakeso
Kinga Daga lokacin Alhaji zaisan Cewa idan daddy yayi loosing ummanku ninayi winning Akan yarta
Hararar wasa tayi masa tace dasu umman kake?
Shima cikin Murmushi yace emana ai gaskiya nafada
To nide idan Alhaji yaji kataho wajena Allah babu ruwana
Aikuwa sonake yajima, Dan yasan Cewa mun matsu yayi mana Aure
Fillo tadauka ta rufe idonta dashi
*** *** ***
Meyasa Zaki tafi?
Da mamaki ta kalleshi tace ai dare yayi Yaya, Kuma akwai