Showing 18001 words to 21000 words out of 39414 words

Chapter 7 - WAZAN ZABA by Amnah El Yaqoub

14 May 2026

111

to kunji Yanda abin yake



Billy tasaki Ajiyar zuciya aranta tace Kenan Aliyun ma sun hada dangantaka dashi, hartakewa Yaya Iman
tsiya tana San bare bataso dan'uwantaba



Iman ce ta iyayin magana tace yanzu hajiya Kenan ahaka za'aci gaba da zama? Shi bazai sauyaba?



Hajiya tace kuyiwa mahaifinku Addu'ah wataran zai sauya



Miqewa tayi tace Bilkisu Bari nadauko Miki saqo kikai musu, tafice tabarsu a dakin



Tana fita, Bilkisu tace tab Yaya Iman kice soyaiyar ki da Aliyu akwai matsala,

Kuma kinji dazu hajiya tana Cewa mahaifiyarsa mune yayan zainab, Kenan itama tasan mama



Ajiyar zuciya Iman tasaki tace dama dole tasan mama mana, Tunda mijinta yaso maman, ni Bama
wannan ba, tsoron haduwa nake dashi wallahi, da'ace kina nan zan danji sanyi



Kiyi hakuri Yaya Iman insha Allah zan lallaba baba nadawo, Iman tace kinyi Alqawari? Billy tace nayi Miki
Yaya Iman



Hajiya ce tashigo da Leda a hannunta tace to gashi Bilkisu kikai musu Kuma kice Ina gaishe su
Atare suka futo Daga dakin Dukansu,babu kowa afalon, hajiya Takoma ciki wajan mamy, Iman Kuma
tarako Billy harabar gidan



Zaratan mazan guda biyu ne kawai atsaye aharabar gidan, Barrister yana waya yajuya bayansa, yayinda
Aliyu yake fuskantar kofar shiga falon



Dan haka Suna futowa yagansu, a gefe suka tsaya itada Billy, driver ne Yazo da sauri yakarbi babbar ledar
hannun Billy



Iman tariqeta tana share hawaye tace Billy Dan Allah kidawo da wuri, wallahi ni yanzu shi kansa Yaya
Imran dinma kwarjini yakemin bare Kuma wannan miskilin



Kafeta yayi da idonsa, fuskarsa atamke cikin ransa yake tambayar kansa meyasa take kuka? Anya kuwa
tasan Yanda kukanta yake taba Zuciyar sa!?



Abin tausayi Billy ce ta share mata hawayen Kamar itace babba😃



Tace karki damu Yaya Iman insha Allah zan dawo



Iman nagoge hawaye tayi cikin falon su da gudu



Bilkisu najuyawa tafara tafiya wajan driver

Taji ance mata



"jimana"



Juyawar dazatai taganshi atsaye, gaban tane yafadi, kaki ne ajikinsa tunna safe dasukazo, itafa batasan
harkar sojojin nan, bare Kuma shi fuska atamke
Sharhi please,🙏🏻🙏🏻shike qaramin qaimi wajan sanbado muku typing



Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖



Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem



14



Kasa yi masa magana tayi, gaba daya ta rikice, koshi saida ya lura da Hakan, domin ya kawar da wannan
tsoron dayake gani a fuskarta yasa yasaki wani irin tsadaddan Murmushi sannan yace "Ina zakije?"



Cikin ranta tace tab, ashe yana Murmushi



Ahankali cikin nutsuwa kanta aqasa takasa duban qwayar idonsa tace "zantafi gida ne katsina"



Har zai sake tambayar ta meyasa ita bazata zauna anan ba, kawai Kuma sai wani tunani Yazo masa
yashare

Jijjiga kansa yayi Cikeda gamsuwa yace "ok you can go...



Ai tun kafin yaqarasa tajuya tayi gaba, dama tarasa dalilin tambayar



Bayanta yabi da kallo, masha Allah dukansu haka suke da baiwa, Amma meyasa yakasa tambayar ta
abinda yataso dashi Daga inda yake? Meyasa yakasa tambayar dalilin kukan dayar?
Dafashi yaji anyi, yana Juyawa yaga Imran ne,

"Bros mekake tunani anan? Kaga muje ciki, domin kuwa kasan bazan yafewa kainaba muddin naganka
cikin tunani



Shima yace no ba tunani nakeba Bros, kawai de na tambayi wancan yarinyar ne Ina zataje?



Sai a lokacin hankalin Imran yakai wajan da motor su Billy tafara tafiya, ta glass din motor yaganta, kawai
yadaga mata hannu yana Murmushi, Itama haka

Kallan Aliyu yayi yace OK Wai Dr. Billy, may be zata tafi gida ne



Cikin zaquwa dason sanin dalili Aliyu yace but meyasa zata tafi?



Murmushi Imran yayi yace ai baban su akwai tsauri dayawa, anan yabashi labarin komai, game dasu



Aliyu yace to Amma aida anyi masa magana



Zaro ido Imran yayi, yace wa?

Bros bakasan halin wannan mutumin bane, wallahi gwaska ne



Kafada Aliyu yadaga yace ai shikkenan, muje ciki na watsa ruwa na kwanta



Part din Imran suka nufa dukansu, Amma Aliyu cikin ransa tunani yake Yanda zaiyi Bilkisu tadawo gidan
dazama, Amma yaza'ai tatafi ita Kuma wannan tadinga kuka, ai kawai tayi zamanta, Dan gaskiya bazai
juri ganinta tana wannan koke kokenba, yanzu waya sanima Ko Hakan ya haifar mata da ciwon Kai



*** *** ***
Suna shiga part din yacire kayansa yashige wanka, ya futo daure da towel aqugunsa yayi gaban mirror
yana goge jikinsa da wani Dan qaramin towel din



Shima Imran wankan yashiga, lokacin daya futo Har Aliyu ya shirya cikin wata farar jallabiya



Kallan Imran yayi wanda yafara wanka da turare spray yace bro Bari indan rintsa kadan kona 30mnts ne



Imran yace to Bros atashi lafiya, sannan shikuma yasaka qananun Kaya yadauki computer yajuyo yadubi
Aliyu dahar ya kwanta yace Bros Ina falo zan danyi wani aiki



Idanunsa a lumshe yace to

Barrister na fita, Yaji yakasa yin baccin, meyasa yakejin farin ciki? Wata Zuciyar ce tabashi amsa da fadin
saboda Iman ne

Juyi yasakeyi idonsa arufe, Iman ta Bros ce bazai taba samun taba, Gara yasawa Zuciyar sa salama tun
kafin soyaiyar ta tayi masa illah



Sumar kansa ya hargitsa, afili yace ya Allah kakareni da aikata abinda zaisa Yan gidannan Susan abinda
yafaru tsakaninmu da yarinyar Nan

Fillo din dake gefe yadauka ya rungume sannan yafara samun bacci, jiyake Kamar itace atare dashi



Yana falo yana nazari acikin computer, Saida yagama sannan Yarufe yabarta anan ya shiga dakin domin
duba brother dinsa

Yana shiga dakin yaganshi yana bacci rungume da Fillo, Murmushi yasaki afili yace Bros kawai kafuto fili
kace mamy Aure kakeso



Be tasheshiba Yarufe masa dakin yayi part dinsu Hajiya

Yana shiga yaga Farhan da Iman Suna kallo, kallo daya tayi masa cikin sanyin murya tace Yaya sannu da
Zuwa

Beji kunyar qaninsa dayake wajan ba yace saunawa zan sanar dake Bansan Jin wannan sunan
Murmushi tayi batace masa komai ba, ganin Farhan na nan



Yaya sannunku da dawowa, inji Farhan

Yauwa Farhan, sannu



Farhan yace Yaya ya banga yaya Ali ba, Koya fita?

Barrister yace no, yana daki



Miqewa yayi yace a a Bari natafi, Bana rasa abin samu ba idan naje



Dasauri Imran ya tareshi yace to sarkin son kudi, yana bacci saura Kuma Naga kaje katadashi



Kallan Iman yayi yace muradina Ina hajiya ne? Cikin ladabi tace masa tana cikin daki



Tashi yayi yashige dakin hajiya, Farhan naganin tashinsa yacewa Iman yarinya dama nafada Miki inawa
Yaya magana zai siyamin waya, yanzu gashi Yazo Har gida, Kinga kuwa nahuta da renin hankalinki



Murmushi Iman tayi tace au Wai dama shi kake nufi zai siyama wayar? To inka Isa jeka fada masa, yanzu
zakaci duka, wannan me fuska Kamar an aiko masa da mutuwa din tab



Farhan yace emana soja Kenan yarinya, Nima shi zankoma ai, Ina zama soja zan hadaku gaba dayanku
indinga jibga, Billy kawai zan ragawa Itama dannaga saliha ce shiyasa



Tabe baki Iman tayi tace a a kadaki wasu de,



Farhan yace aishi Yaya Ali daban yake, yanada kirki, kawai de kema Dan Baku saba bane, Amma ai zaku
saba ne kafin su koma Abuja
Suna zaune Suna kallo tareda musun dasuka saba, Har barrister yafuto, yana Zuwa yadubi Farhan yace
Kai Tashi kafita da Allah



Sosa Kai Farhan yayi, yace to Yaya Amma babu abinda zan samu ne?

Kallansa yayi yace Wai Farhan mekake da kudi ne, ba rannan nayi ma transfer 50k ba?



Kafin Farhan yabashi amsa Iman tace yanmata



Harara Farhan ya aika mata sannan yace Yaya wallahi bawasu yanmata,



Imran yace naji jeka, zan turo ma

Saida yasake dalla mata harara sannan yabar cikin falon



Yana fita, barrister yamaida hankalinsa kanta, yace muradina, nayiwa hajiya maganar bikinmu



Batasan dalili ba, kawai de nan take faduwar gaba ta ziyarceta

Kenan Hakan fa yana nufin shikkenan tarasa Aliyu? Ni Iman na shiga uku karfa nayi Aure da soyaiyar
wani daban acikin zuciya ta



Maganar sace tadawo da ita Daga tunanin datake yace kinyi Shiru, kobakya maraba da angon naki



Ahankali tace I nayi yaya



Matso da fuskarsa yayi dab da Tata cikin muryar sa maisa jiki yamutu yace na matsu Naga na aureki
muradina, na matsu Aure kawai nakeso Kuma dake
Suna wannan halin yasako kansa cikin falon, Baisan dalili ba nan take yaji gefen inda Zuciyar sa take yayi
zafi



Zuba masa ido tayi tana kallansa, saiyau tataba ganinsa da qananun Kaya, sosai kayan yayi masa mugun
kyau, Kodan baicika sakawa bane oho



Barrister Jin Iman tayi Shiru yasa ya kalli inda take kalla

Nan take fara'ah ta wanzu a fuskarsa, yace Bros shigo mana,



Cikin danne kishin sa yashigo falon ya zauna



Ahankali cikin zazzakar muryar ta tace masa Ina yini?

Fuska ahade yace lafiya



Imran yace Bros wannan itace muradina, matar danakeson aura



Kamar Bai santaba yasaki Murmushi yace to Bros Allah yakaimu musha biki

Tashi yayi tsaye yace Bari Naga mamy, batare daya jira amsar dan'uwan nasaba yayi gaba, wanda azahiri
yana kishin ganinta da Ko wanne da namiji ne, hakanne yasa yagudu yabar wajan, kome yake fada mata
suka wani hade Kai Kamar zaiyi kissing dinta, mutsw yasaki tsaki shi kadai



Aliyu na tafiya, barrister yace kiyi hakuri fa, Bai Miki maganaba Daga gaisuwa, haka yake, baida Yawan
magana, pls kada Hakan yabata Miki rai



Cikin ranta tace ah iskanci de ba rashin magana ba

Amma afili saitace babu komai muradina, Hakan tada fada saiya sanyayawa barrister zuciya
*** *** ***



Yana shiga cikin dakin yaganta tana shirya Kayanta cikin wardrobe



Mamy Wai yaushe zamu koma gidane, Naga Har kayanki kike shiryawa Kamar wanda zamu Dade



Zama Zamu yi Har lokacin daka sauwaqewa kanka kadena tunani kawarke ras Kamar Yanda Yaya yace

Nikam ai inabin umarnin sane



Kamar zaiyi kuka cikin shagwabar daya saba mata yace Amma mamy Taya zanji sauqi Bayan yarinyar Nan
tana cikin gidan nan, yanzu fa mamy kinganta can fa afalo tana tare dashi



Yaqarasa maganar Kamar zaiyi kuka



Zuba masa ido mamy tayi ganin karfin Hali irinnasa



Tace to menene danna zauna tare dashi, batare ka gansu ba? Dama can ai tare suke



Amma mamy kamarfa zaiyi mata ki..... Tunawa yayi tare yake d mamy hakanne yahanashi qarasa
maganar tasa



Murmushi tayi, Sarai tagane abinda yake nufi, Dan haka tace baby, banasan fitina kaji Ko, tun wuri ma
kasawa Zuciyar ka salama Akan sha'anin yarinyar Nan, kayi hakuri Kamar Yanda mahaifinka yayi, kukuma
haka Allah yadoramuku



Cikin mamaki yace mamy menene yafaru da daddy din?
Tana shirya kayan nata tace daya nemi mahaifiyarta yarasa, ya hakura yanemeni Kuma yasamu, gashi
Har mun sameka, to kaima inaso ka hakura kaji baby



Mamy Nikam aina Dade da hakura, haba mamy Kamar wanda banajin maganarki



Daria tayi, tasan Sarai yafada ne, domin hankalinta ya kwanta, Amma so Kam yana nan, itade fatanta
daya, Allah yakare mata shi Daga wata rashin lafiyar



Mamy Ina wannan yarinyar ne, kike aiki da kanki?



Mamy tace Wai atika? Yace yes



Nace tatafi gida tahuta, idan zamu koma Abuja saita dawo



Wandonsa na jeans yafara nadewa Daga qasa Kamar wanda zai tsallaka wuta yace to mamy Bari na
shirya Miki



Batayi musu ba tasakar masa



*** *** ***

Washe gari da Rana dukansu Suna zaune Suna cin abinci, Farhan, hajiya, Imran, Aliyu, Iman, mamy



Mamy tayi Shiru tana wani tunani ita kadai, saida tagama yanke shawara ita kadai sannan ta dubi Hajiya
tace Hajiya nikam yaushe Bilkisu zata dawo ne?



Cikin ransa yace Alhmdlh mamy Kamar tasan inda yakemin qaiqayi
Hajiya tace Bilkisu may be muganta da wuri, tace zata lallaba baban su tadawo



Jijjiga Kai mamy tayi tace Yarinyar babu ruwanta, nayaba da hankalinta Kamar Fatima, idan ba'a yi
maganar auranta ba inayiwa Baby Ali sha'awar Auranta



Lokaci daya Iman ta qware da abincin datake ci



Shikuwa gogan

Gabansa ne yayi muguwar faduwa



Sharhi please 🙏🏻



Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖



Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem



15



Dasauri Imran yatashi yazuba ruwa a cup yabata, Har bakinta yakai mata cup din tamkar zai Bata ruwan
da kansa, qirjinta ne yariqe, daqyar take shan numfashi, haka ta karbi ruwan Tasha Dan kadan, hannunta
dafe da kirjinta



Atake mamy tagane Cewa dalilin fadar wannan maganar tatane yasa Iman wannan qwarewar, Kenan
Hakan yana nufin Itama tanasan Aliyu Har yanzu
Hajiya ce tace sannu Iman, nahanaki magana idan anacin abinci Amma bakyaji, yanzu haka nasan may be
magana zakiyi Tunda kinji anyi zancen Bilkisu, Bayan Kuma abinci kikeci



Mamy tace sannu Fatima

Iman Bata Iya cemusu komai ba, Idanunta jajir alamar Taji ajikinta dalilin tarin datayi, ta daga Kai ta kalli
Aliyu, sannan tatashi tsaye tace Hajiya banajin dadi zazzabi nakeji, zanje na kwanta



Miqewa Imran yayi yanufeta tareda kama hannunta daya, dayan hannun nasa Kuma yazagayo dashi ta
kafadarta, yace mata muje dakin

Babu musu tajuya sukayi dakinta



Jikinsa ne yayi sanyi, ya tabbatar dalilin maganar mamy ne yasa yarinyar Nan shiga damuwa lokaci daya,
bayansu yabi da kallo, babu abinda yataba Zuciyar sa irin Yanda Barrister yariqe kafadarta

Nan take ransa yabaci idanunsa suka kada sukai jajir

Spoon din hannunsa ya Ajiye Shima yatashi yafice batare da yakalli Hajiya Ko mamy ba



Hajiya tace ikon Allah Kinga duk sun watse, sai a lokacin Farhan yayi magana yace saini ba



Mamy ce taimasa Daria kawai, domin kuwa tasan dalilin dayasa Aliyu yatashi



Hajiya tace Hajiya fati naji maganarki, ni kaina zanso ace acikin gidannan Bilkisu tayi Aure kokuma cikin
dangi, Amma mahaifinsu yabada ita ga wani yaro daya Daga cikin danginsa



Batare da damuwa ba mamy tace to ai shikkenan



Acan daki kuwa Suna Zuwa tazube agado, kirjinta zafi yake mata sosai, dasauri yafita saigashi yadawo da
magani ahannunsa, daqyar tatashi Tasha maganin, yaja mata blanket yafita Daga dakin
Tun Rana Har dare Iman Bata sake futowa falon ba, tana cikin dakinta akwance, Daga cikin bargo take
goge hawayen dake tsiyaya afuskarta, Yaya zatayi dason Aliyu? Ta tabbatar Zuwa yanzu Kam yadena
kaunarta, Tunda yafuto fili Kai tsaye yace yafison Yaya Imran fiye da ita, gashi yanzu mahaifiyarsa tana
sha'awar ya auri Bilkisu, Kuma bataga ya nuna wani Abu dazai nuna baya kaunar hadin ba, Kenan ita
kadai take haukanta banda shi, tun tana kukan hawaye harta dawo yi afili



Da daddare Suna zaune a falo gaba dayansu,wayarsa yake dannawa Amma gaba daya hankalinsa ba'a
wajan yakeba, yajita Shiru Kamar Bata gidan, ya matsu yaji awanne Hali take ciki



Mamy Kamar tasan abinda yake tunani tace Nikam Hajiya banga takwarata ta futo ba



Tashi Hajiya tayi tace um yanzu haka Taji relief ne tana aikin kallo a computer, Bari inje ingani kar'azo
anamin fishi

Hajiya natafiya dakin Iman, yasaki wata yar qaramar Ajiyar zuciya



Tana shiga ta hangeta ta tuqunqune akarshan gado, sai riskar kuka take ita kadai

Dasauri Hajiya ta karasa tace subhanallah Iman!!

Tafadi haka tana yaye bargon da Iman din ta rufa

Idanunta jajir taci kuka Kamar ba gobe, Hajiya tace nashiga uku Tashi, Tashi muje akaiki asbiti



Dan qaramin mayafi tadauka mata tareda yafa matashi akanta



Gaba daya tasaki jiki ajikin Hajiya, Suna tafiya Iman tana kuka wiwi



Suna Zuwa falon gaba dayansu suka kalleta, Hajiya tace yau Naga takaina Iman kincika raki wallahi, haba
Daga zazzabi saiki kama kuka Kamar wanda akai mutuwa



Jikin mamy ne yayi sanyi, tasan itace silar komai datasan haka dabatayi maganar agabanta ba
Cikin sanyin jiki mamy tace haba Hajiya kidena yi mata fada mana, kika sani Ko akwai abinda yake
damunta Bayan haka

Juyawa tayi ta kalli Iman dake kuka, tace Fatima zazzabin ne Har yanzu? Cikin kuka ta girgiza Kanta tace
mamy qirjinane yakemin ciwo, idan zanyi numfashi sainaji ciwo



Mamy takalli Hajiya tace to ai kinji, Bata lura da Aliyu da Imran dasuke zaune ba tasake Kallan Iman din
tace, Ko kina kwana brezia ajikinki?



Tambayar tabata kunya, danhaka kanta aqasa tace a a mamy



Quri yayi yana kallanta, jiyake dama ciwon yadawo jikinsa ita tahuta



Cikin damuwa Imran yatashi yace Bari muje asbiti Hajiya, yakama hannun Iman suka fara tafiya, juyowa
yayi yace Bros taso muje



Babu musu yatashi yabisu domin kuwa hankalinsa zaifi kwanciya Akan ayi mata komai agabansa Akan
yazauna agida



Barrister kwarara gudu yake, tana kwance Abaya, shida Aliyu agaba, nan da nan suka Isa Juwairiyya clinic
and maternity



Yana parking Aliyu yafuto, Shima Barrister yabude mata motor, Saida yatemaka mata sannan ta futo,
hannunta cikin nasa suka qarasa cikin asbitin

Sun yanki Kati da komai aka turasu wajan wata doctor, mace ce, Suna zama a office din barrister yayi
Mata bayanin abinda yake damun Iman



Tashi tayi tadubata da kanta, sannan sannan tarubuta mata magunguna tabashi tace zanyi mata allura
yanzu insha Allah zataji dadin allurar musanman wajan yin numfashin, yanzu kaje office din gaba zasu
baka sauran magungunan kakawomin
Cikin kulawa yace OK doctor Amma kiyi mata Ahankali Dan Allah banaso Taji zafi kokadan



Murmushi matar tayi tace wow da alama de mijinta ne Ko? Naga kana Bata kulawa Yanda yadace

Sosai yaji dadin maganar Tata yace no, matar dazan aura cede insha Allah, tace masha Allah, gaskiya kun
dace, Kuma kun birgeni, Allah yabada Zaman lafiya



Yace amin, tareda fita



Shikuwa yana zaune Akan kujera yayi Shiru, wato shine baya sonta Tunda baya Bata kulawa, it means
haukan banza yake akanta



Ransa abace, yasake hade girar Sama data qasa



Allura doctor tahada tadubi Iman data Dora kanta Akan cinyarta tace to madam juyo nayi Miki allurar



Ai Iman naji zancen allura tafara yarfe hannu, cikin hawaye tace nide wallahi banason allura



Doctor tadubi Aliyu dayake zaune tace Amma Kai yayantane Ko?

Agajarce yace "eh"



Tace aikam naga alama gashinan Kuna kama sosai, Naga alama Kamar tanajin maganarka, kayi mata
magana tayi hakuri ayi mata allurar



Cikin Jin Haushin maganar doctor tunta dazu yadubi Iman yace "kitsaya ayi Miki, kina Bata mana lokaci"



Doctor cikin ranta tace ah wannan bawasa, saikace wani soja, wannan ai dole Taji maganar sa
Tana yarfe hannu tamiqe tsaye tareda Juyawa doctor baya, alamar tayi mata allurar Kenan



Sunkuyawa doctor tayi tafara yimata allurar, Iman najin shigar allurar tasaki qara tana sake yarfe hannu,
doctor tace kidena motsi fa, karkisa naji Miki ciwo, kisaki jikinki



Iman Kamar bada ita akeba tana yarfe hannu ga hawaye shabe shabe tace ni wallahi banaso



Tashi yayi Daga inda yake yanufesu, baiyi wata wataba yajata jikinsa ya rungume ta tsam afaffadan
qirjinsa



Yadubi doctor yace "yimata"



Tace to tareda Sunkuyawa tanayi mata Allurar



Jinta akirjinsa yasa tayi luf tana shakar qamshin dake Tashi ajikinsa, Shima anasa bangaren hakane,tudun
dayaji akirjinsa na dukiyar fulaninta shine ya sanyashi shiga cikin wani irin yanayi, nan da nan idanunsa
sukai jajir



Basusan tagama allurar ba Saida ta dubesu tace nagama, sannan ya janyeta Daga jikinsa yazauna akujera
cikeda mutuwar jiki



Itama Iman kwanciya tayi Akan kujerar, tana shaqar qamshin sa dayayi saura ajikinta



Suna zaune Shiru, doctor na rubuce rubuce Barrister yakawo magungunan, Saida aka daura mata ruwa
Leda daya yaqare sannan suka tafi gida, ba laifi Taji karfin jikinta dalilin qarin ruwan da aka mata,
dakanta tataka Har Zuwa gaban Mota
Suna Zuwa gida taci abinci Tasha magani sannan tajedaki ta kwanta, Hajiya da mamy Har dakin suka
rakata sannan suka dawo falo Suna fira



*** *** ***

Shabiyu nadare Suna zaune adaki shida barrister, takardu ne agabansa yana cikewa, fira suke jefi jefi

Hankalin Aliyu Kam baya tare dashi, tunani yake Ko yanzu Taji sauqi? Yasan de Zuwa yanzu insha Allah
zataji relief Tunda sun Dade da dawowa Daga asbiti



Tashi yayi yakalli barrister yace Bros Bari naje wajan mamy nadawo, Barrister yace OK



Futowa yayi yanufi part dinsu Hajiya, babu kowa a falon, tsayawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login