Showing 9001 words to 12000 words out of 39414 words
*** ***
Tunda sukai wannan mgnr da Iman acht ya tsinci kansa cikin farin ciki, shida kansa yasan yasauya, komai
yanayinsa cikin walwala, hatta da abokan aikinsa sun fahinci Hakan, saide musty ne kawai yasan sirrin
Mamy kanta tana lura da yanayinsa, saide tayi Murmushi taqara godewa Allah, daya karkato mata da
hankalin danta izuwa abinda takeso
Kamar Koda yaushe yauma break sukeyi shida mamy, atika tana goge kayan falon, Bayan tagama
mopping
Ruwan tea yakesha Amma wayarsa tana hannunsa yana danne danne, wanda azahiri pic din Iman yake
kalla, mamy data kula hankalin sa baya Kan abincin
Tayi Murmushi tace" baby mekake kalla ne bakasan cin abinci? "
Kamar wani marar gaskiya haka yadauko wayarsa yanuna mata screen din wayar,
Pic din Iman tagani, tace to yanzu Haidar aida kabari kagama saikaje kayi ta kallanta Ko"
Babu kunya Aliyu yace "mamy ai idan Ina ganin photon zanfi cin abincin?"
Girgiza kanta mamy tayi, tace um duniya Ina Zaki damu?
Wai yau Kaine me kallana kace in kana ganin girl friend dinka zakafi cin abinci
Sai a lokacin ya lura da katobarar dayayi, ashefa mamy ce
Dan haka kawai saiyayi Shiru yana sosa kansa, wayar ya ajiye asaman dining din sannan yamaida
hankalin sa Kan tea din dayakesha
Mamy data zuba masa ido tana kallansa cikin ranta tace damafa hakane, duk wanda zakaga baya kule
kulen yanmata, Ko Kuma yanmatan Suna sonsa baya saurarensu qarshe sai kaga soyaiyar wata daban
tana wahalar dasu
Farfesun datasa atika tayi, tadauko flet tazuba masa, spoon tasa tadiba ta nufi bakinsa dashi, tace "dauki
wayarka kayi kallanka, saina baka abincin,
Shima baiyi musuba yadauki wayar, yana kallan pictures din Iman mamy Kuma na bashi abinci
Saida ta tabbatar ya qoshi sannan ta qyaleshi
Tissue yadauka yana goge bakinsa, yace" mamy ai dole ne inkira Bros awaya in bashi labarin yarinyar
Nan, "
To ai daka Bari idan muka koma gida saika fada masa, Nima sainayiwa Yaya magana, kaga sai manya su
shiga cikin maganar
" to shikkenan mamy nah yanzu Bari inji muryarsa kawai, ni kada ma yayi fishi, kullum saide yakirani
bancika nemansa ba
Ringing biyu wayar tayi, akayi picking Daga dayan bangaren
"Bros ya akayi?
Aliyu yace "normal ya gida ya harkoki, dafatan mutanan gida kowa lafiya
Lafiyarmu kalau Bros, kasan akwai wasu zafafan motoci Ahmad muhd marzuq yakawosu Daga Cairo,
inaso saika dawo Nigeria saimuje mu siyosu, but yaushe zaka dawo ne,? Saina tura masa da kudin da
wuri
Murmushi Aliyu yayi, yace no, wannan Karon bakaine zaka siya manaba, nine zan siya mana
Shima yace no Bros
Aliyu ma yace karka damu, ai ABIN BROS NA BROS NE
Daria sukasa gaba dayansu, sannan sukai sallama
Mamy tace wato Aliyu bazaku Dena wannan sarar taku bako?
Yana Daria yace mamy ai wasa ne kawai
*** *** ***
Tundaga wannan lokacin Iman Bata sake magana da Aliyu ba, Har tsawon kwana biyar, adede wannan
lokacin Har hutunsu yaqare sunkoma school, sai yau yayanke shawarar kiranta awaya, domin yasan
Cewa Zuwa wannan lokacin ai ta Riga data gama yanke shawara
Tana zaune adakinsu ita kadai, su Billy sun fita itada yusy, taji wayarta na ringing
Zuciyar ta daya tadauka, cikin Isa da taqama irin tasa yayi Mata sallama
Bata Gane wayeba, kawai de abinda tasani shine taga number wata qasar tana kiranta, amsawa tayi
tareda Cewa waye
Agajarce yace Ali Sa'ad
Lokaci guda ta ganeshi, tace OK yakake
Kai tsaye yace Alhmdlh,
Dama nakirane inji Yaya kike, sannan Kuma me kika yanke game da maganar da mukayi
Handout din dake hannunta ta ajiye tace kasan abinda ake nufi da Trailer irin babbar motar Nan?
Da mamaki yace nasani mana,
To Kamar haka samari na suke, inada samari dayawa, akwai wanda nakeso, da Kuma wanda banaso
Cikin yarda da Kai da Kuma ji dakai irin nasa yace "zanso shiga daya Daga cikin wannan motocin, harma
nazama nine nake Jan motar watarana
Taqamarsa ce tasata Daria, tace bazaka iyaba, domin sudin ba qananun qwari bane Kamar Yanda kake
tunani
" kidena hadani da irin wannan samarin, nasan kaina, ni ba irin su bane, Zaki Gane hakanne idan kika
bani dama guda daya tak, damar kuwa itace ki amince da soyaiya ta, zakiga Yanda zanyi fatali da
gwamnatin kowa, tawa gwamnatin ce kawai zata mulki birnin Zuciyar Ki
Aranta tace waishi irin jiji da kannan zai nuna min, nikuwa zan nuna masa yayi kadan, zanga karshan
qaryar tasa
Domin ta qureshi tace shikkenan nabaka dama
Wani sanyi yaji acikin ransa, Murmushin Nan take ya wanzu a fuskarsa yace godia nake MATAR ALIYU
yakashe wayarsa
*** *** ***
Wayar ta riqe a hannunta cike da mamaki, afili tace waishi ji yake irin babban qwaron nanne a soyaiya
Karatun ta taci gaba dayi, tana cikin karatun su yusy suka dawo
Suna zama ta dubi yusy tace Besty wannan gayen fa yakirani yanzu, Nan tabata labarin komai
Yusra tace ai kuwa zamu qureshi, muga karshan cika bakin nasa
Bilkisu tana jinsu tatabe baki tayi Shiru, to basu sata acikiba, yanzu tana magana Yaya Iman zata hauta da
bala'i
*** *** ***
Tundaga wannan lokaci Aliyu yafara shigar da kansa awajan Iman, Kiran safe daban, na Rana daban na
dare wannan daban ne
Wataran tayi picking wataran Kuma ta share shi
Duk lokacin da taqi dagawa yusra ce maiyi mata fada Akan ta saurareshi ai Suna so su qureshi ne
Ahankali take kulashi, harya kasan ce kullum sai sunyi chatting
Kamar kullum yauma Suna chatting taje tasaka pictures dinta a status masu zafi
Bata dauki lokaci dasakawa ba, kiransa yashigo cikin wayarta
Tana dagawa, yace "kije kicire pictures din dakika saka yanzu,
" meyasa zan cire? "
Damafa Ina sakawa
Zuciyar sa na quna yace nasani, nikwa nasan kina sakawa, Amma abinda nakeso kisani shine, Ina sonki,
Qasa yayi da muryarsa cikin Shagwaba yace" Ina kishinki Iman, bazan Iya ganin pictures dinki wasu
mazan Suna kallah ba
"batasan meyasaba haka kawai ta tsinci kanta da Cewa to shikkenan Bari nacire
Tana cire pictures din, tarufe datar Tama gaba daya
Duniyar tunani tafada, shi wannan yana sonta, yana kishinta bayasan wasu mazan suga pictures dinta
Haqiqa kowacce mace tanaso asota, Kuma nuna kishi shine alamun soyaiya, Aliyu halinsa daya yar'uwar
ta Bilkisu, inama ita yanema da farko, da halaiyarsu ta dace da Juna, Bilkisu tana saka Kaya na kirki na
mutunci, Bata da rigima, Kuma Bata da magana, Haka Kuma saka pictures dinta a yanar gizo Bai
dametaba
Shikuma wannan
yasonta, yana Bata kowacce irin kulawa, Amma Kuma shine yake kaita wajan photo da kansa tadauka,
harma tasa a Internet Amma Bai taba hanataba
It means yana sonta, bayasan ganin laifinta, yana Bata dama tayi duk abinda takeso
Runtse Idanunta tayi, kanta fa yafara daukar zafi
Jaruman maza guda biyu, ma banbanta awajan Halaiya
Yusra na bacci, Sai Billy dake zaune a gefe duk tana kallan duk wani motsi na yar'uwar Tata
Duban ta tayi tare da Cewa Yaya Iman ya akayi ne? Meyake damunki?
Wayarta ta ajiye a gefe daya, sannan takamo hannun yar'uwar Tata,
Bilkisu cike da mamakin yayar Tata tace Yaya Iman, keda waye kike waya yanzu?
Bata amsa mata tambayar tataba tace "Bilkisu idan mutum yana kishinka me Hakan yake nufi?
Manyan idanuwanta ta juya tace Yaya Iman Hakan yana nufin yana sonki ne mana
Jijjiga kanta tayi, sannan tasake jefo mata wata tambayar
" Tokuma yanzu misali kece mutum biyu suke sonki, daya yana kishinki, daya Kuma yana nuna Miki
soyaiya Amma Bai cika nuna Miki kishi ba, kullum zakici kwalliya ki fita babu ruwansa da wanda zai ganki
da wanda bazai ganki ba
Abu daya kawai yasani shine kece Muradinsa
Shin wazaki zaba acikinsu?
Murmushi Bilkisu tayi Kamar ba yar'uwarta ce take cikin damuwa ba
Tace "Yaya Iman, idan na fahinceki kina magana ne Akan Yaya Imran da Kuma wannan sabon boyfriend
din naki dakika yi, Yaya Iman ki godewa Allah, Yaya Imran yana sonki, yana qaunarki,, kowa dayake
familynmu ya shaida Hakan, bance Miki wannan sabon saurayin naki baya sonki ba, a a
Amma abinda Zaki duba shine, Yaya Imran dashi muka tashi, yasanki, kinsan shi, yana sonki, kina sonshi
To meyasa ma Zaki tantama a kansa?
Ki godewa Allah da baba yabaki dama kika saurari Imran, kinsan halin mahaifin mu Yaya Iman
Kina gani de, Ina zaune yakawo Haroon yace shine mijina, shine wanda zan aura, baya sona, Bana sonsa,
Amma ahaka nayi hakuri nayi masa biyaiya
Yaya Iman ni kadai ma na isheki ishara, dazatasa kici gaba dason Yaya Imran
Ni yanzu na Isa na saurari wani namiji Bayan Haroon? Ban isaba, Tunda umarnin babane Hakan
Maganar dakikemin ta innice wazan zaba Kuma, shine idan nice adduah zanyi, Allah yaciremin son sabon
saurayin araina
Shikkenan an zauna lafiya
Iman tace "nagode da shawarar Ki Bilkisu, insha Allah zanyi Yanda kika ce
Itama Billy cikin Murmushi tace yauwa Yaya Iman
Rungume Juna sukayi cike da kaunar juna
*** *** ***
Agajiye yadawo Daga wajan aiki
Hajiya dake sake gwadawa Zeey auta home work, ta dubeshi tace sannu Imran
Kaine bakasan zama, kullum cikin yawo kake
Cike da Shagwaba yace to hajiya ai hujjoji nake nema, Kuma yanzu ai shari'ar ma taqare, nine nayi
winning
Murmushi tasaki tace to Dana, Allah yaqara temakawa
Duban zainab tayi tace auta riqe littafinki nabaka Yaya abinci Ko?
Kyabe fuska yarinyar tayi alamun kuka
Imran na ganin haka yace Hajiya zauna, Naga alama Yan gidannan gaba dayansu kishi suke Dani
Ai Gara Zeey Akan Farhan ma
Kusha Zaman ku Bari inje inyi Sarving din kaina
Yana gama fadar haka yatashi yayi dinning
Bayan yagama yadawo wajan hajiya, lokacin zainab tatashi, kansa yashafa yana kallanta
Murmushi tayi tace Imran Dina, Kamar akwai abinda yake damunka Ko?
Sosa kansa yayi sannan yace Hajiya dama inaso ne kifadawa Alhaji idan su Iman sun qare semester dinsu
sun dawo, Dan Allah dasun dawo atsaida ranar bikinmu
Yana gama fadar Hakan, yatashi yayi part dinsa kansa aqasa
Ha'ba hajiya takama, oh yaran yanzu zai Ahankali, Imran Ko kunya babu? To dama Yanda ake wannan
rashin kunyar agabanta shida Iman, ai yaran nata Suna gamawa za'a tsaida lokacin biki ayi kowama
yahuta
*** *** ***
Kuka take sosai, Idanunta sunyi jajir, yusy ce me rarrashinta
Best ki fadamin mana me yake damunki ne Wai? Ko akwai abinda yake faruwa a gida?
Girgiza kanta tayi alamun a a
Yusy tace nashiga uku, Kinga Bari nakira Barrister nafada masa
Dasauri tariqe hannunta, cikin kuka tace yusy.... Pls.. Karki kirashi, nashiga ukuna Besty Yaya zanyi?
Nifa Iman kin dauremin Kai, Dan Allah ki sanar Dani me yake faruwa
Kasancewarta fara yasa kukan datasha yasa Kan hancinta yayi jajir
Cikin kukan tadago da kanta ta kalli Yusra tace
"Besty nashiga ukuna wallahi Ina sonsa"
Adede wannan lokacin Billy tashigo cikin dakin, wannan maganar ce tasauka akunnanta
Iman taci gaba da Cewa
"Bansan yaushe Hakan tafaru ba, bilkisu tabani shawara, Kuma nayi Amfani da ita, duk addu'oin
danakeyi abinma qaruwa naji yanayi
Halayensa, kulawarsa agareni, ajinsa da komai Nasa sunja hankalina, wallahi idan ban sameshi ba
ayanda nakeji cikin zuciya ta Besty akwai matsala
Nashiga ukuna, shikkenan nazama butulu ni Iman "
Cikin zafin rai Billy dake gefe aqame, tace" Butulu kuwa ta gaske Yaya Iman "
Dukansu Juyawa sukai suka kalleta, domin kuwa ba Susan da zuwanta ba
Cikin hawaye Iman tace Dr.
Daga mata hannu Billy tayi tace, babu wani Dr. Ayau Yaya Iman, wallahi kin bani mamaki, Har yaushe
Zaki Bari Zuciyar Ki takamu dason wani bare, bakisanshi ba, besankiba, haduwar network, Har yaushe
Zaki soshi Akan Yaya Imran?
Ina shawarar Dana baki Yaya Iman? Tsautsayin dayasa kika amince dashi shi zaisa kije kirabu dashi
Wani lokacin kina bani mamaki Yaya Iman, Wai kokin manta da wacece Hajiya awajanmu ne?
Halaccin Hajiya agaremu Dani, dake, da baba, kadai ya Isa yasa kiso Yaya Imran
Yusy dake gefe ta dafe kanta da hannunta duka biyu, tace ni duk kun dauremin Kai wallahi
Please ku fadamin wacece HAJIYA? Kuma Yaya kuke da BARRISTER IMRAN?
(tonima de inaso naji wacece hajiya,🤔)
(Anya kuwa Hatsaniyar da Iman ta debo me bullewace 😱😱?
Ba anan Hatsaniyar ta qare ba, fatana kuci gaba da hakurin bibiyata
Share
Comments
Sharhi
Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
9
Alhaji Abubakar, shine cikakken sunan Mai gidan, gogaggen Dan kasuwa ne, daya Shahara aharkar Saida
yari
Yanada shaguna dayawa akano duk na Saida yari ne, mugun me kudi ne dayasan mutane dayawa
manyan Yan kasuwa dakuma manyan Yan gwamnati
Matarsa daya Hajiya Maryam, wadda ake Kira da Hajiya, tana business dinta a gida, tana Saida kayan
mata irin su less da shadda da atamfofi, idan mutum yatashi Aure kawai waya za'a yi mata tahada kayan
lefe saidai kawai katura mata da kudin ta account
Yawan sanyin halin ta da haba haba datake da jama'ah yasa mutane dayawa suka Santa
Kowa kataba Hajiya Maryam hajiya Maryam
Sai Maryam din tabuya, kowa yake kiranta da Hajiya
Hatta da yaran gidan Hajiya suke kiranta, Alhaji Abubakar da kansa Shima Hajiya yake Cewa
Ita Ana kiranta da Hajiya, shikuma suke kiransa da Alhaji, wani lokacin suce Alhaji wataran Kuma suce
Abba, Amma alhajin yafi yawa
Yanada zafi, musanman Akan iyalansa, shi mutum ne Mai magana daya, idan yayita tota zauna agidansa,
zaiyi wahala yayi Maka magana biyu
Kowa na gidan shakkarsa yake, more especially yayansa
Lokaci dadama saide yaran suyiwa Hajiya magana Akan su tunkareshi da magana, saide suce Hajiya
kifadawa Alhaji Abu kaza
Taurin Kai Gare shi Kamar mutanan farko
Mutum ne Mai aqida daya
Dansa na farko shine Imran, cikakken saura yi Mai aji dakuma qwalisa
Baida Yawan magana sosai, idan kaga yana zuba surutu tofa saide da Yan gidansu ne
Yana 33 years yanzu,yayi karatunsa na bangaren lauya degree da masters yanzu yana aiki A hight court
dake Garin kano
Sai Farhan dayake 23 year's
Yagama degree na farko ajami'ar ghanah
Saikuma yar auta wato zainab
Hajiya Maryam tanada yar'uwa guda daya, wadda suka tashi tare Kamar wasu Yan biyu sunanta ZAINAB
hawaye bilkisu dake bada labari ta share, sannan taci gaba dacewa,wannan ZAINAB din itace
mahaifiyarmu Nida Yaya Iman, agarin katsina aka haifemu, Bayan mun girma munyi wayo, Allah yahada
mahaifiyarmu da cutar asma, Bata dauki tsawon lokaci ba, tana Fama da wannan jinyar Allah yayi Mata
rasuwa
Awajan mahaifinmu mukaci gaba da zama, dagamu saishi a gida, yau muci me dadi gobe muci akasin
haka, kasancewarsa talaka
Ganin dagamu saishi a gida ne yasa mutane suka fara surutu Akan ya ajiye mu a gida shibai nemi mace
ya aura ba,da wannan damar Hajiya tayi amfani wajan nunawa baba tanason riqonmu yadawo hannunta
Bamusan dalili ba haka baba yaqi yarda, agabanmu Hajiya take zarya tsakanin kano da katsina, Akan
baba yabata mu Amma yaqi, daqyar ya yarda yabata Yaya Iman, nikuma na zauna ahannunsa, Kuma Har
gobe Bamusan dalilin dayasa baba baya Shiri da yan'gidan Hajiya ba, kwata Kwata bayaso yaga mun rabi
Hajiya, gashi Kuma itace kadai muka sani wadda zamu Kallah amatsayin mahaifiyarmu
Zamana da baba mu biyu a gida ne yasa baba ya auri wata yarinya Mai hankali nuriyya, muna kiranta da
anty
Yanzu haka yaranta biyu tareda baba, mace da namiji
Riqon Yaya Iman yana dawowa hannun Hajiya komai yasauya
Sai abinda Iman takeso akeyi agidan, ke Hatta abinci sai wanda Yaya Iman takeso akeyi agidan
Tasamu kulawa sosai, Baga Alhaji ba, Baga Hajiya ba
Saikuma Barrister daya dauki son Dunia yadora mata
Tunda tazo gidan, ya wayar mata dakai, kasancewarsa mutum wayaiye, duk wani abin gayu na qawata
mace budurwa Imran yayiwa Yaya Iman shi
Shine yakoya mata Yanda zata soshi tun Bamusan kanmu ba, Haka Hajiya Bata taba nuna mana wani
banbanci ba tsakaninmu da yaranta
Idan ta nuna ma to mu taso Akan yaranta
Kuma Har gobe idan kikaje gidan Hajiya idan ba fada Miki akayiba, bazakice ba itace ta haifemu ba
Umma kawai haifarmu tayi da renonmu nadan wani lokaci, Amma Hajiya itace komai namu
Duk zafin Alhaji, shi da kansa yana son Yaya Iman, domin kuwa da kansa yasai mata Mota, wadda muke
yawanmu aciki, muje duk inda ranmu keso
Yusy ta duba sannan tace Kuma ahakan idan ban Kira Yaya Iman da butulu ba, da wannne Suna kikeso na
kirata saboda tana nema taqi jinin Hajiya?
Sake duban Iman tayi sannan tace da kinqi da kinso Yaya Imran jinin Hajiya ne Kuma shi muka sani
bawani bare ba, Dan haka shi Zaki aura
Cikin fada tace wallahi bilkisu idan bakimin Shiru ba zan sabar Miki anan wajan
Itama cikin Haushi tace a a to Yaya Iman saboda me bazan fadi gaskyaba
Dakeda yusy Yanda kukaje kuka qullah haka zakuje ku warware
Baqin ciki ne yakama Iman, cikin kuka tace to Wai Dan Allah Nina dorawa kaina sonsa ne?
Nimafa haka naji, shikkenan Zaki zauna kinamin rashin kunya, Wai harda Cewa haduwar network
Shiru bilkisu tayi tana kallan yar'uwar Tata da karfin Hali
Tace ikon Allah, to Yaya Iman ba haduwar network din bane? Qarya nayi?
Itama cikin kuka tace Ko haduwar iska ne ahakan Yamin, Kuma inasonsa, bazan Dena sonsa ba, inyaso
Haushi yakashe ki
Abin natama saiya Bawa Billy Daria, Dan haka batace mata komai ba, tayi Daria kawai ta kwanta, tareda
juya musu baya
Sai asannan yusra tasaki nannauyar Ajiyar zuciya, tace Gaskiya Teemah al'amarin Nan ba Dan qarami
bane, ni inda nasan tun farko haka kuke da barrister gaskiya da bazan baki damar kallan namiji Bama
bare ince ki saurareshi
Kanta ta Jijjiga cikeda gamsuwa sannan taci gaba da Cewa Barrister mutum ne Teemah
Dole ki Rabu da Ali Sa'ad
Cikeda masifa ta Daga Kai ta kalli yusra tace dallah malama Niki kyaleni, duk ba kece kika sani kulashiba,
Kuma yanzu zakice narabu dashi, anqi arabu dashi din, banzaye kawai
Tatashi fuuuuuu tayi waje
Billy najinsu tana ta Daria qasa qasa, ita kadai
*** *** ***
Kinsan me?
Teddyn dake gefen gadon ta taja ta rungume sannan tace "um um saika fada"
Inaso ne kibani dama nazo Ghana naganki, but da sharadin saina gama da wannan seminar din
Cikin shauqi da Jin dadi tace kabari saina koma Nigeria saikazo, saboda yanzu semester dinmu yayi Nisa
Shima cikin wani irin shauqi yace kin amince Bayan kin koma Nigeria nataho Nida mamy nah duka muzo
gidanku?
Batare da tantamaba tace why not
(nikwa nace jama'ah a wanne gidan 🤔🤔)??
Zara zaran gashin idanunsa ya Lumshe cikin Jin dadin Yanda yasamu karbuwa awajan ta, yasan Cewa
Zuwa wannan lokacin idan baiyi fatali da kowanne namiji acikin ranta ba Toya kusa
Domin tabbatar da Hakan saiyace Ina samari?
Zuwa wannan lokacin babu kowanne irin tsoro acikin Zuciyar Iman, Yanda take jinsa acikin ranta gani
take bazata Iya boye masa komai daya shafeta ba
Dan haka tace, samari Suna Nan kalau
Cikin taqaicaccan Murmushi yace, wato ban koresu ba Kenan duk Suna Nan Kamar da
Wannan karfin halin nasa yana birgeta, yanada iko Kamar wata Matarsa
Tace, kayi nasarar korar kowa but banda mutum daya
Cikin mamaki yace waye Hakan?
Kai tsaye tace MURADINA
mamaki ne yakamashi yace shikuma hakane sunansa?
Idanunta alumshe tace bahaka sunansa ba, kawai de munhana Juna fadar sunanmu ne, saide wannan
sunan
Cikin dakiya yace Zanso kituromin pic din wannan muradin naki naganshi
Kai tsaye tace OK, tareda kashe wayar
Zuwa tayi tatura masa ta whatspp, already yana online Dan haka Nan take ta tura masa pic din Barrister
Imran
Akwance yake agado,