Showing 15001 words to 18000 words out of 39414 words
Iman, Hajiya ni
zatayiwa fada Cewa ba kula dakeba, Kamar Yanda Kema idan nice Hakan tafaru Dani fada zakisha
Kina nan kinata Haqilo akansa, Bama lalle shi yanayi Miki irin wannan soyaiyar ba
Cikin yatsina fuska alamar tanajin zazzabin tace Bilkisu yana sona wallahi
Kawai de Bansan meyasa yace bazai Iya Aure naba, Kuma Bansan alaqar datake tsakaninsu da Yaya
Imran Ba, Amma Ina komawa gida zan tambayeshi naji
Karma kifara Hakan Yaya Iman, Kema kinsan dole Yaya Imran zai tambayeki Ina kika hadu dashi,? Kuma
kinsan Cewa de Bai baki damar kula kowaba, tun kafin mukai yanzu
Toshikkenan na hakura da tambayar nashi, Amma gaskiya inason Aliyu, bazan Iya mantawa dashiba
Yayar tata tabata tausayi, Dan haka tace to Yaya Iman Allah yayi mana zabi mafi alkhairi,
Tashi Kisha magani, mutafi, kibazaki Iya rubuta exam dinba?
Cikin dauria tace zan Iya, muje
Tashi sukai, suka tafi, already yusy tatafi, dayake Suna zana exam dinsu na qarshe ne
*** *** ***
Yana kwance Akan kujera, yadora kansa Akan cinyar mamy
Lallausar sumar kansa tasha tace, baby Kamar jikinka akwai zazzabi, Ko de asbitin nan zamu koma ne?
Cikin shagwaba yace mamy Allah nawarke fa, kinjifa
Yafadi Hakan yanajan hannunta yadora awuyansa
Murmushi tayi tace Aliyu Kenan, tasan Cewa kawai yafadane, Amma yanajin jiki, yade boye mata ne
gudun kada tashiga damuwa
Waya tadauka takira doctor tasanar dashi yanayin jikin na Aliyu, babu dadewa Yazo Har gidan
Yana gama aunashi yadago kansa Cikeda damuwa yace Hajiya, Har yanzu fa BP yana nan Yanda yake,
dole saikin sake dagewa Akan rashin lafiyar Yaron ki
Mamy Kasa magana tayi, haka doctor yayi masa allurai yatafi
Aliyu naji mamy tayi Shiru, yadago da kansa yace mamy ki kwantar da hankalinki.....
Bai qarasa magana ba ta dakatar dashi, Zuciyar ta karyewa tayi Saida tafashe da kuka tace dakata Aliyu,
sai yaushe ne zaku Dena cemin in kwantar da hankali na?
Saika mutu kaima narasaka Kamar daddynka Ko?
Tafadi Hakan idanunta jajir
Jikinsa ne yayi sanyi, yama Kasa yimata magana, yasan Cewa tabbas yasa mamynsa a damuwa, dole zai
San matakin dazai dauka Akan haka
Mamy Bata sake ce masa komai ba, tadauki waya takira yayan mijinta
Bugu daya aka Daga wayar tata
Cikin kuka tace Yaya Ina wuni?
"lafiya Fatima, meyake faruwa ne naji kina kuka?
Wallahi Yaya Aliyu ne bashi da lafiya, tsawon sati biyu Kenan kullum Bama cikin kwanciyar hankali, yanzu
ahalin da ake ciki likita yace yanada hawan jini, dole yarage damuwa
Amma Aliyu yaqi Jina, shine nace zan fadama, Saika fada masa da kanka, kozaifi Jin maganar taka Akan
tawa
Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yanzu Fatima dannawa ne yake kwance a gadon asbiti babu lafiya, kikasa
sanar Dani inzo Inga halin dakuke ciki?
Hawaye ta share tace bahaka bane Yaya.....
Ya'isa Fatima, waikoke kadai kike da iko Akan Aliyu ne?
Cikin girmamawa tace a a Yaya
To inbaso kike ki nunamin iko Akan Aliyu ba, nabaku kwana daya ku tattaro yanaku yanaku kudawo gida,
Kuma ba Abuja zaku sauka ba anan gida zaku zauna Har sai jikin yarona yayi kyau, yazaki barmin yaro ya
lalace da jinya Fatima
Mamy tace kayi Hakuri Yaya
Cikin fada yace kinji abinda nafada Miki de, yakashe wayar
Mamy tagoge hawayen idonta tace basai na maimaita maba, ai kaji abinda yace, Itama tatashi tayi cikin
daki
Tana tafiya yadafe goshinsa cikeda damuwa, shikkenan Kuma komai ya lalace ai Tunda mamy tafadawa
wannan masifaffan, ai dolensa yakoma
*** *** ***
Yusy kide cika alqawarin dakika dauka, Dan Allah kidaure watarana kizomin katsina, Kinga Yaya Iman
kullum Kuna tare akano
Karki damu doctor Billy insha Allah zan shigo Miki
Farhan dayazo Airport daukarsu yace Dan Allah malamai kushigo mutafi, haba a dinga fira de
Iman tace to jarababbe ai Kuma mun dawo saita Allah
Yusy ce tayi musu sallama tatafi, yayinda suma suka shiga Mota Farhan yajasu sai gida
Suna Zuwa gida Zeey tataho da gudu ta taryesu, Billy tace iyeee mamana fa yanmata take zama
Iman tace Kuma tana qara fitsarewa ba
Buga kafafunta tafara yi aqasa tace anty Bilkisu kinji ta Ko
Kama hannunta Billy tayi tace Rabu da Yaya Iman mamana, nan sukai ciki gaba daya
Hajiya bakinta Kamar gonar auduga, yau taga yayanta
Saida sukai wanka, sannan suka Suka nufi dinning dukansu domin cin abinci
Hajiya tace Bilkisu yaude babu inda Zaki tafi, kibari idan kika huta gobe saiki wuce katsina, kikira babanku
kifada masa sai gobe Zaki tafi
To Hajiya, zan sanar dashi, inji Bilkisu, cikin ranta tana adduah, Allah yasa Kar yayi Mata fadan daya saba
Iman ce ta kalli ko'ina Bata ganshi ba, tajuya de taga babu wanda yake da niyyar yi mata zancensa
Ta dubi Farhan zatai magana ya katseta
Muradin ki kike nema, baya nan yatafi Abuja, sai gobe zai dawo
Gaba dayansu sukasa Daria harda Hajiya da kanta
*** *** ***
Suna idar da sallar asuba Hajiya taje dakin nasu tace toyau babu komawa bacci, munada baqi, atashi
ashiga kitchen
Dukansu suka hadu a kitchen din, Iman tafi kowa dagewa wajan girki, Jin Hajiya tace Yaya Imran yana
hanya
Bilkisu aranta tace oh Yaya Iman Kamar ba itace take Cewa Bata sonsa ba
Abinci suka hada Mai rai da lafiya, aka jera komai a dinning
Hajiya suka Bari suka koma daki, Bilkisu tafada Kan gado tace Kai wallahi saina huta zan shiga wanka,
nagaji
Iman ma tace ai in kika ce hutu dayama Kenan, Itama zama tayi tana daddana waya, fira suke gwanin
sha'awa abinsu
Iman wata yar qaramar Riga ce ajikinta, takama jikinta rigar, na shanun nan gasu nan atsaye, sai sket din
jeans
Bilkisu Kuma doguwar Riga ce ajikin ta, Amma roba ce rigar, hips dinnan ya baiyyana muraran
Hon sukaji anyi da karfi,atare suka ce Kai waye wannan
Billy tace Bari muga Ko Yaya Imran ne, Tafadi haka tana Daga labulen window
Abinda taganine yasata Cewa la'ila sojoji Yaya Iman
Da mamaki Iman tace mun shiga uku mezai hadamu da sojoji, lokaci daya jiniyar motocin suka cika
unguwa
Billy ce tayi karfin Hali tace zomuje falon, Tafadi Hakan tana Jan hannun Iman
Adede lokacin dasu Iman suka futo falon, suma alokacin suka sako kansu cikin falon, mamy ce Akan
gaba, sai Aliyu da Imran abayanta
Daskarewa Iman tayi atsaye
Shima anasa bangaren gabansa ne yayi muguwar faduwa, meya kawo wannan yarinyar gidansu BROS?
Billy tana ganinsa taganeshi, ita kanta ta razana da ganinsa
Cikin farin ciki hajiya ta karbi handbag Din hannun mamy, tana Cewa Hajiya fati sannunku da Zuwa
Tajuya ta kalli su Iman dasukai mutuwar tsaye tace Bilkisu bakwa ganin baqi ne Wai kun tsaya Kuna
kallansu kun barsu da Kaya ahannu
Billy ce tayi diri diri Tama rasa Yaya zatayi,Daga qarshe de takarbi jakar hannun hajiya
Hajiya ta dubi mamy sannan tace Hajiya Fatima wannan fa yaran Zainab ne yar'uwata
Mamy tana Kai idonta Kan Iman kallo daya tayi mata taganeta, cikin ranta tace akwai babbar matsala
Kenan
Amma afili saita saki Murmushi tace masha Allah, waisu ne suka girma haka?
Hajiya tace eh wallahi "
Sannan ta kalli Iman data tsaya Kamar gunki ta dalla mata harara tace cikin fada, Iman me yake damunki
ne kin tsaya Akan mutane kina aikin kallansu
Nuna mamy tayi da hannunta tace wannan Matar qanin Alhaji ce daya rasu, wannan na Abujan danake
Baku labari Alhaji Sa'ad
Sannan ta nuna Aliyu dayayi mutuwar tsaye tace wannan Kuma Haidar ne danta,BROS din Imran Kenan
Ahankali Bilkisu tace tab lalle Yaya Iman kina cikin Dalalaπ€π€
(tonima de nace Iman tana cikin dalala, kuyi hakuri jiya kinjini shiru wallahi naje unguwa ne, bansamu
zama ba,)
Wannan page din kukadai naturawa a Facebook saboda qorafin da kukaimin na rashin babbar waya
@Maman mamaaa
Team din Aliyu
Team din barrister
Tofa saikunyi hakuri dukanku ππdomin kuwa abubuwa da dama zasu faru a wannan Zaman na gida
daya
Sharhi pls ππ»
Mrs Usman ce βπ»βπ»WAZAN
βπ»βπ» ZABA?πβπ»βπ»
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
13
Kallan su Aliyun tayi, tasaki yar qaramar dariyar yaqe
Ahankali cikin siririyar muryarta tace Sannan ku dazuwa, Kai tsaye Imran ta tunkara zata karbi jakar
hannunsa, kashe mata ido daya yayi, sannan cikin kulawa yace no barshi, karbi ta hannun Bros, shine
baida lafiya, yana fadar haka yayi ciki
Shikuwa gogan nan take yahade rai Kamar an aiko masa da mutuwa, yakoma sojansa, Yanda yayi Kamar
arayuwarsa Bai taba sanin wata Iman ba
Ahankali takai hannunta zata karbi jakar, baiyi mata musu ba yabata,Garin karbar jakar hannunsu yagogi
na juna
Gaba dayansu wani irin shork ya ziyarcesu, atare suka kalli junansu, saide Yanda taga ya tamke fuska
Kamar wani kumurci hakanne yasa cikin sauri tajuya da jakar tayi cikin daki Itama
Dukansu Suka baje a luntsuma luntsuman kujerun falon
Mamy tacire mayafinta tace Kai tafiya yankin azaba
Wallahi nagaji
Hajiya tace ai dole ku gaji hajiya Fatima, tundaga Abuja amota, meyasa Baku biyo jirgi bane?
Nuna Aliyu tayi tace rigimar danki mana, Wai akwai mutanan dazai gani a Abuja domin ya turasu
Switzerland su wakilceshi, Akan qarasa seminar dayaje
Tokuma daya gama memakon mu biyo jirgin shine yace mutafi amota, yaga gari
Hajiya tace ashe sun gama qulla abin su shiyasa jiya Imran yacemin shikam yatafi Abuja, bazai Iya jira
harku zoba, shi Tunda aka fada masa rashin lafiyar Aliyu shikkenan yadaga hankalinsa da gashi Har Alhaji
Duban Aliyun hajiya tayi sannan taci gaba da Cewa Aliyu yajikin Naka?
Saida yashafa sumar kansa sannan yace cikin Murmushi Dasauqi hajiya, dafatan mun sameku lafiya
Cikin farin ciki tace Lafiya kalau Aliyu
Iman Da Billy kuwa Suna cikin daki Yanda kasan munafukai sunqi futowa falon
Alhaji ne yashigo gidan, mutum Mai dattako da riqaqqen Hali, fuskarsa babu alamar wasa yaqaraso cikin
falon
Mamy cikin girmamawa tace Yaya sannu da Zuwa, ya gida?
Adake yace "lafiya Fatima, yame jikin Kuma?"
Kanta aqasa batare data kalleshi ba cikin ban girma tace Jiki da sauqi Yaya
Yana zama acikin kujerun ya amsa mata da Allah yaqara afwa
Zamansa Akan kujerar yayi daidai da saukar Imran da Aliyu qasa
Atare suka ce Alhaji Ina wuni?
Bai amsa musu gaisuwar ba, saima tambaya daya jefowa Aliyu yasauqin jikin Naka?
Kansa aqasa Cikeda girmamawa yace Alhmdlh Alhaji, jiki yayi sauqi
Shima cikin iko yace, ban gamsu da wannan sauqin nakaba, nayi magana da likita zai dinga Zuwa dubaka
duk Bayan kwana biyu, idan kagama warwarewa saika koma bakin aikinka
Cikin ransa yace Innalillahi.... Ai kuwa zamana acikin gidan nan babu abinda zai sauya saima qaruwa da
rashin lafiyar tawa zatayi
Amma afili sai yace To Alhaji
Kallan Imran yayi, yace kadena barinsa yana shiga tunani shi kadai, gaba dayanku Bana San abinda zai
haifar muku da damuwa
Shima Imran din cikin nutsuwa da girmamawa yace to Alhaji, insha Allah
Anan qasan sukaci gaba da zama, hajiya tace aida Zuwa mukai kukaci abinci saikuje kuhuta, Ko kuwa
Hajiya fati?
Taqarasa zancen da Kallan mamy
Mamy tace to hajiya, sannan tayi hanyar dining din
Hajiya tabita Abaya
Alhaji ne ya kalli su Imran da Aliyu yace Kai kutashi muje kuci abinci
Suma sukabi Bayan Alhaji, suka dunguma Zuwa dinning din
Alhaji ne yawaiga baiga kowaba yajuya ya kalli hajiya yace Ina yaran nan ne?
''autata tana school, Farhan yafice yawonsa, saide su Iman Suna cikin daki
Babu wasa a fuskarsa yace Tome suke jira su bazasu futo suci abinci ba?
Murya ta Daga tace Bilkisu kuzo nan
Daga nesan Billy tace to hajiya
Miqewa tayi zata fice Iman ta riqeta, da mamaki Billy tace menene Yaya Iman?
Ni wallahi tsoron fita nake, Dan Allah karmu fita, ni wallahi tsoron sa nake, ni da nasan haka yake tun
farko wallahi daban kulashiba, Kinga Yanda ya hade rai Kamar zai rufeni da duka?
Daria ce takama Billy tace to yanzu Yaya Iman, Kiran hajiyan zamu qi Zuwa? Keda masoyinki?
Kamar zatai kuka tace wallahi tsoron sa nake, Wai dama haka yake afili? Yamin kwarjini Billy,
Jikinta ta kalla sannan tace, Toni mema yagani awajena dahar Nakai matsayin da wannan zai furtamin
kalmar so?
Wallahi ba inda zamu, Kema bazaki fita ba, kibari idan suka gama saimu fita
Kafin Billy tayi magana, Suka juyo muryar hajiya tana Cewa Wai me kuke jirane?
Ai aguje suka futo falon, Ahanya Billy ta kunce dankwalin kanta tayafa Dan tana kunyar futowa haka,
Amma abinda Bata saniba shine, Bai gama rufe mata gashin kantaba, hakade tayo gaba
Iman kuwa ahaka tatafi abinta, to waye banqonta aciki? Aliyun Ko Imran?
Directly Suma dining din suka nufa, tun kafin su qaraso Imran ya kafe Iman Da kallo
Shikuwa gogan Ko dago kansa baiyi ba, bare yasan da halittarsu
Kujera sukaja Suma suka zauna, Hajiya ta kalli Iman tace toko nice zanyi sarving dinsu?
Batacewa hajiyan komai ba, Ahankali tatashi tsaye tafara zubawa Alhaji tatura masa gabansa, Bai jira
komai ba yafara ci
Sannan tafara zubawa mamy, Mamy kallanta take, sosai ta Yaba da yarinyar, komai tanayinsa ne anutse,
batada makusa Ko kadan
Yanzu ZAINAB harta haifi ya Kamar wannan? Kenan de tarihi ne yakeson maimaita kansa
(nikwa nace to wanne tarihi Kuma π€)
Tana zuba mata sannan tasawa Hajiya, Bata kalli gwarazan samarin nataba, takai hannu tadau flet din
gaban Imran zata saka masa
Dasauri ya katseta yace no zubawa Bros tukun, "
Miqewa tayi Daga Dan sunkuyawar datayi tana Zuba abincin, Ahankali takai kallanta wajansa
Shikuwa Aliyu baima dago kansa ya kalleta ba, yace " no"
Shima Imran din yace no Bros tazuba ma tukun
Batare dayace komai ba ya girgiza kansa, still Bai dago ya kalleta ba
Kafada Imran yadaga yace to shikkenan ai ni dashi duk dayane, abin Bros aina Bros ne, yadubi Iman yace
zubamin
Alhaji yana jinsu baice musu komai ba, inda Sabo ai yasaba da irin wannan shirman nasu, Wai ai abin
wane na wane ne
Itama Iman cikin ranta tace Yan renin hankali gaba dayanku, sannan tafara zuba masa
Shima Aliyun ta zuba masa, sannan tasaka musu itada Billy
Bakajin motsin kowa, sai qaran spoon dakakeji yana tashi
Aliyu cikin ransa yace watode wannan gidan Har yanzu Suna nan da dabi'arsu ta idan Alhaji yana wajan
cin abinci babu wanda ya Isa yayi magana
To yaukam saide ayi hakuri, domin kuwa bazaiqi fadar gaskiya ba
Gyaran murya yayi sannan yace Ahankali,"Hajiya girkin ki yayi dadi sosai "
Cikin Jin dadi hajiya tace ashe yayima dadi Aliyu, aiba nice nayi ba, ga gwanayen girkin nan, ta nuna masa
su Iman
Sannan taci gaba da Cewa musanman stew din, Iman Hana kowa tabawa tayi, tace Dakanta zatayi yau
Sai a lokacin yadago da manyan idanunsa Zuwa gareta,
Idanunsa Basu sauka ako'inaba sai Akan nashanunta
Dasauri yajanye idanunsa yakalli qwayar Idonta
Adede lokacin Itama ta dago karaf idanunsu suka sarqe Dana Juna
Lokaci daya ya tamke fuskarsa, Itama sunkuyar da kanta tayi, taci gaba da cin abincin
Billy ce take kallansu, Daria tana kamata Amma Kuma babu damar yi, a ranta tace tab lalle wannan
miskili ne dayawa
Iman kawai wasa tayi da abincin bawani cin kirki tayiba, tatashi tayi cikin daki, domin kuwa Zaman wajan
gaba dayanta gani take kowa yasan abinda yake faruwa
Billy na bin Bayan yar'uwar ta tayi, Suna shiga daki, Iman ta zuba tagumi, Billy tadubi Iman tana cire
kayanta domin yin wanka, tace ya'akayi ne Yaya Iman?
Cikin damuwa tace ya tsaneni Bilkisu
Billy tace Hakan shine mafita Yaya Iman, tana fadar Hakan tashige toilet, Saida ta futo sannan Iman ma
tashiga tayi wanka
Laffaya Bilkisu ta nada, Iman Kuma tasaka doguwar Riga ta atamfa dinkin fitet gown, sai shafaffan cikin
ta ya buya aciki, yayinta hips dinta suka cika rigar, dinkin ya karbi Jikinta yayi Mata Dass
Wayar Billy ce tayi qara, tana dubawa afili tace babane
Iman tace Daga muji menene
Billy tana dagawa Bayan sun gaisa, naji tace to baba yanzu kuwa insha Allah, sallama sukai, tajuyo
tacewa Iman, baba yace natafi yanzu
Cikin damuwa Iman tace wayyo Bilkisu yanzu tafiya zakiyi kibarni cikin wannan rikicin?
Cikin tausayawa Billy tace Toya zanyi Yaya Iman
kawai sai Iman tasaka kuka, Bilkisu cikin tashin hankali tace Yaya Iman me aka Miki Daga maganar tafiya
sai kuka?
Cikin kuka Iman tace wallahi bazaki tafi ki Barni dasuba, Billy tace suwa din?
Cikin hawaye tace su su Aliyun, Allah ba inda Zaki
Suna wannan halin Hajiya tashigo cikin dakin tana Cewa biyoku nayi Naga yaude me kuke yi a daki Kamar
wasu baqi... Maganar ta ce ta tsaya ganin Iman na kuka, tace ita Kuma me aka mata take kuka?
Billy tace Wai Dan baba Yamin waya yace natafi yanzu, shine take kuka Wai kada natafi
Kuka hajiya Nima banasan tafiya wallahi, kawai de danya zama dole ne
Jikin hajiya yayi sanyi, gaba daya tausayinsu ya kamata, kafin tace musu komai Iman cikin kuka tace
hajiya Dan Allah yau ki fada mana, meyasa baba bayasan mu rabeki?
Cikin sanyin jiki hajiya tanemi waje tazauna agefen gadon, Suma binta sukai suka zauna
Cikin damuwa hajiya tace Haqiqa yau zan fada muku dalilin dayasa babanku bayasan zamanku ahannuna
Nida yar'uwata zainab, mun kasance kyawawa a lokacin damuke yanmata kamarku, basai nafada muku
ba kunsan halin duk wani qabilar shuwah basason Auren talakan mutum, to hakane yafaru awjanmu
Nida zainab
Munzo kano wajan biki nahadu da Alhaji Abubakar mahaifinsu Imran, ban Bata lokaci ba nakulashi,
saboda Ina kaunarsa, yan'uwanmu damukazo biki dasu kowa dayaji shiyake sona zai bani goyon baya a
kansa saboda shidin mutum ne Mai mugun kudi
Soyaiyar mu tayi Nisa harta kaimu gayin Aure, watarana zainab tazo hutu kano gidana, anan qanin Alhaji
wato mahaifin Aliyu yanuna yana sonta
Yayansa Alhaji wato mijina yatsaya masa yanayin abinda yaso da kudi, gakuma aikin soja dayake, nanma
yana samu kasancewarsa babban soja, haka duk yabi yan'uwanmu na maiduguri yake Raba musu
kudade, bawai danya siyesuba a a yayi hakanne kawai domin zainab
Aikwa nan yan'uwanmu suka ce basusan kowa ba inba Sa'ad ba, shi zata aura, Amma abinda basu saniba
shine zainab Bata qaunar ganin Sa'ad, kwata Kwata Bata sonsa
Akwai wanda takeso a katsina shu'aib wato mahaifinku
Haka akayi akayi zainab ta auri Sa'ad taqi yarda, Daga qarshe mahaifin Aliyu daya gaji da bibiyarta saiya
hakura, wataran yaje yola daurin Auren abokinsu yahadu da wata bafulatanar yola ya aura, wato hajiya
Fatima, Aliyu yana kiranta da mamy
Aurensu shekara daya ta haifi Aliyu, beyo Kamar Alhaji Sa'ad ba, saiyayi Kamar mahaifiyarsa
Shekarar Aliyu daya aduniya nahaifi Imran, Imran baiyo kamataba saiyayi kamar Alhaji
Yan'uwanmu ganin Alhaji Sa'ad yahakura da zainab harma tahaihu yasa suka tsaneta, komai tayi sai an
hantareta, nice na tsaya mata tareda Alhaji iyayenmu suka yarda ta auri mahaifin ku,
Saida tadau tsawon lokaci Allah Bai Bata haihuwa ba, saidaga bayane Tahaifi Iman, sannan Bilkisu
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, Sa'ad yana rayuwa da Matarsa a Abuja, mukuma muna kano, yayinda
zainab take katsina
Ina qaunar naganku awajena tun Bayan rasuwar zainab, idan na kalleku tunamin kuke da rayuwar da
mukai nida ita, Hakan ne yasa Bayan ta rasu, nanemi abani ku kudawo hannu na, da farko mahaifinku
yaqi yarda saboda yana ganin Cewa zamanku awajena zaisa kukoyi Hali irinna yan'uwanmu kuqi talaka
Kamar Yanda danginmu suka nuna qarara basa kaunarsa da zainab
Hajiya ta dubi Bilkisu tace Kuma nasan yahadaki da Haroon ne saboda kada kihadu dawani me kudi anan
gidan idan kinzo, shiyasa yayi Miki katanga da duk wani namiji dazai soki a gidan nan
Yayarda da soyaiyar Imran da Iman ne saboda Alhaji ne yagoya masa baya Dari bisa Dari Har ya samu
auren zainab a lokacin dayake nemanta
Wannan alkunyar dayakewa Alhaji ce tasa Itama Iman, baiyi mata miji talakaba
Tadubesu sannan tace