Showing 3001 words to 6000 words out of 41315 words
maman Ilham, fatan kun tashi lafiya".
Duk da naga sanda yanayin ta ya canja lokacin da na sumbaci Salees amma tuni ta
ture tare da maye gurbin matsewar fuskar ta da wadataccen murmushi tana amsa min
har da yar dariyar ta
"Lafiya lau Auntyn yara, fatan kema haka".
"Alhamdulillah kam".
"Ehm nace dan Allah kiyi haƙuri da abinda ya faru jiya, sha'ani na yara ne me sa
mutum ya rude amma ba da wata manufa nake kawo Amir ba, kin san al'amarin raino in
ba wanda ya taɓa yi ko yake cikin yi wani abin ba yarda zaka yi in an fada ba, ni
kaina da Umma ke faɗa min akwai yara masu kukan dare ban yarda ba seda na haihu,
amma karki damu kema soon zaki fahimta in Kika haifa".
Duk wannan surutun da take yi ni tuni nayi nisa da zuba abincin da zan karya dan
Ina zama na zubawa Salees, ban ɗago ba duk da naji me tace ban kuma yi mamakin
maganar da ta fa min a wayance ba dan indai ita ce nasan zata yi fiye da haka dan
tuni na dade da gane da kuma fahimtar inda ta dosa.
Wahalallen murmushi na kakaro na ɗorawa fuska ta na ɗago ina duban ta
"Haba ai ba wani abu bane maman Ilham karki damu".
Haka muka fara cin abinci tana ta zungurin Salees da hirar Amir da ta Ilham shi
kuma ya biye mata dan a bayyane yake yana mugun son ƴaƴan sa tare da kulawa da duk
abinda ya shafe su, gane hakan ne kuma yasa mariya ta samu damar kuntata min kamar
yadda ta dauri niyyar yi tun haihuwar Ilham zuwa yanzu kan Amir.
Tissue nasa na goge baki na ina miƙewa daidai fitowar Ilham daga dakin mamanta goye
da skul bag ɗin ta na tafiya makaranta, tun da yarinyar ta fito na kalle ta na kau
da kai batare da na sake duban ta ba duk kuwa da yadda nake son yin hakan.
Allah ya sani ina matuƙar kaunar Ilham saboda yadda ta dauko kamaninn Salees kamar
yayi kaki, yanayin ta na surutu da sakewa yasa take da farin jinin jama'a ciki kuwa
har da ni sedai dole nake koyar dannewa tun wani incident da ya taɓa faruwa.
"Good morning Daddy, good morning Mommy".
Ilham ta gaida iyayen ta batare da ni ta kalle ni ba, ban damu da hakan ba na sake
daidaita zaman mayafi na tare da ɗaukan handbag dina na kalli Salees
"Ni na tafi se na dawo".
"No ki tsaya ki sauke baby a school yau ba zan fita da wuri ba".
Ya katse ni da sauri daga nufar falo da nayi, dole na ja na tsaya cike da damuwa
dan na makara na kuma san se na kara wata a kan wadda nayi saboda sanin halin Ilham
wanda uwar ta ta gama poisoning mind din ta a Kai na
"Yi sauri kiyi breakfast ku tafi baby, yau Aunty ce zata kaiki".
"To Daddy".
Tace tare da zama ta shiga tsakuran abincin gaban ta kamar ba zata ci ba, ni kam
daga tsayen da nake mamakin Salees ne ya cika min rai ganin yadda be damu da rashin
gaishe ni da Ilham tayi ba, na jijjiga kai kawai tare da kallon wristwatch dina me
tsada dake daure kan tsintsiyar hannu na kana na maida kan Ilham da se lokacin take
yin spoon na uku a abincin.
"Eat fast pls Baby, am already late".
Ba wanda ya tanka min cikin su ukun haka kuma ba ta fasa cin abincin yadda ta ga
dama ba, nikam tuni raina ya ɓaci dan nasan da hujja take yi dan ta bata min lokaci
saboda i overheard them once tana fada wa uwar bata san tafiya dani saboda ni nake
kai ta wataran kamar dai irin yau in baze fita da wuri ba, budar bakin uwar ta bata
shawarar dinga bata lokaci in tare zamu tafi, a cewar ta har na gaji na tafiya ta
kafin ta gama shininnikin ta.
"Ina ganin zan wuce fa Abban Ilham dan na makara tuni gashi kuma naga ita bata gama
ba".
Ban jira amincewar sa ba bare umarnin tafiya na shiga takawa zuwa waje dan da kyar
ma na lallashi kaina na yi maganar dan kar yaga laifi na sedai ashe ban tsira ba
"Wai meke damun ki ne a kwanakin nan Khadijah, ina fa lure dake duk sanda nace ki
sauke baby a school se kin kawo uzuri, makara, ba zaki fita da wuri ba and many
more, me kike nufi ne?".
Seda na lumshe ido jin wata sabuwar fitinar kuma da sanyin safiya kafin silently na
juyo Ina tausar Kai na
"Babu abinda nake nufi fa Abban Amir, kalli agogo it's already past eight kasan
Kuma ka'idan aikina thirty minutes past seven ne na makara".
"Ba matsala, zaki iya tafiya zan kai ta da kaina Allah yasa uban ta na da motar".
Ɗan jim nayi kamar na tafi sai dai zuciyar neman zaman lafiya ta rinjayi me tunzura
ni se kawai na koma cikin falon na zauna tare da rufe ido, daga haka nake jiyo
maganar Mariya murya kwance cike da tsantsar kissa da yaudara
"Haba baban yara, me ye na fusata haka, ai kaga tana da uzuri me ƙarfi, ko rannan
ma ta tafi ta bar baby ne saboda tana da meeting, se kana mata hakuri fa, kasan
bata saba da hidimar yara ba".
Abin dariya wai Salees se ya dubi mariya
"Abin da Khadijah ke min a gidan nan ya fara isa ta, amma ba komai ta cigaba".
Se kawai fuuu yayi sama,
"Dan Allah Auntyn yara ki dinga kiyaye abinda ze sa Abban Amir ya dinga miki faɗa
haka, wallahi bana jin dadi".
Ban iya cewa komai ba saboda kullutun da ya tare min makogaro, da na buɗe baki
nasan ba me daɗi zan fadawa Mariya ba wanda da nayi hakan nasan wani tashin
hankalin ze Kuma zama so se kawai na zabi yin shiru, ina jin ta tashi ta bi mijin
ta sama ta bar ni nan zaune na kasa motsi cike da ɓacin ran da ta jagoranci zama
silar sa, seda siririyar muryar Ilham yet cike da rashin kunya ta ratsa kunne na
"Ni kin ga Malama in baki shirya tafiya ba ki bari in faɗawa uba na ya kai ni, atoh
tun da ina da iyayen da suka haife ni su ba juya bane".
Wal haka na ware idanuna na sauke kan fuskar yarinyar me cike da kuruciya hadi da
yarin ta da a lokacin take shekara na sha uku, fuskar nan irin ta mahaifin ta a
yamutse ta turo baki gaba cike da tsiwa yayinda madaidaitan idanun ta ke wulkitawa
da hararar da take min.
Cike da wani kudiri a raina na mike tare da fita daga falon ina dan karkada
mukullin mota na har na karasa tare da budewa, farar mota ce me kyau tasha wanki
tana ta ƙyalli, da addu'a na bude mazauni na na shiga tare da rufewa kana nayi
unlocking sabida ta shiga dan ina hango ta biye da bayana, murmushi nayi jin shigar
ta bayan motar wato ta mai da ni driver Kamar yadda ta saba in tafiya ta haɗa mu
tun da ta fara wayo.
Sai da muka hau titi sosai bayan na bawa me gadi ihsanin da na saba na cigaba da
tuki na cike da nutsuwa, ba wata tafiye me nisa muka yi ba dan bamu gama fita daga
unguwar ba na tsayar da mota tare da bude murfin na fita, door ɗin da Ilham ke
zaune na bude tare da finciko ta a fusace har seda ta tsorata, na bude gaba na
sakata bayan na watsa mata wani shegen kallo me cike da gargadi hakan yasa bata yi
yunkurin komawa bayan ba har na shiga mazauni na.
Kyakkyawan mari me kyau nayi wa bakin ta da ya gama zuba min rashin kunya ta yadda
seda ta sa ihu tana rike bakin ga ba halin guduwa na rufe motar, kunnen ta na kama
na riƙe da kyau ta yadda na san gargadi na ze shige ta na fiddo kyawawan ido na
waje na haske ta dasu ina zare su
"Duk sanda kika kuma yi min rashin kunya, kallon banza ko harara se na ci uban ki
tun da baki da kirki, kina zuwa school kina haduwa da marasa tarbiyyan yara kina
koya ko?".
Da sauri ta girgiza kai jikin ta na rawa dan yadda na mata ba ƙaramin tsorata tayi
ba ga bakin ta dake zafi dan har lips din sun fashe
"Ni ba sa'ar ki bace balle ki kawo min iskanci, duk rashin mutuncin da ke kan ki se
na sauke miki shi dan duk kika kuma min ɗaya daga abin da na faɗa se na kulle ki a
daki na zane ki ciki da bai ko kuwa in wullo ki daga sama ki fado ki mutu kowa ya
huta, zaki kara?".
Yanzu ma da sauri ta girgiza kai na kuwa sake haɗe rai tare da zare mata ido
"Baki da bakin magana ne kike min knodding?".
Yadda nayi maganan a tsawace yasa bakin ta na rawa ta furta
"A'a...a'a...ba zan kuma ba...".
A firgice, haka na mata warning me kyau kafin na sake ta bayan nasa ta gyara kan ta
na tashi mota muka cigaba da tafiya ina bin karatun Alkur'ani da nasa suratul Noor
cikin raina kuwa cike fal da tunanin yadda zamu kaya da boss dina wajen aiki saboda
nayi makara fiye da ka'ida a tsukin.
Har cikin school premises din na kai ta tare da kara mata kudin break ta karba tare
da barin wajen da sauri, na bi bayan ta da kallo ina tariyo tsoro na da na hango
cikin idan ta sannan na fita, se kuma tunanin yadda zamu kwashe da Salees in ta
faɗa masa ya fado min, dogon tsaki na ja ina jin na shiryawa duk ma me ze faru, abu
ɗaya na sani ba zan dau raini daga uwar ya in Kuma na dau yarinyar ba, yar da da na
sami haihuwa da tuni ina da sama da ita sosai, kai baze sabu ba wannan karon nima
na shiryawa duk abinda Salees ya taka.
Da wannan tunanin na karasa wajen aiki na inda nake aiki da ma'aikatar haraji wato
revenue nake kuma da office na bakwai mafi girma a wajen, sai da na kai uzurin
rashin lafiya wa me gidana kan na koma office ɗina Ina istigfar na karyar da Salees
yasa nayi.
Aikina nayi cikin nutsuwa duk da sa'i da lokaci wasu abubuwan na daga rayuwa ta kan
fado min cikin rai sai dai bana bari ya zauna balle ya hana ni aiki na ke ture shi
gefe.
Waya ta ce ta dauki soft ringtone me daɗi wanda na sawa duk family na, ina dubawa
na ga Ummi na ce, take naji wani sanyi ya shiga sauka cikin raina na dau call din
cike da farin cikin jin muryar mahaifiya ta
"Ummii naa"
"Dijeehh naaah".
Itama ta amsa min cike da so da kauna ta wanda suka fallasa kan su sanadin rashin
haihuwa da Allah ya jarrabe ni dashi
"I miss You Ummi naa, hope kina lafiya ba abinda ke damar min mamana".
Sai da tayi yar dariya sannan ta amsa min
"Ina lafiya Khadijah, ina fatan kema haka kuma babu wani matsala ko?".
"Alhamdulillah, Allah ya kara muku lafiya ke da Abba na, matsala kam babu Ummi sai
dai duk da haka muna bukatar addu'ar ku".
"Wannan kam a kullum ba'a fashi Khadijah, kullum addu'a ta da fatana shine Allah ya
azurta ki da rabo me albarka, Allah ya kare min ku ya tsare ku daga dukkan wani
sharri ya albarkace ku ya kuma hada min kan ku".
"Amin Ummi na, Allah ya saka da alkhairi ya kara girma tare da nisan kwana me
albarka".
"Amin, ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da rayuwar ki cike da tawakkali tare da
godiya ga Allah, har kullum ina faɗa miki be manta dake ba ba kuma baya son ki bane
ya jarrabe ki, ki rike addu'a ki tsarkake zuciyar ki ki kuma zauna da abokiyar
zaman ki Lafiya, dan Allah Khadijah kar ki bari sheɗan ya zuga ki a kan ƴaƴan ta ko
ita, in da kara da mutuntaka ya'yan mijin ki naki ne, ki gyara musu ina suka
kuskure amma ban da cutar wa dan Allah".
Wani irin rauni ne ya lulluɓe ni kamar yadda ya kasance yana faruwa duk Ummi take
min nasiha
"Insha da Ummi na, ina iya kokari na ki cigaba da taya ni da addu'a, ina autan ki
ne ban ji shi ba kwana biyu?".
"Allah ya shige mana gaba, auta yana can ya fita neman maganar da ya saba, ai ni
dai wannan da se Allah ya shirya min amma jin magana kam ba'a cewa komai".
Da haka muka bar waccan maganar muka koma hirar mu har lokacin da muka yi sallama
na aje wayar ina sauke numfashi.......................!
Ouummey ✍🏻.
Ouummey 03 {4/29/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 003
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
____________________________________________________________________________
_Free Chapter Three_
Hankali a kwance na tashi aiki tare da tattaro kaya na na fito, tsayawa nayi ina
gaisawa da abokiyar aiki na me suna A'isha
"Yau ba zaki jira oga ba kenan?".
"Ai bana tunanin oga ya shigo yau dan a gida na bar shi".
Na bata amsa, akan Salees take magana dan wajen aikin mu daya da shi sai dai ya fi
ni matsayi da office uku, mataki na uku yake a ma'aikatar ni ina na bakwai
"Eh na manta fa, kin san zasu je meeting a main branch so yau zasu tafi".
Da yake na amsa mata dan na manta da batun haka kuma da zan fito be min sallama ze
tafi ba, da haka muka rabu na wuce wajen mota na na shiga tare da barin ma'aikatar.
Sannu a hankali nake driving zuciya ta cike da tunanika barkatai, wato dai yanzu
ban da sauran matsayi a wajen Salees, da ni da banza kwance kusan ɗaya muke, to in
ba haka ba ai ya cancanta ya min sallamar ze tafi ko.
Wai a duk cikin yanayin da nake sai da wani bangare na zuciya ta ya dinga tursasani
yiwa Salees uzuri, ban ja ba na yi masa ta hanyar yin tunanin maybe dan yasan na
san zancen ne tun a office.
Seda na tsaya a mall nayi siyayyan kaya shafa na da suka yi kasa tare kuma da
undies dina da naga kaman sun ɗan yi sanyi, ban fito ba se da na siyowa baby wato
Ilham wata gown me kyau da ta burge ni Amir kuma wani takalmi me kyau, wannan sabo
na ne bana yin siyayya ban musu tsaraba ba har Salees, Mariya ce dai ban taɓa
ɗorawa kaina yin wannan karyar ba dan ba zan iya ba, shima Salees ɗin daga baya aje
wa nayi ganin ba sannu bare na gode.
Sai da na adana motar inda ya kamata sannan na kwashi ledoji na zuwa main falon mu,
da sallama a baki na na shiga , yuuuu haka Mariya da ƙawayen ta suka zuba min ido
kamar sun ga wata sabuwar halitta lamarin da yasa naji na tsargu dan kafin na shigo
kaya kaya haka nake jin surutun su.
Kadaran kadahan na musu sannu da gida na wuce daki na ina tafe ina jin kaifin
idanun su da suka min rakiya da shi, zube ledojin nayi kan bed tare da zama ina aje
numfashi, seda na huta sannan na cire kaya tare da shiga toilet na yi wanka.
Jakar shopping ɗin su Amir na ɗauka na fita bayan na shirya cikin atamfa ta purple
color ɗinkin riga da skirt da suka zauna a jikina suka kuma kama ni wanda yawancin
dinkuna na duka haka suke, duk tsadar kaya bana bakin cikin kacaccala shi wajen yin
dinkin da nasan zasu zauna a jikina in birge me gida.
"Sannun ku fa, maman Ilham ga wannan nasu Amir ne".
Na faɗa ina aje mata ledar a gaban ta kana na juya zuwa kitchen dan yin girki
"Oh mace har mace amma bata da wani amfani, to meye amfanin juya da bata haihuwa?".
Kalaman daya daga cikin su da na jiyo dan dama a yadda ta daga sauti take magana ta
faɗa ne dan naji
"Haba ke kuwa Asmah, bana san neman magana, ya muna zaune ƙalau da yar uwa ta kina
min irin wannan kalaman?, Gaskiya bana so".
Mariya ta fada da murya me kaman tana dariya ne ko kuwa, nidai ban tsaya ba na
shige kitchen din na Kai jingine jikin Island da sauri ina sauke numfashi a jere a
jere kamar wadda tayi tseren gudu, makogaro na ya bushe kamar wadda ta shekara bata
sha ruwa ba, da kyar na iya lakato wani yawu me daci na haɗiye ina lumshe ido, a
kuma lokacin ruwan hawaye ya fara zarya kan kunci na, halin da na shiga a lokacin
ba me bayyanuwa bane.
Sanin suna falon yasa na daure zuciya ta na lallashi kaina na hada fruit salad
maimakon noodles da na shigo da niyyar yi, juice na ɗauka me sanyi tare da bowl
dina na fita cike da fatan kar wata ta kwata faɗa min irin maganganun nan dan a
yadda nake ji zan iya biye musu muyi duk wadda ta kama.
"Auntyn yara angode fa".
Yatsu biyu na daga mata batare da nace komai ba na shige ɗaki, da kyar da sidin
goshi na sha salad din nan dan wani daci naji yana min a baki.
Kuskure baki nayi bayan na gama na ture plates din gefe tare da ɗaukan waya ta ina
dubawa wai ko zanga missed call din Salees, sedai ga mamaki na ko text babu balle
kira, murmushin takaici nayi tare da kiran shi ni, ta dade tana ringing be dauka ba
har ta katse na sake kira shima be ɗauka ba, seda na masa miss call biyar sannan ya
turo min short text
"Busy".
That's all he said, Ina gani na aje wayar jiki a sanyaye, saboda gudun tunanin da
ka iya rufe ni na janyo tablet dina na hada mata keyboard na shiga ayyuka a ciki,
duk wanda ya ganni kallo ɗaya ze min yasan ina aikin ne kawai amma ba dan jin dadi
ba.
Dake