Showing 6001 words to 9000 words out of 41315 words
Allah Alhakeem ne se gashi tashi ɗaya ya aiko min da sanadin farin ciki
madaukaki, ba komai bane face karin matsayi da ake shirin yi a ma'aikatar mu, cikin
rahamar Ubangiji kuma har da suna na cikin wanda za'a yi reviewing Wanda muna sa
rai in mun tsallake review shikenan promotion ya tabbata.
Ban yi farin cikin ni kaɗai ba na kira Ummi na na faɗa mata tare da fatan a taya mu
da addu'a ta amsa, yayata Salima na kira itama na sanar da ita, ba tun yau ba na
fahimci kunya da nauyi na ta take ji ba sedai ni a raina wani irin girman ta nake
gani domin tai min abinda ba kowa ze iya ko kwatanta wa ba.
Ta taya ni murna tare da fatan dacewa, tana neman kashe wayar na tare ta da sauri
"Ina yaro na?, Shiru baya neman mommy?".
"Ba haka bane ba maman Haidar, kin san baban makarantar wuni ya kai shi saboda yaki
maida hankali a waccan".
"Ayya, dan Allah yaya a kula min da shi sosai, kar a bar min shi da yunwa da
damuwa".
Daga cikin wayar na jiyo faffaɗan murmushin da tayi tare da amsa min mukai sallama
na kashe wayar sabon zafi na sake hudowa daga kirji na sedai tuni na dakatar dashi
saboda bana san abinda ze dinga tuno min da baya, duk da present din ma ba dadi ne
dashi ba amma bayan nan akwai ciwo me matukar raɗaɗi.
Seda na tabbatar ƙawayen Mariya sun tafi dan gidan yayi shiru ba hayaniyar su kana
na dau bowl din da nayi amfani dashi na fita zuwa kitchen.
Zama nayi a kujera tare da kunna Tv na shiga kallon wata drama da ake yi a mbc
Bollywood, cike da zallar nishadi na kalli abina har aka gama na tashi zuwa daki
dan It's evening, akwai bukatar in kwance kai na dan sati na biyu yake ciki.
Seda nayi Asr sannan na fara tsifar a falo ina yi ina sauraren wani hirar
classmates dina a group da sukai ta hanyar voicenote, a lokacin ne kuma baby ta
shigo dan se five ake tashin su, da karfin gwiwar ta ta shigo murya a sama tana
ihun kiran sunan uwar ta ita kuma tana saukowa daga sama tana amsawa sedai tashi
ɗaya taji dif yarinyar tayi shiru.
Wai ashe ni da ta tarar cikin falon ne yasa ta ɗauke wuta jikin ta ya shiga rawa,
sam ban ma lura ba ni hankali na na kan abinda nake ji seda naji babar na tambayar
ta
"Me haka, lafiya na ga jikin ki na rawa?, Me ya faru?".
Da mamaki na daga kai ina kallon su, yarinyar ta maza ta faɗa jikin mamanta tana
zare ido, ko da na gane abinda ke faruwa se kawai na dauke kai na cigaba da abinda
nake yi ita kuma taja ta daki tana tambayar ta.
Ban san me ta fada wa uwar ba se ganin Mariya nayi a gabana a tsaye kamar wata
bishiya
"Wane irin rashin imani ne yasa kika yi wa Ilham wannan marin, kin kuwa ga yadda
bakin ta ya kumbura?".
Kamar kar in tanka se kuma na tanƙwasa kai na sanin shi bayani yana da dadi kuma
rigima sam ba abar so bace musamman gare ni da ba hali na bace, zama da Mariya ne
yasa har ban san yaushe na canja ba.
"Ilham rashin kunya take koyowa Mariya, wai kamar ni zata kalla ta zaga, imagine
fa".
"Ban gane zagi ba, kin ga tun kafin raina ya ida ɓaci ki min bayani yadda zan
fahimta, Ilham ta zage ki tace miki me ?".
"Kin san dai ko ke baki isa in miki karya ba balle ƙaramar yarinya kamar ta, ce min
tayi wai Allah yasa tana da iyayen da suka haife ta tun da ba juya bane su".
Ƙanƙance ido tayi cikin rashin mamaki balle damuwa
"To ai ba karya tayi ba tana da iyaye, shima juyan ai ba sharri tayi ba tunda da
juya ne su da basu haife ta ba, shine kawai dan wannan yar maganar zaki nemi
lahantata, to wallahi bari uban ta ya dawo dan ba zan yarda ba".
Iya maƙura raina ya kai wajen ɓaci dan haka na mike tsaye nima kamar yada take
"In Kika yarda ma ba sunan ki Mariya ba, haka kuma in Kika fasa fadawa Salees ba ki
haifu ba, maza faɗa masa yazo yayi wa khadeeja tuf ta mutu kin ji, shashasha mara
tunani, a faɗa miki yarki tayi wannan rashin mutuncin amma ki goyi bayan ta saboda
rashin sanin ciwon kai, to ai karki fasa, dan yau dai ba ayi masa haka in zaki
gyara ki gyara".
"Naki na gyara, nace naki na gyara ɗin, yar ki ko yawa, aikin banza da zaki zo kina
wani kinibibi ai se ki bari se kin haifa se karki goyi bayan naki, ko da yake macen
da ta shekara sha shida da aure bata taɓa ko bari ba ta ina zata haihu, wai wanda
be san ciwon da bane zece ga yadda za'a masa tarbiyya, mtsww juya kawai mara
amfani".
Wannan kalma ta juya itace kalma mafi ciwo a duk cikin kalaman Mariya, sanin babban
weakness dina gorin rashin haihuwa ne yasa Mariya daura damarar cewa se ta ga
karshe na, gashi ni kuma bana iya daurewa wannan gorin, ko nayi kokarin haka se
fuska ta ta bayyana halin da nake ciki, idanuna da suka yi jajir na kalli mariya
dasu se kuma na juya na shige ɗaki da sauri ita kuma ta raka bayan da harara.
Cikin son karfafawa kaina gwiwa na dinga tausar kai na dan na gaji da kukan da nake
yiwa mariya, na gaji da bata hawayena kan ta, na gaji da komai ma na ta.
Haka na wuni a daki saboda bana san fita balle shaidan ya raya min wani abu na biye
mata balle kuma azo ace laifi na ne kamar yadda ake ɗora alhakin komai dake faruwa
a kaina, saboda ita ɗin kirsasshiyar mace ce da gane halinta na gaskiya se wanda
Allah ya ciyar kamar dai iri na da zama ya haɗa ni kishi da ita na zama victim.
Washegari ban taya jiran wata Ilham ba na tafiya ta aiki, ko da na gama na dawo a
nan na tadda me gidan ya dawo dan ina shiga falon idanun mu suka sarƙe cikin na
juna, wani kallo me zafi na watsa masa cike da jin haushin sa, tun da mutumin nan
ya tafi be kira ni ba balle text, ni nakira shi ya turo min kalmar "busy", daga ita
kuma be kuma cewa komai ba haka kuma be neme ni ba, wanda in rayuwa da adalci
kamata yayi ko da ace busy din ne in yayi free ya Kira ni yaji ya nake, ya bani
haƙurin tafiya batare da ya sanar dani ba tun da ina da hakki amma duk be yi haka
ba se dawo wa nayi na tadda shi a dararraje cikin iyalin sa suna hira cikin farin
ciki da alamar rayuwa ta gama yi musu daɗi.
Ko da nayi sallama ban lura da sun amsa ko ba su amsa ba nasa kai ciki, kamar in
wuce batare da na kula shi ba se kuma zuciya ta tuna min da zaman kishiya a
tsakanin mu wato Mariya, haka na daure cikin son nuna babu wata matsala tsakanin mu
na tafi gare shi da niyyar yi masa side hug amma se ya goce yana watsa min zazzafar
harara lamarin da yasa na ɗan yi turus cike da kunyar yarfa nin da yayi a gaban
kishiya
"Daga ina kike?".
"Wajen aiki".
Na bashi amsa a sanyaye idanuna na cika da hawaye
"Me ya hana ki kai baby school?".
Ɗan jim nayi kafin na buɗe baki
"Bata shirya ba ni kuma zan makara".
"A'a Khadijah kiji tsoron Allah gwara ki faɗa masa gaskiya kawai, wallahi dear tun
seven na safe baby take a shirye, dalilin ta na kin kai baby kawai dan tayi abu ba
daidai ba na yi magana ne. Wai baby ce tayi mata rashin kunya shine ta mari bakin
ta da kuncin ta tare da murde mata kunne, to ganin yadda ta dawo da zazzaɓi a jikin
ta fuska a kumbure yasa na yi mata magana, daga cewa ta dinga sassauta hukunci
shikenan take fushi da mu a gidan nan, ko magana bata kuma yi min ba tun jiya har
yau da ta fita shine kuma dalilin barin Ilham, dan Allah ka bata hakuri, Khadijah
kiyi haƙuri ni ba da wani abu na faɗa ba".
Irin yadda take tsara labarin abin da be faru ba tare da cakudawa da burbushin
gaskiya yasa kawai na zuba mata ido na ma kasa magana, shi kuwa Salees batare da
binciken gaskiya ne ko karya bane ya hau kai ya zauna ya dinga surfan bala'i, yi
yake kamar bazai daina ba, nikam da na gaji kawai na wuce su na shige ɗaki na kama
kuka dan na kasa daurewa.
Wai ashe laifi nayi da na tafi na bar shi a wajen, bawan Allahn nan be yi duba ga
halin da nake ciki ba, be min adalcin jin ta baki na ba, be tausaya wa ƙaddara ta
ba ya kira Hajiya Iya ya shiga faɗa mata karya da gaskiya.
Kiran wayar Hajiya Iyan ne ya katse min kuka na inda tace tana jira na gobe a gida,
da toh kawai na amsa na kashe wayar raina a bace, zuciya ta cike da kunci dan nasan
a can ɗin ma ba za'a saurare ni ba, ba za'a bani dama ba, za'a yanke min hukuncin
da aka so ne kawai bisa doron son zuciya, nikam ina ganin ƙaddarar
rayuwa.............!.
Ouummey ✍🏻
Ouummey 04 {4/30/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 004
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
____________________________________________________________________________
_Free Chapter Four_
Ragowar ranar nayi ta ne cikin damuwa da tunani, kwata kwata na rasa meke min dadi
a duniya, irin yadda kaddara ke kwallo da rayuwa ta abin ba'a cewa komai.
Ko da dare yayi kasa barci nayi, so nake na samu wani mu zanta ko naji sanyi cikin
rai na sai dai na rasa wa ya kamata na yi maganar da shi, Ummi na kullum cikin son
ganin ta kwantar min da hankali take inda ni kuma nake tabbatar mata lafiya nake a
kullum ko da ba hakan bane saboda gudun shigar ta damuwa, yaya ta daya mace wato
Salima sai dai bana jin zan iya maganar nan da ita saboda gudun sa ta jin kunya,
ragowar yayye na biyu maza ne, duk da suna tausaya min suna kuma so na sai dai bana
jin zasu gane halin da nake ciki.
Ban san yadda aka yi hannu na ya danna number Abban mu ba kamar yadda muke kiran
mahaifin mu se jin muryar sa nayi yana min sallama, a lokacin dukkan wani rauni da
nake ta boye wa da dannewa ya bayyana kan sa ta yadda ban san ya akayi ba se ji
nayi na fashe da matsanancin kuka me tada hankalin duk me saurare, shiru Abba yayi
be kuma cewa komai ba tun bayan amsa min sallama da yayi, haka ya bar ni nayi kuka
na har na gaji murya ta ta dusashe kafin can kasa yayi gyaran muryar da ya shaida
min yana bukatar in saurare shi, ban musa ba na katse ragowar kuka na se yar
sheshsheka da ajiyar zuciya.
"Uwatah".
Yadda ya kira sunan cike da kwantaccen lafazi da sanyin murya yasa naji sabon kuka
na neman kufce min, na amsa masa da murya me rawa
"Na'am Abban mu".
"Bani hankalin ki nan ki saurare ni sosai".
A wannan karon itama sheshshekaar dakatar da ita nayi tare da sake shigewa cikin
katifar gado na me aminci
"Rayuwar duniya gaba ki dayan ta jarrabawa ce, ita kuwa rayuwar aure yar hakuri ce,
uzuri a gurin da babu muhallin sa, kau da kai a abinda yake zahiri ko da an cuta
maka, danne bukatar kai saboda ta abokin rayuwar ka, ji ka nuna baka ji ba, ka gani
ka nuna baka gani ba haka kuma a taba ka ka nuna baka san an yi ba ta hanyar
yafiya.
Base kin ce min komai ba ba kuma se kin fada min halin da kike ciki ba, kukan ki ya
bayyana min komai, sai dai ina so in tuna miki da abin d kika manta, ni baban ki
ne, dan Adam kuma ajizi, da ni dake Allah muke bautawa gaba ki daya haka kuma wajen
sa muke neman taimako, kama ta yayi da damuwa tayi miki yawa ki tashi ki dauro
alwala ki fuskanci qibla ki kai kukan ki wajen me duka cikin kaskan da kai, yi masa
kirari da kuma tsarkake shi, ina me tabbatar miki da wallahi in kika yi hakan zaki
sami saukin kome ke damun ki, damuwar ki zata yaye, ruhin ke ze aminta haka kuma
zaki sami nutsuwar zuciya.
Ba kamar ni ba da in kika fada min sai dai in miki kalamai wanda bayan haka ba
abinda zan miki in Kuma ba so kike in zama uban kawai me shiga sha'anin rayuwar
auren yar sa ba.
Yanzu maza ki tashi kiyi kamar yadda na fada miki kinji, insha Allah nima zan taya
ki, a kullum cikin addu'a ta kike uwatah ke da sauran yan uwan ki amma zan kara da
izinin Ubangijin mu, ina fatan Allah ya yaye miki kome ke damun ki, ya aminta da
ruhin ki ya kawo miki sauki da salama a rayuwar ki, zan kira ki da safe, Allah ya
bamu alkhairi".
Kit Abba ya kashe wayar sa da ya gama min wannan bayanin, be saurare ni ba, bance
masa komai ba game da halin da nake ciki amma ga mamaki na wallahi se na ji kaso
fiye da hamsin cikin kuncin da nake ci ya kau, lallai na gaida iyayen mu, ya
Allah kasa iyayen mu su cika da imani ka saka musu da mafificiyar aljanna, Amin.
Batun yanzu ba ina sha'awar rayuwar Abban mu da Ummin mu, so da yawa ina fadar in
da ace kowane miji kamar Abban mu yake da ba'a samu gurbacewar rayuwar aure ba, da
ba'a sami yawaitar matsalolin aure ba, da ba'a samu yawaitar zawarawa ba haka da
mata basu ji tsoron aure ba, in Kuma na dube shi ta fuskar uba se in ga lallai babu
ya'yan da suka kai mu yin dacen uba nagari, se in dun ga tausayin wanda Abba be
kasance mahaifi gare su ba har in dinga ganin lallai sun yi rashi babba.
Alwala nayi na shimfida tsaftatacciyar pray mat dina dake nan kamar sabuwa saboda
samun gyara na sa wadataccen hijab dina na kabbarta sallah, a cikin kowace sujjada
kuka nake yi gaban Ubangiji ina rokon sa sauƙin rayuwa, farin cikin rayuwa, haka
kuma yayewar bakin ciki tare da cikawa da imani, irin kukan da nayi ba zan ce ga
sanda nayi shi ba dan tun da na dora goshi na a kasa naji bani da wani sauran karfi
ko kwarin zuciya.
Cikin ikon Allah na yi raka'a goma wato sallama biyar sannan na daga hannu na
cigaba da addu'a, ina shafawa na dau Kur'anin da na aje gaban sallaya ta na budo
Suratul mu'umin na soma karatu cikin kyautatacciyar kira'a murya can kasa dan gudun
takurawa abokan rayuwa ta a gidan, sai da nayi surori uku bayan ta sannan na rufe
tare da sake wasu addu'o'in na kuma shafawa, abin babu karya ba kuma yaudara tun
kafin na kai ga idar da sallar naji zuciya ta wasai tamkar ban taba sanin wani abu
wai shi damuwa ba, farin ciki da walwala suka cika rai na tamkar wadda akayi wa
bushara da kujerar hajji.
Agogo na kalla wanda ya nuna karfe biyu da rabi na dare na tashi na cire hijab din
da na sa na rataye shi tare da maida daurin dan kwali na na nufi gado na na kwanta
hannu na rike da calbi ina ja cikin kirari wa madaukakin sarki, cikin rahmar Allah
se gashi na samu salamammen bacci me cike da jin dadi kamar kar na farka dan se da
nayi da gaske na iya tashi asuba ba kamar ragowar ranaku da ake kiran farko a kunne
na ba saboda damuwar da kan hanani bacci, lallai Allah buwayi ne garara misali haka
kuma duk wanda ya bar Allah tabbas yayi hannun riga da nutsuwar fili har ma da ta
boye.
Ba fa wai na manta da abinda Salees ya min bane, ba kuma na manta da kara ta da ya
kai wadda zamu je yau bane kawai dai damuwar hakan Allah ya cire min daga rai na.
Ban yi gigin yin breakfast ba dan ban manta layin d ya shata min ba na cewar in har
ban kwana dakin sa ba to bani da girki gaba daya, ma'ana har dafa abinci, a can
baya da yasa dokar na damu amma a yau se naji ni hakan ma yayi min dan gashi na
samu damar bajewa a gado ina baccin safe kasancewar asabar babu aiki.
Se after 10 na tashi nayi wanka da shower gels dina da ragowar turarukan wanka masu
kamshi da gyaran fata wanda a kullum yanayin yadda nake kula da jikina yake bawa
wanda suka san ainihin shekaru na mamaki, dan da yawa mutane basa yarda na kai
shekaru na, so da yawa se kiga ana bani shekara Ashirin da biyar da shida koma da
hudu, nidai in irin haka ta faru sai dai nayi dariya kawai, amma fa bana mamaki dan
ko ke kika kalle ni ba zaki ce nayi talatin har da biyu ba wanda sune shekaru na na
gaskiya da gaskiya .
Doguwar riga na sa kirar Morocco, kafin kace me na zama wata bakar balarabiya
saboda yadda rigar ta min ainihin kyau ta bi dirarren jiki na ta zauna Kamar yar
asalin ƙasar, kai har ma nafi dan su ba su da cikakken diri irin nawa.
Karamin fridge dina na bude tare da zubawa kayan snacks din ciki ido sannan a
hankali na debi samosa uku tare da drink na maida murfin na rufe, a tsanake naci
abina na kora lemo na kara da ruwa me dan sanyi, take naji ciki na y dauka masha
Allah na koma tare da zama kan doguwar cushion din dakin ina bibiyar chats