Showing 39001 words to 41315 words out of 41315 words
kin san kan me nake
magana, a rayuwar ki ki rasa wa zaki cutar se jina na saboda duniya babu amana, is
okay bari in fito Miki a mutum ki sakar min kurwar yaro da kika kama dan ina
bukatar ganin sa a raye, in zaki yi kwadayin ki kar ki kuma sauke idanun ki kan
yayana".
Yanayin da na shiga alokacin baze bayyanu ba dan kasa magana nayi, baki na da
zuciya ta suka yi min nauyi se idanu na da suke zubar hawaye Masu tsananin radadi
da azaba.
Ko a jikin Salees se ma wani uban tsaki da ya ja yana nuna ni da yatsa
"Bar ganin ina cewa ina son ki a kan yayana na sha fada Miki zan iya komai, tun
muna mu biyu ki saki yaron nan ya mike, na baki awa biyu zan je na dawo, wallahi in
baki sake shi na se kin hadu da mafi munin tozarci dan se na tabbatar na sanar da
duniya wace ce ke bakar muguwa, green snake under green grass, kina zaluntar mutane
da wannan innocent fuskan da kike displaying alhalin bakar kumurci ce ke, banda
kaddara me ze hada rayuwa ta da taki, wallahi i curse the day I met you".
Da kyar na iya daga kai na kalli lokaci wanda ya nuna min na ci awa daya da mintuna
cikin awanni biyun da Salees ya diba min, hannu na karkarwa na janyo waya ta daga
jaka na shiga call logs dina, akan number Ummi na tsaida idanu na kafin na danna
mata kira, bata dade tana ringing ba kuwa ta dauka da sallama cikin dattijuwar
muryar ta kamar yadda ta saba
"Ummi kizo zan mutu, zasu kashe ni Ummi dan Allah kizo, innalillahi wa inna ilaihi
rajiun".
Abinda na dinga maimaita wa kenan wanda ya tashi hankalin Ummi, ina ji tana kiran
suna na amma na kasa amsa wa hakan yasa ta kashe wayar, kifa wa nayi kan bed din
Ina sauke wani irin numfashi da duk wanda yaji yasan ba lafiya ba, kwakwalwa ta ta
daina tunani ta tushe, kaina yayi wani dummm.
Ina nan a haka Salees ya dawo, a lokacin kuwa tuni Amir ya bar duniya domin a yadda
naji kururuwar Mariya da yan uwan ta ko awa da fitar Salees ba'a yi ba lokacin,
irin yadda take fadar ta shiga uku ta lalace na kashe mata da shine ya shaida min
ya rasu, tun lokacin da naji haka na tashi na kulle kofa ta na koma na zauna ina
jiran tsammani, ganin hakan ba ze min ba ne yasa na kira Ummi na.
Kamar sun manta dani ba wanda ya kuma bi ta kaina aka shiga kokarin mika Amir gidan
sa na gaskiya, se bayan an kai shi an dawo sannan Salees yayi lokaci na, irin yadda
yake dukan kofar yana kiran suna na tare da zagi da munanan kalamai yasa gidan ya
rikice, wanda basu san abinda ke faruwa ba ma aka dinga tsegunta musu, ni kuwa
hankalin tashe ta ciki na daga kai na dubi agogo se naga ko awa uku ma ba'a yi ba
da kiran Ummi na, alhalin tafiyar awanni goma sha biyu ce daga garin Darma zuwa
Bakwarni, so se na saddakar dan nasan kafin su zo maybe sedai gawata dan yadda
Salees ke dukan kofar ya na tabbatar min se ya kashe ni abin ba magana, ga can kuma
taron mata makwabta da suka shisshigo suma suna fadin a fito da ni se sun yi
maganin na.
A firgice na mike tsaye lokacin da Salees ya sami nasarar balle kofar dakin, yadda
ya koma kamar wani mahaukacin zaki shine y sake rudar dani na fara girgiza masa kai
ganin yana nufo ni
"Na rantse da girman Allah Salees ni ba mayya bace ban kashe maka da ba, ka kawo
Kur'ani ma dafa wallahi bani na kashe shi ba".
Ina Salees da alama baya ma fahimtar me nake cewa dan wani irin shaka yayi min
kamar me shirin raba ni da duniya, take na fara kakari idanu na na juye na shiga
kokarin fisge kai na amma na kasa, a yadda nake shaƙe a hannun sa ya shiga kashe
fuska ta da maruka yana zagi ta uwa ta uba, hanci da baki na suka fashe suka dinga
jini amma bawan Allahn nan be yi imanin bari na ba, can sama sama nake jin wasu
muryoyi na fadin ya sake ni kar ya kashe ni sedai ban tantance na waye ba na sume a
hannun sa.
_____________
Ko da ta suma be fasa dukan ya ba seda kyar aka samu aka kwace ta a hannun sa ana
fadin ya bari kar ya daukar wa kan sa masifa, ruwa me sanyi Hajiya Iya da basu dade
da zuwa ba dan ma jirgi suka biyo tasa aka watsawa Khadijah dake kwance helplessly
sedai ko motsi bata yi ba, ruwa cikin bokiti ya sa aka watsa min wannan karon amma
duk a banza, a nan ne hankalin ta ya tashi dan tunanin shikenan Salees ya kashe ni
shima za'a kashe shi dan tafi kowa sanin dangin Khadijah ba zasu zuba ido ba, gashi
in maganar kudi ake yi ko alfarma da hanya ne sa ba kusa ba su din ba sa'an danta
bane.
A daidai lokacin Ummi mahaifiyar khadeejah tare da yayyen ta maza biyu Hashim da
Hashir da kuma autan su Hisham suka shigo, gaba daya hankalin Ummi a tashe yake ta
yadda bata tsaya kallon kowa ba ta shiga nema na
"Khadijah, Khadijah, ina Khadijahn take".
Se kuma aka rasa wanda ze bata amsa inda tashin hankalin Hajiya Iya ya ninku haka
ma Mariya, ga tashin hankalin rashin da ga kuma wani na miji yayi kisan kai, ja
baya Ummi tayi jin kafar ta ta taka mutum ya kai duba se kuwa idanun ta suka sauka
kan fuskar mafi soyuwar yar ta Khadijah, fuskar ta kumbura da shatin hannu haka
kuma tayi kacal kaca da jini, wani irin juwa ce ta dibi Ummi yasa tayi taga taga
zata fadi ya Hashim da shine babba kuma yafi kusa da ita ya maza ya tare ta, kwace
wa tayi daga hannun sa ta kai tsugunne ta shiga tattaba fuskar Khadijah kana ta
dube su cikin wani yanayi
"Hashim, Hashir wannan khadeejah na ce ko, Deeje ce wannan ko?".
Se lokacin suka lura dani suka kuma shiga rige rigen durkusawa waje na, cikin wani
irin kururuwa Hashir ya mike yana bin jama'ar falon da kallo
"Waye yayi mata haka, wane dan iskan me tsautsayin ne yayi laying filthy hands din
sa kan kanwata, nace waye shi".
Tsit falon aka rasa me magana kafin Salees cikin jin shima wani jan wuya ne ya
furta maganganun da suka ja masa shiga wani hali
"Ni ne nan na dake wannan asararriyar mayyar me fuska biyu, akwai abinda zaka
iya....".
Ko kafin ya karasa abinda yayi niyyar fada ya Hashir ya danke shi ya shiga sauke
masa naushi a ko ina da hannun sa ya kai, idanun sa ya rufe kawai Khadijah yake
gani a halin da take ciki da kuma zancen salees na cewa shi ya mata haka, se da ya
Hashim da hisham suka rike shi da kyar dan Salees ya jigata ga kuma jin da mutanen
falon ke yi, wani irin fincikewa ya Hashir ke yi yana fadin a bar shi ya koyawa
Salees hankali be kuma tsaya ba seda Ummi ta daka masa tsawa
"Kazo ka ɗauke ya mu wuce asibiti su duba min in ta rasu ne".
Ta fada directing to ya Hashir aikuwa ya taho da sauri tare da ɗaukan ta gaba daya
Hisham ya bi bayan shi ita kuma ta dubi ya Hashim
"Kayi duk abinda ya dace kan shi dan ba zan bar digon jinin khadeejah ya zuba a
kasa ba, ni da ku shege ka fasa wanda yace a zauna lafiya yaci uban shi, auren da
ya haɗa ma Allah ya tsine masa albarka".
Ta fada tana kallon su Hajiya Iya ya fusace kana ta nufi kofar falon kafin kuma ta
tsaya ta juyo
"I'm coming back to you, zaku san kun taba jinin Ma'aruf Nasidi".
Ta sa kai ta fice, shi kuwa ya Hisham tuni ya kira yan sanda, babu dadewa da fitan
Ummi suka karaso aikuwa ya nuna musu Salees
"Ku tafi dashi, kowa ye yazo kar ku yadda ku ba da bail din shi se da izinina, for
now bani da lokaci amma daga baya zan shigo".
Kamewa suka yi tare da sara masa suna fadin
"Yes sir". Kana suka tattara Salees da be san inda kan sa yake ba suka watsa a mota
suka fice ignoring all the kururuwar da Hajiya Iya da jama'ar ta ke yi.
________________
"Amma dai Aunty kin san bake na dafawa abincin nan ba, kalli yadda Miemie ke jin
yunwa kuma kin hana maids su dafa komai yanzu kuma na dafa mata kin dauke, this
isn't fair kin sani".
Haanah ta fada rai bace sedai tana kallon Rahinatu dake amsa sunan kanwar maman su
haka kuma matar baban su a yanzu, tsaki tayi tana cigaba da cin abincin wanda
indomie ne da yaji hadi matuka, kifi kaman yayi magana a ciki ga kuma veggies da
aka sa wanda ya sa abincin ya zama gwanin sha'awa.
"To ki hana ni ci mana karamar mara kunya, yara duk an bata ku da iskanci da
sangarta, kamar ku tula tula a gida amma an zube wasu masu aiki, abinci har kusan
kala uku ake dafawa dan samun guri, kowace munafuka ta bude ciki tana zurawa ko
tausayin me kawo wa bakwa ji".
"Amma dai kin san a gidan uban mu muke ko?".
Ameerah ta fada cike da tsiwa
"Kuma gidan miji na ba dan haka ba za'a sake dafa min abinci biyu ba, daya za'a yi
shima wanda na zaba sannan dolen ku ku zaku dinga gyaran gida dan na sallami masu
aikin tun da ni ina tausayin sa, itama wannan yar tatsutsuwar duk abinda aka dafa
shi zata ci ba zancen wani a dama mata oat ko cerelac or something, and mind you ki
koya wa kannen ki da'a kafin in darji bakin daya daga ciki, tarka tasu ku wuce
bedroom dan ina bukatar hutawa a falo bana bukatar kowa ya dame ni".
Cikin wani yanayi Haanah ke kallon ta idanun ta na cika da hawaye, bata taɓa sanin
kanwar uwa kan iya behaving a'a matar uba wa ya'yan yar ta ba shiyasa har ta bada
goyon bayan Dadan ta ya auri Aunty Rahinatu, da ta san things can turn out to be
like this da ba zata fara ba.
Gashi babu yadda zata yi ta fadawa Dada dan yayi tafiya zuwa Moscow and bata san me
ya faru ba yau kwana biyu shiru be kira su ba sedai tafi tunanin yayi busy ne, tun
bayan dawowar su daga gidan Yaaya after a month da auren Dadan komai ya canja masu
na yadda suka saba rayuwa, kome suka yi ba su iya ba a wajen Aunty Rahinatu, komai
suka ji laifi ne, kallo ta hana, zaman falo ya hana, kayan snacks da ake musu na
zuwa school ta hana ta ce ai ana basu kudin break, tafi tafi tace su daina daukan
juice in zasu tafi school, a nan islamiyya tace malam Lawan ya daina kai su ai ba
nisa, kai duk wani abu na jin dadi ta hana yanzu kuma gashi har ta zo ka abinci,
inaaaa ba zata bari ba dole ta taka mata birki, bari dai Dada ya dawo dole ayi
wacce za'a yi.
______________
Rike suke da hannun juna kowacce hawaye a fuskan ta,
"Ban sani ba ko akwai rabon mu cigaba da rayuwa Farida, ban sani ba ko kuwa iya
wa'adi na Kenny, abinda nake so kawai shine dan Allah in na bata miki ki yafe min,
ina matukar kaunar ki Farida dan bani da yar uwar da ta fiki, kin zame min, kawa,
aminiya, yar uwa haka kuma mahaifiya a wasu lokutan, kina kan kashe ko nawa ne dan
sama min farin ciki, ba zan taba mantawa dake ba Farida, ba zan iya biyan ki abinda
kika min ba, Allah y saka miki ya biya ki da mafificin alkhairi".
Hajiya Farida bata iya cewa komai ba saboda kukan da yaci karfin ta, a haka aka
tura gadon da Falmata take zuwa dakin theatre din idanun ta a rufe cikin tunanin
Alh Usman, yadda ta baro garin batare da sun yi sallama ba abin ya tsaya mata a
zuci, ya fa san da maganar tafiyar amma ya sa kafa ya bar garin zuwa wai daurin
auren dan abokin sa, tayi ta kiran wayar sa kuma baya dagawa dole ta hakura, a haka
ta bar kasar baya nan har kuma yau da za'a shiga da ita dakin aiki be kira ba bayan
ko a nan tayi kiran wayar sa be dauka ba................
*TOOOOOO ALLAH YA KAWO MU LOKACI YA KAWO MU YAU GASHI MUN KAWO KARSHEN FREE
CHAPTERS".*
*KAKAKARA KAKA, CAKWAKIYA KAN CAKWAKIYA, SALEES YA YI WA KHADIJA DUKAN MUTUWA AN
TAFI DA ITA ASIBITI RAI A HANNUN ALLAH,*
*GASHI SHIMA YAYA HASHIR YA FITAR DASHI HAYYACIN SA KUMA YANA HANNUN HUKUMA*
*SHIN ME ZE FARU A GABA, KHADIJAH TA MUTU KO KUWA?, SHIN YA ZAMAN SALEES A HANNUN
HUKUMA?*
*KAI KU TSAYA, YAYA MAKOMAR AUREN SALEES DA KHADIJA?*
*SHIN ME YASA SALEES YA AMINTA KHADIJA MAYYA CE BAYAN A DA YA KARYATA HAKAN?*
*WAI SHIN WANE FAMILY NE NA MA'ARUF NASIDI DA UMMI TACE ZA'A SAN AN TABO SU?.*
*MEYE MATSAYIN YA HASHIM DA YAKE BAWA YAN SANDA UMARNI HAKA?.*
*YA YA TARIHIN SOYAYYA DA KUMA FARKON AUREN KHADEEJAH DA SALEES YAKE DAN MUN JI DA
FARKO TACE AUREN NASU CIKE YAKE DA SO DA KAUNA?.*
*MEYE SILAR TARWATSEWAR WANNAN SO DA KAUNAR IN HAR AKWAI TA.*
*GA AUNTY RAHINATU GASU HAANAH GA KUMA DADA, KO WANE MATAKI DADA ZE DAUKA IN YAJI
ABIN KE WAKANA A GIDAN SA NA TAKURA YAYAN SA DA RAHINATU KE YI?*
*SHIKENAN SHI DADA BAZE YI DACE DA MACE TA GARI BA HAKA ZE RAYU DA YA'YAN CIKIN
UKUBAR MATAR UBA KK KUWA RABUWA ZE YI DA ITA SU RAYU HAKA BATARE DA UWA BA?*
*SHIN WAI WANE KUSKURE HAJIYA YAAYA TAYI WA RAYUWAR DADA DATA KE NADAMAR SA HAKA?*
*HAJIYA FAKMATA ABAR TAUSAYI AN SHIGA DA ITA THEATRE, KO YAYA AIKIN ZAI KASANCE?,
SHIN ZA'A YI NASARA KO KUWA?, SHIN ZA'A FITO DA ITA A RAYE KO KUWA WA'ADIN YAYI
KAMAR YADDA TA FADA?*
*Kai, tambayoyin da yawa da ba zasu lissafu ba haka kuma kowanne yana da amsar shi
wadda ba wanda ya sani se ni kadai wato Ouummey, ku dai ku biyo ni domin warware
duk wani kulli dake cikin wannan tafiyar, domin cigaba da samun damar karanta
littafin RASHIN HAIHUWA KINDLY make your payment via*👇
9013101854, Rabiatu Abdullahi Aminu, opay
Or
2391368231
Rabiatu Abdullahi Aminu, zenith bank.
HURRY up Dan muyi my fara wannan tafiyar dan endpoint din akwai nisa, se kun zo💃💃💃💃
Ouummey ✍️
.