Showing 15001 words to 18000 words out of 41315 words
kai mi ne wajen kokawa dashi dole ya hakura ya daga ni tare da tsura min
jajayen idanun sa da ke cike da neman magana ga kuma bacin ran da na tusa masa,
yana daga ni na tashi ina gyara riga ta na mike tsaye tare da kakkabe jikina nayi
hanyar barin garden din ina karkada masa jiki, ko banza na san shima na bata masa
kamar yadda yake bata min.
★★SALEES★★
Duk yadda yake tunanin iskancin khadeejah ya wuce wajen, kalli yanzu abin da tayi
masa kamar wani kwarto alhalin yana matsayin mijin ta shugaban ta, a yanzu kam dari
bisa dari ya yarda raini ne tsagwaron sa tsakanin sa da Khadijah, ta raina shi ne
take masa haka, ai da datake ganin girma da kimar sa musu wannan ze iya kirga so
nawa ta masa, lallai se ya dau kwakkwaran mataki kan ta, ba dai jikin ta bane take
masa wulakanci dan ya bukata?, To ta rike abin ta ta jika tasha dan alkawari ne
baze kuma neman ta ba, in kuwa ta kawo kan ta lokacin zata san ita bata iya
wulakanci ba dan se ya nuna mata shima tantiri ne kamar ta, yana ji da fiye da duk
abinda take ji.
Ya dade zaune a wajen kafin ya iya mikewa ya koma gida, fita ya so yi ko yaji
sauƙin bacin ran sa sedai baze iya ba, a yadda marar sa ke damun sa cikin ma da
kyar yake taka kafa.
Ganin yadda ya wuce su rai bace fuska hade yasa Mariya tashi ta bi bayan sa da
sauri, sedai ko kafin ta kai gare shi tuni ya shige tare da datse kofar, turus ta
tsaya tana kallon kofar dan this is unlike him, bugawa ta shiga yi hankali tashe
sedai duk iya bugun ta yayi mata banza ko uhm bece ba haka ne bude kofar ba har ta
gaji ta juya jiki a mace ta sauka kasa.
Shi kam Salees duk bugun da take yi yana ji kuma yana sane yayi mata banza, abinda
bata sani ba dan ita ya rufe kofar dan ya san se ta zo takura masa shi kuma baya
bukatar takurar ta dan ba abinda zata iya yi masa, khadeejah ce kawai maganin sa
ita kuma ya fahimci hayaki kan ta keyi amma yayi alƙawarin sauke mata duk ma uban
dake kan.
Haka ya cigaba da juyi dafe da marar sa se uban gumi yake haɗawa kafin wani
wahalallen bacci yayi gaba dashi me cike da mafarkin Khadijah kala kala.
Be tashi ba se after Six, a gurguje yayi wanka ya fita Masallaci jikin sa duk ba
kwari, sallar ma ranar cikin wasi wasi yayi ta dan gaba daya hankalin sa na kan
Khadijah, tunane tunane kawai yake yi a kan ya, wata zuciyar na fada masa ya sake
gwada ta ko zai dace wata kuwa na bashi shawarar fita harkar ta har ta gane kuren
ta, be bar masallacin ba se da yayi isha kana ya nufo gidan cike da karbar shawarar
zuciyar shi ta sake bata dama.
★★★★
Fadawa nayi kan bed fuska ta cike da murmushi me fadi wanda na manta rabo na da
irin shi, wato yau da naga Salees cikin irin yanayin da na kan shiga a dalilin da
se naji raina yayi sanyi, sanyi fa sosai dan ba karya naji dadi wallahi.
Juyi nayi tayi ni kadai ina sake shirya yadda zan cigaba da zama da kowa na gidan
da halin sa, na daina daukar cin kashin kowa tun da ina hakuri amma ba'a san ina yi
ba, da ace duk abinda ke faruwa Salees na bin bayana in Ina da gaskiya da maybe ban
sare ba haka, amma babu ruwan sa dani, babu ruwan sa da zan damu ko zuba cutu, shi
dai duk abinda aka tsara masa shi yake hawa, duk abinda aka fada masa a kaina se ya
yadda, nayi ban yi ba duk ba ze bin cika ba, kamar ba shine a baya yake fada min ba
wanda ya kai shi sani na ba, ba wanda ya kai shi sanin hali na, ba wanda ya kai shi
sanin abin da zan aikata ko ba zan aikata ba, duk ya manta wannan, duk ya zubar da
komai ya watsar da komai, baya kallo na a komai face Khadijah, matar da yake aure
wadda bata haihu ba, ba'a ma maganar soyayya, dan yanzu ina tantama in akwai so na
a ran sa, dan abinda yake min masoyin gaskiya baze yi shi ba.
Kiran sallah ya sa na mike tare da shiga toilet na dauro alwala na tada sallah, ina
idar wa na yi azkhars dina kana na cire hijab din na fita zuwa kitchen dan yunwa
nake ji, noodles na dafa na zauna na ci acan kana na wanke plate din na aje na koma
daki, system na jawo na shiga aiki na dan yanzu na sake maida hankali dan bana san
abin d zesa suna na ya fita daga cikin masu samun promotion din nan, na saka rai
sosai ina kuma fatan Allah ya sa na dace.
Karfe tara na tattara komai na aje na shiga wanka, sleeping dress na saka kana na
feshe jiki na da turarukana masu sanyin dadi wanda ko ba zan je dakin Salees ba
bana fashin sa su, se da nayi addu'a sannan na kwanta bayan na kulle kofa ta.
Har bacci ya fara dauka ta na ji kamar an bude dakin an shigo, a tsorace na mika
hannu na kunna wuta dan switch din na daga saman kai na ne, a boye na sauke ajiyar
zuciya ganin Salees sedai a fili se na bata fuska in bin shi da kallon mamaki da
kuma gajiya da ganin sa, maida kofan yayi ya rufe tare da takowa ya zauna bakin
gado yana kallo na nikuwa na kau da kai gefe ina bata rai.
"Tashi zaune muyi magana".
Kamar ba zan tashi ba se kuma na fara tashin a hankali kamar me ciwon laka wanda
ina sane nayi dan na bata masa dan tuni na dade da sanin baya san jira a rayuwar
sa, kusan minti biyu kafin na zauna sosai sannan na kai kai gefe.
"Bana san tashin hankali Khadijah, ki fuskance ni mu sami fahimtar juna".
Juyo da kaina nayi na zuba masa ido kamar yadda ya bukata, seda ya dan yi shiru
alamun yana tunanin ta ina ze fara kafin ya riko hannaye na, na kalli hannun sannan
na maida duba na kan sa
"Bana san irin wannan zaman da muke yi Khadijah, ban taba tsara hakan tsakani na
dake ba, in laifi nayi miki ki fada min na baki hakuri a wuce wajen amma bana san
gaba da fushi".
Shiru nayi kawai, lallai namiji bai da kunya, wai ni Salees ke tambaya in laifi
yayi min saboda yanzu tashi ta kawo shi, duk abinda ke faruwa be ga ni ba, duk
abinda yake min ba laifi bane, aikuwa ze ga rainin hankali in dai nice dan nq
shirya masa
"Kiyi magana, ki fada min laifi na and we'll sort things out komai ya wuce".
"Baka yi min komai ba zuma na".
Zuba min ido yayi na tsayin mintina kafin ya sake matsowa kusa na har nunfashin sa
na sauka kan fuska ta
"No nayi miki, Ina ji a jikina nayi miki laifi, in haka ne meyasa da baki min haka
ba se yanzu?, pls ki fada min me nayi miki dan iya tunani na na kasa ganowa".
Murmushi nayi jin wai ya kasa gano laifin sa
"Ka kwantar da hankalin ka pls, baka min komai ba ni hutu kawai nake bukata, pls ko
zaka iya komawa wajen Mariya har zuwa wani dan lokaci?".
Izuwa yanzu ina iya hango bacin ran d Salees ke ta kokarin boyewa sedai ko gezau
ban ji komai ba a raina akasin da da ban so ko kadan in ga fushi ko damuwa tattare
dashi
"To kuwa baze yiwu ba, na biki na lallaba ki, na kwantar da kai na sanyayar da
murya duk dan mu zauna lafiya amma kin ki bani hadin kai, zama da nine kika gaji ko
kuwa wani salon wulakanci ne?".
Zare hannyeye na nayi daga nasa na koma na kwanta ina bashi amsa
"Babu ko daya cikin biyu kawai dai kamar yadda na fada maka ne ina bukatar hutu,
Allah ya bamu alkhairi, pls in zaka fita ka kashe min wutar ka kuma rufe min
dakin".
Daga haka na ja bargo na lullube ƙafafuwa na tare da kulle ido na, tabdi bala'i ni
kaina na san na tsokana masifa sedai sanin na shirya mata yasa nayi banza da duk
bala'in da Salees ke yi
"Kar ki maida ni wani shashasha mana, bar ganin ina bin ki ina lallaba ki amfada
miki tsoranki nake ji, ko kuwa kin fi karfi na ne, to wallahi kyale ki nake yi
kawai darajar su Abba, amma ban da haka ke in ance kiyiwa Salees iskanci ba zaki
fara ba, wacece ke da za'a dinga bin ki kina wani daukan kai, ban da ma kin kasance
butulu duk rufin asirin da nayi kiki baki gani ba, duk suturar da nayi miki amma
nine zan zama abin wulakancin ki, to bar ganin ana wani cewa kin raina ni kin
mallake ni, wannan duk karya ne dan ba macen da ta isa ta raina ni, ba'a haife ta
ba wallahi dan kuwa se ta koma gidan gyatumi tun da babu abinda ya zama dole, kuma
wallahi tun muna shaida juna maza ki koma hayyacin ki kafin mu kai ga yin batacciya
dan akan haka wallahi komai ze iya faruwa, in nace komai ina nufin komai".
Ya sa kai ya fice tare da banging min door din, duk da cikin fadan nasa akwai
kalaman da suka zafafa min amma se ban bari sun yi tasiri a raina ba, mafi aala
shine na bata masa rai wanda shine aiming dina kuma na ci riba dan haka se na tashi
na maida kofa ta na rufe tare da kashe wuta na koma na kwanta tare da rufe ido
bayan nayi addu'a, aikuwa ba jimawa bacci yayi awon gaba dani.
Washegari tun bakwai saura na fice dan bani ce da girki ba bana kuma bukatar abin
karin su, a office na hada tea da heater na dan ina da komai na bukata, na karya a
nutse hankali kwance sannan na shiga aiki na raina fes.
Karfe tara daidai na kwaso takardu zuwa cikin hall din da zamu yi meeting din
ma'aikata gaba daya, a nan naga Salees sedai kallo daya yamin ya dauke kai ni ma
kuma ban kuma kallon sa ba muka shiga abin da ya kawo mu, muna gamawa na koma
office dina, karfe biyu nayi na tashi aiki, yau kam ban iya dauke ido daga hanyar
gidan mu ba duk da zuciya ta na fada min kar nayi amma wata bangaren na tunzura ni
kan naje dan ko na tambayi Salees baze bari ni ba, tun bayan auren Mariya ya dauki
wata banzar akidar kulle ya ɗorawa kan sa, har gwara ma ni ina zuwa aiki ita Mariya
ba inda take zuwa se ta rufe watanni shida bata fita a gida ba, sauƙin ta yana kai
wa iyayen ta ya'yan ita ce dai se sanda ya so sannan ze kai ta da dare, nima haka
se dare yake bari na zuwa gida ko ya kai ni, daga baya ne nake takura masa in wuce
daga wajen aiki shima ba ko yaushe yake yadda ba.
Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama daidaita parking a compound din gidan mu kana
cike da matsanancin kewa nake bin ko ina da ido ganin an sake gyara shi yayi kyau
fiye da da, gwanin sha'awa ko ina ya sha sabon paint ga kuma shuke shuke masu
daukan hankali, ba karamin kokari su yayan mu ke yi ba akan gidan mu shiyasa kullum
cikin sa albarkar Abba da Ummi suke, gidan mu babban gida ne tun a da dan Abban mu
na cikin masu kudin unguwar mu, compound din gidan mu babbane dan yana daukar
motoci sama da biyar, a takaice dai ze dauki mota bakwai ko takwas batare da takura
ba, sassa uku ne a gidan mu, bangaren samari wanda yanzu duk sun yi aure, bangaren
Abban mu se part din Ummin mu inda a nan muka rayu ni da yayata salima.
A hankali na bude kofa na fito me gadi ya washe baki yana min sannu da zuwa haka ma
sauran ma'aikatan mu, na amsa a mutumce muka gaisa kana na nufi main falo din
mu.......................
Ouummey ✍️
Ouummey 08 {5/6/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 08
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
____________________________________________________________________________
_Free Chapter Eight _
A hankali na tura kofar na shiga baki na dauke da sallama, Muryar Ummi da ta amsa
min yasa na san tana zaune a falon so ina cire takalmi na na shige gaba daya na
cike da dokin ganin ta, aikuwa da gudu na karasa na fada kan ta ina dariya
"Kai kai kai, kayar dani kike son yi Khadijah, irin wannan fadowa ai se ki karya
ni, wai ke bama ki san kin girma bane?"
Ummi ta fada cikin dariya itama tana rike ni a jikin ta, gyarawa nayi na zauna kusa
da ita kamar zan koma cikin ta na kwantar da kaina kan kafadar ta ina fadin
"Nayi kewar ki ne sosai Ummi na, wata uku fa rabon da nazo naga Ummi na ai nayi
kokari".
"Ba wani kokari, mu da ada mace se tayi shekara bata je gida ba in ba wani abun ne
ya faru ba".
Zaro ido nayi, shekara, lallai
"Tab wallahi ba zan iya shekara banzo gida ba, waiiii".
Hararata Ummi tayi
"To in ba'a barki ba ya zaki yi ai dole ki zauna".
"Ai ko daga wajen aiki ne se na biyo, yanzu haka fa Salees be san zan zo nan ba,
kawai na kasa daurewa ne na biyo".
Ban san abinda ya kaini da shegen surutu na na fadi haka gaban Ummi ba bayan na san
halin ta, aikuwa ture kai na tayi da sauri daga jikin ta lamarin da yasa gaba na ya
fadi ga kuma amon muryar ta cikin ban umarnin in juyo gare ta cikin tune me shaida
sam babu wasa a tattare da ita.
Matsawa nayi daga kusa da ita da dan sauri kadan dan Ummin mu na da saurin hannu
wataran duk da bata fiye yi min ba amma ina shakkar bacin ran ta
"Kika ce ba da sanin mijin ki kika zo nan ba?".
Yadda nake raba ido a wajen zaka dauka kisan kai nayi dan Ummin mu bata wasa da
yaro akan gaskiya, duk shirin da kuke da son da take nuna maka baze hana ta rikide
ba a take.
"Uhm ko na tambaye shi baze bar ni bane Ummi".
"Okay se hakan ya zama excuse din da zakiyi satar fita?, Saboda kina takamar kina
aiki ko?, Ita yar uwar ki ba haka take zaune ba, ko kuwa kin fita iya son gida da
iyaye ne?".
Da sauri na girgiza kai alamun a'a kana murya na rawa na shiga bata hakuri, aikuwa
na sha fada kafin ta hakuran sannan ta ɗora da nasiha kan biyayya da hakuri cikin
zamantakewar aure.
"Ummi wallahi na gaji da zaman gidan nan, jiya zuwa yau ne fa kawai nayi farin ciki
amma kusan kullum cikin damuwa da bacin rai nake".
Shiru Ummi tayi bata ce komai ba se tsura min ido da tayi, ban so na fada mata ba
dan nasan zata damu amma waye nake dashi bayan ita, uwa tafi kowa fahimta da kuma
sauraren ya'yan ta haka kuma cikin hikima da basira zata kwantar musu da hankali,
duk da mun yi magana da Abba har naji sauki sedai ba kamar Ummi ba dan Abba da yace
ze kira ni da safe be kira ba, nasan kuma ba komai yake gudu ba face ji na cikin
tashin hankali, sedai nasan da Ummi ce wallahi se ta kira ni, ba kira ba kiraye
kiraye ma dan uwa daban ce, ina son iyaye na duka amma matsalar mace a gidan aure
yar uwar ta mace ce kawai zata fahimta.
"Akwai abinda ke faruwa wanda ya kamata na sani ne Dijeh?"
Seda na sauke ajiyar zuciya kafin na shiga bayyana mata halin da nake ciki, sedai
dole na boye wasu abubuwan dan nasan ze sa Ummi taji haushin Salees sosai wanda
maybe har mu shirya ita tana kallon shi da abin, ba kuma wai Ummi bace kadai haka
duka iyaye suke so pls yan uwa mu dinga sanin iya abinda zamu fada a gidan iyayen
mu.
"Ki kara hakuri khadeejah, ina da tabbacin Allah baze bar rayuwar ki haka ba insha
Allah, ki cigaba da kau da kai akan shi da matar shi da ƴaƴan shi, ban da daukar
hudubar banza duk da nasan ba kawaye ke gare ki ba, amma zuciya ma na iya kai mutum
ta baro, ki rike addu'a da karatun Kur'ani, komai yayi zafi maganin sa Allah, nima
ina ta taya ki kullum, insha Allah Allah zai dube ki da duk ma masu iri matsalar
ki".
"Ameen Ummi na Nagode sosai".
"Se kuma batun gudun mijin ki, kar in kuma jin wannan shashancin a wajen ki, ban
sani ba ko sakarcin autanci ke damun ki, wataran in kika yi wani abin kamar in zane
ki, nasan kin sani amma bari na tuna miki duk randa kika bijirewa bukatar mijin ki
zaki kwana ne Mala'iku na tsine miki in har baki roki gafarar sa ba, dan haka
umarni ne na baki in kin koma kije ki bashi hakuri kuma ban yarda ki bar shi ba har
se kin tabbatar ya hakura, ban da wautar ki khadeejah ai ita mace zata iya kwatowa
kan ta daraja cikin ruwan sanyi batare da tashin hankali ta hanyar irin haukan da
kika yi ba, ga kuma kishiya a kusa dake da take jiran kowace dama dan sake karbe
miki miji amma baki lura ba".
Haka Ummi tayi ta min nasiha tare da karin tips din kula da miji iri iri, kar kuyi
mamaki dan dama ni bani da kawaye, Ummi ce kawata ita da salima haka kuma itace
uwata, wajen shawara ta bani wajen gyara tayi min wajen fada ma duka haka.
Kayan gyara masu kyau da inganci