Showing 27001 words to 30000 words out of 41315 words

Chapter 10 - RASHIN HAIHUWA by Ouummey

Ouummey   

08 May 2026

69

ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________

_Free Chapter Twelve_

Haka ya wanzu dafe da kan sa da ke masa matsanancin ciwo cikin wani hali, kirjin sa
wani irin bugu yake masa kamr ze faso waje, irin yadda kan sa ke sarawa ji yake
kamr ya cire ya yar.

Wuni guda haka ya wuni cikin wannan har zuwa karfe biyar da ya iya tashi yana dafe
bango saboda jirin dake dibar sa, yana ji ana kiran sallar Asr amma ya kasa tashi
har aka idar duk akan kunnen sa.

Anan bedroom din yayi alwala ya gabatar d sallah a zaune saboda jiwar da yake gani,
addu'ar da yake so yayi ma kasawa yayi dole ya silale ya kwanta kan praymat din
yana runtse ido.

Oat din ta damawa Miemie kamar yadda suka fi kiran Meemah saboda sunan
Maamahn su da taci sannan ta fita zuwa dining dauke da ita a hannun ta ta zaunar da
ita kan seat daya itama ta zauna a daya, Ameerah ta zubawa abinci a plate ta tura
mata gaban ta hakan yasa ta kalle ta cikin rashin fahimta dan mostly tare suke ci
"Eat your food Ameerah and pls do take care of Miemie bari na gano Dada".

Gyada mata kai Meerah tayi iya kuma ta shiga zuba abinci cikin plate daban, faten
dankalin turawa me ruwa ruwa ta zuba masa da ya sha kayan lambu da kuma hanta
sosai, cikin nutsuwa ta dora kan madaidaicin tray tare da dora goran ruwa me
madaidaicin sanyi se kuma lemon kwali ta dauka ta nufi falon sa.

Kan Centre table din sa ta aje abin kana ta karasa kofar bedroom din sa ta shiga
knocking ganin bata gan shi a falon ba, a hankali take knocking din dan har ta
takura masa sanin da tayi baya san hayaniya, jin shiru yasa cike da fargaba ta fara
tura kofan a hankali har ya bude sosai kana ta shiga bakin ta dauke da sallama.

A gigice ta karasa wajen da yake kwance ta shiga girgiza shi tana kiran sunan sa
sedai ya kasa amsa wa, wannan ya kara gigita Haanah ta nemi fita a guje dan neman
wanda ze taimaka mata a kai shi asibiti amma dole ta tsaya jin yadda ya riko hannun
ta.

"Yanzu zan zo, am coming Dada, zan kira maigadi ya taimaka min mu kai ka asibiti
ne, sannu Dada yanzu zan zo".

Da kyar ya motsa bakin sa yayi magana cikin muryar sa dake fita da kyar

"Dauko min drugs dina a drawer Haanah".

A rude ta shiga amsa masa tana mikewa
"Toh Dada, sannu bari na dauko, sannu Dada".

Da tarin magungunan ta dawo gaban sa ta zauna kana ta dauko wanda ze sha kasancewar
ta san prescriptions din sa, bottle water din ta bude ta aje kana ta fara kokarin
taimaka masa ya tashi zaune, duk da yanayin da yake ciki seda murmushi yayi
escaping daga lips din sa, yo Allah ya tuba Haanah ko motsa shi zata iya yine balle
ta daga shi.

"Sannu Dada, sannu, open your mouth ka karbi maganin kaji".

A hankali ya bude bakin ta sa masa kwayoyin kana ta sa masa bakin robar ya shiga
shan ruwan, seda ya hadiye maganin gaba daya sannan ya janye bakin sa yana sakin
numfashi kasa kasa, komawa yayi ze kwanta tayi sautin rike hannun sa tana girgiza
masa kai

"A'a Dada, kar ka kwanta maganin ze dame ka, ka dan zauna kadan ya fada maka, lemme
bring your food tukuna".

Jingina yayi kamar yadda ta bukata ita kuma tayi saurin fita zuwa inda ta aje
abincin sa ta dauko masa, cokali tasa ta debo tare da kai masa baki taba fadin

"Dada haaaaa". A tausashe, girgiza mata kai yayi alamun a'a se kuwa ta kwabe fuska
tana neman yin kuka

"Pls Dada ka daure kaci ko ka sami karfi kuma ciwon ya tafi, You know bamu da kowa
a duniyan nan da ya kai ka Dada, we loose our Maamah ba zamu so muyi loosing din ka
ba, you're all we have, our only strength and source of happiness, pls eat for our
sake Dada, for your little ones kaiiii".

A sannu ya bude bakin kamar baya so ko da yake ba kama bane baya so din, ze ci ne
dan su kamar yadda ta fada dan mafi girman tashin hankalin sa shine ganin damuwa
kan fuskokin ya'yan sa, har can go to any limit dan ya sa su farin ciki ko da kuwa
shi baya ciki, a hankali a hankali ya dinga karbar abincin har ya koshi, she's glad
ganin yaci da yawa dan farin cikin ta sosai ya bayyana kan pretty face din ta taba
ta sakin cute smile

"Ka gani Dada, dama kana jin yunwa, kalli fa ka kusan cinye wa na ji dadi, yanzu
zuwa anjima zaka iya kwanciya amma da zaka hakura har kayi isha tun da kaji ana
sallan magrib yanzu".

"Allah yayi Miki albarka Rayhanah, Allah ya hada kan ku da yan uwan ki ya albarkace
ku da mazaje nagari".

"Ameen Dada, Ameen, in kama ka kaje kayi alwalan?".

Dariyar sa me kyau yayi

"Haba dai, Dadan ki is not as weak as you're thinking, zan je da kaina, kema je ki
kuyi sallah da yan uwan ki and stay with them nima yanzu zan fito".

Pecking goshin sa tayi tana wide smile
"Okay Father, a fito lafiya".

Ta fice rike da tray din kayan abincin sa, a falo ta tadda su Miemie da Ameerah
zaune suna kallon cartoon, kallon ta Meerah tayi tare da daga mata gira alaman yaya
yake and she answered cikin yi mata alama da hannu alamun he's fine.

Duk suna yin body language ne saboda Miemie dan tana jin ance Dada sun san zata
addabe shi ne ta hana shi sukuni da kiran Maamah da a rana se ta kira yafi cikin
calbi.

Rayhanah bata mamakin hakan dan a bayyane yake Miemie Maamah's girl ce akasin su da
suke Dada's babies, a rayuwan su basu taba sanin wani abu wai shi kulawar uwa ba
hakan yasa tsakanin su da ita kallo ne da gaisuwa, daga nan kuma se su takure waje
daya, walwalar su kuwa har se idan Dada na gida.

Zama tayi kan dining ta dan ci abinci a gurguje kana ta tashi zuwa bedroom tana
musu magana

"Oya girls, time for magrib prayer".

Tashi duk suka yi zuwa dakin inda one after the other suka yi alwala Ameerah tayi
wa Miemie sannan suka saka hijabs din su da Rayhanah ta dauko musu kana suka jeru
kan praymat daidai lokacin da Dadan ya leko, ganin su a haka ya juya ya fita zuwa
Masallaci suma suka tada nasu sallan.

Suna idarwa suka yi azkhars din su again Rayhanah ta tashi ta dauko musu kur'anan
su dake bedside drawer ita da Meerah suka fara karatu inda Meerahn ke biya mata
karin da aka yi musu juya zuwa na yau, seda suka gama sannan ta kara mata verses
biyar inda ita kuma ta cigaba da maimaita wa Haanah kuma ta koma ga Miemie.

Cikin wayo da dabarar da Allah ya mata ta yi sa Haanah ta biya mata aya dayan da ta
kara musu yau a school, tar yarinyar ta kawo karatun ba ko tuntube hakan yasa ta
kara mata aya biyu marasa tsayi, shima se da ta ga ta iya sannan ta bar ta.

Hijab ta cire ta karbi nasu ma da suka cire ta ninke tare da maidawa cikin wardrobe
kana ta juyo se kuwa idanun ta suka fada cikin na Dadan ta da ke tsaye yana bin ta
da kallo cike da soyayya da kauna me tsanani, a ko da yaushe ya kai kan sa kasa da
sunan sujjada baya dagowa face yayi godiya ga Allah da ya albarkace shi da samun ya
daya tamkar da dubu, yar dake matukar so da kaunar sa hadi da tsananin tausayin sa,
yar da ba dan ita ba be san yaya rayuwa zata kasance masa da yaran sa ba alhalin
yanzu da ba mahaifiyar su ta gushe.

Rayhanah yarinya daya ce amma a wajen sa tafi yaya dari domin kuwa ta share masa
hawaye tun kan ta san kan ta, tun tana karama take da basira da wayo hadi da
nutsuwat fahimtar abubuwan da suka girmi hankalin ta, a maimakon abin ya dame ta
yasa ta cikin wani hali se ya koya mata tausayin mahaifin ta da halin da yake ciki,
wanda ta taso ta girma dashi ya ke kuma karuwa a kowace kwana da wuni, kaunar ta
gare shi bata buya a ko ina a kuma ko wane irin yanayi, ita ce rai daya dake gane
kowane irin hali yake ciki tun kafin bakin sa ya furta, ta san shi ciki da waje
sedai kawai yayi mata ta babba da yaro ya layance mata wasu abubuwan amma ba wai
dan bata fahimta ko gane ba.
Tana fifita cin sa kan nata, walwalarsa kan nata, farin cikin sa kan nata haka kuma
tana damuwa da damuwar sa tayi dariya da dariyar sa, shiyasa ita din daban ce cikin
yaya ukun da Allah ya azurta shi dasu, ita ce kuma *RIBAR AUREN* Maryam da kullum
ya kalla baya dana sani balle nadama yake kuma alfahari da kasancewar ta ikon sa
mallakin sa.

"Barka da dare Dada na".

"Barka kadai yaran Dada, hope you all fine?".

"Yes Dada". Suka amsa masa gaba daya ban da Haanah dake ta murmushi tana kallon su,
seda ya gama gaisawa da su gaba daya sannan ta durkusa har kasa ta gaida shi, be
amsa mata ba seda ya shiga har dakin yasa hannu ya dafa kan ta sannan ya amsa cike
da walwala

"Jikin naka yayi sauki ko Dada?".
"Eh babyn Dada, Father baze mutu ya bar babies din sa ba har se ya aurar dasu gaba
ki daya insha Allah".

Dariya suka yi su duka ita da Ameerah suna rufe ido at the same time wai kunya,
shima dariyan yayi kana ya dauki Miemie a jikin sa ya fita falo suma suka biyo
bayan sa, a kan three sitter ya zauna tare da zaunar da Miemie kan laps din sa su
kuma suka zauna each by his side.

Cartoon me kau and educational ya kunna musu suka shiga kalla Ameerah da Miemie se
hira suke akai, ganin hankalin su ya dauku yasa Rayhanah juyawa a hankali ta
fuskanci Dada

"Dadaaaaah".

Ta kira shi cikin low tone dan kar tayi calling attention din su Meerah, ganin
yadda ya zuba mata ido yana bata full attention din sa yasa ta karyar da kai gaban
ta ba faduwa haka tana ta addu'a a ranta kan Allah yasa ya yarda da abinda zata
fada

"Pls Dada kayi aure".

Ta fada tana sunkuyar da kai haka tan jin effect din piercing eyes din sa akan ta,
kirjin ta na duka jin yayi shiru ta cigaba da magana da rawar murya

"You're suffering Dada, kullum baka samun bacci, You're always having sleepless
nights saboda mu, abubuwan sun maka yawa Dada, kai din namiji ne, ga matsalan
office, ga na jama'a ga na namu ga kuma nasu Yaaya, Dada na damu da yawa, tun
tasowa na nake ganin ka cikin kunci da damuwa, i want you to live a happy life
Dada, fatana da buri na be wuce in dinga hango kwanciyar hankali, jin dadi da farin
ciki a idanu da fuskan ka ba, pls dan Allah do me a favor in ga Dada na cikin
yanayin da nake fata kafin Allah ya dauki raina kaji Dada".

Tun da ta fara magana babu kalmar da ta doki ran sa kamar irin kafin Allah ya dauki
ran ta, abu na zuciya kawai se ya dinga hango har gashi ance ta mutu, ga ta ance
itama ta tafi kamar Maryam, se kawai ya shiga girgiza kai yayinda zuciyar sa ta
dinga ayyana masa ze iya rasa yar sa mafi soyuwa a ran sa, ze birne rai mafi damuwa
dashi

"A'a, a'a, no Haanah, ba inda zaki je, a'a ba zaki mutu ba".

Ganin yadda Dadan ya rikice yasa ta riko hannun sa tare da matsewa cikin nasa

"Calm down Dada, nima ba zan so in mutu in barka ba, I'll not leave you Dada, not
now not after, ka kwantar da hankalin ka kaji".

Ajiyar zuciya ya sauke tare da rufe ido ya kwantar da kai kan makarin kujera se
kuma ya bude ya zuba kan fuskar Haanah da ta cigaba da magana

"Zaka yi aure Dada?, Zaka cika min buri na?".

Da sauri ya hade rai

"Kar na kuma jin maganar nan a bakin ki Rayhanah, ko ba yanzu ba, okay?".

A sanyaye idanu cike da kwalla ta gyada masa kai zuciyar ta na karyewa dan ta san
ba dan kowa Dadan yaki aure ba se dan su, yana tsoron ya auri wadda zata gallaza
musu ko ta nemi raba shi da su
"Insha Allah ba zan Kuma magana ba Dada, a koyaushe ni me bin umarnin ka ne, komai
zan yi kai nake fara tunani kuma wannan ne dalilin da yasa na kawo batun aure dan
nasan insha Allah in kayi dace da mace nagari zaka yi farin ciki a rayuwa, zaka
sami nutsuwar da ka rasa tun zamanin kuruciya hak kuma zaka sami kwanciyar hankalin
da baka taba tunani ba.
Na sani saboda mune kake dodging maganar aure Dada saboda kana tunanin makomar mu
in ba'a yi dace da tagari ba, sedai ya kamata akan komai mu zama positive, what if
muka yi dace da tagari, kai ma da muma duk zamu sami jin dadi da walwala, and above
all hankalin Yaaya ze kwanta, kayi tunani akan Yaaya, itama mahaifiya ce kamar
yadda kake mahaifi, yadda kake kaunar mu haka Yaaya ke kaunan ka, yadda kake son
ganin mu cikin farin ciki da walwala haka itama Yaaya ke son ganin ka, na sani ka
san yanayin da take ji tun da kaima kana jin makamancin sa, shiyasa na kawo maganar
da na san zata faranta maka da ita amma ba zan kuma ba insha Allah tun d baka so,
am sorry for upsetting you Dada, am sorry pls forgive me".

Gaba daya se yaji Haanah ta daure shi da jijiyoyin jikin sa, se yake ji kamar ta sa
wata igiya me karfi ta zazzarge shi dasu, kawo batun Yaaya ya sanyaya gabban jikin
sa gaba daya, eh ba karya tayi ba domin duk wanda ya kwana ya tashi a gaban Yaaya
yasan babu abinda take fata da burin gani irin yayi aure a yanzu, ta sha zaunar
dashi tayi masa nasiha, ko kuma tayi ta bashi labari mai cike da hannun ka mai
sanda amma duk se ya nuna baigane ba, yanzu kuwa da ta alakanta abinda mahaifiyar
sa take ji da wanda yake ji se ya gane radadin me girma ne, haka kuma akwai ciwo a
zuciyar mahaifiyar sa dangane dashi

"Na amince Haanah, amma not now, ban kuma ce a zaba min ba, a bar ni har zuwa
lokacin da zan ga wadda ta kwanta min da kaina".

A zabure ta ke kallon Dadan nata ido waje,

"Da gaske Dada?, Da gaske ka yarda zaka yi aure?".

Gyada mata kai tayi babu digon fara'a a fuskar sa, sedai ga mamakin sa hakan be
sanyaya jikin Haanah ba balle har ya hana ta fara'a se ma wani karsashi da ya ga ta
samu lokaci daya, karo na farko kenan da Rayhanah tayi farin ciki lokacin da shi
yake cikin damuwa................

_*3 PAGES TO GO, FREE CHAPTERS A YET TO END*_.

_*KAR KU MANTA LITTAFIN NAN NA KUDI NE KAMAR YADDA TUN FARKO NA FADA HAKA KUMA NAKE
ADDING PREFIX DIN _FREE_ A HEADINGS DIN KOWANE PAGE, SO GA MASU BUƘATA SHOULD HURRY
UP AND START MAKING THEIR PAYMENTS DAN 15 PAGES NE FREE*_.

ME BUKATA ZE IYA DM TA WNN NUMBER👇
*09013101854*


Ouummey ✍️
.




Ouummey 13 {5/13/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey




Ouummey 13
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________


_Free Chapter Thirteen _

Yana lura da yarda Haanah ke walwala da farin ciki har zuwa lokacin da suka yi masa
sallama suka tafi daki dan yin bacci, da ido ya raka su har suka shige daki yayinda
ya sake gyara zaman sa kan cushion din da yake yana kwantar da kan sa kwakwalwar sa
na yin nisa cikin tunani.

Seda ta tabbatar ta Miemie tayi bacci kafin ta sauko daga gadon ta dauki wayar ta
da sauri, curiously ta shiga kiran layin kakar ta without minding dare ya fara nisa
dan ita after ten lokacin, seda wayar ya kusa karewa kafin aka daga tare da
sallama, a dokan ce Haanah ta amsa wa kakar ta and without sauke numfashi ta ɗora
da dalilin kiran

"Albishirin kin Yaaya".

Daga can bangaren dattijuwa ce zaune ina gadon ta me kyau kamar na yaran amare yan
gata, ba wani shekaru ne da ita da yawa can ba sedai zata kai sittin da wani abu
zuwa close to saba'in, cike da son jikar tata ta amsa mata da

"Goro fari kakal Rayha".

Ta bangaren Rayhanah duk da bata san yadda Yaaya ke bata mata suna amma farin cikin
da take ciki yau ya hana ta complaining

"Dada ya yarda ze yi aure Yaaya" ta fada excitedly tana washe baki kamar gonar
auduga, unbelievably Yaaya ta zaro ido tana sake manne wayar da kunnen ta

"Kai haba dai, wa ya fada miki wannan tatsuniya?".

Seda ta tura baki gaba jin yadda Yaaya ke neman karyata ta bayan ta san karya bay
acikin habits din ta sannan ta bata amsa

"To wallahi da gaske nake kuma ba tatsuniya aka bani ba shi da bakin sa muka yi
magana dashi kuma ya yarda yace ya amince ze yi aure".

Wani irin kwallan farin ciki ne ya taru a idanun Yaaya da yasa muryan ta ya raunana

"Allah yayi miki albarka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login