Showing 21001 words to 24000 words out of 41315 words

Chapter 8 - RASHIN HAIHUWA by Ouummey

Ouummey   

08 May 2026

64

ta ciro wani tablet guda biyu manya ta sa a baki tare da
korawa da ruwa, Wani ta dauko different from the first shima ta sha biyu sannan ta
cire doguwar rigan jikin ta tasa na bacci yayi light off tare da kwanciya bayan
tayi addu'a.

Kashegari da wuri ta shirya, tayi matukar kyau cikin Abayan da tasa kirar Dubai,
sosai ramar ta ta buya se wadda ba'a rasa gani ba, sallama tayi da su harira sannan
ta fita cikin motar ta wadda bata wata me kyau bace can amma kuma ba wai ba ta da
kyau bane.

A compound din gidan Hajiya Farida tayi parking ta fito tana sakin murmushi, Farida
ce kawai kawar ta ita ce kuma kadai yar uwar ta haka kuma aminiyar ta, gurbin da
Farida ta cike mata ba kadan bane haka kuma halaccin ta gare ta me yawa ne duk da
dai ita ce ta fara yiwa Faridan amma ba kowa ke iya rama alkhairi ba.

Da sallama ya shiga falon, ihu Hassana ta saki tare da tashi ta nufo ta a guje, duk
kai kai kai din da Hajiya Farida keyi be sa ta fasa ba se da ta fada jikin falmatan
har da wani dan tsalle kafin ta kankame ta, ita ma sa hannu tayi ta sake riƙe ta a
jikin ta suna dariya Farida kuwa ta soma fada

"Ke dai wallahi ban san yaushe zaki yi hankali ba Hassana, ban da rashin mutunci
kayar min da ita zaki yi da zaki dane min ita haka bayan kin san ba wani lafiya ne
ya ishe ta ba salan ki cuce ni, to Allah ki ka kuma se ran ki ya baci, bana son
shashanci, yarinya ga uwar nauyi kaman buhun shinkafa kawai ki nemi illata min yar
uwa".

Bata fuska Falmata tayi ganin yadda Hassana tayi rau rau da idanu,

"Gaskiya ni dai Farida kina min abinda bana so, kawai shikenan se ba zata zo ga
uwar ta ba saboda bani da lafiya, ko kuwa ke kadai ce me yar uwa da zaki ce haka,
dan ma kin samu ana yin yar uwar ta ki, to ni dai kiji ma ya'ya na are above
anyone, maza matso ki sake yi min oyoyo sweetheart ".

Ta fada tana sake buɗe mata hannu bayan ta matsa nesa da ita daidai lokacin da
Hussaina ta fito daga bedroom suka kuwa kwaso da gudu su duka biyun suka fada kan
ta gaba daya suka zube kan kujera suna dariya, ita kam Farida bata kuma bi takan su
ba ta cigaba da abinda take yi a kitchen jin yadda Falmata ta gwale ta sedai tana
jiyo kyakyacin dariyar su daga nan wadda ta manta rabon da taji dariyar Falmata har
haka.

Wani irin tausayin ta ne ya sake kama Farida tuno yadda Falmata ke masifar son yara
tun suna kanana se gashi Allah ya jarraba ta da rashin haihuwan kuma ta bata mamaki
dan bata taɓa zaton Falmata zata iya karbar wannan kaddarar ba.

Seda ta gama aikin ta sannan ta fito ya same su kamar wasu kawaye

"Oya aje a fito da komai a shirya kan dining bari nayi wanka nima".

Da haka suka tashi zuwa aikin da aka sa su ita kuma ta wuce wanka aikuwa itama
Hajiya Falmata ta tashi ta shiga taya su jera abincin, tare suka yi gaba daya
sannan suka wuce wanka suma ita kuma ta zauna kallon wata hira da ake yi da wani
mawaki a TV.

A shirye suka fito dan tare zasu tafi dukan su zuwa gidan marayu wanda nan ne gidan
su Farida da Falmata kasancewar marayun da suka tashi suka budi ido a gidan batare
da sanin su waye iyayen su ba, hakan yasa suka riki gidan marayun gida duk kuma
wanda ke cikin gidan suka dauke su yan uwa kuma dangi, Hajiya Farida bata taɓa
kunyar nuna wa ya'yan ta gidan matsayin nasu gidan iyayen ba, a kullum tana
alfahari da gidan dan acewar ta ba'a yi musu rikon wulakanci ba.

Seda suka karya gaba daya har Falmata sannan suka dungu ma zuwa compound suka shiga
motar Hajiya Farida leaving behind motar Falmata a gidan.

A motar na hirar su suke yi ita da Farida dake tuki yayinda Hassana da Hussaina ke
baya suma suna tasu har suka kai gidan, kayayyakin alkhairin da suka saba bayarwa
na kayan abinci duk suka dire haka kuma suka dinga zagaye gidan bangare bangare
suna gaisawa da jama'a, da suka tashi tafiya wannan karon Hajiya Farida ce kawai ta
bada kudi kamar yadda suka saba dan ita Falmata babu kudi hannun ta.
Haka suka yi sallama da jama'a suka koma gidan Farida suka sauke yan biyu su kuma
suka sake fita domin tafiya meeting din kungiyar su wadda Farida ta shiga ne kawai
saboda Falmata dan kungiyar purpose din ta babu irin su Farida ciki.

*NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS*

Babbar kungiya ce da ta cika ta tunbatsa da Manyan mata iri iri, kungiya ce da aka
kafa ta solely dan matan da basa haihuwa, zaka yi mamaki in ka ga dimbin mutanen
dake ƙarƙashin kungiyar domin ta haɗa mata kala kala, manyan masu kudi masu rufin
asiri kai har ma d talakawa.

An kafa wannan babbar ne domin kwantar wa d matan da basa haihuwa hankali, samar
musu da aikin yi da kuma kwatar musu yancin su a inda ya dace, haka kuma domin
taimaka su a gurin da suke buƙatar taimako.

Suna yin meeting din wannan ƙungiya ne annually ma'ana duk shekara, a nan za'a
zauna a ji koken juna, me bukatar taimako ayi mata, sababbin members kuma ayi masu
rigister tare da councelling kan abubuwan dake jawo rashin haihuwa, in abin me
magantuwa ne suna tsayawa kai da fata har se sun ga an ci nasara da izinin Ubangiji
batare da duba da ko nawa za'a kashe ba while the treatment...........


Ouummey ✍️
.




Ouummey 10 {5/9/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey




Ouummey 10
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________

_Free Chapter Ten_

Hajiya Falmata da Hajiya Farida sanannu ne a kungiyar saboda irin gudunmawar da
suke badawa, ba wai sun fi kowa taimako d kudi bane, a'a irin matsalar da Falmata
ke ciki da yadda take da jarumta da juriyar mai da komai ba komai ba yasa ka bata
mukami dan na kasa suyi duba izuwa ga rayuwar ta su kuma yi koyi da tawakkali hadi
da karfin zuciya irin nata.

Kamar ko da yaushe yau ma cikin nasara aka gama gabatar da meeting din, inda yau
taimakon nasu ya karkata ne kan wata mata da ke da matsalar karin mahaifa da ya
hana ta haihuwa gashi kuma mijin da iyayen ta ba masu karfi bane hakan yasa jin
labarin kungiyar da irin taimakon da ake yi a cikin ta yasa ta kawo kanta haka kuma
aka saurare ta duk da bata kasance wata hamshakiyar me kudi ba, ba kuma wata
celebrity ba haka kuma ba wata kusar gwamnati ba, motto din kungiyar shine mu'amala
da kowa with equality, babu ruwan su da mai kudi ko talaka, abinda suka sani shine
they all are one family and have almost similar problem so they'll come together in
finding a solution.

Miliyan uku da rabi ake bukata domin aikin dan abin yayi worsting ta yarda har ya
fara neman lalata mahaifar hakan yasa ake bukatar aikin urgently, wani abin burgewa
shine a wannan zaman da suka yi da kowa be san za'a iya kawo matsala ba se gashi
tashi daya har an hada miliyan biyu da rabi, inda wasu suka karbi bank account na
kungiya domin sending kudaden wasu kuma suka tura, abinda be isa ba za'a cika a
asusun kungiya.

Compound din building din tuni ya cika da kayayyaki, kayan masarufi, kayan amfanin
mata kama daga kan sabulai da turarukan wanka, kayan sawa, mayukan gyaran fata da
gyaran gashi, takalma, kai abubuwa dai da yawa da mace zata bukata na gyara daga
wajen mijin ya, ba mutum daya ne ya kawo ba, kowannen su kan zo da abinda Allah ya
hore mishi ne in aka hada se a raba, suna yin hakan ne dan ragewa mata takaicin
namiji da wani baze iya bada kudin gyaran jiki ko wani gyaran gashi ba, musamman ma
masu irin matsalar su da mata ke kallon basu kudin gyara ko wani abu as a waste of
resource.
Kowanne ka kalla fuska cike da farin ciki ana wasa ana dariya suka rabu, Falmata
cikin ranta bata ji dadin yadda abun ya zo mata cikin rashin kuɗi ba sai dai taji
dadin yadda yar uwar ta kuma aminiyar ta Farida ta rufa mata asiri domin kuwa ashe
kayan masarufi ne cike damkan a bayan motar ta bayar da sunan Falmata.

Gida ta mai da ta bayan sun zagaya gari duk saboda tayi lightening mood din Falmata
wadda duk abinda Farida ke yi ta na ankare haka kuma zuciyar ta cike take da
matukar godiya ga Allah bisa kyautar wannan rai mafi tsananin so, kulawa hadi da
tausayi gare ta, bata san me yasa ba se take jin wani matsananciyar kewar Faridan
tare da ita duk da gata a gefen ta suna tare.
Har bedroom Farida ta rakata, duk yadda take fada mata ita fa lafiyar ta lau bata
bar ta ba se da tayi wanka ta canja kaya gaban ta ta ci abinci sannan ta kwanta
kana hankalin Farida ya kwanta har ta iya ta mata sallama ta tafi nata gidan.

Kallon Hassana tayi dake zazzage karamar akwatin yan kunnen ta, wani babban saiti
ta dauka me hade da awarwaro, zobe, sarkar kafa da kuma zobe, jujjuya su tayi kana
ta dauka ta sa a handbag din ta dake gefen ta kana ta umarce ta ta maida ragowar,
cike da dimbin mamaki Hussaina ke kallon ta wanda duk Farida na hankalce amma se ta
nuna kamar bata gani ba ta mike tare da nufar bedroom din ta tana umartar Hussaina
da ta bi bayan yar uwar ta su kwanta se kuma gobe, haka dole ba dan taso ba
Hussaina ta yi dakin su ranta cike fa mamakin me maman ta zata yi da babbar sarkar
auren ta, sarkar da iya rayuwar ta zata iya fadar so nawa ta sa ta saboda son da
take mata.

Washegari tana tashi Falmata ta fara kira, jin ta garau yasa hankalin Farida
kwanciya sannan ta gabatar da ibada ta koma baccin da bata samu yi da wuri ba
saboda tunani.

★★★

A hankali na kashe datan waya ta fuska ta dauke da madaukakin farin ciki, a duk
lokacin d nake kallon mutanen nan ta cikin waya ji nake kamar na budi ido na ganni
cikin su, wata irin kaunar su nake ji kamar irin yan uwa na ne na kusa kusa, na san
ba komai ke sa min wannan feeling din ba se dan ya kasance matsalar mu iri daya ce
dasu, damuwar mu iri daya ce sedai wata tana fin wata samun kwanciyar hankali.

A duk sanda nake kallon su wani irin kwanciyar hankali nake samu da nutsuwa sanin
ba ni kadai Allah ya jarraba da wannan ƙaddarar ba muna da yawa haka kuma ina
karuwa da shawarwari da nasihar da ake yi a karshen meeting din.

A kalla shekara goma sha daya kenan da nayi joining kungiyar NATIONAL ASSOCIATION
OF INFERTILE WOMENS, yaya Salima ce ta ga sunan kungiyar a facebook lokacin bata
bunkasa haka ba se kuwa ta fada min tana yabon yadda suke gudanar da tsare tsaren
su, aikuwa ban yi sanya ba bayan tafiyar ta nayi searching sunan kungiyar na kuma
gan ta, ban gushe ba se da nayi wa daya daga cikin admins din magana privately ita
ce ta fada min dukkan procedure din da zan bi wajen yin register haka kuma nayi.

Takaici na daya da ya zama kungiyar tana garin Bakwarni ne ni kuma ina garin Darma
ne so ba ta yadda zan dinga attending meetings din su, lokacin da aka kawo shawarar
yin live vedio yayin meeting din ba karami dadi naji ba, tun daga lokacin kuma ban
taba missing ko daya daga cikin meetings din ba, haka kuma sanadiyar watsapp group
da kungiyar ke da mata da yawa sun kulla zumunta tsakanin su, nima akwai wata Zuhra
da muke so close da ita saboda yanayin yadda naji Kaddarar ta kamar tawa har kuwa
irin dangin miji da surukar da Allah ya bamu.

Numfashi na sauke tare da tashi zuwa kitchen bayan nayi offing data na, yau girki
na ne gashi kuma me gidan yayi tafiya se yau ze dawo shiyasa zan shiga kitchen da
wuri dan sama masa abin tarba.
Kusan wuni nayi cikin wajen ina aiki, dishes kala kala na hada wanda nasan miji na
na so kuma ze yi farin ciki in ya gani, seda na jera komai a dining tare da yin
decorating sannan na tafi daki dan yin wanka.

Staright gown na saka na wani dark purple material da ya sha wani azababben dinki,
ko ta ina jikin rigar stones ne sune shining suna daukan ido, yadda rigar ta kamani
kam yasa na tabbatar eh nayi kiba fa dan last sawar da nayi mata bata kama ni haka
ba.

Light purple head nayi anfani dashi na kafa a kai na ta yadda ya zauna sosai kai
kace a haka yake tun ainahi, turare kuwa kamar wadda nayi wanka dan bana iya kirga
adadin turaren da nayi wa kaina feshin, kawai duk wanda naji kanshin sa ya min dadi
ɗorawa nake kan na baya.

Falo na dawo na zauna ina dan girgiza kafa ta tare da taunan cingum a hankali, duk
wannan kwalliyan fa ba komai a face na ban da powder da kohl se mascara kawai, ba
dadewa kuwa naji shigowar motar da driver ya je dauko shi, cike da madaukakin farin
cikin da na kasa boyewa na tashi zuwa bakin kofa na tsaya dan na kasa tsayawa jiran
sa, kwana ukun da yayi baya gida se naji tamkar mun shekara uku ne bamu ga juna ba,
ni kai na wannan zumudin nawa akan Salees na bani mamaki, sedai na fi dangan ta
hakan da yadda muke zaune lafiya kalau cikin kwanciyar hankali tun bayan alkawarin
da yayi min wanda kusan two month kenan yanzu baya, daga Salees dai ban kuma ganin
wani abin bacin rai na azo a gani ba se wanda ba'a rasa ba na yau da gobe wanda
shima mostly akan ya'yan sa ne dan Allah ya jarraba Salees da mugun so da gudun
zuciyar ya'ya wanda nake jiye masa wataranan da idanun su shida mahaifiyar yaran ya
rufe basa hango ta.

Daga wajen Hajiya Iya da yan uwan sa ne kan nake Fuskantar Matsala dan sun matsa
min a kwanan nan, har gidan nan suke zuwa su ci min mutunci yadda suka so, ba yadda
zan yi haka nake shanye wa nake kuma hana kai na damuwa tun da dai muna zaune
lafiya dashi.

Maybe ku ga rashin zuciya ta akan nacewa zaman gidan Salees sedai ba naci bane,
sanin ciwon kai ne da kuma biyayyar iyaye domin a kullum Ummi na na fada min babu
suturar da ta kai ta aure wajen ya mace, gidan miji shine bigire mafi daraja a
wajen mace haka kuma shi mijin shine rai mafi girman biyayya, taya kuke tunanin zan
biye wa zafin zuciya da bacin rai wajen yin fatali da nasihar uwar da na tabbatar
tafi kowa so min kwanciyar hankali da zaman lafiya.....?.

Rundunar da Salees yayi min ce ta dawo dani hayyaci na, ban yi wata wata ba nima na
bude hannaye na na zagaye shi dasu cike da tsananin farin ciki da jin dadi, se kuma
nayi saurin yin baya jin sautin yaran na fadin

"Oyoyo Daddy, oyoyo".

Se lokacin na kula tare suke da maman su, yo Ina na kula, ganin miji na ya mantar
da ni kowa, daya bayan daya ya daga ya'yan suna dariya yana amsa musu sannun da
suke mishi, daga karshe ya karbi Amir a hannun Mariya muka taka cikin falon gaba
daya muka yi masauki kan kujerun wajen.

Sannu da zuwa muka shiga sake yi masa yana amsa wa cike da walwala haka kuma muka
dora da hira gaba daya wadda sa'i da lokaci Mariya ke kokarin zare ni cikin su
sedai yaki bayar da kofar hakan, ko akan yan uwan ta tayi magana se ya sako ni nima
kuma bana gwale shi zagawa nake na amsa shi, na kula hakan ba karamin batawa Mariya
yayi ba, wanda dama tun da taga yadda muka dinke da Salees yake gudun bacin rai na
kamar farkon shigowar ta cikin mu shikenan ta rasa walwala.

Yanzu ma tashi tayi ta tafi daki ta kwanta wai bata jin dadi kan ta na ciwo haka
kuma tana ganin jiri, sannu duk muka yi mata yaran suka bi bayan ta nikuma na wuce
dakin Salees ya biyo ni dan yin wanka da kuma samun hutu.

Duk yadda nake son kwalliya ta seda Salees ya bata min dan dagewa yayi tare zamu yi
wanka, haka ba yadda na iya na biye masa, muna fitowa na wuce dining na kwaso
abinci na kawo masa saboda yadda yake ta kiran yunwa yake ji, ashe fitowar da nayi
Mariya ta gan ni, zuciyar ta ta kuma cunkushewa da bacin rai na gani na da towel
kai na a jike, ita a tunanin ta wani abu ne na daban niku wa ba da gangan nayi ba
kaya na ne ya jika min wajen wanka gashi kuma ya ruda ni da kiran yunwa shiyasa ba
shiri na dauro towel na fito.

Cikin annashuwa nake kallon sa yana cin abinci a nutse, irin yadda nake farin cikin
zaman lafiyar mu wallahi ba zan iya kwatanta wa ba, ganin yadda na tsare shi da ido
yasa ya dago kai ya kalle ni tare da dage min gira daya

"Ya dai yan mata, irin wannan kallon haka kamar za'a cinye ni?".

Murmushi nayi me fadi da yasa haƙora na bayyana

"Kawai inq tunani ne".

"Tunanin me kunq bayan gani a gaban ki".

"Tunanin rayuwa zuma na, irin yadda muka samu kwanciyar hankali se nake jin ba
abinda ya kai hakan dadi".

Seda yayi dariya kafin ya kashe min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login