Showing 30001 words to 33000 words out of 41315 words

Chapter 11 - RASHIN HAIHUWA by Ouummey

Ouummey   

08 May 2026

70

Rayhanatu, Allah ya jikan mahaifiyar ku ya sa ta huta, ke
kuma Allah baki miji na gari da yaya masu albarka da zasu ji kan ki kamar yadda
kike jin kan mahaifin ki".

Da Ameen Ameen Haanah take ta amsa Yaaya har ta gama addu'ar ta ta shiga share
hawaye

"Dama na fada miki ki daina raina karfin talakar gani, kina ta wani fada min ba zan
iya ba b azan iya ba se gashi ba baki mamaki, kuma ina nan ina jiran alkawarin mu
dan ban manta ba kince zaki bar min murjanin ki in dai na sa ya yarda, bye dare
yayi se anjima".

Rayhanah ta karashe tana dariya jin muryar Yaaya itama tana darawa, aje wayar tayi
tare da kallon bed din Meerah se ta ga tuni ta yi bacci so se itama kawai ta kashe
wuta ta kwanta kan gadon ta wanda kowa da nashi a dakin.

Ta can wajen Hajiya Yaaya kuwa tana jin Haanah ta kashe waya itama ta aje taya tare
da daga hannu ta shiga godewa Allah idanun ta na zubar da hawayen farin ciki, a
cikin kaf rayuwar ta a yanzu dai bata da wani rai da take kauna kamar dan ta
mahaifin su Rayhanah, tsananin soyayyar da take masa ne ya jagorance ta wajen
aikata son zuciya ko kuskure zata kira abin wanda ya zama Mabudin duk kan wani
kunci, damuwa, tashin hankali da rashin walwalar dan nata haka kuma suka zama
makullin farin ciki da jin dadin sa, bata fahimci tayi kuskure ba seda lokaci ya
riga ya kure ta yadda bata da wani abin yi musamman ma da duk lokacin da ta nemi
yin wani hobbasa dan nata ke dakile t ta hanyar nuna mata ai komene tun da ya
kasance zabin ta to he can endure it even if it'll cost his whole life ne.

Bata yi kasa a gwiwa ba t shiga toilet ta dauro alwala tare da tada kabbara dan
mika godiya ga Allah tare da fatan ya sallada abin a ran dan nata ba se nan gaba ya
tubure yace be san zancen ba wanda a yanzu wannan opportunity din kadai take kallo
as hanyar gyara kuskuren ta dan haka zata yi iya kokarin ta wajen ganin ta bawa
mafi soyuwar dan ta farin ciki.

________

Rayuwa na ta tafiya abubuwa na faruwa masu dadi da akasin ta, a kalla yanzu kusan
wata hudu kenan da muke zaune lafiya a gidan mu se yan abinda ba'a rasa ba, duk da
zan iya cewa a kwanakin nan yanayin namu ze fi kyau da a kira shi kadaran kadahan
dan kuwa dai ba wai muna cikin farin ciki bane, haka kuma ba wai ana tsananin
tashin hankali ko rigima bane.

Fushi ne dai yake yi kan wani incident da ya faru shekaran jiya, abin ba wani me
zafi bane amma dake a wajen Salees ko me ya shafi ya'yan sa me zafi ne ba ya daukan
shi da wasa se kuwa ya daukaka abin har fiye da misali.

A shekaran jiyan ni ke da girki, hakan yasa na shiga kitchen kamar kowane lokaci na
shirya launch kasancewar Sunday kowa yana gida, before in fara girkin da se da nabi
ka'idar da ya tsara na cewa duk wadda ke da girki zata fara tuntubar yaran sa
abinda suke so, in bakin su ya zo daya su biyun shikenan se a yi wanda suke so din
gaba daya ko kuma ayi musu su biyu sannan me girki ya dafa abinda yayi niyya daga
baya, in kuwa bakin su be yi daya ba to kowa a dafa masu wanda yake so
individually, tun lokacin da yasa dokar na fada masa hakan wani karin aiki ne na
daban gare mu amma se yace shi haka ya tsara dan in yaran sa ba su ji dadi sun yi
walwala a gidan su ba a ina zasu yi?, Dole haka na yarda a wancan lokacin dan
maganar shekara hudu baya nake yi wannan.
Abinda ya faru shekaran jiya kuwa shine na tambayi Sahal abinda yake so kafin na
shiga kitchen se yaron yace me zan dafa, take nace masa jallof couscous se
watermelon juice, da farin ciki da komai Sahal yace min shi zai ci meaning base na
masa different girki ba, ita kuwa Ilham da na tambaye ta se tace rice and stew zata
ci, daga haka na shiga kitchen na hau ayyukana, nan da nan na hada abubuwan da zan
yi na jera kan dining sannan na wuce daki na yi wanka tare da canja kaya kana na
kwanta na huta ina jiran dawowar mijina daga masallaci

Karfe biyu ya shigo wanda tun da na hango shi ta window na fito falon yana shigowa
na masa sannu da zuwa tare da masa jagoranci zuwa dining din Mariya da yara suka
biyo bayan mu, seda kowa ya zauna sannan na shiga serving din su daya bayan daya
har n gama kafin na zubawa kaina na zauna dan fara ci sedai abin kamar almara se
kuwa Sahal ya ture plate din gaban sa a shagwabe yana tura baki nan da nan kuma
idanun sa ya tara hawaye, irin yadda baban ya rude yana tambayar sa lafiya se kawai
na zuba masa ido ina jiran jin me ze ce, zuciya ta kuwa har da ayyana min may be
shi da mahaifiyar sa ne

"Bana son abincin nan Daddy".

Da sauri na zaro ido jin abinda yace fuskar sa a kwabe kamar ba shi ne har da
tsalle dan nace jallof din couscous din zan yi ba

"Why didn't you tell your Aunty da zata yi girki?, She would have cooked your heart
desire for you".

Salees ya fada trying to rarrashi dan sa yaci abincin

"Daddy I've told her ni pounded yam nake so while Ilham tace rice and stew, but see
what she serverd me after serving Ilham her favorite".

Strictly Salees ya dago yana dubana with plain expression a fuskan sa

"Shi meyasa ba'a dafa masa abinda yake so ba after kuma yayi mentioning?".

Seda na hadiye wani yawu ganin yadda yake interrogating dina kamar wata yarinya
gaban ya'yan sa da matar sa sannan na iya na bada amsa

"I've asked him me zeci and shima se ya dawo min da tambayan me zan dafa so i
replies with jallof couscous, har da tsallen sa yana cewa yana so kafin na tambayi
Ilham ta fadi nata, and here's the same boy narrating different story dan ban San
yaushe yace pounded yam yake so ba".

Daga yadda yake kallo na na fahimci ba wai zance na ya gamsar dashi bane sedai be
yi hukunci directly yadda ya saba ba se ya dubi Ilham

"Wane amsa yayan ki ya bawa auntyn ku da tambaye shi kan abinci?".

Wlh a lokacin I was speechless, kenan salees na nufin be yarda da abinda na fada
ba?, Mu sa ma be yarda ba, mu sa a ransa kawai yana ganin karya nayi, in ma hakan
ne kenan baze iya rufa min asiri gaban yara ba se ya zubar min da kima, ko so daya
shin Salees be kamata yayi tunanin tarbiyyan ya'yan sa ba, gaba daya se naji komai
ya fita a raina, shikan sa Salees din naji ya zube min a ido na

"Daddy naji fa sanda yake cewa couscous ze ci fa, Allah be fada mata sakwara yake
so ba".

Irin yadda Mariya ke bin Ilham da wani mugun kallo ka dauka kisan kai yar nan tayi
bayan gaskiya ne kawai ta fada, shi kuwa Sahal yana jin me Ilham ta fada se kuwa ya
ture plate din a matukar fusace da har yasa abincin kai ta zube kana ya tashi yana
jan tsaki ya nufi barin dining din, zuba ido nayi kawai in ga hukuncin da salees ze
yi ko da dai ba wani sabon abu bane cewa zeyi yaro ne.

To ny utmost surprise se kuwa Salees ya mike a hanzarce har yana neman ture table
din ya maza ya riko hannun Sahal dake huci kamar ze daki wani, cikin lallashi da
kwantar da murya ya shiga lallaba shi kan yaje yaci abincin

"Wallahi ba zan ci ba Daddy, kawai saboda ba'a sona ita Ilham se aka dafa mata
abinda take so ni aka ki, shiyasa ma ni na tsane ta dan bata da kirki, mtsww".

Ya sake jan tsaki, burin salees dan sa yaci abinci kar ya zauna da yunwa so se duk
be yi overlooking wannan rashin kunyar da yayi a gaban sa ba, shi dai damuwar sa
yaci abinci, ganin yadda uban ya damu se ita ma Mariya ta shiga maganar playing her
own role Wanda ina gani na gane makirci ne

"Haba Sahal wannan wane irin wulkanci ne, ka tashi kaci abincin nan ko se ranka ya
ɓaci".

Kawai se yaro ya fashe da kuka tare da shigewa jikin baban sa yana maganganu

"Ka gani ko Daddy, itama Mommy bata sona, i won't eat this food ko zan mutu
wallahi, Daddy pls ka maida ni wajen Granny".

Aikuwa kamar wanda ake dannawa remote se salees ya ture Sahal daga jikin sa ya
shiga zazzaga masifa

"Wannan wane irin rashin mutunci ne da wulakanci, akan me zaku samin yaro a gaba da
tsangwama har yana gwammace wa rayuwar wani wajen kan gidan uban sa, ba tun yau ba
na sh fada muku ban hada son da nake ma ya'ya na da kowa ba dan a kan su wallahi
zan saba ma kowaye, har kema ki bar ganin kece kika haife shi dan babu ruwa na ke
mahaifiyar sa ce hukunta ki zan yi in kika nemi takura min yaro, gargadi na karshe
kowaccen ku ta kiyayi taba min yara, ku kiyayi bata musu dan a maimakon yaro ya bar
gida sedai ku kubar shi dan nan ne dolen sa gidan mahaifin sa akasin ku, ke
khadeejah tashi ki dafa masa sakwarar".

Tun da ya fara magana ban janye daga tagumin da nayi ina bin shi da kallo ba har
seda naji last statement din shi

"...ke Khadijah tashi ki dafa masa sakwarar"...

Na sake maimaita kalaman a ƙwaƙwalwa ta dan in tabbatar da eh abinda salees ya fada
kenan, bayan na tabbatar din se na dago na zuba masa ido wai dan in gane akan
fuskar sa wasa yake yi ko da gaske sedai daga look din fuskan shi babu wani alamu
dake nuna wasa, he look so serious ma'ana dai sakwarar yake so in yi wa dan gwal
din dan sa

"Is okay boy, kar in Kuma jin kace zaka je wani gidan, you've no home other than
this house which is your father's house, and stop crying, your pounded yam is yet
to be ready".

Ya fada cikin lallashin dan sa da ya dauka ya dora kan cinya, murmushi sosai Sahal
yayi yana kankame baban sa

"Thank you Daddy, I love you so much".

"Thanks so much boy, daddy loves his little ones so dearly".

Se kuma suka saki dariya Salees na mikawa Ilham hannu itama tayi joining din su
yamutsa fuskan da Sahal yayi yasa cike da kulawa ya shafa kan sa

"Yunwa ne ko, dan yi hakuri yanzu zaka ci abinda kake so".

Se kuma ya juyo inda nake

"Why are you still seating, pls je ki masa abinda yake so yunwa na damun sa".

Yanzu kam na tabbatar da gaske yake abinda ni kuma ba zan dauka ba kenan, haka
kawai saboda san ran sa da na dan sa ya hana mu cin abinci cikin kwanciyar hankali
dan ko spoon daya ban yi ba yaron nan ya tashi hankalin mu yanzu kuma ana batun in
tashi in masa pounded yam

"Am sorry bazan iya masa pounded yam ba yanzu its too late, gashi ko abinci ban ci
ba and ka san dadewan sakwara in nayi sauri in gama in an hour ga kuma abincin dare
na jirana".

"So kina nufin ya zauna d yunwa kenan".

Se da na nunfasa kana na dubi sashin da Sahal yake tsaye

"Ba haka nake nufi ba, yau kam yayi hakuri yaci couscous din gobe se in masa
sakwarar ko kuma in yi ta as dinner".

Ko kafin salees yayi magana Sahal y riga shi

"Allah ba zan ci couscous ba, akuya ne ni da zanci abu me kaman dusa, ni ba zan ci
ba".

"And I'll cook the pounded yam as dinner, now lemme cook indomie for you da sauri'.

"Ni i won't eat sakwara for dinner, ai kin san bana cin abinci me nauyi da dare
malamin mu yace mutum yanayin katon ciki".

Confusedly na tsaya ina kallon yaron jin kome nace se ya kushe, ko ta ina na fito
se yace ba haka ba, gyaran murya yayi yana kallona strictly yace

"Kawai kiyi masa tun da ya nace, ina ce muna da pounder".

"Ka fa san ya lalace tun kwanaki".

Na fada kaman zan fashe da kuka, se shima yayi shiru na dan lokaci kafin pleadingly
yace

"Pls pound it a turmi tun da bashi da yawa, i can't put an eye yaki cin abinci".

"Am sorry Salees, Mariya tayi masa ko kuwa kuje restaurant dan wallahi ba zan iya
yin sakwara yanzu ba".

And this my reply shine dalilin da yasa Salees ke ta min fuskan shanu yau kwana
biyu kenan, dan kamar yadda na fada ba zan yi ba ban yin ba, ban san yaya suka yi
ba, Mariyar ce tayi ko kuwa siya suka fita suka yi...................


*TWO PAGES TO GO💃💃💃, SAURA PAGES BIYU FREE CHAPTERS SU KARE, KINDLY MAKE YOUR
PAYMENT FOR IT'S PAID BOOK*

*INTERESTED BUYERS SHOULD CONTACT* 👇
*09013101854*
Ouummey ✍️
.




Ouummey 14 {5/14/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey




Ouummey 14
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________

_Free Chapter Fourteen_

Daga aiki na taso a matukar gajiye, jiki na gaba daya ciwo yake min dan kwana biyu
ina overworking kaina saboda gujewa tunanika ga kuma promotion din da ya matso
sosai, yanzu haka gobe za'a sanar da sunayen wanda suka yi nasarar samun wannan
cigaban, dukan mu ma'aikatan da muka san an yi nominating sunan mu cikin zulumi
muke dan kuwa bama fatan list ya fito babu sunan mu, promotion abun farin ciki da
so ne ga duk wani ma'aikaci, yanzu haka ji nake kamar in jawo gobe tayi tayi dan
kawai in samu peace of mind.

Mayafi na a hannu na shiga falon dan tun a kofar falo na cire shi saboda wani nauyi
dana ji ya min, ba abinda nake bukata a lokacin kamar wanka da bacci ko naji
daidai.

Turus nayi ganin Hajiya Iya, kannen Salees Rukayya, Sadiya da kuma auta Hannatu se
matar kanin sa Sani me suna Lubabatu, kanwar Mariya me suna Safiya, da yayar ta
Safara'u se maman su Hajiya Ramatu.
Ban san me yasa gaba na ya fadi ba ganin wannan taron sedai na daure na karasa
falon ina kaiwa tsugunne na shiga gaida Hajiya Iya da bata amsa min ba se kare min
kallo da ta shiga yi kafin ta karkata kai tana kankance ido

"Wato yawon tambadewar da kike kenan kika fake da aiki, yanzu mayafin ma a hannu
kike yawo dashi".

"A'a a kofar falon nan na cire saboda gajiya". Na bata amsa kai a sunkuye

"Uhmmm kowa dai yayi me kyau kan sa".

Jin tayi shiru bata kuka cewa komai ba yasa na juya ga mahaifiyar Mariya itama na
shiga gaida ta amma itama bata amsa min ba dan gara ma Hajiya Iya dan ita ko
kallona bata yi ba se kau da kai da tayi tana jan tsaki.

Lamarin ya daure min kai dan kuwa ba haka ta saba min ba, ko da ba haduwa muke yi
masu wani frequently ba amma in dai na gaishe ta tana amsa wa ko da dai ba wani da
tsayi bane dan iyaka ta da ita 'Lafiya' shine amsar gaisuwa ta d ita koyaushe.

Cikin sanyin gwiwa na dan mike sannan na gaida yayar ta Safara'u, ban tsaya jin
zata amsa ko kuwa ba na yiwa sauran magana wanda kannen Salees ne da matar kanin sa
se kuma kanwar Mariya

"Sannun ku da gida". Da sauri nayi gaba dan jiki na ba bani wannan taron bana
lafiya bane, ga kuma kallon banzan da na lura duk suna bina dashi, wankan da nake
dokin yi duk se naji ba zan iya ba, kawai so nake in San meke faruwa a gidan namu
inda na shiga addu'ar Allah yasa ba shida alaka dani dan to be sincere tuni na gama
gajiya da wannan tashe tashen hankulan, kwanciyar hankali nake bukata a yanzu.

Kamar wanda aka karanta min se kalaman da kunne na suka jiyo min lokacin da nake
bude kofar daki na suka dawo min cikin ƙwaƙwalwa

"Hmmm, lallai mugu bashi da kama, kalli matar nan kamar wata saliha alhalin
kungurmar munafuka kuma azzaluma ce, yanzu ban da mun san hali ai da se mu karya ta
abinda muka ji da kunnen mu".

Rukayya kanwar Salees me bi masa ta fada in da Safara'u ta cafe

"Ke ni fa a wannan zamanin bana tantama kan duk abinda aka ce mutum yayi dan
wallahi wani mutumin in zaki shekara goma dashi ba zaki taba sanin wasu bakin halin
nasa ba se Allah ya ciyar dake, to balle kuma wannan matar da tun a baya bakin
halin ta ya fito fil, kina zaton zata bar Mariya ne cikin kwanciyar hankali bayan
Allah ya bata haihuwar da ita ta rasa?".

"To wa ya hana ta haihun ita, aikin banza, Allah ne fa ya san nufin jaki da be
bashi kaho ba, wannan da ta haihu ba musan me zata yi ba, a haka ma muna fama da
ita, ai ni na godewa Allah da be Kaddara min hada jini da wannan bakar jarabar ba".

Hajiya Iya ta fada tana wani tsuke baki, sauke numfashi nayi bayan na gama tunani
na, lallai akwai wani abu, tabbas akwai sharrin da aka kulla min da har yaja min
wannan bakaken maganganun sedai ina fata Allah yasa komai ya zo min da sauki ya
kuma bani juriya da hakurin dauka.

Da kyar na iya nayi wanka na canja kaya, yunwar da na shigo da ita kuwa tuni ta
fece haka ma baccin da nake kuzun nayi shima duk ya yi nasa wajen, jira nake kawai
in ji an doko min kira an fara tuhuma ta, dalilin tuhumar ne dai ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login