Showing 24001 words to 27000 words out of 41315 words
ido cikin tsokana
"Ke dai fadi gaskiya, kina tunanin rayuwa babu ni ne, uhm fada min".
Nima dariyar nayi
"To meze raba mu balle har in yi tunanin rayuwa ba kai?".
"In ba rabuwa fa akwai mutuwa Khadijah, kin san wannan?".
"Na sani sosai Salees sedai ina fatan Allah ya dauke ni kafin kai dan i can't
imagine a life without you, beside haka kana da wasu rayukan da kai ne jigon su ba
kamar ni ba da ban aje komai ba, rabuwa kuma, hmm bana zaton akwai wannan kaddarar
a tsakanin mu".
Aje spoon din hannun sa yayi ya zuba min ido har na gama magana kafin cikin serious
tone yace
"Rabuwa tsakanin mu itace zata zama mafi munin kaddara da bana fatan kasancewar ta
a gaske, dan Allah kar ki kuma kawo wannan maganar a ran ki ko da kuwa a mafarki
ne".
Kallon sa kawai nake zuciya ta na bugawa saboda tuno wani incident da ya faru
shekaru tara da suka wuce, wani irin faduwa gaba na yayi kamar a lokacin abin ya
faru, irin yadda na runtse ido tare da dafe kirji yasa Salees saurin riko hannu na
a rikice
"Lafiya kuwa Deejah, me ya same ki?".
Seda nayi dan sakwanni kafin na bude ido na kalli Salees murya ta na rawa
"Shekaru tara da suka wuce, salees anya......".
Da sauri ya rufe min baki yana girgiza kai kamar shima ya rude
"Kar ki karasa, a wancan lokacin na sharrin zuciya ne da kuma zuga, bayin kai na
bane ba Deejah, dan Allah ki daina tuna min da mafi girman kuskure na".
A hankali na cire hannun sa daga baki na ina gyada masa kai alamar toh.
Gaba dayan mu jikin mu yayi sanyi amma muna kokarin ganin mun danne komai mun nuna
ya wuce sedai har lokacin bugun zuciya ta ya kasa sasssaitawa balle ya daidaita.
★★★
*BURAIMA QUARTERS, BAKWARNI STATE*
Plate din da ta gama cin abinci dashi ta dauko zata kai kitchen, tsaya wa tayi
ganin yadda yake sanda zai fice kamar wani barawo, takawa ta shiga yi har ta kai
bayan sa daf sannan ta tsaya kana ta ambaci sunan sa cike da mamaki
"Dada".
A firgice ya juyo yana kallon ta ido waje se kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da sa
hannu a bakin sa ya mata alamar tayi shiru, seda ya kalli babban falon ya ga babu
kowa sannan yaja hannun ta da sauri suka shige kitchen din ya bude kofar suka fita
compound ta cikin kitchen din.
Ajiyar zuciya ya sauke kana ya sake mata kyakkyawan murmushin da bacin ya'yan sa da
iyayen sa ba wanda yake samun alfarmar ganin sa balle ace shi a ka yi wa.
"Dada lafiya kuwa?".
"Where's pretty".
Ya fada da dakakkiyar muryar sa yet kuma me taushi
"Tana shirya wa ne Dada, wani abu ya faru ne?".
"Wa ita nake wannan sandan, bana so ta ganni dan kin san rigimar kanwar ki, da kyar
tayi bacci da dare wai ita a kai ta Maamah".
Ya karasa sunan in a bitter tone haka itama matashiyar take yanayin fuskar ta ya
canja daga mamaki zuwa alhini da damuwa......................
Ouummey ✍️
.
Ouummey 11 { 5/10/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
____________________________________________________________________________
_Free Chapter Eleven_
"Kaje Dada zan kula da ita, insha Allah ba zata yi rigima ba".
Gyada mata kai yayi tare da pecking goshin ta ya juya ze cigaba da tafiya
"Dada".
Ta tsaida shi, da sauri ta karasa gare shi tare da shan gaban sa ta shiga bin shi
da kallo
"Baka yi bacci ba jiya ko?".
Kau da kan sa yayi daga kan ta yana hadiye wani daci a ran sa jin yadda tayi magana
da wani sassanyan sauti me cike da tausayawa
"Dan Allah kar ka fita Dada, kaje ka sami bacci, i promise to look after Meerah and
Meemah".
Wani murmushin ya sake yi mata kana ya riko hannayen ta yana mata magana a hankali
ransa cike da so da kaunar wannan yarinyar tasa me matukar nutsuwa, wayo, hankali
da kuma fahimta
"Bana tare da bacci Haanah, idanu na ne na tashi suna ciwo, take a look here".
Ya fada yana zira hannu cikin aljihu ya fiddo da maganin ciwon ido, a hankali ta
sauke ajiyar zuciya kana ta sake masa kyakkyawan murmushin da ya haska matashiyar
fuskar ta me cike da kuruciya
"Oh Dada, har hankali na ya tashi fa na zata bacci ne baka samu ba, shikenan a dawo
lafiya Dada na".
"Allah yasa Haanahn Dada, pls do take care of your little ones, I won't take long
insha Allah ".
Gyada masa kai tayi har lokacin murmushin ta na nan, da sauri yayi gaba jin wayar
sa na daukan ringing, da kallo ta bi bayan baban nata me cike da tsananin tausayi
hadi da kauna me yawa kafin ta juya zuwa cikin falo ta same hanyar da suka fito.
A falo ta tadda Meemah da Meerah both decently dressed cikin islamiyya uniform din
su, dage musu gira tayi while tana sake musu tattausan murmushi kana ta bude
hannayen ta, da gudu suka karaso suka bata a huge sisterly hug ta sa hannu ta sake
kai su jikin ta sosai, kusan minti biyu kafin ta sake su tana bin su da kallo inda
tayi branching kan fuskar Meemah dake yatsuna fuska tana wani tura baki.
Tun kafin ta kai ga tambayar ta meye Meemah ta fara magana cikin zazzakar muryar ta
me cike da tsiwa
"Kai gaskiya kadai ya Meerah baki iya hug ba, jibi yanda kika matse ni kamar zaki
da kayan ciki na su fito ta baki na, da kyar fa nake numfashi, tabdi".
Meerah da abinda Meemah ta fada ya kular tayi kan ta zata kai mata duka hakan yasa
Haanah yin intervening da sauri
"Me ye haka kuke yi?".
"Jibi yadda take min rashin kunya Adda bayan ke da Dada kun hana ta".
Wani kallo Haanah tayi wa Meemah da yasa ba shiri ta kalli Meerah
"Koyi hakuri Adda Meerah ba zan sake ba amma kema ki daina matse ni gaskiya".
Meerah zata sake magana Haanah ta daga mata hannu kana ta tashi tana pointing musu
hanya
"Oya let's have our breakfast, we're almost late".
Ba musu suka yi gaba ta bi bayan su har kan dining din su dake shaƙe da kayan kari
wanda a kalla mutum goma zasu ci a wadace, babban plate Haanah ta dauka ta zuba
musu gaba daya chips din wajen ta aje musu gaban su ita da Meerah sannan ta haɗawa
kowa tea a cup, ita kuwa Meemah farfesun hanta ta sa mata a karamin bowl ta bata
bread da Egg.
A nutse suka karya cikin nutsuwa babu me yin magana har suka gama kowa ya zari
tissue ya goge bakin sa da hannu kana suka wanke a wash hand basin dake dining area
din.
"Ku dauko jakan ku muje na san Lawan na can na jira".
Da toh suka amsa mata suka yi yadda tace, a tare suka fita daga falon tayi locking
din sa suka wuce parking space inda suka tadda Lawan na jiran su kamar yadda tayi
zato, Meerah da Haanah suka shiga baya Meerah kuma gaba, har ya tada motar zasu
fita ta wani zaro ido tana fadin
"Lalalala, tabdi malam Lawan tsaya tsaya".
Tsayar da motar yayi yana kallon ta haka ma su Adda Haanah jira suke suji tace tayi
mantuwa se suka ji tana fadi
"Ban yi wa Dada sallama ba Adda, bari in maza in je".
Da sauri Haanah ta dakatar da ita da fadin
"Ba kya ganin mun yi late ne, ki bari mu dawo dan Dadan ma baya nan, Malam Lawan
muje ko".
Turo baki tayi gaba ta gyara zaman ta dan dole dan yadda taga Addan ta hade rai ta
san ba ta isa ta kawo wargi ba.
Har bakin kofar class ya kai su Meemah da Meerah inda Haanah ta sauka a ajin su
Meemah kasancewar ta malamar su shi kuma ya juya ya tafi.
Karfe biyu suka tashi daga makarantar, Meerah tazo ajin su Meemah dan a nan suke
haduwa su tafi bakin makarantar inda Lawan ke tsayawa, sedai ga mamakin su yau
Lawan yayi late xan kuwa be zo daukan su ba.
Zama suka yi suna yan hirar su tare da kallon yaran dake fitowa daga makarantar har
suka ji horn din motar da yasa su juya wa dukan su a tare dan ko a mafar ki suna
iya banbance sound din wannan horn din daga na kowace mota.
"Wallahi Dada ne, Dada na ne yeeeeehhh".
Meemah ta fada tana kokarin rugawa da gudu zuwa wajen motar dake parke gaban su
kadan
"Kar ki fara yi mana gudu a nan, ki jira muje tare me rawar kan kawai".
Meerah ta fada tana hararar ta, tsayawar ta yi bisa dole sedai bakin nan a tale
kamar wadda zata yaga shi, jira take kawai su shiga mota ta haɗa Adda Meerah d Dada
dan ta gaji da yadda take mata fada da abubuwa.
Seat din gaba Haanah ta budewa Meerah ita kuma da Meemah suka shiga baya
"How's the school babies".
"Alhamdillah Dada". Suka fada a tare har Haanah da ta fara girma dan in a gaban
Dadan ta ne jin ta take yi kamar wata yar baby.
"Yauwa Dada, malamin mu yau ya fada mana ba kyau karya shiyasa zan fada maka abinda
Adda Meerah tayi dazu".
Da sauri Meerah ta zaro ido jin iya shegen da Meemah zata mata dan kawai ta hana ta
gudu,
"Kai Meemah kiji tsoron Allah ni kuwa me nayi da zaki fada in ba kalin sharri ba".
Dariya Meemah tayi ganin yadda Addan tata ta firgita
"Ki bari kawai na fadawa Dada da Adda Haanah kin sha ruwan sanyi immediately after
you wake up".
Rau rau da ido Meerah tayi tana kallon Haanah wadda itama ke kallon ta jin abinda
tayi bayan likita ya hana ta kuma ta sani
"Why, meyasa kike yin haka Ameerah?".
Sharrr hawaye suka zubo mata dan suna bala'in tsoron baban su dan duk yadda yake
wasa dasu yake son su baya hana ya hukunta mutum in yayi ba daidai ba
"Am sorry Dada Allah ba zan kuma ba".
Shiru yayi mata hakan yasa ta kara volume din kukan ta tana bashi hakuri
"Will you pls keep shut, ko baki ga tuki yake ba?".
Kamar an yi ruwa an dauke haka ta hadiye kukan ta bayan Haanah ta mata magana, ba
wanda ya kuma magana se Meemah dake wasan ta ita kadai har suka kai gida, kowa ya
dauki bag din sa suka yi falo.
A tsakiyar falon ya tsaya ya zuba wa Meerah ido cikin hukuntata dasu wanda duk yayi
musu irin haka suke gwammace wa yayi fada ko ma duka akan wannan silent punishment
din.
"Ciki na ne naji yana zafi Dada shine nasha amma ba zan kuma ba, am so sorry pls
Dada".
Kallon Haanah yayi se ta langwabar masa da kai alamun itama tana bashi hakuri,
dauke kai yayi ya kalli me kawo gulmar Hajiya Meemah, wai dan gulma itama yarinyar
nan se ta karyar da kai gefe wai itama hakurin take bashi, wannan dabi'a tasu na
matukar burge shi tare da faranta masa rai.
Gashi dai basu yi laifi ba Ameerah ce kadai tayi, amma yanzu da zai nemi hukuntata
se duk hankalin su ya tashi ba kuma zasu koma daidai ba har se ya hakura kamar dai
yanzu.
Girgiza kai kawai yayi ya wuce bedroom din sa leaving them behind Wanda Haanah ta
fahimci ya hakura ne dan haka ta ce
"Se ki tashi ai babar marasa jin magana,ban da wulakanci so nawa kike so in nanata
miki ki daina shan ruwan sanyi da safe after kin fi kowa samun you're not fine Amma
shine bakya ji, to go ahead and kill yourself se mu zauna mu uku, kinga se mu dinga
lissafin ke da Maamah bakwa tare da mu".
Yadda muryar ta ta shiga rawa bayan ta kai karshen zancen ze tabbatar maka tana
cike da kewa da alhinin wadda ta kira ga Maamah a ran ta, fashewa da kuka Meemah
tayi tana kiran Maamah, ita wallahi Maamahn ta yasa hankalin su tashi.
Shaf Haanah ta manta da cewa tan wajen ya sa ta ambaci sunan Maamahn ashe rabon ta
jawo musu jidali ne .
Fitowar Dada da sauri daga dakin yazo ya dauki Meemah tare da ɗorawa a kafada ya
shiga aikin lallashin ta, wannan yanayin ya karyawa Haanah zuciya ta shiga hawaye
da shessheka abinda yasa itama Meerah fashewa da kuka.
Gaba daya se ya rude ya rasa ya ze yi, waye ze lallasa ma ya rasa se kawai ya juya
ya zuba musu idanun sa da suka kada sukai jajir, hada idon da suka yi da Haanah da
yadda taga jan da idon sa yayi yasa ta san lallai sun tayar masa da hankali, hakan
yasa tayi saurin dakatar da kukan ta ta shiga lallashin Meerah har tayi shiru,
jakunkunan su ta dauka ta kai bedroom ta dawo taja hannun Meerahn zuwa bathroom din
da ta haɗa mata ruwan wanka, se da ta shiga wankan ita kuma ta fito mata da kayan
sawa sannan ta fita.
Kan kujera ta tadda shi zaune ya dafe kan sa ga Meemah a kan shi tana birgima da
kuka, da gudu ta karasa tana kokarin daukar ta wanda se lokacin ya bude ido ya
girgiza mata kai a hankali sannan ya dago Meemah daga jikin sa
"Shhhhhh, is okay pretty".
A hankali ta fara reducing volume din kukan ta har ta daina gaba daya se ajiyar
zuciya da take yi a kai a kai
"What's the problem pretty nah?".
"Dada Maamah".
Ta fada a shagwabe da muryan kuka, seda ya hade abin da ya tsaya masa a makoshi
sannan ya iya daurewa ya kakaro wani busasshen murmushi yayi mata yana riko yan
mitsi mitsin fingers din ta
"Maamah tayi tafiya na fada Miki sweery".
"Yaushe zata dawo?, Ni dai akai ni wajen ta".
Ta fada tana neman fashewa da wani kukan sedai be bari ba yayi saurin tallafo habar
ta
"Look ta kusa dawowa, taje can aljanna ne fa, kin san aljanna akwai dad'i ko
shiyasa Maamah bata dawo ba amma zata dawo".
"Da gaske tana paradise Dada?".
"Eh mana princess".
"Yanzu tana can tana cin fruits din aljanna? Su Apple, banana, orange, pineapple,
mango, strawberry and...se me ma Adda Haanah?".
Ta fada directing the Question to Haanah, murmushi ta mata trying to karasa calming
nata tare da dauke mata hankali
"Eh mana dear, har dasu pawpaw fa, ga kuma su plantain and more".
"Allah yasa zamu shiga aljanna irin na Maamah mu ma muje mu yi ta cin dadin mu".
"Ameen pretty jeki Adda tayi Miki wanka a canja uniform ko".
Tura baki tayi tare da girgiza kai
"No Dada, yau kai zaka yi min, ka manta ka ce min zaka min wankan so biyar in naje
school ban yi kuka ba, and kuma ban yin ba ko".
Gyada mata kai yayi yana yake ya mike da ita dauke a jikin sa ya wuce dakin su
Haanah na bin su a baya, ita ta haɗa ruwan wankan shi kuma yayi mata, ana yi tana
wasan ta tare da bashi labarai kai baka ce yar shekara uku da rabi bace, seda ya
shirya ta cikin jeans da riga sannan ya nufi fita se kuwa ta daga murya tana magana
irin wai ita tayi masa yadda ze ji ne tun da yayi nisa
"Kar kace wa Maamah ta dawo da Dada, ka bar ta a paradise din ta tayi ta cin dadin
ta amma ka fada mata kar ta cinye duka ta rage min".
Wannan karon kam ba yake bane sahihiyar dariya yayi jin wani shirme amma se shima
ya dan daga muryar sa kadan ya amsa mata da
"Okay princess bari in je in fada mata".
Da "toh Dada" ta amsa masa tana kwanciya kan dan Karamin gadon ta me kyau shi kuma
ya fita,
"Je ki sa a shirya mana table Meerah, lemme take a shower nima".
"Okay Adda ".
Ameerah ta fada itama tana ficewa saura Haanah da Meemah
"Kar ki je ko ina ko da kuwa falo ne har se na fito, and kar ki fara yi min barna
if not".
Ta fada tana mata kallon gargadi sosai, cike fa biyayya ta gyada kan ta tana sa
bmhannu cikin baki, shigewa bayin haanahytayi daure da towel yana saurin tayi tai
wanka kafin Meemah ta bata matsala.
_____
Yana shiga dakin sa ya fada ka bed hannun sa biyu dafe da kan sa da yake jin kamar
ze rabe masa biyu, wani irin ciwo kan ke masa na tsananin damuwa da rashin bacci ga
kuma yawan tunani dake addabar sa.
Da kyar ya iya mika hannu ya bude drower ya debo maganin da be tsaya duba na mene
bane ya afa a baki batare da ruwa ko wani abu ba ya shiga taunewa, dacin da ke
ratsa bakin sa be kai wanda zuciyar sa ke masa ba, jiki ba kwari yasa hannun ya
sake dafe kan yana rurruntse idanu
"Me yasa Maryam, me ye laifi na, me muka yi miki da zafi da kika zabi yin nesa da
mu bayan kin san muna tsananin bukatar ki?, Me yasa kika zabi barin yayan ki da
mijin ki cikin wani hali?".
Dan juyi yayi kadan a gadon se kuma ya cigaba
"Na sani laifi na ne ko, shikenan am sorry Maryam, am really sorry but pls do
believe that I so much love you Maryam, Ina matukar son ki mairo na, dan Allah ki
dawo gare mu ko dan ya'yan mu, kin ga kullum se pretty tayi kukan ki, pls Maryam ".
Kamar kuma wanda ya farka daga bacci se ya bude idanun sa wal wanda suka yi jajir
kamar wanda jini ya kwanta
"Astagfirillah, forgive me ya Allah, astagfirillah ".
Se kuma ya sake dafe kai
"Ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagees".......
Ouummey ✍️
.
Ouummey 12 {5/11/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 12
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA,