Showing 12001 words to 15000 words out of 41315 words

Chapter 5 - RASHIN HAIHUWA by Ouummey

Ouummey   

08 May 2026

63

sa".

"Da toh". Husaina ta amsa kana suka shiga kitchen yin girki.

D daddare kuwa se ga dan ta Safwan kamar yazo kamar yadda Hussaina ta fada masa
tana kiran sa, bayan sun gama gaisawa da tambayar yaran sa da matar sa ta kawo masa
batun da yasa ta kira shi.

Albarka tayi ta sa masa bayan ya amsa wa kudirin ta kana ta sallame shi ya tafi
bayan ta bashi tsarabar yaran tace ya kai musu..............

Ouummey ✍️
.




Ouummey 06 {5/3/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey




Ouummey 06
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.


____________________________________________________________________________



_Free Chapter Six _


Tun da akayi wannan case din na janye jiki na daga mutan gidan gaba daya, ba shi
Salees din ba ba ya'yan sa ba balle matar sa d dama kissar ta ke kawo ta gare ni,
gaba daya na dauke musu wuta, tsakani na dashi gaisuwa, daga ita kuma se maganar d
ta zama dole.

Abin dariya wai kuma se hakan ya dame shi, ko da yake amfanin kan sa ne yasa ya
damu dan har kwana na daina zuwa dakin sa, wannan kuma ba karar da ya kai ni bace,
kudiri na ne hakan tun ranar da yace Amir baze bar daki ba saboda gidan uban sa ne
yasa na sawa raina to kuwa ba zan kuma bin shi dakin sa ba, in ya matsu da son
kasamcewa dani se ya biyo ni daki na.

Sati biyu muna cikin wannan halin dashi, wata magana kwakkwara bata hada mu in ba
wajen aiki ba dan a yadda nake hade rai duk na gan shi yasa yake shakkar yi min
magana.

Yau mun tashi daga aiki d wuri saboda matar ogan mu da ta haihu yasa cikin farin
ciki ya sallame mu tun kan lokaci yayi, tun da na fito daga ma'aikatar nake tunanin
zuwa gida wajen Ummi na sai dai ba ze yiwu in je din ba dan ban tambaye shi ba,
haka nake kallon hanyar har na wuce.
Ina yin parking na tattara kaya na na fito tare da rufe motar na shiga falon da
sallama, Mariya da kanwar ta na zaune suna hira duk suka juyo gare ni, daga
sallamar nan ban kara komai ba na wucewa ta kofa ta ina kokarin ciro mulki dan bude
dakin se dai ganin kofar a bude yasa na tsaya cike da mamaki.

Daga ni se Salees ne masu key din kofar, to waye ya bude min dakin?.

Da dan sauri na matsa jikin window tare da daga labulen ina surveying compound din,
se kuwa naga motar shi ajiye alamun ya dawo nice ban kula ba da na shigo.

A hankali na saki labulen na karasa dakin na shiga da sallama ina tunanin me ke
dalilin da ze kawo Salees daki na balle ma ya bude min kofa bayan bana nan, kan bed
na same shi kwance yana pressing phone ya bararraje kamar gadon sa, na dan yi turus
ina kallon sa wanda hakan yasa ya dago tare da aje wayar shima ya shiga bina da
ido.
Ganin kallon nasa ba na kare bane yasa na wuce shi cikin son basar dashi na aje
kayan hannu na na rage mayafin jiki na kana na nemi cushion na zauna Ina bude
fridge din gefe na na ciro bottle water me sanyi na bude da bismilla na sha, ina
sauke ajiyar zuciya na aje ragowar na sake kishingida ina lumshe ido cike da
gajiya, seda na dan huta kafin na tashi na shige toilet na maida kofa na rufe
sannan an shiga rage kayan jiki na dan yin wanka.

★★SALEES★★

Tun da ta shigo yake bin ta da kallo cikin son ganin gudun ruwan ta, ya gaji da
wannan zaman da ta tsiro tsakanin su, ya gaji da shariyar da take masa, ya gaji da
ko in kula din da tayi dashi, ya gaji da komai ma dan yana bukatar kasancewa da
ita, yana bukatar jin dumin jikin ya sai dai ya lura in ya biye mata to fa haka
zasu cigaba da kasancewa har zuwa lokacin da shi kan sa be hango zuwan sa ba.

Baki bude ya ke kallon ta ganin yadda ta shigewar ta toilet ta rufe kamar bata lura
da zaman sa cikin dakin ba alhalin so biyu suna haɗa ido dashi.

'me Khadijah ke nufi dani' ya ayyana cikin ransa, koma me take nufi yana nan yana
jiran ta har ta gama ko me take cikin toilet din dan ba ze dau raini da wulakanci
ba, yana zaune ta wuce shi wato ga shara banza mata amfani ko, shiyasa Hajiya Iya
ke cewa ta raina shi, a da be yadda ba amma a yanzu tabbas yana hango burbushin
hakan.

Ya dade zaune kafin ta fito daure da guntun towel din ta da be gama sauka kan
kosassun cinyoyin ta ba, jikin ta dauke da abin ruwa shaidar wanka tayi, haka kuma
kan ta da ta wanke shima kulle cikin wani karamin pink towel.

★★★

Tun da na fito nake jin tasirin idanun sa a jikina alamun kallo na yake sedai ban
nuna na fahimta ba na wuce na zauna kan stool din mirror, a hankali na warware
towel din kaina hakan yasa jikakken gashi na ya kwanta kan kafada ta, hand dryer na
jona na shiga busar da kan a nutse har na gama kana na shiga shafa mayukan da nake
amfani dasu wa gashin, take ya shiga kyalli haka kuma ya sake kwanciya sosai a
kafaduna bayan na taje, ribbon me dan tudu kadan na sa na kama shi sannan na kitse
jelar na sake ta ta na reto a keyana.

Mai na dauko tare da murzawa a hannu na na shiga bin cinyoyi na dashi bayan na
sassauta zaman towel di na, a nutse nake komai kai baka ce na san da zaman wani dan
Adam a dakin ba, wani na kuma murzawa na shiga bin kafaduna, kirji zuwa ciki na a
tausashe cikin raina ina yabawa taushi da santsin fata ta ko da dai ba banza ba dan
kudin da nake kashe wa iya mayuka da shower gel ba kadan bane.
Dagowar da zan yi ba kalli mirror se kawai na ci karo da jajayen idanun Salees a
kai na, da mamaki nake kallon yadda ya tsaya bayana daf yana sauke ajiyar zuciya da
nishi kamar wanda yayi tsere, dauke kai nayi na fara kokarin mikewa sai dai yadda
ya sake matse min waje tare da zuba hannayen sa kan kafada na yasa dole na cigaba
da zama.

Lotion dina ya zuba cikin hannun sa da ya dauke kan jikina bayan ya matse min waje
ta yadda ba zan motsa ba, bin shi na dinga yi da kallo cikin mamakin me ze yi da
man da yake murzawa a tafin hannun sa, na dan fito da ido waje jin ya sauke
hannuwan kan bayana ya shiga shafa min cikin wani irin salo da yanayi me tafiyar da
mutuwa, ban san sanda na lumshe ido ba sedai ban fasa dakatar dashi ba ta hanyar
rike hannun sa kana na bude ido na zube su kan fuskar sa dashi ma ni yake kallo

"Na shafa ai". Na fada ina kubcewa da sauri na nufi wardrobe di na cikin kokarin
dauko kaya, hannuwan sa yasa a kugu na ya zagaye ni dashi tare da hade ni da jikin
sa yana magana kasa kasa

"Aje dauko kayan nan kizo muyi magana".

"Magana? Ai yanzu ma ita muke yi".

"Maganar na da matukar muhimmancin da nake bukatar nutsuwar ki, muje ki zauna ki
saurare ni".

"Ba zan iya zama tsirara ba, ka jira na saka kaya tukuna".

Da alama ya fuskanci yadda nake kokarin hade rai shiyasa ya sake ni ya dan koma
gefe, doguwar riga na dauko ta wani yadi me kyau da sulbi na zura, ba kadan ba
rigar tayi min kyau haka naji dadin saukewa cikin ta dan bubu ce, hulan da ya hau
da rigar na dauko tare da sawa a kaina na kara sa gaban mirror ina sake daidaita
mata zama kana na shafa turaren kaya haka na kara da na feshi bayan wanda na shafa
wa jikina tun farko.

Waya ta na dauka tare da zama kan cushion na shiga kokarin kunna data sedai ban kai
ga haka ba na ji an zare ta, nasan ba kowa bane se Salees, ya zauna kasan ƙafafuwa
na tare da zuba hannayen sa kan cinyoyi na

"Dago ki kalle ni Khadijah".

Ban ki ba na dago kaina a hankali tare da sauke duba na kan fuskar sa, ya langwabe
kai tare da karyar dashi gefe kamar wani Maraya, idanun sa sun yi jajir, in ba gizo
idanu na ke min ba se n aga har ya dan fada dan kwarmin idanun sa sun nuna rama,
take naji zuciya ta ta karye, tausayi hade da son miji na suka rufe ni

"Khadijah bani da Lafiya".

Ya fada yana kama hannu na ya kai wuyan sa, tabbas bashi da lafiya dan zazzaɓi ne
ma a jikin sa

"Ban san me nayi miki ba kike fushi dani Deejah bayan kin dade da sanin fushin ki
ba karamin illa yake yiwa zuciya ta da jiki na ba, kin saka zuciya ta cikin rudu da
halin ko in kulan da kike min".

Yayi shiru tare da kallo na, nima kallon sa kawai nake ba ni da alamun yin magana
sedai zantukan sa na shiga ta yadda ya kamata dan wani irin sanyi na ji jiki na
yayi wanda na san hakan Salees ya karanta yasa ya matso sosai tare da shige min

"A da ba zan iya kwatanta girman soyayya da kaunar da Khadijah ke yi wa Salees ba,
soyayyar da tasa take hakuri da duk wanda ke tare dashi dan kawai tayi rayuwa
dashi, soyayyar da ta kasa boyuwa har a gaban iyaye da jama'ar da ke kewaye dasu,
haka shima Salees yake mutuwar san Khadijah, yake yin komai dan farin cikin ta har
wasu ke ganin an mallake shi ne bayan tsantsan kauna ce kawai ke aiki, shin Salees
yayi wa khadeejah laifi ne da yasa ta daina ko take kokarin daina son sa alhalin
shi a yanzu ne yake kan ganiyar so da kaunar ta?".

Wani irin laushi da rauni zuciya ta tayi a lokacin, kai wallahi maza sun iya dadin
baki ta yadda zaki yi abu se bayan kin aikata ki dinga tunanin taya ya kika yi, me
ya kai ki, wanda ko gobe se kin kuma yi in baki jajirce kin kai zuciyar ki nesa ba.

Idanunsa da suka cika da hawaye na dago na kalli Salees, soyayyar sa ta cika min
rai, na far kokarin bude baki na dan shaida masa ban dena son sa ba, ban bar kaunar
sa ba haka kuma zan cigaba da hakuri dan kawai in yi rayuwa dashi, sedai kamar
wadda aka dannawa pause haka na tsaya ina kallon sa na kasa fada, ba komai yasa
hakan ba face abubuwan da ya dinga aika ta min a kwanakin baya, irin bakin ciki da
bacin ran da ya kun sa min, wai har a gabana yake fadawa kishiya y fara gajiya da
hali na, meaning ya fara gajiya dani, wanda a da be san da halin nawa bane ya so ni
da a yanzu ze ce wai hali na, kawai nice ya gaji dani yake neman wulkantawa shine
kuma yanzu ze dauko wasu shanyayyun kadafun sa ya zo yana karanta min karya.

Eh karya mana a yanzu, na san a da Salees ya so ni Kamar yadda ya fada, nima kuma
nayi haukan son sa, sedai ko rantsewa nayi ba zan kaffara ba a yanzu baya min ko da
rabin rabin son da yayi min a da, akwai dai abinda yake bukata daga gare ni, akwai
abinda yake so nayi masa ko yake nema a waje na shine bari ya yaudare ni da kalmar
soyayya.

Murmushi na saki bayan na gama kallon idon sa, se yanzu na gane me ya kawo shi daki
na, se yanzu na fahimci soyayyar d yake fada yana min, ni dama nayi mamakin wai
Salees ke fada min kalaman soyayya haka abinda in ban mance ba rabon da in ji irin
wannan kalaman a bakin shi tun bayan haihuwar Sahal shekara goma sha biyu kenan
yanzu.

Be yi tsammani ba be yi tunani be se ji yayi nq ture shi daga gare ni na dauki waya
ta nayi waje a hanzarce dan bani da lokacin zama magana dashi, ban shirya hakan ba
tukuna dan wallahi alkawari nayi se na rama ko da kashi daya ne cikin kashi darin
bacin ran da yasa ni.

★★SALEES★★

Ido ya zuba mata yana sake kankance ido cikin son tabbatar mata eh da gaske yake
yanzu ya fara son ta ma, ganin yadda itama take kallon sa yasa zuciyar sa ta shiga
tsalle a kirjin sa yana addu'ar Allah yasa ta yadda da abin da ya fada mata dan ya
kai makura wajen san kasancewa da ita.

Ba karya ya fada ba har yanzu yana son ta yana kaunar ta, sedai wasu halaye da ta
ara ta yafa wanda be san ta dasu ba yasa yake yi mata abinda ya ga dama don ba zata
bata masa rai a banza ita tayi farin ciki ba, be san wake koya mata bakin hali ba
da yasa har take tsanar masa yaya da kuma neman ta ringa tsallake umarnin sa wanda
shi kuma baze dauki haka ba.

Be aje ya'yan sa a kusa ba a ran sa, sune abu mafi soyuwa gare shi so baze lamunci
yaji ko ya ga tana musu wani abu na rashin kyautawa ya kau da kai ba, haka Mariya,
tana iya kokarinta wajen ganin sun zauna lafiya amma Khadijah taki bada dama bayan
da farko ita ta nuna ba abinda take nema daga Mariyar face zaman lafiya se gashi ta
tankwabe rokon ta da kan ta, amma ban da wannan abubuwan yana son matar sa,
Khadijah ce macen da ya fara so haka kuma macen da ya fara kasancewa da ya ke kuma
samun gamsuwa wajen ta fiye da kowa, ta ya ya baze so ta ba?.
Yana cikin tunanin yaji ta ingiza shi gefe tare da ficewa daga dakin da sauri, a
rikice ya mike ze bi bayan ta se kuma ya tuna da Mariya da kanwar ta dake zaune a
falon, dole ya tsaya ya koma dakin ya shiga kai da kawo ransa yayi mummunan ɓaci da
abin da tayi masa......................



Not edited ❎
Ouummey ✍️
.




Ouummey 07 {5/5/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey




*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________

_Free Chapter Seven_

Ban tsaya a falo ba na wuce garden din mu dake can bayan gidan, ba wani babban waje
bane sedai gwargwado yayi kyau, kan elephant grass din wajen na kwanta abina ina
sauri numfashi, kalaman Salees na sake dawo min cikin rai na, lallai Salees ma,
yanzu shi after all that happened har yana da karfin halin nufin na da bukatar da,
ko da yake ba abin mamaki bane.

Amma fa ba karamin juriya da karfin hali nayi ba wajen ture kalaman sa daga raina
haka kuma ba karamin kokari nayi ba wajen ganin be yi galaba a kai na ba, dan da
gaske zuciya ta ta raunana, so da kaunar sa sun rufe ni.

Ko yanzu ma da nake kwance tunanin rayuwar mu ta baya nake yi, haduwar mu, soyayyar
da muka zuba zuwa rayuwar auren mu me cike da farin ciki kafin Mariya ta shigo
cikin mu kuma komai ya canja.

Ajiyar zuciya na sauke jin mutum a jiki na da na tabbatar Salees ne, nima dama ban
yi zaton ya bar ni haka da wuri ba dan yana cikin maza masu naci kan abinda yake
so, sedai na kudire ko yafi antaru taurin kai da naci wallahi baze sami komai daga
gare ni ba.
Da sauri na mirgina jin hannun sa ta cikin riga ta, tunkurkur na zauna tare da zuba
masa idanu na da mayen son sa suka sa yayi ja lokaci guda ina bata rai matuka, cike
da basarwa irin tasa ya nuna kamar be gani ba ya matso tare da son sake shige min
sedai tuni nayi baya da sauri Ina turo baki

"Bana son irin abinda kake min wallahi, baka na dawo nan bane, ya kamata ka gane
hutawa nake son yi".

Dan tsai yayi yana duba na da mamaki dan zan iya cewa ban taba yi masa gardama ga
bukatar sa ba cikin rayuwar da muka yi ya tsawon shekaru goma sha shida, na san
dole abin ya dake shi gashi kuma nayi fuska abina tare da komawa na kwanta na bashi
baya.

Sosai jikin Salees yayi sanyi sedai he's the type that doesn't give up easily so se
ya Kuma matsowa tare da sa hannu ya juyo dani ta karfi, be kuma jira komai ba ya
danne ni cikin son se ya hade bakin mu guri daya, aikuwa kamar me haka na shiga
fighting din shi na kuma ki bashi duk damar da yake so, ya zata abin wasa ne ya
shiga kokarin kashe min jiki sedai ya ga ko kadan ban da niyyar saduda asali ma na
kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login