Showing 33001 words to 36000 words out of 41315 words
sani ba.
Kwankwasa kofar da aka yi yasa na dan zabura kadan kafin na kurawa kofar ido, da
kyar na iya mikewa naje na bude, kallo daya za'a min a san a firgice nake.
"In kin ga dama ki fito Hajiya na magana".
Hannatu ta fada min tana wani yatsuna fuska haka at the same time tana harara ta
kasa kasa, tsabar kidima ko dankwali na da ya fadi ban tsaya dauka ba na bi bayan
ta ina kiran Allah a zuciya ta.
Wannan karon gaba dayan su ne a falon har da Mariya da Salees da kuma wasu mata
biyu manya da nake kyautata zaton yan uwan ta ne dan ban san su ba cikin familyn
Salees, kowanne ka kala fuskar sa a hade take babu alamun wani abu wai shi fara'a
yayinda idanun su ke kara kaina a jiki na kamar zasu dauke ni da ido.
Daga fuskar su zaka hango tsantsan hasssada da kishi ganin irin kirar da Allah ya
zuba min, riga da skirt din jikina ya kama ni dam kamar yadda kayana suke dan
faranta wa miji na, ban lura a haka na fito ba dankwali ba balle mayafi se da
Hajiya Iya dai ta yi magana
"Sannu isasshiya, hamshakiya mandiya, shima dankwalin kina jira yaron naki ya je ya
dauko miki ne?".
Gaba dayan su suka kuma watso min na mujiya lamarin da yasa naji na takura matuka,
na mike da sauri dan daukowa se ta kuma dakatar dani
"A'a koma ki zauna dan na tabbatar da kina sane kika fito, koma me kike so mu gani
mun gani sedai Allah wadaran irin wannan kyan na dan maciji".
Komawa nayi na zauna jiki na kamar an min duka, wai shi dai wanda baya sanka kome
kayi se ya kushe, kome kayi baka iya ba, kuskure a wajen sa ganganci ne, Allah ka
rabu mu da wahala Ameen.
"Dago ki kalle ni nan Khadijah, ba na tsoran ki bana tsoran fada miki magana dan ba
zan zuba ido ki cigaba da cutar min da da matar sa tagari ba uwar ya'yan sa bayan
ke ko kara baki aje ba.
Na dade da sanin ke din ba karamar muguwa bace munafuka kuma azzaluma tun
lokacin da kika nemi raba ni da dana sedai Allah ya fiki ya tankwabar da mummunan
nufin ki, sedai ban san rashin imanin ki har ya kai ace ki karbi maita dan cutar da
matar Salisu ko yayan sa ba, kin yi asara, wallahi kin yi asara Khadijah dan kin
dade da kwashe kayan ki daga gaban Annabi".
Wani irin dam kunne na yayi, ƙwaƙwalwa ta ta dakata daga aiki, kwata kwata kaina ya
toshe, gaba daya na daina ganewa d fahimtar komai da suka cigaba da fada se aikin
kallon bakin su d ana cigaba da yi dan tun da Hajiya Iya ta ambaci maita na dago
kaina daga sunkuyar dashi da nayi.
Fiye da mintina biyar kafin ƙwaƙwalwa ta gama accessing all she've said, maita, na
karbi maita, meaning suna nufin ni din mayya ce, mayya fa, innalillahi wa inna
ilaihi rajiun.
A lokacin wani irin Hajijiya nake ji cikin kaina, kaina ya shiga juyawa kamar wanda
ake wujijjigawa, dakin ya shiga juyawa dani kamar zan kife yayinda kalman maita ya
shiga yawo a kunne na, lamarin da ya tilasta min saka hannaye na toshe kunnuwa na
tare da runtse ido na da sauri haka kuma at the same time Ina girgiza kan tare da
furta kalman a'a, a'a da karfi cikin wani irin yanayi me ban tausayi ga masu
zuciyar imani.
A lokacin da na budi ido se gani na nayi kwance kan gado na Salees tsaye a kaina ya
jingina da bango, nauyin da naji kaina yayi ya tilasta min mai da ido na rufe kafin
kuma in a blink of an eye na sake budewa lokacin da tiryan tiryan abin da ya faru a
falo ya dawo min kaina, a gigice na fara kokarin mikewa wanda hakan ne ya ankarar
da Salees cewa na farka, da saurin sa ya matso ze rike ni na goce na nufi kofar da
ke rufe wadda ake kan bugawa tare da kiran sunan sa, da sauri ya riko ni na shiga
kokarin kwace wa
"Ina zaki je haka a gigice, ki tsaya kar ki je ki fadi".
"No, sake ni, ka sake ni in je in fada musu ni ba mayya bace, ka sake ni in ji me
na musu da zafi da zasu hada ni da kalmar maita, dan Allah ka bar ni naje na musu
bayani ko zasu fahimta suyi withdrawing wannan mummunar kalmar daga gare ni".
"Naji zan sake ki, but first ki tsaya ki nutsu kar ki jiwa kan ki ciwo".
Duk yadda Salees yaso dakatar dani naki, so nake kawai na fita na fada musu ni ba
mayya bace, so nake in ji sun ce Khadijah wasa nake muke miki ke ba mayya bace.
Kubcewa nayi na nufi kofar tare da murza key din da ya sawa kofar na fita, Rukayya,
Sadiya da Hannatu duk na tsaye bakin kofar, ashe suke bugu tare da kiran sunan sa
suna fada masa Hajiya Iya tace ya fito daga daki na kafin ran shi ya baci.
"Rukayya Sadiya ai kun san ni kun san ni ba mayya bace ko, kema Hannatu kin sani
ko?".
Wani matsiyacin tsaki Sadiya taja tare da juyawa ta nufi falon ragowar suka rufa
mata baya suma bayan sun yi nasu tsakin Hannatu na kunkuni kasa kasa, a haukace na
rufa musu baya ina kuma yi musu magana, ni dai buri na kawai su yarda ni ba mayya
bace.
Fisgo ni Salees yayi jikin sa ya rungume, duk yadda nake ture shi ya sake ni ya
kiya har seda ba hakura na lafe jikin sa na shiga maida numfashi da karfi da karfi
kafin kuma wani maraitaccen kuka yi kwace min, kuka nake yi me suna kuka wanda tun
d nake shiga tension a gidan Salees ba na tunanin na taba makamancin sa, Muryar
Hajiya Iya ce ta sa Salees janye wa da sauri yana sosa kai
"Sake ta sallamamme, sake ta nace karamin mara mutunci, mara zuciya kawai, kai in
da kasan kan ka har ka kuma kallon wannan abar bayan abinda tayi, wuce muje, kema
munafuka muje dan yau ko mutuwa zaki yi karewar mutuwa se an yi maganar nan yau".
Hak ta tasa mu gaba har ciki falon, na sake neman waje na zauna haka ma Salees
itama ta koma wajen ta ta zauna
"Abinda y faru jiya d dare zuwa yau ya zama na farko na karshe, wallahi tallahi
rantsuwar dan musulmi kika Kuma taba min suruka ko jikoki se ran ki ya baci, in
zaki yi maitar ki kiyi ta can a waje amma ban da nan dan b zaki ci riba ba".
Seda na saki sheshshekar da ta taso tun daga kasan zuciya ta sannan na dago
"Na rantse da girman ubangijin da ya halicci sammai da kassai Ni ba mayya bace
Hajiya, a cikin trend din dangin mu wallahi babu maye balle in gada".
"Yo Allah na tuba maitar da ake siyarwa yanzu kamar alawa a kasuwa, ai ba abin
mamaki bane dan babu a dangin ki kuma an same ki da ita, ni dai na fada miki
wallahi ba zan lamunta ba dan gwara ki cinye kan ki da ki taba min zuri'a".
"Me nayi muku da zafi hak da zaku jefeni da kalmar maita, me na tare muku da zaku
min wannan accusation din, auren Salees gare ni ne laifin da har yaja min wannan
zargin ko kuwa tsabar tsana ce?".
Na tambaya hawaye na kafewa a fuska ta yayinda ya koma zuba ta cikin zuciya ta
"Yi man shiru munafuka mara tsoron Allah, wa zaki yaudara da kalaman ki ko da wani
fuskar tausayi bayan ke baki tausaya wa kan ki ba, daga yin mafarkin ki kin biyo ta
a guje kin daki cikin ta yarinya ta tashi da ciwon ciki da zubar jini, hankali be
kwanta ba har seda cikin jikin ta ya zube, cikin yan uku annamimiya kin yi mana
asarar rai har uku, wallahi Allah ya isa tsakanin mu dake dan ba zamu taba yafewa
ba".
Hajiya Ramatu mahaifiyar Mariya ta fada tana fashewa da kuka yayinda Hajiya Iya ta
shiga sharar ido itama su kuma ya'yan su suka rufe su suna basu hakuri da fadin
Allah ze saka musu, ni dai tun jin wai Mariya tayi mafarki na se na juya gare ta na
zuba mata jajayen ido na ina kallo na tsayin lokaci kafin cikin wata irin murya na
tambaye ta
"Na zubar Miki da ciki ta hanyar maita ko Mariya?, Kin yi mafarki na na daki cikin
ki gashi kuma ya zube ko?".
Kallo na Mariya take yi kawai bata ce komai ba hakan ya sa na saki wani busasshen
murmushi mara kyau balle fasali haka mara ma'ana
"In har na zubar Miki da ciki, in har na taba yin wani abu dan cutar da ke ko
ya'yan ki Allah ya saka Miki da gaggawa Mariya".
Na fada da karfi ta yadda kowa ze jini kana na maida duba na kan Hajiya Iya da
Hajiya Ramatu
"Kuyi hakuri Hajiya, kuyi hakurin cinye muku cikin Mariya da nayi kuma ku kwantar d
hankalin ku domin ba zan kuma saukar da kwadayi na kan ya'yan ku ba".
"Kuma kuyi hakuri". Na fada directing to su Safara'u da ragowar matan da kuma su
Rukayya kana kuma na tashi da sauri nayi daki na tare da kullewa da key, irin ciwon
da zuciya ta ke yi a lokacin ba me sauki bane, hawaye ya kafe a idanu na, ƙwaƙwalwa
ta ta tushe na rasa tunanin da zan yi, daga karshe se na samu kaina da nufar toilet
na dauro alwalar da ban san daidai nayi ta ba ko akasin haka, Kur'ani na dauka na
shiga karatu a zuci kafin a hankali murya ta ta fara fitowa kadan kadan har ta fito
sosai kana kukan ya biyo baya.
Ina jin bugun kofa tare da muryar Salees amma ban ji a raina zan bude kofar ba, ina
kuka haka ina karatu ban fasa ba har se da naji mafi girman kason nauyin zuciya ta
ya ragu, wani irin bacci ya dinga sanda ta sannan na aje Kur'ani na bingire a
wajen.
Ban farka ba se bayan magrib, a lokacin kam alhamdillah bana jin wani bacin rai me
girma sedai kalmar maita ta samu wajen zama na musamman a ƙwaƙwalwa ta, seda nayi
wanka na canja kaya na ci snacks dina sannan na bude kofar na fito, babu kowa a
falon haka kuma gidan yayi shiru alamun duk sun tafi, fridge na bude na dau ruwan
da ya fito dani sannan na nufi komawa daki se Salees da ban lura dashi zaune kan
kujera ba ya dakatar dani
"Khadeejah".
Juyowa nayi na kalle shi tare da sake masa murmushi ganin yadda duk yayi wani iri,
tasowa yayi gare ni tare da riko hannaye na
"Are You fine, ba abinda ke damun ki, ba inda ke Miki ciwo?".
Wani murmushin na sauke jin tambayoyin da yake min wanda shima ya san in nace bana
jin kome ya fada karya ne sedai dan na kwantar masa da hankali se na amsa masa
"Ka kwantar da hankalin ka, am perfectly fine and okay".
"Abinda hajiya iya su.....".
Rufe masa baki nayi da hannu na har lokacin murmushi na be bace ba
"Hajiya Iya kamar Ummi na ce, so karka damu da abinda ya faru".
Daga haka nayi gaba leaving him speechless.
Kwanciya nayi kan bed tare da janyo waya ta, ina bukatar shawara a wannan lokacin
dan ina jin bazan bar wannan maganar ta tafi haka ba, dole zan dau matakin wannan
bata sunan da ake kokarin yi min, kotu zan kai kara, shigar da kara zan yi abin min
hakki na, amma kafin nan ina bukatar tattaunawa da wani, ina bukatar wani da ze yi
supporting dina ya fada min Yes kin yi daidai Khadijah sedai waye wannan?.
Ba ze yiwu in fadawa Ummi ba balle har hankalin ta ya tashi, yaya Salima kuwa na
san in na fada mata kamar na fadawa Ummi ne dan se ta sanar da ita, Abba kuma is
not a solution dan hanani ze yi yace in yi hakuri, yayyu na kuwa ba ma zan iya
maganar dasu ba dan suma maza ne ba fahimta zasu yi ba.
Na dade rike da waya a hannu kafin na shiga facebook, group din mu na NATIONAL
ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS na shiga nayi posting anonymous message, in brief
na fadi matsala na tare da neman shawara bayan na canja abubuwa da yawa daga abinda
ya faru dan gudun halin mutane na daukan matsalan mutum suyi ta yadawa.
Kafin kace me members suka shiga reacting tare da comments, ban duba ba seda na
tara da dan yawa sannan na shiga bi one after the other, sannu a hankali nake
karantawa ina analysing bangaren shawarar da tafi yawa, in yi ko kar inyi da
dalilin haka, sedai mostly duk suna cewa kar in Kai karar ne saboda ba kowa yayi
accusing din ba face uwar miji na, duk kuma so d kaunar da mijina ke min base goyi
bayan kai mahaifiyar sa kotu ba hakan kuma ze iya kawo karshen aure na, in bar su
da Allah kawai in cigaba da fada masa ze min sakayya da gaggawa.
Wannan itace shawarar da na dauka, se da na gamsu da ita sannan na kashe datan na
koma na kwanta ina cigaba da tunani.
Washegari haka na shirya na taci aiki na sedai kukan da nayi juya yasa fuskana duk
ya tasa duk da kuwa na dan shafa powder da kohl dan ya boye yanayi na, karfe goma
na safe muka shiga meeting din da anan ne za'a fadi list din sunan mutanen da suka
yi dace da samun promotion da kuma gurin da aka canja musu na aiki in an canja din.
Suna na ne na biyar a list din, wani irin sassanyan farin ciki da ya sauka a raina
a lokacin ba zan iya fada ba sedai be yi nisa ba ya gushe jin an canja min garin
aiki an maida ni garin Bakwarni maimakon garin Darma da nake, sanyi jiki na yayi
dan a bayyane yake dole haka zan hakura da promotion din in cigaba da zama a nan
dan baze yiwu in tafi wani garin aiki ba bayan aure na da mijina na garin Darma ne.
Sunan Salees shine na goma sha biyu dan daga kasa aka fara zuwa sama, shima ya samu
promotion me girma haka kuma shima an canja masa gari zuwa Bakwarni lamarin da ya
faranta min fiye fa komai dan bana tantama yanzu kam zan je tun da shima dole ya
koma can.
Da wannan farin cikin na dawo gida ina tsara yadda zan je in yi wa family na
sallama dan sati kadai aka bamu muyi reporting sabon wajen aikin mu, ranar kam a
gidan Ummi na na wuni dan saboda guilty din abinda su Hajiya Iya suka yi min Salees
ya bar ni na wuni can.
Shawarwari masu yawa Ummi ta bani wanda naji dadin su n al'umma kudire niyyar
aikata wa insha Allah, na ziyarci yan uwa da yawa a satin har ranar tafiyar mu
yayi.
Ranar asabar da yamma muka yi sallama d jama'a muka dauki hanyar garin Bakwarni ni
da Salees da driver, tafiyar awanni goma sha biyu da mintina ya kai mu cikin garin
Bakwarni, gidan da Salees ya siya muka sauka dan shi ya zo so daya ya duba yanayin
garin tare da siyan gidan da zamu zauna.
Tsananin gajiya be bar ni na yi komai ba a ranar se washegari na gyara ko ina na
shirya mana kayan mu, gidan yayi min matuka dan bedroom uku ne se kitchen da toilet
a falon, haka kuma each bedroom na da nashi toilet din.
Washegari monday muka yi reporting wajen aikin mu in da Salees ke da matsayi na uku
a ma'aikatar ni kuma matsayi na biyar, aiki sosai muka yi dan daidaita alamura ta
yadda aiki ze mana sauki, a ka'ida a ranar zamu yi meeting da general head na
ma'aikatar gaba daya sedai ya bada uzirin baze samu zuwa ba so a ka daga meeting
din zuwa ranar da ya dawo daga tafiyar da yayi.................
*GEN GEN GEN, END OF FREE PAGES YA ZO, DAGA GOBE ZA'A GAMA FREE CHAPTERS AND D SAGA
IS YET TO BEGINS.
KINDLY HURRY UP AND MAKE YOUR PAYMENT BASE MUN FARA A ZO ANA KOMAWA BAYA BA,
OUUMMEY IS VERY AND VERY READY TO ENTERTAIN, EDUCATE AND MOTIVATE YOU WITH HER
NOVEL RASHIN HAIHUWA, KAR KU BARI A YI TAFIYAR NAN BABU KU DAN WALLAHI YOU'LL
MISSED.
INTERESTED BUYERS SHOULD CONTACT 👇
09013101854
Ouummey ✍️
.
Ouummey 15 {5/15/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 15
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
____________________________________________________________________________
_Free Chapter Fifteen _
____________
____________
Zuba mata ido kawai Falmata tayi tana kallo ta rasa me za tace, she's totally
speechless da wannan aikin na Farida, ta sani su din sun dade da zamar wa juna yan
uwa, sun fi karfin a kira su aminai balle kuma kawaye, matakin alakar su ya koma
tamkar blood relatives sedai bata san har haka Farida ke matukar kaunar ta ba se
yau.
A hankali ta kuma juya katin hannun ta wanda ba komai bane face passport, kana ta
Kuma maida duban ta kan Farida da ita ma take bin falmatan da ido
"Dan Allah maimaita min me kika ce Farida".
"Wani abu na fada na daban ne?, Nace ga shi nan dan ki ya gama yi miki komai da ya
kamata na tafiyar ki India, kuma insha Allah jibi jirgin ku ze tashi ke da harira
saboda ta kula dake ni kin ga baze yiwu in bar su Hassana su kadai ba ga kuma
Business din mu, amma tare zaku je da dan naki ya daidaita komai sannan ya dawo,
nima kuma kafin ku dawo din zan zo dan jira nake ayi hutu su tafi gidan yayan nasu,
a cikin wannan maganar me ne baki fahimta ba?".
Fashewa Falmata tayi da kuka, kukan farin ciki da kuma takaici