Showing 18001 words to 21000 words out of 41315 words
ta hado min na karba cike da godiya dan Ummi
tsohuwar likita ce, komai zata yi tana yin wanda tasan baze zama illa ga lafiya ba,
shiyasa tun muna gida ta ɗora mu kan akidar fruit dan tace babu abinda ya kai shi
amfani jikin ya mace shiyasa har yanzu ya bi jikina kullum se na sha shi kafin na
kwanta.
A sanyaye na ke tuki dan fa Ummi bata bar ni na wani zauna ba, kwata kwata ko minti
talatin ban rufa ba ta kore ni da tsattsauran gargadi, kalaman ta nake tariyowa
lokacin da ta rako ni compound
"Ita mace nasarar rayuwar ta shine gidan miji Khadijah, nasan bakya jin dadin zaman
sedai hakuri zaki yi dan bake kadai ke irin wannan situation din ba, bar ganin taki
Kaddarar wallahi da za kiji ta wata se kin ji taki shafar mai ne, se kin ji ke taki
ba komai bane compared to ta wata, so ki godewa Allah da niimar da yayi miki ki
rike ta hannu bibbiyu ki cigaba da hakuri, masu irin Kaddarar ki da yawan su wasu
na gidan iyayen su, ba dan komai ba se dan sun kasa hakuri, ko kuwa an kasa hakuri
dasu, ke kuwa kin yi hakuri wanda shine ya zaunar dake har yanzu, haka shima Salees
ya yi hakurin da ba kowane namiji ze iya ba saboda abin yayi masa yawa, ga iyayen
sa da yan uwan sa basa son ki, ga Kaddarar ki sannan kuma kema se ki basu gudunmawa
wajen kai shi bango har se an zo an yi batacciya Khadijah?, Ko kuwa kin daina san
Salisun kin ne?".
Nayi dariya tuno yadda ta karasa cikin zolaya, na sauke numfashi ina yin alkawarin
cigaba da hakuri da kau da kai insha Allah ko dan Ummi na, na lura bata san duk
abinda ze raba ni da aurena, a ganin ta maybe ba wanda ze yarda ya aure ni bayan
yasan bana haihuwa shiyasa take ta kara min kwarin gwiwa da tausa ta dan na rayu
gidan Salees.
Da wannan tunanin na karasa gida na kashe motar tare da fita zuwa gida, a falo na
same su gaba daya Salees har ya dawo, cikin murmushi na masa barka da gida na wuce
ban kalli Mariya ba.
Ina shiga shima ya shiga dakin, ban kalle shi ba na shiga cire kayan jiki na har na
gama na daura towel, ta bayan sa na zagaya na rufe kofar da ya bar mana a buɗe
sannan na karasa gaban sa na zuba masa narkakkun idona wanda na shanye shi ina
langwabar da kai gefe, lamarin da yasa Salees kasa cewa komai ya shiga kallo na
kawai
"Wanka zumaaa naaaa".
Na fada a narke cikin wani salon murya, ban yi wata wata ba na ja hannun sa zuwa
bathroom dina, tare mukai wankan ina bada hakuri a aikace, ko da muka fito tuni na
ruda Salees ta yarda ya kasa jurewa bare daure alkawarin sa ya shiga min wani salo
ne rikita ƙwaƙwalwa nima kuma ban yi kasa a gwiwa ba na taya shi yadda yake so har
ma fiye, bayan mun sake wanka kan gado na fada dan na gaji matuka gaya, shima bed
din ya biyo ni tare da daga ni gaba daya ya dora kan chest din shi ya na shafa
gashi na dana busar, duk shiru muka yi se sautin bugun zuciyar juna da muke ji
kafin a hankali na ji muryar Salees di na
"Nagode sosai khadeejah, Nagode matata, Allah yayi miki albarka".
Murya ta na rawa na amsa da Ameen dan ba abinda ya fado min rai se shekarun baya da
muka wanzar da tsantsan so da kauna a zaman mu, haka Salees ke min wannan godiyar
duk lokacin da ya samu nutsuwa dani.
"Na san ni me laifi ne, na san ina bata miki sedai wallahi kin ji na rantse
khadeejah ban san me nake yi da yake bata ran ki ba, jiki na ne kawai yake fada min
nayi laifi, dan Allah ki fada min kuskure na I promise to repent insha Allah".
Shiru nayi cikin harhado laifukan Salees gare ni na shiga analysing wanne zan fada
wanne zan bari dan wallahi ba zasu fadi duka ba saboda yawan su.
Jin yadda yake hura min iska a kunne yasa a hankali na bude baki na
"A kullum fatana da buri na be wuce karasa rayuwa ta da kai ba Salees, ban taba
hasko rayuwa da wani da namijin ba bayan kai, kai na fara so kuma har yanzu kai
nake so sedai abubuwa da yawa na dakatar dani a kan ka.
Allah be bani haihuwa ba Salees, da siyar wa ake yi wallahi bana jin da ko shekara
zan kai a gidan ka batare da da ba, da kwatowa ake yi shima ko da zan rasa raina
zan fita nayi gwagwarmaya na kwato, haka kuma da soyayya ke bada haihuwa nasan da
tun farkon auren mu ka bani, sedai Allah ne me badawa ga wanda yaso ya zaba ba kuma
dan mu da ya hana baya san mu ba amma mutane basa fahimtar hakan, ba damuwa nayi da
wasu se sun fahimta ba in har Kai da nake tare da kai ka fahimta, sedai abin da ke
tayar min da hankali kai ma din kallon mara amfani kake min, kai ma din ka gaza
fahimtar ba kasawa ta bace, so da yawa se in ga kamar jira na kake abu ya hada mu
kayi min gorin rashin haihuwa, wannan shine babbar matsala ta a gidan nan se kuma
na matar ka ya biyo baya, amma a kan ta ba zan ce maka komai ba dan duk abinda take
yi Allah yana kallon ta kuma i do believe yasan yadda ze yi da ita".
Shiru dakin ya dada yi na tsawon lokaci kafin Salees yayi breaking silence din
"Am sorry for all my mistakes, am sorry na saki bacin ran da nayi times without
number, am sorry for everything khadeejah, dan Allah kiyi hakuri and am ready to
change, for good and for you khadeejah, ki fada min me kike so nayi wallahi i
promise you zan yi".
Abin mamaki kawai yake ban dan rabon da mu sami mutual agreement kamar haka wallahi
ba zan ce ga yawan shekarun ba, abin da na rike kawai its too long, an dade sosai.
"Ka ringa bincike kafin yanke hukunci, ka dinga sauraren both side kafin zaban me
gaskiya, ba abinda nake bukata a wajen ka face adalci, kulawa da kuma tausaya wa,
this is all I need from you Salees, dan Allah".
Na hade hannaye na alamun roko hawaye na zuba a ido na, da sauri ya dora nasa kan
nawa ya jimke kana cikin taushin murya ya amsa min
"I promise you love, care and justice daga yanzu har zuwa ranar da numfashi ze bar
gangar jiki na, insha Allah ba zan kuma yanke hukunci batare da bincike ba, insha
Allah zan zama me adalci gare ku baki daya, ke kuma abu biyu nake so wajen ki dan
Allah, uzuri da soyayyar ki, ina barar wannan abubuwna khadeejah".
"And i promise you also".
Ba muyi bacci ba seda muka cimma matsaya wa rayuwar mu, wannan daren ya shiga cikin
tarihin rayuwa ta domin dai tun da muka shiga daki da shi tun dawowa ta karfe hudu
da rabi Salees be sake fita ba se washegari dan hatta sallah tare muka dinga
gabatarwa a daki.
Tun daga wannan lokacin zance alhamdillah domin kuwa Salees ya tabbatar da
alkawarin sa ko ince yana kan tabbatar wa dan haka har wata kiba nayi ta kwanciyar
hankali da samun nutsuwar zuciya.
★★★FALMATA★★★
Yau ma zaune take a falon ta, sedai tun da gari ya waye take jin ta ba daidai ba,
cikin ta wani irin ciwo yake mata da ya hanata zama guri daya, tun tana daurewa a
daki har ta kasa ta janyo wayar ta ta shiga kiran me gidan, wayar na ringing amma
ba'a dauka ba, azaba ta sa itama ta kasa daina kiran wanda a kalla ta masa miscall
kusan ashirin amma no answer.
Azabar ciwo da radadi yasa ta wurgar da wayar ta shiga malelekuwa kan carpet din
kasan gadon, gaba daya ta fita hayyacin ta , a haka Allah ya jefo daya daga cikin
masu aikin ta, cikin tashin hankali ta fice a guje dan zuwa sanar da mutan gidan
halin da uwardakin ta ke ciki, sedai bata sami Alhaji ba dan baya gida, ita kuwa
Hauwa da ta fada mata Allah ya sawwaka kawai tace ta dauke kai.
Dole harira me aiki ta kuma kwasowa a guje ta dawo, ita ta zauna da ita sedai ta
rasa me zata mata, cikin ikon Allah ta hango wayar Hajiya Falmata ta dauka hannun
ta na rawa, dake tayi makaranta har zuwa secondary se ta lalubo number Hajiya
Farida ta kira, shine fa ta zo, ashe maganin ta ne ya kare ga ba kudi hannun ta,
dole Hajiya Farida ta tafi siyowa ita kuma harira ta taimaka wa uwardakin nata zuwa
falo kafin Hajiya Faridan ta dawo..........................
Ouummey ✍️
.
Ouummey 09 {5/7/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
____________________________________________________________________________
_Free Chapter Nine_
Babu dadewa Hajiya Farida ta dawo rike da maganin, kusa da yar uwar ta ta zauna
tana mata sannu ganin yadda ta damke cikin tana runtse idanu, da sauri ta balla
maganin harira ta miko bottle water ta haɗa ta kamo falmatan ta sa mata maganin a
baki kana ruwan, da sauri ta hadiye tana dan jujjuya kai na ciwo.
Babu dadewa ciwon ya lafa dan maganin babban magani ne haka kuma fast action
shiyasa yake da tsada sosai, seda ta dawo hayyacin ta harira ta zuba mata abinci
bisa umarnin Hajiya Farida ta karba ta dan ci ta aje ragowa.
Ganin yadda hankalin ta ya dawo sosai yasa Farida kasa iya cigaba da rike abinda ke
cikin ta
"Wai haka zaki yi ta zama da ciwo a ciki sai dai ki sha magani ki kwantar dashi?,
Wait taya ma aka yi yau maganin ya yanke miji?".
Dan murmushin takaici Falmata tayi
"To y azan yi Farida, tun da kaddara ta kenan?, D ana sake wa Alhaji magana yace
wai in jira next month yanzu kam dai babu kudi wajen sa, magani kuma yace na bawa
Adam kwalin ya siyo, to tun da na bashi ban ma kuma ganin sa ba".
Kankance ido Farida tayi cike da mugun mamaki
"In ji shi Alhajin yace ki cigaba da zama da ciwo har zuwa karshen wata?, Lallai
mutumin nan ya wuce duk yadda nake zato, ke dama kin sa ran ya kawo muku maganin,
wannan tambadadden dan da uwar sa ta riga ta gama poisoning mind finishing, ai na
fada miki kin ki yadda, wallahi hau da za'a ce kin mutu dukkan su murna zasu yi
domin dadadden burin su ne ya cika".
"Kuma fa cewa nayi ko a asibitin nan ne ya biya ayi min aikin duk da akwai risk me
girma amma na gaji da wahalar da nake sha Farida, wataran har na kan gwammace
mutuwa saboda radadi da azabar da ni kadai na san me nake going through, ki dena ce
musu tambadaddu, Allah ya shirye su su gane gaskiya ".
"Uhm". Kawai Hajiya Farida tace cikin takaicin yar uwar Tata, kalli dai wahala ta
gama sha ta sanadin Alhaji da ƴaƴan sa amma wai a daina ce musu tambadaddu, ita ta
rasa wace irin zuciya Allah yayi wa Falmata amma komai ya kusa zuwa karshe dan ita
ba zata zuba ido ba, dole ta dauki mataki ko dq da ba da sanin Falmata bane.
Yin wannan tunanin yasa ta saki ranta ta shiga kwantar wa da yar uwar ta hankali
kana ta tashi ta gyaggyara mata daku na inda masu aiki basa shiga mata, se daf da
magriba ta yi shirin tafiya bayan ta jaddada wa Falmata cewan ko yaya taji wani
ciwo ta kira ta haka kuma ta tambayi Alhaji suje su ga yan uwan su.
Da toh Hajiya Falmata ta amsa mata kana suka yi sallama Farida ta wuce.
Bedroom din ta ta koma ta yi wanka ta fito ta tsaya gaban mirror dan yin shirin ta
sedai se ta bige da kallon kanta cikin madubin.
Gaba daya tayi baki ta rame kamar ba ita ba, farar fatar ta me sheki duk ta yi
duhu, kyakkyawar fuskar nan duk ta mokade saboda rama, baka ganin komai a fuskar se
dogo siririn yancin ta da ya kara tsayi se kuma kodaddun idanun ta da kallo daya
zaka musu ka hango rashin lafiya, damuwa, rashin nutsuwa da rashin kwanciyar
hankali cikin su.
Hannu tasa ta shafo wuyan ta inda kasusuwa suka bayyana kan su a wajen, ta dade ta
na shafa wajen cikin tunanin tana hawaye batare da ta san tana yi ba, tsayin lokaci
kafin ta farga ta share fuskan ta kana ta karasa gaban bed da ta aje kayan da zata
sa ta dauka ta maida wardrobe, a yadda tayi wannan ramar sam ba zata sa kayan mu na
al'ada ba dan ba kadan ba zasu bayyana ramar ta kasancewar duk an dinka su ne
lokacin da take falmatan ta ba yanzu da se sunan kawai ba.
Doguwar riga ta sa kirar Oman kana ta aje dankwalin a gefe ta shiga gyara kan ta
wanda shima se d aya samu tangarda saboda halin da take ciki, seda ta tufke jelan
sannan ta daura dankwalin kan ta, ba karamin kyau tayi ba duk da kuwa fuskar ta
babu komai face kwalli da ta sawa idan ta dan ya rage kodewar da yayi.
Kai daga yadda ta daura dankwalin abayar zaka san lallai a da an zuba gayu an kuma
kafa dauruka ba kadan ba, ita kan ta murmushi tayi da ta kalli kanta sannan ta
kwashi wayoyin ta ta fita falo.
Tare da harira suka zauna dan duk cikin masu aikin ta tan matukar kaunar harira
haka kuma ba matsayin me aiki take kallon ta ba, kallon yar uwa kuma karamar kanwa
take mata dan ta girmewa hariran nesa ba kusa ba, hirar su suke yi suna kallo sama
sama abinda yasa zuciyar Falmata dan samun nutsuwa daga tunane tunane.
Yadda hankalin su ya dauku yasa har basu ji sallaman Alhajin ba balle shigowar sa
seda yayi gyaran murya, da sauri harira ta tashi tayi waje ta kofar baya bayan ta
gaida shi, kusa da Hajiya Falmata ya karasa ya zauna inda ita kuma ta tashi zuwa
kitchen domin kawo masa ruwa.
Kan karamin tray ta dauro bottle water da juice na kwali me dan sanyi kana ta hado
da glass cups ta kawo gaban sa ta aje kana ta zuba ruwan ta mika masa ya karba ta
kuma shiga zuba juice din.
Seda ya karewa juice din kallo kafin yayi bismilla da karfi sannan yasha, ita dai
tana kule dashi sedai bata bashi wani muhimmanci ba har ya shanye lemon ya aje.
"Wanka zaka fara yi ko abinci zan kawo?".
Da sauri kamar wanda tace zata kawowa mugun abu ya shiga kada kai
"A'a, a'a ai ba zan ci abincin nan ba, na riga naci abinci a waje cikina a cike
yake".
Dan tsai tayi tana kare masa kallo kafin kuma ta girgiza kai tana dan murmushin da
kan kallo zaka san ba na jin dadi bane
"To shikenan, wankan fa?".
"Yanzu zan je can part di na nayi, dama dai nace ba wata damuwa ko?"
Seda ta dan hadiye miyau kan ta bashi amsa
"Maganin da na bawa Adam ne dai har yanzu be kawo ba".
"Se fa kina yi wa yaran nan uzuri, yana da harkoki da yawa ne, yanzu haka ya ma
tafi can kudu kan kayayyakin mu da ze shigo dasu, amma kiyi min texting sunan
maganin se na taho dashi".
"Ko kawai ka bawa Bala ya siyo min?".
Ta fada sanin in dai shi ze siyo maganin to kuwa har ta mutu be kawo ba.
"Shikenan zan bashi kudin ya siyo kawai, shikenan ko?".
"Maganar aikin nan alha......".
Tun kafin ta karasa ya katse ta yana mikewa tsaye daga zaman da yayi
"Ai tuni muka gama magana akan wannan, na fada Miki babu kudi a hannu na yanzu amma
watan gaba insha Allah se ayi aikin ko a nan asibitin Shehu ne dan gaskiya fita
wata ƙasa ze ci miliyoyin kudade kuma kin ga yadda yanzu harkokin suke se a
hankali".
Tun d aya fara maganar take kallon shi har ya kai karshe
"Allah ya kara budi, gobe ina so inje gida".
"Gida kuma, wane gidan kenan?".
Ya fada yana bata rai kamar wadda tace masa zata je gidan karuwai ".
"Gidan marayu mana, muna da wani gidan da yafi nan ne?".
"Ba zaki je ba".
Ya fada yana kade babbar rigar sa ya nufi fita waje
"A'a Usman ka bar ni kawai dan wallahi goben nan se naje".
Ta fada da rawar murya, shima Alhaji tsayawa yayi kana ya juyo cike da mamakin yau
Falmata ke ja da hukuncin sa, anya be fara kure hakurin baiwar Allahn nan ba kuwa.
"Shikenan kije Allah ya tsare, ki gaida su".
Bata amsa masa ba ta zauna tana kallon tv sedai hawaye ke zuba a idanun ta, yana
fita itama ta tashi zuwa daki da sauri, kan gadon ta ta fada tana kuka me shiga
jiki, wani kuka me tafe da sheshshekar dake fitowa daga can karkashin zuciya, a
hankali nunfashin ta ya fara seizing kadan kadan kafin kuma tari ya turnike ta , da
sauri ta tashi daga kwancen da take tare d da finciko tissue dake aje kan mirror
din ta tasa a bakin ta zuwa hancin ta dan ta ana abinda ze faru gaba.
Seda tarin ya tsaya mata da kyar sannan ta zare tissuen dake kan hancin ta ta aje
haka ma na bakin ta, gaba dayan su sun ɓaci da jini, wani irin bakin jini me kauri,
ganin bata firgita ba yasa nasan ta dade yana ganin hakan kenan.
Wata tissuen ta sa ta goge bakin ta sosai kana sa ruwa ta kuskure bakin, ta dauko
wani ma ta goge hancin, take fuskan ta yayi tas kamar ba ita ta shiga yanayin ba.
Kora tissues din tayi cikin closet ta karawa toilet din spray sannan ga fito,
bedside drawer ta bude