Showing 1 words to 3000 words out of 39414 words
💖WAZAN ZABA?💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Ya Allah kabani ikon kammala wannan littafin nawa lafiya, kamar yanda nagama da BURINAH lafiya, Ya
Allah kabamu ikon yin amfani da abinda yake me kyau aciki
1
Wasu tsala-tsalan yanmata ne guda biyu agaban mirror suna shiryawa, dukanninsu komai yaji babu
makusa, da alama akwai inda zasu
"Haba YAYA IMAN, kindauki wannan, kindawo kin dauki wanda nace shi nakeso, gaba dayama Naga
alama bakida alqibla"
hannu tasa ta fizge laffayar me launin green ahannun Iman tafara nadata ajikinta, wadda aka Kira da
Iman dince tajuyo takalli yar'uwartata da Dara-daran shanyaiyun idanunta masu kama dana mejin bacci,
kadan yarage nayarda wayar hannu na, Jin wata irin zazzaqar murya tace "yaro de yaro ne"
Itama dayar cikin sigar shagwaba tace "to yaya Iman hada ki riqe gaba daya kawai"
Saida tayi mata gwalo ta gefen ido, yanda bazata ganta ba, sannan tasaki wani murmushi wanda yayi
silar lobawar kumatunta (dimple)
Sannan cikin sanyin muryarta tace haba DR.BILLY menene Kuma abin fishi anan?
Bata jira amsar ta ba itama tafara nada Tata laffayar me launin baqi, wadda taji adon fararen stones,
sosai laffayar tahau ajikinta, farar fatarta ta haska aciki, goshinta kadai zaka kalla kagane cewa Allah yayi
baiwar gashi awajan
Da alama ta hada jinsi da wani yaren daban
Itama dayar Jin ankirata da Sunan datake mutuqar so, yasa tasaki ranta, Dan ita aduniya babu abinda
takeso kamar taga tazama cikakkiyar doctor
Shiyasa yar 'uwar Tata takeyi mata yanda takeso, dazaran taga ranta yabaci zata fara lallashin ta tana
cewa haba dr. Billy, tofa shikkkenan zance yawuce
HAJIYA datake tsaye abayansu tasaki murmushi ita kadai, Jin irin yanda yaran nata sukeyin abinda suka
saba Akan abinda ake siya musu, ba komai suka tuno mata ba Sai lokacin dasuke gida itada yar'uwarta
ZAINAB, Hawaye ne suka gangaro asaman fuskarta wanda batasan da zuwansu ba face duminsu daya
ankarar da ita, Yatsun hannunta dasuka ji zobunan gold tasa tashare hawayen, sannan ta girgiza kanta ta
wuce ta gefen su Iman wanda basu San da tsayuwar tabama.
*** *** ***
Ahanzarce yake shiryawa, yanayi yana kallan agogon dake manne abangon Dakin, bottir din gaban
rigarsa yake rufewa, rigar takarbi jikinsa sosai me launin light blue, Parfums ne agabansa Kala Kala masu
mutuqar tsada, dauka yayi yafara fesawa kamar wani sabon ango
Wata yar qaramar kit yabude agaban mirror, agogo nagani aciki ajere iri-iri, yasa hannu yadauki wani
baqi qirar Rolex yasaka
Wajan takalmansa ya nufa yadauki wani baqi qirar Italy yasaka
Brief case dinsa yadauka sannan yazo gaban mirror yadauki wayoyinsa, anan naqare masa kallo, dogo ne
dede misali, yanada doguwar fuska, haka yanada dogon hanci, bakinsa dede misali,girarsa acike take da
gashi, kalar fatarsa wankan tarwada ne, ba fari ne tass ba, hutu da Jin dadi dakuma Zaman waje daya
yasa fatarsa tayi wani irin fresh kamar saurayin qasar Ethiopian
Har yazo bakin kofar Dakin, sai Kuma yadawo yadauki jacket din suit din dake jikinsa
Besakata ajikinsaba, kawai Lanqayata yayi ahannunsa,dayan hannun Kuma yana riqe da brief case din,
yafuto yana wani irin taku tamkar wani yarima, wajan haduwa Kam wannan gayen yagama haduwa,
babu macen dazata ganshi yagaza tafiya da imaninta
Harabar gidan yafuto, anan na qarewa gidan kallo makeken gida ne, da alama mamallakin gidan yajiqu
da nera
Parking space nakalla motocine guda hudu manya
Banda guda biyu dasuke gefe
daya angama wanketa, dayar Kuma Sani yana kan gogeta
Cikin sauri- sauri yaqaraso wajan motor da aka gama wanketa qirar Mercedes Benz yabude yasaka jakar
hannunsa aciki, sannan Yarufe motor yanufi cikin gidan
Cikin azama sani dayake goge Mota yaqaraso yace barka da futowa BARRISTER
hannu kawai yakada masa yayi gaba Dan yau bayajin surutu, saboda yayi latti dayawa
Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
2
Yana shiga falon Adede lokacin hajiya tana dining tana bubbude flaks din domin tagani babu de matsala
kamar yanda tabada umarni ayi
Direct wajanta ya nufa
cikin murmushi kamar Koda yaushe tace
"IMRAN har anfutone"
Saida ya gaisheta sannan ya kalli agogon hannunsa yace"
eh hajiya zan fita office duk da Naga nayi latti ma"
tace "oya zauna kayi break fast saika fita"
No hajiya kibarshi kawai
Bata jira yatafi ba tayi sauri tahada masa tea dakanta, kujera ta nuna masa ya zauna
Sannan takai masa cup din bakinsa domin tabashi tea din
babu musu yafara Sha
Farhan dake gefe yana daddanna waya, yatabe baki, Wai hajiya saitaita lallaba yaya Imran kamar wani
sarki
Cikin kamala da sanyin Hali tace ya za'ai kafita office bakaci komai ba imran
Jin yayi shiru ne tanayi masa magana yasa Takai kallanta wajansa
Gani tayi hankalin sa gaba daya ya tattara waje daya
Tana duban wajan itama tasaki murmushi
"hajiya mun futo zamu tafi"
Ok harkun gama shiryawa?
Billy ce tace eh hajiya
Toku zauna kuyi break mana
Iman ce taja kujera kusada imran ta zauna, tace ai hajiya anty tace ta ajiye mana hadaddan abinci, kawai
ki barshi, idan mundawo mahadu
Tace hmm to maji magani, in Kuma da rabon kundawo min da yunwa to
Gaba dayansu sukasa dariya
Qasa qasa yayi da muryarsa cikin rada ya matso da fuskarsa dab data Iman yace
"MURADINA har zaku tafi "
Tana wasa da Yatsun hannunta tace" eh yaya, kasan halin baba, idan bamujeba yaji munkoma school,
zaiyi mana fada"
Gaba daya ya tattara hankalin sa akanta, da alama yamanta akwai mutane awajan
Hajiya datake riqe da cup din tea ahannunta tasaki murmushi tayi gaba
Billy ma data lura dasu tace "morning yaya"
Dagowa yayi yana ajiyar zuciya yace Bilkisu kunde dage saikun tafi
Tana murmushi tace yaya ai kasan halin baba, yace hakane, to kutashi mufita Nima dama fita zanyi
Dukansu suka tashi, hajiya tace nasa ankai muku Wasu kayaiyaki boot din motar saiku kaiwa antynku
Gaba daya suka amsa da to hajiya
Kai tsaye Iman tatafi wajan Farhan ta meqa masa hannu, Malam bani wayata
Dago kansa yayi daga danne dannen dayake da wayar yace "danma kinsamu na ari wayarki, abinda
inawa yaya magana zai aikomin da sabuwa"
Tace "eh naji, ayi zuciya asiya "
Anqi ayi zuciyar, wallahi Bazan Dena daukar wayarki ba,abinda Kema ba kudinki ne yasiyaba, samari ne
suka baki,
Tace edin, kaima kaje yanmatanka su siyama
Imran da hajiya da Billy suka saki murmushi gaba dayansu, inda Sabo sun saba
Sallama sukai da hajiya suka futo harabar gidan, gaba daya laffayar dasuka saka ajikinsu take wani irin
walwali,
Sunyi mugun kyau kamar asace su
Sani ne yataho aguje yace hajiya angama wanke motor
Saida ta yatsina fuska sannan tace, sani, sani saunawa zancema banason hajiyan nan
Kiyi hakuri za'a kiyaye insha Allah
Har gaban motar dazasu shiga ya rakasu, ya budewa Iman murfin motar, tace to yaya zamu tafi, saimun
dawo
Shima yace Wai kina nufin kece zakiyi driving da kanki? Tace emana yaya
No banyarda ba, gaskiya driver yakaiku, bansan ki wahala
Murmushi tasaki tace yaya karka damu
Yace to saikinmin alqawari idan kika gaji, Zaki Bawa Dr.taqarasa daku
Tace to yaya nayi ma alqawari
Toki kula da kanki, saikun dawo, Nima zanje Court
OK yaya bye
Shiga motar tayi,yar qarama mai kyau qirar Acura, already Billy tana zaune aciki, saboda itakam bazata
iya kallansu ba,key tayiwa motar, mai gadi yabude musu gate suka fita, sannan Barrister yabisu Abaya
Shima
*** *** ***
KATSINA STATE
da wuri suka Isa, aikuwa kamar hadin baki suna Zuwa kofar gidan baba yana Nan a zaune, shida
maqocinsa, suna futowa wajansa suka qarasa har qasa suka tsugunna suka gaidasu, maqocinsa ne ya
amsa musu faram faram
Amma shi baba,babu wani sakin fuska da nuna Jan Naka ajiki, ya amsa musu, duk da cikin ransa yanaqin
abinda yake musun, Amma Kuma babu yanda zaiyi ya boye bacin ransa idan yatuno da abubuwan
dasuka faru Abaya
Tashi sukai sukayi cikin gidan, Wasu yarane mace da namiji suka taho da gudu, suna oyoyo ga anty,
saura kadan su yarda Billy aqasa, Iman tace owk, wato ni Baku ganni bako?
Saikuma suka saki Billy itama suka rungume ta
Anty ce tashimfida musu babbar tabarma atsakar gidan
Suka baje, anan aka fara gaishe gaishe, suka Bata saqon da hajiya tabasu su kawo, less ne da atamfofi
guda biyu
Tace Kai hajiyan taku de Bata gajiya, Allah yasaka da alkhairi, suka amsa da ameen
Saida suka huta, sukaci abinci, sannan anty tace zataje tadawo
Tana fita Billy tasaki tsaki, Iman tace menene Kuma?
Tace wallahi HAROON ne yayimin 3miss call, wayar nacikin hand bag dina, banjiba, shine nakirashi yanzu
yaqi yin picking sai text yaturomin Wai yana busy ne
To menene abin fishi Kuma Billy, Kema kitura masa text din mana
Wallahi yaya Iman bazan tura masaba, Kenan ma nice na matsu dashi, yaje yayita aikin
Ninagaji da wannan soyaiyar wallahi, kekam kinji dadinki yaya Imran yana sanki
Iman tace Kema komai zaiyi daidai insha Allah, ki kwantar da hankalin ki kinji?
Ajiyar zuciya tasauke tace to yaya Iman
Saida yamma tayi, sannan suka fara haramar komawa gida, inda anty taitayi musu nasiha Akan karatu,
shikuwa baba dama bawani jansu yake ajikiba, haka de ya qara yimusu fada suka tafi
*** *** ***
Sai yamma liss suka dawo gida, suna shiga falon wata yar qaramar yarinya bazata wuce 11 years ba
tataho da guda ta rungume su
Tace anty Billy shine kuka gudu Baku tsaya nadawo daga school ba, Kuma nace muku zanje
Kumatunta Billy taja, tace sorry princess, tuba nake
Turo bakinta tayi gaba tace a a sai kinsaimin alawa, tace to zan siyo, shikkenan?
Daga mata Kai yarinyar tayi
Hajiya ce tace ku kyale zeey kuci abinci kuyi wanka ku huta
Jan zeey sukai dakinsu, saida suka huta, sannan sukaci abinci, suna falo gaba dayansu suna fira, Yashigo
falon yahade cikin qananun Kaya, farin wando jeans sai baqar Riga me adon fari
Sumar nan tasha gyara kamar ba gobe
Iman ya duba yace kungama shiryawa ne mufita?
Eh munshirya yaya, cewar Billy
Iman de batace komai ba, saboda yanda ya wulla zuciyar ta cikin tunanin tafi sauran mata sa'ar masoyi
Daki suka koma aka sake kwalliya, riguna ne ajikinsu ready made, har Gara Billy tasaka babban mayafi,
Amma Iman wani Dan siriri ne tayi rolling dashi
Suna futowa falon Farhan yace Dan Allah kar'agaji dani, wayar de
Saida ta harareshi sannan tace haka de aka iya,da'an tabaka zaka fara cewa Ina magana yaya zai siyamin,
gashinan kakasa
Yace please sisi
Wayar tabashi suka fita, wajan shopping suka je, suka zazzabo abinda zasu qara domin tafiyarsu school
gobe, kowa yagansu saiya sake kallansu saboda yanda sukai bala' in haduwa, duk inda Iman tayi yana
manne da ita, Billy ce tariqe hannun zeey sukayi wajan ice cream da sweet
Ita kuwa Iman, banda uban kayan make up babu abinda Barrister yake jida, sai Diba yake kamar ba kudi
ne zasu biyaba
Agajiye suka dawo gida,kayan suka nunawa hajiya tace suje daki su fara shiryawa acikin jaka
*** *** ***
SWITZERLAND
Sosai yayi kyau acikin kakin, wandon dark blue ne sosai, wanda zaka iya kiransa da ruwan shanshan bale,
sai farar Riga wadda ta karbi kakkarfan jikinsa, dantsansa kadai zaka kalla kasan cewa mamallakin jikin
kakkarfa ne
Daga kafadun sa jikin rigar wani tambari akayi na sojoji, ba rank bane kawai adone ajiki da akayi da
ruwan gold, Saikuma Akasa dark blue a gefe, kalar wandon jikinsa, Saikuma wani adon agaban aljihun
rigar
Baisaka hulaba, hakanne yabawa Sumar kansa damar baiyana, ta kwanta luf, tana sheqi, da alama Ana
narkar mata da dukiya wajan gyarata
Fari ne tass, jikinsa amurde yake, baida tsawon hanci, Dan dede ne, haka girarsa yar dede, bakinsa Dan
qarami mai launin ja, Allah yabashi idanu Yan manya
Yanada tsawo, ba siriri bane
tsararren daki ne dayaji kayan alatu ta ko'ina, komai na Dakin fari ne da ratsin dark green, daga labule
har furnitures din cikin Dakin
Wasu hamshaqan kujeru ne ajere acikin Dakin farare, da qananun fillos a kansu masu launin dark green,
a Kalle kallan danake ne, Naga wani babban photo Elergemant a ajiye agefe, shi dinne nede ajikin pic din
Daga qasa Kuma Naga anrubuta
"Chief of Air Staff"
Amma abin da zai baka mamaki shine idan kakai kallanka kan hadaddan gadon Dakin, yayi kaca kaca,
kamar anyi danbe akai
Tsaki yake saki shi kadai, yakama bedsheet din yana kadewa, da niyyar gyarawa, idan ya bazashi Akan
gadon, sai wani gefen ya nade, yaqi warewa gaba daya
Haushi yasa yayi wulli da bedsheet din
Daga bayansa yaji motsi, yana Juyawa yaganta atsaye a kofar Dakin, da alama ta jima da tsayawa awajan
tana kallansa
Kofar Dakin takama da niyyar fita tayi waje, Saikuma ta fasa sannan tace
"ai duk wanda baishirya aure yanzu ba, to wahala Bata qare masaba, ai Yanzu kafara wulli da bedsheet
HAIDAR, tukunnama"
Kamar zaiyi mata kuka cikin shagwabar daya saba yace "Kai MAMY Dan Allah"
Mrs Usman ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
3
Ko kallansa Bata sakeyiba tarufe masa dakin tatafi
Ajiyar zuciya yasauke idanunsa na Kan window din dake dakin, Aure de Aure de, kullum mamy zancenta
Kenan, Bama wannan ne damuwar ba, HAIDAR haka Kai tsaye Ko babyn data saba fada masa yau babu
Yanda yayi wulli da bedsheet din haka yabarshi awajan, yajuya Kan kujerun dake dakin yasaka hannu
yadauki wasu manyan wayoyi guda uku, yafice Daga dakin Shima
Yana Zuwa falon yakalleta yace mamy zanfita wajan meeting saina dawo
Idanunta Akan wasu wasu pictures tace masa "OK to kafin kafita zokaga gani"
Kamar de Yanda yazata hakanne kuwa yakasance photunan Yan matane Kala Kala, ahannunta
Janyoshi tayi yazauna dab da ita, tamiqa masa pictures din tace "gashinan duba acikinsu Ko akwai wacce
tayima"
Dariyace taso kamashi, ganin Yanda tadage bil-haqqi Akan nema masa matar Aure
Amma saiya danne dariyarsa, yakarbi pictures din yadubasu daya Bayan daya, sannan ya ajiyesu
Hannayenta yakama duka biyun yace "mamy na kiyi hakuri, Amma ni duk cikinsu babu wacce
tayimin,asalima mamy gaba dayansu babu wadda zan Iya zaba amatsayin uwar yayana, to banqi ba de
Yan aiki haka, idan su ne Kam, nabaki dama ki zabamin guda dayama ta isa"
Saida tagama sauraron kalamansa sannan tace cikin ranta
Lalle Yaron Nan yagama renamin hankali
Amma saita shareshi tace "baby toka auri Basma mana, yarinyar menene laifinta"?
Kansa yadafe da hannunsa yace mamy Basma fa
To'ai Har Gara wadannan yaran ma, yafadi haka yana nuna mata pictures din yanmatan data bashi
Kallansa tayi sosai ido cikin ido, tana nazarinsa, Basma yarinyace wayaiya, wadda tatara ilmin boko, Bata
rasa komai ba abangaren hallitar mace
Shima kallanta yayi ganin Yanda tazuba masa ido batace dashi komai ba
Adaidai lokacin Kuma mamy tace "baby Anya kuwa kanada lafiya?"
Baisan lokacin daya sunkuyar da kansaba, saboda Yanda tambayar Tata tayi masa nauyi, gakuma kunya
dayaji
Mamy indatasan Yanda yake hakuri aida batayi masa wannan question dinba
Lallausar sumar Kansa yashafa sannan yace mamy lafiya ta kalau,insha Allah, wataran zakiga Aure na,
harma kiga jikokin ki "
Murmushi tasaki, dataji yatabo mata inda takeso
Tace" to Allah yasa, Amma kasamo da wuri gaskiya "
Shima cikin fara'ah yace to mamy nah, ninafita
Rigarsa ta janyo cikin sauri tace" Ina zakaje bakayi break ba, "
Atika! Atika! Tafara kwalawa me aikinsu Kira
Shikuwa mamaki ne yakamashi,Daga cewa zai Nemo matar Aure Har aka fara tarairayarsa haka
Adede lokacin Atika ta iso, Har qasa ta tsugunna tace gani Hajiya
Kallanta tayi tace kiyi sauri ki hadowa baby break fast
Saida ta kalleshi ta gefen ido, sannan tace to Hajiya, tajuya tayi kitchen cikin ranta tana cewa Wai Hajiya
batada aiki saidai ta dubi wannan qaton tace masa baby
Cikin sauri tahada masa chips daflantain, sai tea Mai kauri
Mamy agaba tasashi tana tayi masa fira, yanacin abincin, Shikuwa mamaki ne kawai yakamashi, tun
farko inda yasan haka mamy takeso, aida tuni yasa ansamo masa wata yarinyar yakawo mata ita, idan
mamyn taganta saiya sallami yarinyar Daga baya, shikkenan yahuta da rikicinta
Saida yagama sannan ya kalleta tace "to Allah yadawomin dakai lafiya"
Kafin yabata amsa daya Daga cikin wayoyinsa tadau qara, cikin Murmushinsa Mai tsada yadaga Kiran
"Broth ya akayi?"
Bansan meya fada masaba, nagade yaci gaba da Murmushi, yakadawa mamy hannu yafice cikin takunsa
na kakkarfan soja
*** *** ***
ALIYU HAIDAR Kenan, da guda daya tak awajan Hajiya FATIMAH , wadda yake Kira da mamy, mahaifinsa
SA'AD cikakken tsohon sojane, wanda yayiwa Nigeria hidima da karfinsa dakuma lokacinsa, Allah yayi
masa rasuwa ne awajan fafatawarsa da maqiya afagen yaqi
Tun kafin yarasu yafara Dora dansa Akan turba tasan yayi aikin soja, Kuma Hakan yayi Rana, tunda tun
Bayan rasuwarsa Yayan Alhaji SA'AD Wato BILAL yaci gaba da daukan nauyin komai na Aliyu, Har Allah
yatemakeshi dayake yanada manya asama Aliyu yasamu damar riqe babban maqami na sojan Sama,
qwazonsa da jajircewarsa awajan aiki ne yasa President da Kansa yabashi mulkin shugaban sojin Sama
na Nigeria
Aliyu akwai aiki, yanada qoqari awajan aiki, haka ta bangaren yaqi, ba baya bane wajan fafatawa da
maqiya, ya qware sosai wajan harbi, duk da becika yi da kansaba saide yabada umarni ayi
Aliyu miskili ne naqarshe, bashida magana, mamy itace qawarsa, itace abokiyar shawararsa, idan
yazauna yana yiwa mamy surutu bazakace Aliyu bane, baya shiga harkar yanmata, asalima Koda yayi
niyyar cewa yanason yarinya saiya rasa ta inda zai fara fada mata, saboda Bai sababa
Abokinsa qwaya dayane, daya Daga cikin matemakansa, wato Mustapha
Shekarar Aliyu 34 duk tsawon wannan lokacin baiga wadda tayi masaba, Allah yazuba masa kishi, yanada
kishi sosai Akan abinda yakeso, hakanne ma yasa duk inda zaije to kafarsa kafar mamynsa, yana zaune a
danqareren gidansa a Abuja, shida mamy ne kawai suke rayuwarsu aciki, Saikuma atika me aikinsu data
zama Kamar yar gida,yanzu haka sunje Seminar ne Switzerland Kuma zata daukeshi Zuwa Dan wani
lokaci, shiyasa yadauki mamy Dame aikinsu atika suka tafi
Mamy tanaso taga Aliyu yayi Aure, takawo masa yanmata dayawa ciki kuwa harda yayan qawayenta
nanma abin beyuba, shiyasa takori duk wasu ma'aikata dasuke gyara masa part dinsa, tace yadinga yi da
kansa Ko yayi zuciya yayi Aure, Shima yahuta
Back to story
(kuyi hakuri da Jina dakukai shiru kwana biyu, Hakan yafaru ne saboda matsala da wayata tasamu)
Mrs Usman Ce WAZAN
✍🏻 ZABA?💖
Writing by Amnah El Yaqoub
Bissmillahir-rahmanirraheem
4
Washe gari suka hada yanasu yanasu suka futo tsaf dasu domin tafiya makaranta
Bayan sunyi sallama dasu hajiya direct harabar gidan suka futo, Amma hajiya afalo tayi zamanta, Dan
Bata qaunar abinda zai nisanta ta da yaran nata saide dole
Billy ce tadubi Zeey baby tace "Autar hajiya maza jeki part din Yaya kice masa shi muke jira"
Kafada ta dage alamar bazataba, tace um um anty banaso kisake guduwa ki barni, saide muje dake "
Iman dake tsaye kusada Farhan tace" Bari inje inkirashi "
Kallanta Farhan yayi yace" malama kawai de dama neman hanyar Zuwa kike, tojeki "
Juyowa tayi tace eh zanje kaima kayi zuciya kaje wajan taka mana"
Tana fadar haka tayi part din Barrister
Falon yayi neat sosai Kamar babu mahaluqin dayake rayuwa aciki, komai tsaf dashi, Barrister akwai son
gayu da daukar wanka, inde wajan tsafta ne da kwalliya kazo wajan Barrister toka