Showing 18001 words to 21000 words out of 124573 words

Chapter 7 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

4011

tace "eh Baba yau sha biyar ga wata" ajiyar zuciya ya sauke yace "to Masha Allah
daman abinda yasa nakiraki shine, kinga Isyaku zai karayin walima haddace Qur'ani akaro
nabiyu ranan goma ga watan gobe, August kenan, shine nakeso ranan na daura muku aure,
ranan goma gawatan August din sai ya kasance ranan bikin, nan da sati uku dayan kwanaki
kenan, kinga ga aure ga walima abin zaiyi kyau ahaka, idan yaso sai na baku dayan gidana ku
zauna aciki dazaran kin gama jarabawan saiku tafi sokoton" boye fuskarta tayi a hijabi duk
kunya ya cikata, murmushi Baba yay yace "tashi ki tafi Allah miki albarka su Baaba aiduk
sunsan zancen, kin shadai maganin ki nayau ko?" gyadamai kai tayi yace "to masha Allah tafi
abinki" fita tayi da sauri ta shiga dakin Umma dake tareda Mama suna hira abunsu, kan Umma
tafada tawani fashe da kukan iskanci. "Umma shine ko kufadamin zancen ko" dungure mata kai
Umma tayi tace "zancen me bayan keda Isyaku kun kasa hakuri har ki gama jarabawa ai wlh
malam yamin daidai dayace kawai ranan walimar shi kawai a daura auren". Tashi tai tayo kan
Mama tana kuka Mama ta daure fuska tace "kina zuwa nan saina mammake ki" juyawa tai tafita
daga dakin tana kuka sosai mara sauti, nan fa aka fara gyara amarya Umma da Mama, ba abar
Baaba abaya bama yau abata wanan gobe abata wancan tasha.

****
*kano*
Wani irin mugun kallo yabi yan aikin dake gyara flowers din side din Mami dashi kafin ya bude
kofa ya shiga, stairs yahau yawuce dakin Popsy dake nan bangaren ta, da sallama yabude

kofar ya shiga dakin yabi kowa nadakin da kallo Daga Pops sai Baba sule da Mami sai big
Mummy dake kusa da Mami. gaida su yay Mami tabi tsinannun kayan dake jikinshi da kallo ta
nunamai kofa tace "wuce kaje ka chanzo kayan nan" "ke firdausi kibarmin yaro fa yasha iska a
gidan nan, shida gidan mahaifin shi ba agida yake yasa ba fita yay dasu kinfa takurawa Ayaan
dayawa fa" Big Mummy ta chabe tace "atoh! Duk tabi ta gwanzabi yaro, dududu nawa yake
dabazai sa abinda ranshi kesoba bahaka yaran zamani kesa crazy jeans dinan suyi ass down
ba is normal suwagan kenan, kifita daga idanunshi gaskiya firdausi" "shekara talatin fa hajiya
shine yaro? Sa'anin shi nada yara uku wasu ma fin hakan" Mami ta tai maganan cike dajin
haushi, "ahap gorin aure zaki mana? Ai aure nufine na Allah ingaya miki, kuma mata saiya dirja
ya dirje ta nunawa duniya wlh, ranan bikin shi dole duniya tasan SANGARTATTCE danmu ke
aure" takarashe maganan tana hararan Mami ta gefen ido,
shiru Mami tayi bata sake cewa komiba Abba ya kalleshi yace "shigo kaji dan gata na" shigowa
yayi batare daya bari sun sake hada ido da Mami ba yawani shege jikin Abba, Baba Sulaiman
dai murmushi kawai yay ya girgiza kai dan agidan nan daga shi sai Mami ne ke kokarin gyara
Ayaan tun yana yaro amma Abba da Big Mummy son shi ya rufe musu ido basaji basa ganine
akanshi.
Shafa kumatun shi Abba yayi yace "kowani irin kaya kakeso kasaka gidan ubanka kake, idan
ban maka abinda kakeso ba inada wani wanda zan mawa ne" ya kalli Mami yace "ki kiyayi fushi
na wlh, duk randa kika kara batama Ayaan rai nida kene" yay kwafa yasake juyowa ya maida
hankalinshi kan Ayaan yace "son yau kusan sati daya da dawowan ka baka bamu labarin yanda
kasamu lpy ba".
[7/15, 12:20 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur


19 - 20

"Baka bamu labarin yanda kasamu lpy ba dan from video damuka kalla a haukace kabar gidan
nan, maiya sameka bayan nan dazaka iya tunawa?" shiru yayi yana kallon fuskar mahaifin
nashi kafin ya maida kanshi kan kafadar shi ya yatsine fuska yace "wata yarinya ce haka Popsy
a zaria" saikuma yay shiru Abba yace "wace yarinya Boy? Metayi ita yarinyar? Ya sunanta?"
shiru yay yana kokarin tuno sunanta dayaji wanan marakunyan yakira amma yakasa tunawa,
karamar tsaki yadan ya yace "namanta sunanta Pops buh her brother yace wai itane ta karbo
magani wurin Dad dinta tabani ta dinga kula dani na warke?" Abba yace "yanzu shine baka
gayamin tuntuni ba, yaudin ma inda ban tambaye kaba haka zakai shiru ko" shiru yay baice
komiba. kallon Baba Sulaiman Abba yay wanda shima shi yake kallo bayan gamajin maganan
da Ayaan yayi yace "Sulaiman jeka shirya Zaria zamu yanzu kuwa, muje mu godema iyayen ta
da ita yarinyar, sanan kome takeso aduniyar nan wlh sainai mata shi inhar baifi karfina ba dan
tamin abinda har na mutu bazan iya biyan taba, ta kularmin da Boy" da sauri Ayaan ya kalli
mahaifin nashi murya chan kasa dan bai fiye son magana ba yace "Popsy nifa bansan gidan
suba" "badai zaria take ba, koma inane koma kwana nawa zai dauke mu saimun nemota dan

haka kama debo extra kaya?" "ni fa clinic zani Pops inada patients" yawani daure fuska hakan
yasa Abba ya sassauta murya yace "to idan baka bimu munje ba tayaya zamu ganeta kaine ai
kataba ganinta" kaman zaiyi kuka sabida bakin ciki danyau akwai party da zaije yace "ni
namanta fuskarta i can't recognize her kona ganta" shiru Abba yay saikuma yakamo kafadarshi
tareda jan hancin shi da dan karfi hakan yasa yadanyi murmushi, murmushi shima Abban yay
yace "to me zaka iya tunawa ranan dai daka gansun?" shiru yadanyi saikuma yace "wanta nada
wanan abun da ake xpress dashi?" Abba yace "machine?" girgiza kai yay yace "a'a ni bansan
sunan abin ba, but yellow ne kaman car kaman bike" da sauri Baba Suleman yace "keke
napep?" shiru yadanyi jin kaman ranan fa yaji yaron yana cewa napep hakan yasa yace "i think
so" Abba ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Baba Sulaiman yace "ya za'ayi kenan?" Baba Sulaiman
yace "yanzu dai idan munje zai fara kaimu inda yatashi yaganshi ne daganan kuma zamu iya
tambayan mutanen wajen idan babu wanda yasansu saimu je duk inda yan keke napep ke
taruwa ko parking mu binciko wannata aikasan sunanshi ko?" ya jefoma Ayaan dake danna
waya yana jinsu tambaya, maida wayar yay aljihu tareda saukowa daga gadon yace "am not
sure but i think she called him Muji" Abba yace "shikenan jeka shirya kasa manyan kaya kaji
Boy" shiru yay bai amsaba yafita daga dakin duk ranshi adagule, Big Mummy ta mike tace
"Alhaji mu shirya mubiku muma?" girgiza kai yay yace "a'a kudai hadamin kaya, muda bamusan
gidan suba idan mun gano gidan next zuwa aiduk sai mu shirya mutafi tare". Ranta bai soba
haka tai wajen Wardrobe Mami ma tatashi suka hada kayan tare.
Saida Abba yaje part dinshi da kanshi ya ganshi a kwance sai wani cin magani yake, murmushi
yay yawuce gaban wardrobe dinshi yaciro mai manyan kaya shadda fara da blue sai kuma yadi
mai laushi black daya ijiye mai agefen gado da hula kube agefe dakuma su singlet da boxers,
sauran kuma yahada a akwatin shi karami ya dau turarurukan shi yasaka ciki yarufe sanan ya
kwalama Mike kira ya shigo dakin da gudu ya bashi jakan yace "yaje yasaka a mota" karba yay
yafita, sanan Abba yadawo gadon da kyar ya lallaba shi ya shawo kanshi sanan ya yarda zaisa
kayan, kafin yakamo hanunshi yakaishi bayi sanan yabarmai dakin.

Koda suka fito za'a tafi bai fitoba, Abba yakara komawa part dinshi Mami tabishi da kallo tana
girgiza kai dan wlh bata data cewa amma abu na Alhaji ya isheta, tare suka fito da Abba yawani
sha mur bakaramin kyau manyan kayan sukamai ba bakin soft yard ne da akamai dinkin half
jumper daya kama jikinshi yafito da murdaden jikinshi sosai, ga yadin ya haska shi tareda kara
bayyana farin fatar shi da pink lips dinshi, harara Mami ta watsamai dasuka hada ido hakan
yasa ya dauke kai da sauri, Abba daya kamata lokacin data harare shi ya nunata da yatsa.
"kifita daga idona fa Firdausi wlh inkikace xaki takurawa yaron nan zamu zuba dake nefa" gidan
gaba ya budemai yashiga dudda akwai body guard dake wajen wanda aikinshi bude kofa ne,
Baba suleman ya shiga baya, driver Abba ya shiga mazaunin shikuma Abba yakoma baya ya
zauna Mami da Big Mummy suka musu Allah kiyaye hanya suka tafi.
Wuraren azahar suka shigo zaria agaban wani massallaci suka tsaya sukai salla sanan suka
kara shiga mota hakadai yadinga nuna musu hanya har gaban bolar nan.
Kin fitowa yay daga mota saidai ya nuna musu ginin suka shiga Abba harsaida yay kwalla babu
komi a wajen sai carpet din data sakamai, fitowa sukayi suka shiga motar Abba nata kallon
fuskar shi ta madubin kofar mota yana mamakin wakeson halaka mai da, shi baimasan Abba na
kallonshi ba dan danna waya yake. Duk wani samari dazasu gani a anguwar saisun tambaye

shi koyasan Muji suce basu saniba, hakadai har suka fara zuwa duk inda sukaga yan keke
napep sunyi parking suce basusan wani Muji ba, har akai sallan la'asar suka tsaya sukayi suna
fitowa yace "Popsy ni am tired fa" "shikenan to muje hotel kahuta gobe macigaba da neman
sun" wani hadadden hotel sukai lodging a The Fabs anan suka kwana, washe gari tun wurin 8
Abba ya shigo yatashe shi yace ya shirya su cigaba da nemanta kaman zaiyi ihu haka yatashi
ya shirya cikin farar shadda ya dauko black shade yasaka ta sanan yafito sai uban kamshi yake
mai shegen dadi fuskar nan daure kaman zai fashe.
Tasha tasha haka suke zuwa har wurin karfe biyu suna abu daya, ata bakin kasuwan tudun
wada sukai parking inda masu keke napep ke parking Abba da Baba Sulaiman ne suka fito
suka gaggaisa dasu suka tambaye su ko sunsan wani mai keke sunanshi Muji, wani daga cikin
su ne yace "Mujin filin mallawa?" shiru Abba yay chan yace "wlh bamu san dan ina bane
mundai san sunanshi Muji" mutumin yace "to bari nakira shi kuga ko shine" godiya Abba yamai
cike da fara'a aiko yana gama wayan mutumin yace" yace gashi nan zuwa" Kudi Abba yaciro
masu yawa yamasu kyauta aiko sai murna suke nan fa suka fara koda yazo inba shi bane koma
waye yake nema saisun nemomai shi. Abba yadinga godiya dan shi mutum ne mai fara'a mara
girman kai, dason mutane idan yafita baruwan shi baya yanuna shine mai kudin nan da Nigeria
keji dashi. Shidai gogan yana mota abinshi iskan Ac na hura shi yana danne danne awaya dan
Meram ta isheshi da message.

Cikin minti talatin saiga Muji yazo da keken shi yay parking yafito, ya kalli abokin daya kirashi
yace "Maska yane tasamu ne wanan kira dakamin ina masu nemana din?" daidai nan Abba da
Baba Sulaiman suka taso daga jikin mota dasuka jingina, dafashi dayaji anyi yajuyo ganin
magidanci ne yadafa shi yaci uban babbar riga yasa yay murmushi tareda dan dukar dakai yace
"ina yini alaji" murmushi Abba yay yace "Mun wuni lpy, yar tambaya nake dan Allah Kaine Muji"
gyada kai yay yace "eh sunana Mujittapa amma Muji ake cemin, kaikasa akirani Alaji dafatan
dai lpy?" murmushi Abba yasake mai yace "lpy kalau, dan Allah tambaya nakeson nama kaine
kokuma nace kasan wani mahaukaci haka achan wata anguwa haka gaban wani Bola a sabon
gari. "wanan mara mutuncin mahaukacin na hanyar dogon bauchi, ai yariga ya warke Alhaji,
kanwata data lura dashi tun yana sato buredi ta dinga kawomai abinci yanaci daga bayama ta
karbo mai magani wurin baban mu tabashi yasha shine yana warke wa ya zanemu dagani har
ita, ya kwada mata mari nikuma ya shakeni yakusa kasheni ai namai Allah ya isa wlh" tunda
yake maganan Abba yakasa dauke ido akanshi, saida ya ijiye maganan sanan yace "shine ya
shakeku?" da sauri Muji yanuna mai wuyan shi yace "kagani alaji har yanzu wuyana bai dawo
daidai ba, har yanzu da shati shatin jan dayayi" dan murmushi Baba Sulaiman yayi dan so
kawai yake yaga me Abba zaiyi, ga mamakin shi sai yaga Abba yarike hanun Muji yace "zokaga
wani abu" kofar gaban motar ya bude daidai inda Ayaan dake chatting yake, bakin glass din
fuskarshi Abba ya cire hakan yasa Ayaan dago kai ya kalli Abba, Abba ya nuna Ayaan da
hannu ya kalli Muji yace "wanan ne ya shake kan?" shiru Muji yay yako kafeshi da ido shima
Ayaan Mujin ya kalla rass ya ganeshi amma yawani basar ya cigaba da danna wayar dayake yi,
ta kwayar idonshi masu kama dana mage muji ya gane shi dan har gobe bazai manta da idanun
mahaukacin daya shake shiba aiko ya ballamai harara ganin ya dauke kai ya kalli Abba yace
"shine alaji" Abba ya daure fuska tamau yace "Boy dama abinda kama wayanda suka taimake
ka kenan dan iskanci, oya bashi hakuri right dis minute" tsaki Baba Sulaiman yaja aranshi dan

yazaci Abba zaidan zubama Ayaan mari ne ya ramama yaron amma ina bazai iyaba, tashi ma
yay daga wurin yakoma bayan mota ya bude ya shiga abinshi ya xauna. Ayaan dako dago kai
baiyiba Abba yace "badakai nake ba bashi hakuri" dago kai yay ya zubama Muji ido batare
dayace komiba, bakaramin kwarjini yama Muji ba, dauke kai Muji yayi ya kalli Abba yay
murmushi yace "haba alaji basai yabani hakuri ba, mu dan Allah muka yi kumama wlh inda
nasan dan kane daban fadama ba saiyanzu naga kaman ku wlh kaman kai kaki" murmushi
Abba yay kaman bashine ya daure fuska ba yanzun nan yace "nagode dan albarkan yanzu
kaimu gida mu godema mahaifin naka da ita yarinyar ko" rasa yanda Muji zaiyi yasa yakoma
keken shi dan kunyan tsohon yake ya kunna keken shikuma Abba yashiga mota sukabi keken
nashi abaya har kofar gidan su Bilkisu dake cike da almajirai anata karatu.
[7/15, 12:20 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

21 - 22

Parking Muji yafara yi kafin babbar jeep dinsu kirar range rover tai parking, Muji ne yafara fitowa
kafin Abba da Baba Sulaiman, gaban motar Abba yabude ganin baida niyyar fitowa ya kalleshi
yace "fito mah boy" fitowa yay sai wani cin magani yake, Abba yasa hannu yacire shegen bakin
gilashin dake idonshi tareda turawa a aljihu, Muji ya kalli Abba yace "bari nagaya mai" shiga
zauren yayi almajiran dai sunata karatu sai kallon su Abba suke, karasa wa zauren Muji yayi ya
tsugunna agefen malam dake biyama wani karatu saida yagama sanan ya dago kai yace
"Mujittapa ba'aje sana'a bane yau" dariya yay yace "Baba baki nakawo ma, kai ake nema suna
kofar gida" Baba ya mike tsaye yace "muje" fita sukayi daga xauren shida Muji, Abba na
ganinshi ya washe baki dudda zai girmi Baba bai hanashi dukawa ba lokacin daya mikomai
hannu, shima Baba kunya yaji ya duka ya karbi hanun nashi suka gaisa, sanan ya mikama
Baba Suleman hannu suka gaisa, bugeshi Abba yay tabayan shi hakan yasa yamikama Baba
hannu yanadan murmushin dabaikai ciki ba yace "barka da warhaka" karba Baba yay cike da
fara'a dudda dai bai sansuba amma yaga kaman daga gani dan tsohon nanne, ya kalli Muji
yace "shiga gida kace su gyara zan shigo da baki" da sauri Muji yajuya yay cikin gidan yayinda
Malam yajuya aka cigaba da gaishe gaishe kaman ansan juna, Muji yafito yace "Baba zaku iya
shiga" Malam ya kallesu yace "to Bismillan ku" Muji ne yafara gaba Baba biye dashi abaya sai
Abba daya fizgo hannun Ayaan da baida niyyar zuwa sai kallon almajiran yake kaman baitaba
ganiba, daure fuska yay yabi Abba suka shiga zaure ya nunama Abba allo yana wani yatsine
fuska yace "wats dat Pops" gaba Abba yay abinshi ya barshi tsaye yanata kallon bangon da
yaran daketa kallonshi suna washemai wani harda lashe majinan daya fito daga hancin shi da
sauri yajuya ya tabe baki kafin yabi bayan Abban nashi dayaga ya bude kofa suka shiga cikin
gidan dake a gyare tsaf dashi, simintin sai kyalli yake, babu kowa a tsakar gidan sai kamshin
turaren wuta mai dadin kamshi dake tashi, iso Malam yamusu afaddadden falonshi dake gyare
tsaf an shimfida babbar tabarma a tsakiya duk suka zazzauna sai bin dakin yake da kallo yanda
yaga littatafai kala kala sun cika bangon dakin an jerasu kaman mesuim, Baba ya kalli Muji
tareda ciro kudi a aljihu yace "jeka sawo ruwan gora" ganin yanayin su na yan gayu ne, da sauri

Abba yace "ina ga randa nan ina gani kawani ce ruwan gora malam, ban yarda ba gaskiya" yay
maganan yana nuna randar dakin yana dariya, tashi Muji yay yadebo ruwa ya cika babbar jug
din malam mai tsafta yadaura akan tray dinshi sanan ya sanya kopuna biyun a kai yakawo
musu Abba ya karba yana washe baki diba yay yasha Baba Sulaiman ma yasha ruwan dadi ga
sanyi, tsiyayawa Abba yay ya mikama Ayaan dake gefenshi duk atakure, murmushin dole yay
yace "ina azumi kamanta ne Popsy" shanye ruwan Abba yay sanan ya ijiye cup din, Baba yay
murmushi yace "Masha Allah sassannun ku da zuwa saidai ban ganekuba wlh" Muji ne yadawo
kusa da Baba yace "Baba uhm dama" saikuma yakasa magana Baba yace "ina jinka" ahankali
Muji yace "Baba dan Allah kayakuri daga ni har Bilkisu bamu fada muku komi akaiba, dama
akwai wani.. ...." nan Muji yafadi ma Baba komi, Abba ya chabe da. "Malam babu abinda zamu
iya ce muku sai ubangiji Allah ya saka da alheri yakuma biya bukata yakara daukaka ka, ai da
Ayaan yafada mini shine muka shirya tundaga kano mukazo neman ku, munsha wuya kafin mu
gano nan, Allah ubangiji ya biya muku bukatun ku duniya da lahira, yanda kuka taimaki dana
kuka sani farin ciki ubangiji Allah yasaku ku farin ciki ranan gobe kiyama, watana daya da
kwana goma sha biyu banga Ayaan ba rana daya kawai yadawo ta sanadin ku, nagode nagode
malam" murmushi Malam yay yace "Ameen Alaji mugode ma Allah, a'aa ikon Allah kaji magana
fa, shine kuma yaran nan sukamin karya, inda ace Bilkisu tafadamin ai danasa ma har gida anje
an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login