Showing 75001 words to 78000 words out of 124573 words

Chapter 26 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

4042

biyu kacal wanda tai selfie
daya tayi shine kwance kan gadonta daga ita sai yar rigan bacci kusan rabin kirjinta waje
rungume hoton yayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mai sai kuma nabiyun tana sanye da
doguwar rigar atampa afalo kan kujera tai hoton azaune, murmushin daya dade baiyiba yayi
ahankali yakai bakinshi ya sumbaci hoton yace "i love yhu wifey" hanunshi ya tura cikin aljihu ya
zaro sabon wayan da Abba yabashi sabida fashewar da tashi tayi, dailing number Cp yayi yana
dagawa da kyar yace "an samu hoton ta kazo" yana fadin haka ya katse wayar yasake
kwanciya anan kasan dakin ya rungume wayar sosai, kanshi dayaji ana shafawa yasa yadan
bude ido kadan Mami daya gani ne akanshi yasa zai bude baki ta girgiza mai kai ahankali ta
zauna ta daura kanshi akafafunta tana mai head massage.

Abba yadade yana magana da Malam a zaure kasancewar dalibai sunje bara saida yagama
Malam ya nisa fuskarshi dauke da murmushi yace "da izinin Allah ankusa ganin ta" Abba kaman
zaiyi kuka yace "zamu shiga cikine na fadima mahaifiyar ta?" girgiza kai Malam yayi yace "a'a
banaso suji komi kasan mata da sa zance arai, yanzun nan saisu iya shiga damuwar dazai
haifar musu da ciwo, bari in shiga gida namusu sallama zan bika na dubo Ayaan sanan akwai
addu'a danake so namai sanan nayi agidan da aka dauketan, in sha Allah kwann nan zata
dawo".

Ba'a jimaba malam yafito dauke da wata yar jakan malamai Abba ya mike suka shiga motar
driver yajasu.
Cp na zuwa kasancewa yay bacci Mami ce tabashi hoton ya karba yace "za'a watsa hoton
duniyar yanar gizo da gidan talabijin da sauran kafafun yada labarai hakan zai taimaka sosai.

Wuraren 9 nadare suka shigo gidan sabida go slow daya rikesu akano, bakaramin tausaya wa
Ayaan dake bacci Baba yayiba.




*Bauchi*

Yau kusan satin ta biyu kenan agidan tun washe garin ranan datazo kanwar shi Ummy wacce
yan makarantar su suke cema Ummy fingers tazo Buchin, yarinyar badai kyau da iya gayu ba,
da kyar da kyar yasamu tana dan yarda da Ummy harma su kwana daki daya amma dudda
haka saita ga dama take kula Ummy gashi Ummy na sonta bana wasaba.

Yauma kaman kullum karfe biyar na asuba ta farka sabida wani shegen ciwon ciki daya tada ta,
da kuka ta tashi hakan yasa Ummy dake kusa da ita ta farka daga baccin datake dafata tayi da
sauri ta ture mata hannu tana murguda mata baki dariya Ummy taso tayi amma saita gimtse
inda sabo yanzu ai tasaba Ya Aaman ne kawai bata murguda ma baki amma kowa kam shan
murgudan baki yake, tashin datayi ne yasa taga blood akan gado da sauri tace "ina zaki
Ameerah" juyowa tayi tana share kwalla tace "Uncle" dirowa Ummy tayi daga gadon da sauri ta
kulle kofar tace "haba my sweet sis muje kifara yin wanka zan baki maganin ciwon cikin zai
dena mp kikeyi" da sauri tace "mp?" "eh mp amma karki fadama Uncle fa, muje kiga nahada
miki ruwan wanka" saida tasake murguda mata baki sanan tai gaba suka shiga bayin tana hada
mata ruwa tafito ta cire zanin gadon ta shimfida wani sanan ta fito mata da kayan dazata saka
dakuma magani, fita kitchen tayi dan hado mata tea suka hadu da Ya Aaman yana shirin zuwa
masallaci sanye da farar jallabiya kafin ma ta gaishe shi ya jefo mata tambaya. "kin tashe
Ameerah tai salla?" "eh yayan mu natashe ta, good morning" juyawa yayi yay hanyar fita sanan
ya amsa da "morning" ya sakai yafice.
Wuraren 8 ya shigo gidan dan yabiya gidan kajin su dubusu, yana shigowa tafito daga dakin
nasu da gudu tana sanye da bakin riga abaya mai stones kanta har yanzu kitso biyu ne akanta
sabida bandejin da aka sa har yanzu ba'a cireba, jiki asanyaye ta fito tazo ta xauna kusa dashi
ba kaman kullum data saba zuwa dazaran yadawo daga masallaci da gudu ba, hakan yasa
yadan kalleta yana kokarin ciro wayar shi daga aljihun jallabiya, kaman zatai kuka ta lankwasa
kai ta kalleshi tace "good morning uncle" shima kallon fuskarta yayi nayan sakanni kafin ya
dauke kai ahankali yace "baki da lafiya ne u look somehow" kaman jira take tafashe da kuka
daidai nan Ummy tafito daga kitchen dauke da tray data daura cups din tea akai sakin baki tayi
tana kallonta tace "kedai Ameerah kinada kukan banza" hararan ta tayi kaman idanunta zasu
fadi kasa ta kalli Aaman da tunda tafara hararan ta yake kallon manyan idanuwanta yanda suke
sama da kasa tace "Uncle Ummy is looking for my trouble" dan murmushi yayi yace "bakin riga
kin harare taba to" wani irin ihu tayi ta mike tsaye tai dakinsu tana kuka dudda uban kiran da
Ummy kemata ko juyowa batayi ba, hannu ya mika yadau coffee da Ummy tahada mai yakai
baki saikuma yakasa sha sabida yanda kukan ta ke tabamai rai ya kalli Ummy daketa kallonshi
tana murmushi yace "me kika mata take rigima yau?" "wlh Ya Aaman babu abinda na mata"
shiru yayi kafin ya ijiye coffee yadau tea dinta da chips yay hanyar dakin nasu ahankali ya bude
kofar ya shiga tana kwance ta kifa kanta a pilo tana kuka, ajiye tea da abinci yayi ya zauna a
gefen gadon yay dan murmushi yace "Ameerah" make mai kafada tayi tace "oh'oh" tai maganan
tana dan juyowa tana lekoshi, folding hanunshi yayi a kirji ya daure fuska yace "why are you
crying" lankwashe kai tayi ta nunamai kofa tace "Ummy" ahankali yace "okay to sorry tashi kiyi
breakfast" tashi tayi ta zauna tana goge kwalla ya juya zai fita da sauri ta riko hanunshi hararan
ta yayi. "bana hanaki tabani ba" turomai baki tayi tace "sit down" ahankali ya zauna abakin
gadon dan nesa da ita da sauri ta matso kusa dashi tana leka fuskar shi ta washe baki tace
"Uncle daga yau i will be calling you sweetheart" da sauri ya kalleta sake washemai baki tayi
tace "kaga ko Ummy na kiran saurayin ta sweetheart" yadade yana kallon fuskar ta kafin yace
"to ni saurayin kine dazaki kirani da sweetheart" da sauri ta gyadamai kai tace "eh kai saurayi
nane Sweetheart" tai maganan harda wuntsula kafa tana murna sanan tadau chips dinta ta
daura akan cinya tasa fork ta debo takai bakinshi tace "haa sweetheart" dan hararan ta yayi
kafin ya mike tsaye yafita daga dakin wani irin tsalle tayi tana rawa adakin. "yeeeee uncle is my

sweetheart"
Afalo yasami Ummy harta gama chan tea wani irin kallo yamata ya daura kafa daya kan daya
yadau coffee shi sanan yace "wato soyayya kike koyama Ameerah ko?" ware ido tayi tace "laaa
haka tacema" saikuma tai murmushi ganin shan coffee shi yake hankali kwance, ahankali tace
"Ya Aaman nidai wlh inason ka da yarinyar, she's very pretty and lovely, kaga dama Abba nata
damunka kafito da mata why don't you go for her" yakai kusan 5min maganar na waka aranshi
harta cire rai dazai amsata saikuma yace "I wouldn't risk dat, yarinyar datai loosing memory
saina fara soyayya da ita, wat if tanada wanda takeso kafin abinan yasame ta, karma ki kara irin
maganan nan" kaman daga sama yaji tace "amma ai kana sonta" da sauri ya kalleta ya nuna
kanshi yace "nina cemiki ina sonta" yanayin yanda yake kallonta ne yasa taji wani irin tsoranshi
ya shigeta bakinta har rawa yake tace "dama dama naga ka taimake ta ne, kuma yanzun nan
datake kuka ka kasa cin abinci saida kaje ka lallaso ta and a whole lot of things danake ta
noticing dis past few days" yadade yana kallonta yana karkada kafa idanunshi har sun dan
soma chanza kala har yabude baki zaiyi magana Bilkisu tafito da gudun ta tazo ta zauna kusa
dashi tana murmushi tace "sweetheart i want teddy" ko kallonta baiyi ba yace "stop calling me
sweetheart" make mai kafada tayi tace "ni u are my sweetheart ko Anty Ummy" sumsum Ummy
ta mike tabar falon kafin tasata abala'i, Bilkisu tabita da kallo sanan ta juyo ta kalleshi hada ido
sukayi dan ita yake kallo yanason yagano me Ummy tagani harta ce yana sonta, washemai baki
tayi tace "sweetheart teddy bear" kaman ba zaiyi magana ba saikuma yace "i want to sleep now
anjima zamuje musiyo" tashi tayi tana murna tace "yeeeee" tai dakinsu da gudu da sauri ya
runtse ido yana dafe kai ahankali yace "please please don't do dis to me, tayaya zanso wacce
bansan ko waccece ba, tayaya zanso wacce ita karan kanta batasan kanta ba" ahankali ya ijiye
cup din coffee a wurin yatashi ya shiga dakinshi.

Bayan kwana hudu.

Zaune yake acikin mota ya kafesu da ido yanda suke tsalle tsalle su uku ita da zainab da Ummy
basu lura dashiba wasan yar gala gala suke yi, tana sanye da doguwar riga ta daura sweetar
akai sai tsallake gida gidan take tana dariya daga gani wasan yakai mata, karan wayarshi dayaji
shiya fargar dashi daga dogon tunanin dayake yi ganin Dr Ameenu ne yasa ya dauka daga
tachan bangaren Dr Ameenu yace "kaga news?" shirun dayayi yasa Dr Ameenu yace "nama
san kagani, wat is your plan yanzu kasan dai yakamata ka maidata garin su ko, ka kaita police
headquarter da akace duk wanda ya ganta ya kaita, yaushe zaka kaita yanzu" lumshe ido yayi
yakara budeso ya daura akanta yanda taketa guje guje su Ummy na binta, ahankali yace "i
don't want her to leave Man, tun shekaran jiya nagani a news har a Twitter da Instagram saida
naga hoton ta a page din Nigeria police sun saka, i don't know what to do banaso ta bar wajena,
i don't want her to leave friend" anatse Dr Ameenu yace "i tot we've talked about this, Aaman
tayaya zaka fada tarkon soyayyar wacce bakasan ko wacece itaba, u know nothing about her,
bakasan iyayen ta ba, bakasan daga ina takeba, yarinyar daka tsinta rana tsaka kawai sabida ta
zauna dakai na watanni saika fada tarkon sonta, tun wuri kama tsamo kanka da kanka, and
tomorrow banda office, am off tomorrow bazanje clinic ba inka shirya kaita zan iya binku har
kanon" shiru yayi har lokacin yakasa dauke kanshi akan Bilkisu yayyafi ake duksu Zainab sun
shige barander suna kiranta tabar ruwa amma taki sai tsalle tsalle abinta take, ahankali Dr

Ameenu yakira sunanshi. "Barrister Aaman" ahankali yace "na'am" Dr Ameenu yace "you have
to make a decision now" dan lumshe ido yayi yace "wat if muka kaita iyayen ta sukazo suka tafi
da ita does that mean bazan kara ganinta ba? Yaya zanyi da raina da zuciyata dake cike da
kaunar ta?" "mudai fara kaita tukunna, kayi tunanin wani hali iyayenta ayanzu haka suke ciki,
wata nawa basu saka yarsu a idoba wani hali suke ciki just imagine irin farin cikin dazasu shiga
gobe idan suka ganta, don't think much abinda kamata kayu kenan ka maidata ladan ka naga
Allah" lumshe ido yayi yace "alright Allah kaimu goben" katse wayar yayi ya jinginar da kanshi
akan kujera ahankali yake karanto addu'o'i da zasu sakamai natsuwa kafin ya bude motar ya
mayar ya rufe ya shigo gidan kaman ance ta daga kai ta ganshi yana tahowa wani irin ihu tayi ta
taho da gudu tana murna. "oyoyo sweetheart oyoyo sweetheart dinmu, Anty Ummy sweetheart
is back" ganin ya tsaya yaki cigaba da tafiya yasa itama ta tsaya tana washe mai baki tunawa
da yahanata fadomai, saikuma ta turomai baki kaman zatai kuka tace "oyoyo fa nake maka
sweetheart" ledan snacks din dake hanunshi ya mikamata ta karba tana washe baki tana
kokarin budewa yay gaba abinshi hakan yasa ta fasa budewa ta bishi da gudu ganin zata bishi
har daki yasa ya tsaya ya juyo ya kalleta ahankali yace "jeki chanza kayan nan bakiga kin jike
bane" kara washemai baki tayi tana kallon fuskarshi tace "in chanza" gyada mata kai yayi da
sauri ta juya tai dakinsu, cire kayan tayi tasake saka wani doguwar rigar atampa black ta daura
dan kwali tabar ledan snacks din adaki tafito harda gudunta, afalo ta sameshi rike da ruwa yana
sha ta zauna akusa dashi, cire ruwan yayi daga bakinshi yace "ina Ummy" "sun tafi gidan kaji"
gyada mata kai yayi kawai dan bayason magana ya lumshe ido da sauri takara matsowa kusa
dashi kaman zata shige jikinshi tace "sick?" yagane tambayan shi take ko baida lpy hakan yasa
ya girgiza mata kai ya bude ido tareda sauke ajiyar zuciya hannunshi yasa a aljihu yaciro
wayarshi daga pocket yana daddannawa kafin ya bude page din policeng inda aka saka hoton
ta ya bata wayar ta karba tana kallonshi ahankali yace "look at d screen wacece wanan?" da
sauri ta kalli screen din hoton ta kafe da ido sosai sanan ta kalleshi ta nunamai wayan tace
"nine?" ta tambaye shi, wani irin ajiyar zuciya yayi yace "yea kene ance sunanki Bilkisu Abdul..."
makemai kafada tayi kaman zatai kuka tace "my name is Ameerah ko sweetheart" shiru yayi
yana kallonta daidai lokacin Ummy ta shigo tanamai sannu da zuwa ya amsa sanan yamata
magana da yaren french. "ki hada mata kayan ta gobe zan kaita garin su police sun bada
sanarwa chan police headquarter zamu kaita nida Dr Ameenu na kano, insha Allah once naga
sun kira iyayen ta agabana nagansu dakaina saimu juyo mudawo, zainab ta tayaki kwana
zanma Umar magana ya barta" gabaki daya jikinta yay sanyi hakan yasa ta juya kawai ta shiga
daki dan wani irin kukane yazo mata, sanan ya kalli Bilkisu data tasashi agaba tana kallo yace
"wat? Mesa kike kallona haka" dariya tayi sosai dan har tana buge filon kujera suna faduwa
kasa sanan ta kalleshi cikin dariya tace "sweetheart wlh ina sonka ne" tacigaba da dariya
tsayawa yayi yana kallonta he's sure awajen su Ummy takejin irin maganganun nan, mikewa
tsaye yayi jin ana kiran sallan magrib yace "go and pray zanje masallaci" kaman zatai kuka
tabishi da kallo harya fita sanan ta share yar hawayen daya zubo ta wuce dakinsu.
Wuraren nine yadawo lokacin hartai bacci yaci abincin da Ummy takawo mai yawuce daki duk
jikinshi yay sanyi.

Wahe gari wuraren goma nasafe yafito daga dakin idanunshi sunyi jajir shima sabida uban
knocking kofar shi datake tayi tanamai kuka ne, murmushi yamata bayan ya bude ganin yanda

take uban kuka yace "stop crying oya je Ummy ta shiryaki mufita" ya kalli Ummy dake zaune
akan kujera yamata alamu dakai hakan yasa ta mike tariko ta sukai dakinsu shikuma yakoma
ciki ya shirya cikin manyan fararen kaya dasuka karbe shi sosai yafito da baban trolley dinta da
Ummy tahada takawo dakinshi tun jiya da night yafito dashi yasa a boot din mota daidai lokacin
motar Dr Ameenu ta danno kai compound din dan murmushi yayi yajira haryay parking yafito
shima cikin manyan kaya shada blue yazo yace "guy gaskiya da motar ka zamu bazan kona
maina ba kafini kudi" tsaki yay ya wurgamai key motar ya chabe yace "kai xakai driving" ya
kwalama Ummy kira sabida tafito da ita shikuma ya bude motar ya shiga Dr Ameenu ma ya
zaga ta bangaren driver yabude ya shiga, ita tafara fitowa da gudun ta tana sanye cikin black
body hug da black straight skirt sai Ummy ta daura mata maroon kimono me shegen kyau akai
ta kulle mata belt din kimono ta gaba sanan tamata rolling black vail akai da keda one one stone
ta bakin gyalen tasaka mata takalmi baki maidan tudu daya fito da hasken kafarta, gabaki daya
Yay nisa a kallon ta yanda tai kaman balarabiya tsaban kyau maganar ta dayaji akanshi ya
fargar dashi. "sweetheart wai zamu fita?" gyada mata kai yayi batare dayace komiba, shidai Dr
Ameenu waya yaciro abinshi yakira matarshi suna hira, da sauri tace "ina zamuje park zamu?"
girgiza mata kai yayi yace "shiga mota garinku zamu" "inane garin mu?" tafada tana murna, dan
murmushi yamata yace "shigo mota muje kigani" tsalle tayi ta bude kofar baya ta shiga tanama
Ummy bye bye, kudi yaciro dayawa yabama Ummy yace "I will call u anjima" addua sosai
tamusu sosai sanan Dr yaja motar suka bar gidan saida suka danyi nisa yace "ka kosan na
dauko file dinta na hospital kasan police da tambayoyin banza kafin suce mumuka saceta na
dauko file dinta kai ID card dinama na jikina am not ready to enter any gbese" dariya yadanyi
sabida yanda ya karashe maganan yace "kai kayi aure nazaci zuciyar ka zata chanza ta dena
wanan tsoro ashe babu abinda ya chanza" hararan shi Dr yayi yacigaba da tuki batare dayace
komiba itakuma tana baya saiyima teddy ta mai gashi kitso take tana yar wakarta na yar gala
gala yarinya yar gala gala wasan yara ahankali, ta madubi yake ta kallonta har daga baya bacci
ya kwashe ta.

Dayake wuraren sha daya sukabar Bauchi sai gurin biyu da rabi suka shigo garin kano kafin
sukai police headquarter kuma sai wuraren karfe uku da minti biyar, parking sukayi suka fito ya
zagayo tabaya rike da pringles din daya saimata a hanya da bottle water sabida bacci takeyi
tuntuni ya bubbuga kujeran hakan yasa ta bude ido da sauri ya dauke kai, waige waige tayi tana
kallon wurin tace "sweetheart mun iso garinmu?" dan ita tazaci wani wurine mai suna haka,
gyada mata kai yayi hakan yasa tafito tana Kalle Kalle shikuma ya maida kofar ya rufe ya
kalleta yanda take kallon polisawan daketa harkan su sun ririke bindigogi yace "muje" girgiza
mai kai tayi tana neman yin kuka ta nunamai yan sandan ahankali yace " don't worry babu
abunda zasu miki muje" gaba yayi tana binshi abaya har inda Dr Ameenu yake suka shiga ciki
saida suka rubuta sunayen su sanan sukace inspector Husaini Ahamad suke nema dan
sunanshi aka rubuta a page, kujera aka nuna musu shima dan polisawan sungan su sunyi
shigan alfarma ne yasa sanan wani daga cikin su yatafi office din inspector yay kusan 10 min
sanan yafito yace "muje" tashi sukayi suka bishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login