Showing 9001 words to 12000 words out of 124573 words

Chapter 4 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

4006

tagumi takarayi ta bishi da kallon tausayi tana share hawayen dataji
yazubo da bayan hannu "to baida iyayene dasuka barshi shi kadai sai wahala yake? Ashe ciwo
yaji saisa Allah ya turota ta kula dashi? In sha Allah daga yanzu kullum saina kawoma abinci
kaci, Allah yabaka lpy". daukar kulan da goran tayi tarufe ta saka ajaka sanan tabar wajen tana

waigenshi.
[7/15, 12:18 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦


Maman Abd Shakur

8 - 10

Tafito tawuce school, tun daga gate tahango Sargent na dukan latti. "innalillahi wa innalillahi
raji'un" kasa shiga tayi ta tsaya anan gate tana kuka har saida Sargent yagama dukan duka yan
lattin sanan ya dago kai suka hada ido tana kuka yace "ke bazaki shigo amiki naki bane ko
komawa gida zakiyi?" girgiza kai tayi ta shigo tana hawaye ta mikamai hannunta tana
kokkomawa baya tana kuka, Chau! Ya zuba mata daya wani irin ihu tayi tana tsalle wanda yasa
harshi Sargent din saida yakoma dabaya yana kallonta "ke lpyn ki kuwa?" ko kallonshi batayiba
saima sosa tafin hanun take dayay jajir tana kuka kaman zata mutu, "kawo hannun saura uku"
yafada yana matsowa kusada ita, hijabi tasa tana goge fuska ta makale ajikin bango. "dan Allah
ka yakuri karka karamin, dan Allah" kanta yayo hakan yasa takara makalewa ajikin bango tana
ihu daidai nan principal dinsu tafito tace "Sargent bar dukan turota ta gyaramin office" tun kafin
Sergent dinma yay magana ta tashi da gudu tabi bayan principal tana kuka haka ta gyara office
din kafin takolma aji lokacin har angama first period, ranan haka takaraci zamanta a aji tana
kuka gashi a ranan ne aka manna musu time table din waec dinsu dazasu fara nan da wata
daya.

Wuraren biyar da rabi ta shigo gidan nasu atsakar gida Umma data fito daga kitchen ta tareta
tace "maiya sameki idanunki suka kumbura haka?" shiru tayi takasa magana dan ta tsani yin
Karya, sai hawaye tafada jikin Umma tana kuka, Umma dukta rude tacirota daga jikinta tace
"cikin newai?" girgiza mata kai tayi ahankali tace "dukana Sargent yayi amakaran ta" tai
maganan tana nuna mata hannun dayay jajir "wayyo Allah sannu kinji Allah zai saka miki, jekiyi
wanka kizo nazuba miki tuwo, Maman ku dasu Raiyana suna gidan Baabar ku" daki ta shiga ta
cire kayan makarantar ta dauro zani akirji tafito rike da kayan makarantar ta zuba abotiki, kan
window kitchen takoma ta dauko omo ta zazzaga aciki ta jawo ruwa daga rijiya ta wanke kayan
fess ta shanya kafin takara dauraye botikin taja ruwan wanka tai bayi, tana tafitowa Umma ta
zuba mata tuwo nan tsakar gida ta zauna ta tadashi tass dan miyan kukar harda wake yau
akasa aciki, tana gamawa ta wanke hannu takai kwanon kitchen ta shiga daki ta dauko wayarta
ta kunna, aiko kiran Isyaka ya shigo dauka tayi yay mata sallama anatse. "Assalamu Alaykum
gimbiyar zuciyata, waya tabamin ke amakaranta idanunki sukai ja haka?" kaman zatai kuka ta
harari bangon dakin tace "ba Sargent din school dinmu bane ba, yawani dakeni da bulalar inji a
hannu" dan lumshe ido Isyaka yayi akan dakalin waje dan duk dalibai sun fita bara sai bayan
sallan Isha'i za'a cigaba da karatu, malam ma bayanan, ahankali yace "kece kin dage saikin yi
karatun nasara, mezaki yi dashi? Kinada ilimin addinin ki kin sauke yanzu kina kan hadda
wacce kin kusa gamawa, kin haddace hadisai da dama kin iya littatafai da dama duk wanan
ilimin addinin naki kika dage saikiyi na nasara, mezakiyi dashi, ai dole kisha duka haka kam,
mutumin daba muharmin kiba yakama yana dukan ki, danba wanan makarantar ba dayanzu

munyi auren mu natafi dake garin mu anya Bilkisu kina tausayina kuwa?" gyadamai kai tayi tace
"kayakuri kaga watan gobe ma zamu fara jarabawan, muna gamawa komi yazo karshe" dan
ajiyar zuciya ya sauke yace "shikenan Allah ya bada sa'a, sanan gobe zamuje school din saina
koyama Sargent din hankali waye shi dazai tabamin gimbiyar mata, mar'atu saliha" dariya tayi
sosai tana auna Isyaka da Sargent hakan yasa yace "mekike ma dariya?" murmushi tasake yi
tace "babba nefa Sargent din?" "kina nufin banda karfin dukan shine kome?" zatai magana taji
yakatse wayar, wayar tabi da kallo kafin ta fashe da dariya harda rike ciki tace "to daga fadin
gaskiya Sargent ai babba ne kaiko bama kakai girman Sergent ba balle nasa rai zaka iya
ramamin" kwanciya tayi kafin ta ijiye wayar akan kujera ta lumshe ido haka nan taji tana tunanin
mahaukacin nan.
Wuraren 9 ta shigo dakin nasu dan daga dakin Abba take ta tsugunna agaban Mama dake kada
lagwani, "Mama inje gidan Baaba?" "saikin dawo" da sauri ta zuri hijabin ta dake kan kofa har
kasa tasaka sanan ta wuce uwar daka ta tsugunna karkashin gado ta ciro asusun ta tadawo
palo ta zauna kan kujera tana jijjigawa, Mama ta kalleta tace "mezakiyi da asusun?" adan
tsorace tace "fasawa zanyi Maman mu?" "kiyi meda kudin?" Mama takara jefa mata wani
tambayan kasa amsawa tayi saima wasa da hijabin ta tahauyi, kafin ta dago kanta a tsorace
tace "gidan Baaba zankai" dauke kai Mama tayi daga kallonta tacigaba da abinda takeyi hakan
yasa ta saci kallon maman nasu kafin tadau asusun tafita daga dakin da saurin ta.
Akofar gidansu Baaba ta tsaya ta fasa asusun dayake na katsa ne, ta tattare kudin ciki ta kirga
dubu biyu da dari uku ne sanan ta shiga gidan, Baaba ta gani gaban murhu Baaba tace "yar
arziki kinzo" shiga dakin Muji tayi tace "ina zuwa Baaba" samunshi tayi yana shiryawa zai fita
hakan yasa tazo kusa da shi tawani yi laushi dan tasan halin shi, ahankali tace "Ya Muji
inkanama Allah ka kaini muyi aikin lada" "aikin ladan mene?" ya tambaye ta yana kokarin
daukar sabuwar wayarshi daya saya ta gionee, wayar tabi da kallo kafin tace "dan Allah ka kaini
muje muba mahaukacin nan abinci sanan in sharemai wurin nan dayake bacci kaji" wani kallo
Muji yabita dashi hakan yasa ta tsugunna agabanshi tafashe da kuka, cikin kuka tace "ya Muji
karka manta akwai karuwar data shiga aljanna sabida kare, taimako da kyautatawa sune
dabi'un dakowani musulmi yakamata yanada shi, bamusan dame Allah zai dubemu yaji
kanmuba yasamu a aljanna, kaji dan Allah, kuma karka fadanma Baaba sirrin mune wanan dan
Allah ka kaini, nibanaso naje ni kadai ne, tsoro nakeji kaga jiyama ya yanke sosai akafa saisa
nafasa asusu na musaimai takalmi ahanya da riga sabida ya chanxa yagargiyar jikinshi" kudin
datake nunamai ya kalla mamaki dukya kasheshi ya tabe baki yace "lamarin ki akwai ban
mamaki, daga ganin mutum saikace ubanku daya, nidai mutafi karki batamin lokaci" wani
dadine ya kasheta ta shiga dakin Baaba, kula ta dauko tazo tukunya ganin baba na bayi ta bude
dafadukar taliyar hausa ta gani ta deba sanan tarufe suka fito ta ijiye a keke sanan takoma ciki
Muji yace "ina kuma zaki" bata bashi amsaba saidai tafito da jarkan ruwa da tsintsiya dawani
ledan daki da Baaba tacire dan tasa sabo, dukta saka akeken Muji yabita da kallo, tai murmushi
mai karamata kyau tace "muje" kunna keken yayi suka tafi. Ahanya suka tsaya tasaimai bakin
takalmi kito size 43, irin takalmin nan damasu noma kesawa inzasu gona wanda yake arufe
sanan tasai babbar t-shirt blue suka taho.
Tun kafin suyi parking ta hango shi abola yanata tsintse tsintse, ahankali tafito daga keken
bayan sunyi parkin rike da kulan, mahaukacin na hangota yataho da gudu har saida takoma
baya da sauri amma ya bita ya fizge kulan hanunta yana dariya, da sauri ta kalli Muji daya bisu

da kallo tace "kama gani yaganeni wlh" tabe baki Muji yayi yataya ta daukan jarkan ruwan
itakuma ta dauko tsintsiya da leda suka shiga gidan. Yana zaune akasa sai kiciniyar bude kulan
yake hakan yasa ta budemai ya fizge da sauri zai saka hannu ta rike hanun nashi gabanta na
faduwa tace "tsaya in wanke ma hannun da datti" ta kalli Muji hakan yasa ya tabe baki yakaraso
wajen yabude jarkan ya daga itakuma takai hannunshi tana wankewa Muji na zuba musu ruwan
sanan ya fizge yahau ci, murmushi tayi tana kallon ciwon kafar nashi sanan ta yayyafa ruwa a
wajen tasa tsintsiya tafara shara har takai waje ta shinfida carpet din dayadan yayyage, nan da
nan wurin yay kyau, yana gama cin taliyar yayar da kulan da sauri ta mikamai ruwan ya karba
yasha sosai yay wata irin katuwar gyatsa, takalmin ta dauko tazo ta gabanshi tana kallon
kafarshi daduk yay datti, ruwan tasa ta wawwanke mai kafar yanata kallonta kafin ta saka mishi
takalmin aiko yamai daidai, ya mike tsaye yanata tsalle yana kallon takalmin, ta kalli Muji
kaman zatai kuka tace "toka sakamai rigar dan Allah" atsorace yace "ni? Ni wlh tsoro nakeji"
dariya tai tace "Allah bazai maka komiba baya komi" ta mikamai rigar suka karasa kusada shi
tare, ya juyo yana kallonsu duk suka tsaya chak suna kallon juna, daga mai rigar Muji yayi yana
juyawa asama hakan yasa yadinga bin rigar da kallo sanan Muji yasa hannu zai ciremai ta
jikinshi da sauri ta juya musu baya saida Muji ya ciremai sanan ya samai wacce suka siyo
aikuwa tamai daidai, da sauri Muji yace "juyo kigani" murmushi tayi tana dafa Muji tace "laaa
ashe na cinka size din daidai" ganin yanda yaketa tsalle yasa muji yace "bari namai hoto" ciro
wayarshi yay yadinga daukan shi hoto yanda yaketa tsalle tsalle ya kalli Bilkisun daketa dariya
yace "dalla malama mu matsa kusa dashi dukmuyi selfie, selfie da mahaukaci" yay maganan
yana dariya yana janta har inda yake ai kuwa mahaukacin na ganinsu ya dena tsallen yana
kallonsu duk suka tsaya a gefenshi, Muji ya dau hoton. Tace "zomu tafi to tunda mungama" fita
sukayi suka barshi yanata tsalle tsalle.



Yau kwana ta biyu kenan bataje wurin shi ba sabida weekend gashi ba makaran ta, sanan
Baaba nama wasu dalibai daya yaye walima aiki suketa yi bata samu daman fita daga gidan ba,
haka tai kwanaki biyun nan tunanin shi koya yake oho koma yaci abinci oho duk tabi ta damu
sosai. Yau Monday tun shadaya ta shirya Mama tace "da wuri haka zaki yau Bilkisu?" gyada mata kai
tayi tace "eh inaso nai karatu ne sosai Mama jarabawan mu yakusa" kudi Mama tabata sanan
tafito ta karbi kudin mota wurin Baba kafin ta wuce gidan Baaba dayawa ta dibi wainar yau
tazuba ruwa agora tafito har bakin titi kafin tahau mota dazai kaita sabon gari. Sauka tayi
ajunction sanan tafara dandara wa har zuwa layin mahaukacin, babu kowa a wajen wurin hakan
yasa ta shiga ginin tana karanto addu'o'i, a kwance ta hangoshi abinda bata taba zuwa ta tarar
dashi haka ba kenan, idanunshi sunyi jajir kaman ma rawan sanyi yake, da sauri ta karasa ciki
ta tsugunna agabanshi tace "menene?" ganin ko dago kai baiyiba yasa takai hanunta dake rawa
sosai tadan taba wuyanshi da sauri tajanye hanun jin wani irin zafi da jikinshi yayi, fashewa tai
da kuka sosai tace "kayakuri bankawo ma abinci jiya da shekaran jiyaba halama saisa kake
ciwo, zokaci abinci" hannu tasa zata da gashi ya tunkude ta har saida tafadi ya cigaba da rawan
sanyi yana jan hanci, sake dawowa gabanshi tayi tana goge hawaye tadau kulan wainar ta
bude ta nunamai sanan ta ijiye gefe tasa hannu ta dago shi ya tashi ta jinginashi da bango, wani

irin rawan sanyi yake tadau kulan ta bashi amma yakasa fizgewa yanda yasaba yi, wani irin
mugun tausayi yabata tafashe da kuka sosai, hannu tasaka ta dauko wainar daya tace "ci" bude
baki yay kadan yakarba daga gani kasan yunwa yake ji, biyu kawai ya iya ci daga nan bai kara
bude baki ya karba ba, hakan yasa ta bude ruwa tabashi shima yasha kadan ya ture har saida
ruwan ya zuba afuskar ta bata damuba ta share fuskar, kwanciya yakara yi saikuma taga yafara
mimmikewa yana wani irin iri dabaki kaman yanason yay magana amman yakasa, sai kallon
sama yake yana wani iri dabaki, matsowa tai kusa dashi duktama rude hakan yasa ta mike
tsaye tafita daga wurin dagudu tana kuka har bakin layi, mota ta tare tahau sai gida, Koda takai
gida Baba bayanan Mama ta kalleta tace "lpy kika dawo tun yanzu?" hawaye tasake shareware
tace "Baba nake nema" tabe baki Mama tayi tacigaba da kwashe kayan datake yi daga kan
igiya tace "ai siki jirashi yaje wani jana'izar abokin shi daya rasu ne" to kawai tace tama fita
daga gidan taje chan kofar gida ta zauna tanata kallon almajiran dasuke karatu tana share
hawaye Allah Allah kawai take Baba yadawo, sai wajen karfe uku da rabi Baba yadawo tun
akofar gidan yace "maiya dawo dake Bana riga nabiya kudin makaranta ba" dan azaton shi ko
an korota ne, girgiza mai kai tayi saikuma tafashe da kuka hakan yasa yace "baki da lpy ne?"
girgiza mai kai tayi, ahankali ta shiga goge hawayen sanan tace "Baba kawata yar makarantar
mu yayan ta mahaukaci ne, yau haukan shi yatashi baida lpy sosai, sai wani iri yakeyi da baki
kaman yana magana dawasu, shine suka ce nazo dan Allah kamusu addu'a aruwa dazasu
bashi ko zaiji sauki" "sabida hakane kike wanan uban kukan" girgiza kai Baba yayi yace "Allah
ya shiryaki, je gida ki kawo ruwa mai kyau agora namiki addu'a aciki saiki kaimusu abashi" da
sauri ta koma cikin gidan ta debo ruwa mai kyau agora sanan tafito takawo ma Baba dake
zaune akan tabarman shi na Zaure, karba yayi ta zauna kusa dashi, kara ruwan yay abaki
yafara karanto addu'o'i daban daban da karatu, yafi awa daya ahaka sanan yay topi aciki yarufe
yabata yace "gashi nan ki kaimusu subashi, idan yasha su tofa mai ayatul kursiyu kafa bakwai
aka, kulhuwallahu kafa uku a ka falaki da nasi uku aka, inhar sihiri ne wanan addu'a zai Karya
shi, inkuma haukar ciwo ne daga ma'aiki to wanan kuma duk lokacin da ubangiji yaso warkar
dashine zai warke, amma dai inhar sihiri ne zai karye yabar jikinshi da izinin Allah, i maza jeki
kai musu" hamsin yakara cirowa yabata ta karba tawuce harda gudunta takai bakin titi tahau
bus, sosai ake traffic dan wai hatsari akai a hanya ba ita takai ba sai wuraren magrib, tana
sauka a bus din takara kwasa da gudu zuwa layin da addu'a da shiga ginin.

Juye juye ta sameshi yanata yi akasa Allah kadai yasan meyake mai ciwo, da gudu takara sa
gaban shi ta tsugunna ta dukar dakai tana kallon fuskarshi dataga idanunshi sunyi ja sai rawan
sanyi yake yana atishawa, kama hanunshi tayi hakan yasa yadan dago kai, da duka karfin ta
tajashi tamaida shi kan carpet har tana buga baya da bango ta zauna a gefenshi, goran ta bude
takaimai ruwan baki ta kafamai, karba yay yasha sosai dan dama kishi yakeji, saida yasha
kusan rabi sanan ya cire bakin yasake kwanciya tareda buga kanshi akasa saida ta runtse ido,
ta rufe goran ta ijiye, sake matsowa kusa dashi tayi ta karanta mai su ayatul kursiyu da Baba
yace ta karantamai duka ta tofamai aka, takoma ta zauna agefen shi tana kokarin bude jaka
dan bashi cingum din data tahomai dashi kozaidan ci, gani tai ya zabura ya mike ya dafe kanshi
da duka hanunshi biyu yarda jakan tai tadan matso kusa dashi ta kallai, buga kai taga yay da
bango ta fashe da kuka tareda daura hanunta akan nashi tace "kadena kanka zai fashe" buge
hanunta yayi yawani kwanta akasa tareda rike cinki shi yana numfashi sama sama kaman zai

mutu, bakaramin tashi hankalin ta yayi ba, rasa abinda zatayi yasa tafita da gudu kozata ga
wani amma babu kowa a wajen sai karan speaker wani massallaci dake bayan layin dan
wa'azin bayan sallan magriba akeyi, kakarin aman dataji yasa tadawo ciki da sauri cikin shi taga
yarike sai amai yake kaman zai amayar da hanjin cikinshi, tsugunnawa tayi kusa dashi dan
jitake kaman ta daukemai ciwon, duka wainar dayaci saida ya amayar saikara kakarin aman
yake amma babu abinda ke fitowa ragowan ruwan ta dauko takawo mai ya bude tasaka mai
abaki yadansha kadan sanan yakara komawa ya kwanta akan carpet din yana wani irin mugun
rawan sanyi fiye dana da, daga gani kasan mugun sanyi yakeji rasa mezatayi yasa tacire hijabin
makarantar dake jikinta ta rufamai, yarage daga ita sai faran rigar makarantar mai dogon hannu
da purple dankawalin makarantar dake kanta ta zauna ata kanshi tana sake tofamai addu'a
ganin bai dena rawan sanyin ba, tashi zaune yayi azabure yafada jikinta yawani irin kankame ta
yana wani irin nishi da ita kanta saida taji kaman zata suma wajen tsoro ga jikinshi wani irin
mugun zafi, duk wani addu'a dayazo bakinta karantashi takeyi tana kokarin tureshi amma
takasa sabida wani irin kankameta dayayi fuskarshi akan wuyan ta, sunfi minti goma ahaka
ganin gari yasoma duhu sosai dan bamata iya ganin fuskar shi sosai yasa tafara kokarin tureshi
danya saketa tatafi gida amma takasa, danko motsa hannu takasa, kuka tafashe dashi sosai
tace "ka sakeni natafi gida" ganin baimasan metake cewaba saima jikinshi da ko ina ke rawa
yanata wani irin nishi ya kankameta yasa tai shiru tana kuka ahankali zafin jikinshi na kona ta
sosai, wani irin tsoro ma taji tanaji yanda takejin kukan abubuwa daban daban awurin tafara
karanto addu'o'i tana kuka kasa kasa, jujjuya kanshi taji yanayi awuyan ta yana wani irin nishi
kafin yafara bubbuga kanshi akan kafadarta da karfi, tafashe da kuka sosai dan bakaramin zafi
buga kan kemata ba, dena wa yayi kafin ya burkito ya gangaro da kanshi kan kirjinta, ya
kwantar da kanshi awurin ya kankameta sosai dan kaman zai shige jikinta yana rawan sanyi,
wani irin kuka takeyi gabaki daya yawani irin riketa danko motsi, ko numfashin kirki ma bata
fitarwa, kuka tacigaba dayi har wani irin wahalallen bacci yay gaba da ita azaunen.


Ahankali yake bude idonshi dayaji sunmai wani irin shegen nauyi ga kanshi dake wani irin
fitinannen sarawa, daga hannunshi dayaji yay mai nauyi yay yadaura akanshi yafi minti biyu
ahaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login