Showing 69001 words to 72000 words out of 124573 words

Chapter 24 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

4044

CCTV camera a compound din" sai a lokacin ma Abba yatuna yace "harda
ma falon nan akwai" IG yace "ina computer to zanzo mu kalla dan musan meya faru" da kyar ya
mike tsaye Abba ya rike shi yace "Boy" gyada ma Abba kai yayi da kyar alamun zai iya, Abba
yarike shi sukai sama IG nabiye dasu abaya, Mami da big Mummy ma suka bisu, wani daki
sukaje nan suka tariyo computer har zuwa daidai inda goons din sukazo sukai horn mai gadi
yafita waje dubawa sai gashi daya daga cikin su sanye da mask ya shigo da mai gadi yana
dukanshi kafin ya sumar dashi ya bude musu gate bakin van din ya shigo, pursing video IG yayi
ya rubuta plate number motar down sanan ya danna play suka cigaba da kallo gashi sun shigo
sun fiffito daga motar sunyi cikin gidan sun bude kofa sun shiga falo sukai upstairs, dayake
babu CCTV a sama basu ga maiya faru ba saidai ihunta dasuke ji da lokacin datake kiran Ya
Ayaan, runtse idonshi yay da karfi wasu hawaye masu bala'in zafi suka zubomai da sauri ya
share, saikuma inda daya daga cikin su yasa kafa yatokare mata ciki tafado ta fasa kai wani irin
dunkule hannu yayi zai daki computer da sauri IG ya rike shi calmly yace "be strong Man, i
know how u feeling, zamu kamasu idan ma kidnappers ne dan basuyi kama da yan fashi ba,
inda yan fashi ne da sata xasuyi, indai har kidnappers ne zasuyi contacting dinku, so u people
should stay alert zasu iya kiranku kowani lokaci, yanzu dai one good thing is zamu nemo motar

nan tasu ta hanyar plate number nan koma ina motar take a fadin kanon nan, sanan Alhaji" ya
kalli Abba yace "yakama ta yanzu akwai body guard dazasu dinga yawo da family ka most
especially ur son, yanzu dai zan koma office zan zuba team dina akowani hanya da express
way na barin garin kano zamu kamasu da izinin Allah, one last thing is i need hoton ta, dan nan
CCTV footage fuskar ta is not clear sosai dan musa a media incase idan wani yagan ta" Da
sauri Abba ya kalleshi yace "kanada hoton ta Boy kabamu?" saida yarike hanun Abba sanan ya
iya magana da kyar yace "yafashe" Abba ya kalli Cp yace "wayarshi tafashe dazu amma zasu
samo hoto bari yadawo daidai tukun" ajiyar zuciya cp ya sauke yace "shikenan we will use dis
for now, please take care of him he doesn't look good" yanuna ma Abba Ayaan sanan yawuce
yafita daga dakin, da taimakon Abba suka fito sabida jirin dayake ji sosai suka zauna afalon
sama ya daura kanshi akan kafadar Abba shi kadai yasan yanda yakeji, Abba sai addu'a
yakemai jin yanda zuciyar shi kewani irin rawa, tashi Big Mum tayi ta kalli Mami datai wani irin
tagumi daurewa kawai take danji take kaman tai ihu tace "bare na shiga bayan gida" gyda mata
kai kawai Mami ta iyayi tai shiru tana tunani abu kaman mafarki Bilkisu da dazu dazun nan tana
tare da ita, da dingishi Big Mummy ta shiga dakin dake kusa dana Bilkisu ta maida kofar ta rufe,
bayi ta shiga ta rufe sanan tafito da wayarta daga zani wacce tuntuni ta maidata silent, message
din Bala tagani da sauri tabude;
“hajiya mun dauketan muna warehouse din saidai fa, Ahmad ya bugeta sabida gardaman
dataso tamana kanta yafashe har yanzu bata farfado ba”
Da sauri big Mummy tamai reply
“Bala bakace min gobe zakaje Bauchi ba, inaso da daddaren nan kudau hanyar Bauchi kunemi
wani daji achan ku karasata kuyar, sabida yanzunan za'a baza police ako ina agarin nan,
banason ko gawanta su tsinta agarin nan, ka tabbatar bata numfashin daga yanda nake ganin
yaron ma dazaran ta mutun shima rayuwar tashi karewa zatayi, ka tabbatar kunbar garin nan
yanzu, yanzunan zakaji alert din kudi, kudin aikin ka kuma saina tabbatar kai komi da kyau
sanan zan biyaka miliyan goma, kubar garin nan yanzu, i repeat yanzu! ". Tura mishi dubu dari
tayi sanan ta kashe wayar gaba daya ta wanke fuskarta tafito daga bayin tadawo ta dayan
gefen Ayaan ta zauna tana tofamai addu'a tana matse kwalla, ahankali Mami ta tashi ta dauro
alwala ta shiga daya daga cikin dakunan tafara salla.

Bala na ganin text dinta ya kinkimeta yasata amota sauran ma suka shiga suka bar gidan.


Shigowa dakinshi Abba yayi dauke da cup din coffee da Mami tahada mai, yana zaune ya
jinginar da kanshi a bangon gado ya lumshe ido, lokaci daya wani irin hadadden zazzabi ya
sauko mai, zama kusa dashi Abba yayi yana dafe kafadar shi tareda ijiye tea akan bedside
drawer ahankali yace "Boy" fadawa yay jikin Abba murya chan Kass dake rawa sosai yace
"Pops please bring her back, Pops dan Allah kace sudawo min da ita konawa suke so zanbasu
or they should take me instead" ba karamin tashi hankalin Abba yayiba bayason abinda zai
tabamai Ayaan, Ayaan nada mugun rauni akan abinda yakeso wanan tun yana karami yasan da
haka, wlh koma su waye suka dauke Bilkisu sai yasa hukuma tamusu hukuncin daya dace
dasu, daga kanta bazasu sake marmarin dauke wani arayuwar su ba. Ahankali yace "i promise
u, Boy i promise you, ko ina ma suka kaita saimun nemota, even if it takes nai hiring private

investigator, even if it means putting all i habe at stake saina nemo ma matarka, i promise u
Son, don't worry wanan alkawarin baban kane" sake kankame Abba yayi sosai saiga hawaye
shar sun zubo da kyar yace "Pops they hit her, she's hurt, kanta yafashe, Pops he dare hit mah
wife wlh saina ka.." hawaye yahana shi karasawa, yafashe da kuka ahankali yana shesheka
ajikin Abba, bakaramin damuwa Abba yay ba rabon daya ga kukan Ayaan tun yana grade1,
haka yadinga lallashin shi, ranan yanda sukaga rana haka sukaga dare dan wani irin ciwo ne da
mugun zazzabi yarufe Ayaan sosai, koda gari yawaye baya gani da kyau tsabagen zafin
zazzabin Mami takira Dr.


Wuraren biyar na yamma suka shigo garin bauchi sundanyi tafiya mai nisa kafin suyi parking
agaban wani daji, wani babban buhu daya daga cikin su ya dauko yazo inda take kwance
kaman matatta dan sunma dauka ta mutu ne, ya bude bakin buhun da kyau biyu daga cikin su
suka ciccibeta suka sakata aciki suka kulle bakin buhun sanan wanda ke tukin yafito yazo
tabaya ya bude musu suka daukota da sauri sukai cikin dajin da ita da saurin bala'i. Jogging din
daya sabayi kullum da yamma tunda yazo farm house din Abban shi hutu yauma yafito yanayi,
sanye yake da singlet din sport mai ruwan toka da dogon wando shima mai ruwan toka kafanshi
sanye da bakin sport shoe sai kanshi acikin head phone yana jogging abinshi tunda idanunshi
suka sauka akan bakin van yaji baida natsuwa, barin ma lokacin dayaga sun fito dawani babban
brown sack sunyi cikin dajin dashi hakan yasa yaji bai yarda dasuba, labewa yay abayan wani
bishiya har suka fito duk yana kallon fuskar su kafin yaga sun shiga cikin van din sun tada sun
tafi, da sauri yay cikin dajin daidai ta inda yaga sun fito yasa hannu ya janye headphone din
daga kanshi ya maida wuyanshi sanan ya cigaba da tafiya da sauri sauri yana shiga dajin yana
kalle kalle amma baiga buhun ba har yay giving up yana shirin ya juyo yaga buhun akan wani
babban dutse da sauri yay wurin yana addu'a, ahankali yay bismillah ya daura hannunshi akan
buhun yana tattabawa jin kaman mutum yasa yay maza ya kwance daurin bakin buhun da
kafafun ta yafara cin karo, ahankali hanunshi na rawa yay bismillah ya daura akan feet dinta
kafin yadan dago takan ya zare buhun gabaki daya daga jikinta, yabi jinun daya bata goshin ta
da kallo, da sauri ya kamo hanunta yana checking pulse dinta ganin akwai yasa yagane da
ranta, da sauri ya ciccibeta yana kallon fuskar ta kaman yay kuka yafita daga dajin da mugun
gudu baxai ma iya komawa farm house ya dauko car ba hakan yasa ya tare wani me machine
din dake zuwa yahau kai yace kai ni town hospital. Yana zuwa hospital wani babban abokin shi
mai suna Dr Ameenu ya karbeta aka taru akanta.


*Kano*
Ayaan fa gashinan gashinan ne, kaman zararre kaman lafiyayye baida aiki se sumbatun kiran
sunan Bilkisu kokuma yadau filo yarike yanama filo magana, Abba yay yay dashi sukoma gida
yaki ya makale adakin Bilkisu anan yake kwana yarike kayanta gam ya rungume yana fadin am
sorry, am sorry, please come back. Big Mum dadi kaman zai kasheta har addu'a take Allah sa
bakin cikin rashinta yasa yama mutu gabaki daya yanda dazaran Alhaji shima yamutu ta rike
dukiyar gam gam.
Babu wanda yataba kawo tanada hand abacewar Bilkisu, anjira anjira yan kidnappers din sukira

amma shiru.

Yau satin ta biyu a hospital din, kullum Guy din daya kawota yake zuwa dubata duk wani kudi
da akai bukata na treatment dinta zai biya.
Yauma kaman kullum misalin karfe biyar yay parking motar shi a parking lot din asibitin ya fito
yana sanye da farin lallausar yadi daya haska chocolate fatar shi, sai uban kamshi yake yay
cikin asibitin yana taku daidai yana kada key mota daya rike yay office din Dr Ameenu kai tsaye,
Dr Ameenu na ganinshi ya nunashi da yatsa yace "kaiko Aaman sai shegen gayu babu matan
aure tuzurun banza kawai" tabe baki yayi tareda fizge cold bottle water dake hannu Dr ya zauna
akan kujera saida yadan sha ruwa kadan sanan yaja tsaki yace "sabida kadanyi aure last month
ne zaka faramin iskanci, lallai muma Allah bamu masu sonmu" yay magana yana shafa dan
gajeren gemunshi sanan yaja wata yar siriruwar tsaki agajiye yace "ya patient dina har yanzu
bata tashi daga coma bawai" gyara zama Dr Aminu yayi yace "i think rashin tashin ta has
something to do with buguwan kanta, but once ta tashi we will conduct some special test
akanta, but let's just wait till then" ahankali yace "okay" kafin ya mike tsaye dauke da ruwan
goran a hanunshi yace "bari naduba ta" yafita daga office din dakin dayasa asata na mutum
daya yaje ahankali ya bude kofan ya shiga yana kallonta har yanzu tana kwance as usual cikin
kayan asibiti da nurses suka saka mata bambamcin kawai yau babu oxygen din da aka saba
samata, kanta nannade da bandeji, kujera yaja ya zauna yadan kalleta nayan mintina kafin ya
jingina goran ruwan daya dauko a jiki ya tura hanunshi acikin aljihu ya ciro wayarshi yana
daddannawa. Motsin dayaga bargon da aka lullube dashi nayi yasa ya tsaya da danna wayar
dayake yi ya dago kai ya kalli fuskarta, motsin dayaga saman idonta nayi yasa yadan matso da
kujeran shi kusa da gadon yana kallonta batare dayace komiba, motsin data fara sosai yasa yay
magana cikin calm voice dinshi yace "Hey open ur eyes, u are safe now" motsi tacigaba dayi
kafin ahankali tabude idonta suna rawa harta bude duka ta saukesu akan fuskar wani mutum
data gani yana kallonta ga cool murmushi akan fuskar shi, dakin tabi da kallo tana jujjuya kai
tana wani irin fir fir da ido kafin idanunta su sauka akan goran ruwan data gani akan jikinshi da
sauri ta yunkuru zata tashi da sauri ta dafe kanta tasaki wani irin kuka, da sauri yadan matso
yace "careful" da karfin tsiya ta tashi zaune ta fizgo ruwan data gani ajikinshi tana dambe da
ruwan tana kokarin budewa amma takasa hakan yasa ya tsaya yana kallonta, fashewa tasake
yi sosai da kuka tana dafe kanta dake mata zafi, ahankali ya mika hannu ya karbi ruwan zata
fizge ya girgiza mata kai ya bude marfin ya mika mata, karba tayi da sauri ta kafa abaki wani irin
mugun kishi takeji, daidai lokacin aka bude kofar dakin afirgice ta saki ruwan hanunta tai wani
irin ihu da yasa ya kalleta da sauri dan dama kofar ya kalla sanin either Dr ko nurse ne zasu
shigo, tsalle tayi ta diro daga gadon ta labe abayan shi tafashe da kuka tana bobboye wa, da
sauri Dr Aminu ya karaso da murmushi kan fuskarshi yace "wow alhamdulillah at long last
yaushe ta farka Aaman?" matsawa yayi sabida Dr ya ganta da kyau tasake biyoshi ta labe
abayan shi, ahankali ya juyo hanunshi daya cikin aljihun shi ya nuna Dr Aminu yace "he's ur
doctor zoki zauna" ya koma ta wurin gadon da sauri ta sake bishi ta tsaya a inda ya tsaya tana
tana kallon fuskarshi hakan yasa yama Dr Aminu kallon irin wats wrong with her dinan, singnal
da hannu Dr Aminu yamai hakan yasa yakara kwantar da murya ya nuna mata gado yace "sit"
makemai kafada tayi, hakan yasa ya zauna abakin gadon da sauri itama ta zauna tana kallon
fuskarshi, dan murmushi yay mata yace "sunana Barrister Aaman Muhammad, nina ganki

lokacin wayansu sun shigar dake daji acikin buhu sun yar, now i need you to tell me who you
are sabida mu kira iyayen ki suzo su dauke ki, Ya sunanki?" tunda yake maganan ta kafeshi da
ido ko motsi batayi, anatse yace "ya sunanki?" nuna kanta tayi akaro na farko tai magana cikin
siririyar muryarta tace "ni?" gyada mata kai yayi ahankali tace "nima bansani ba, ya sunana?" ta
wurgamai tambayar itama tareda tsareshi da ido tana kallon fuskarshi, da sauri ya kalli Dr
Aminu, dan matsowa Dr Aminu yayi hakan yasa ta matsa kusa da Aaman da sauri hartana
neman bigeshi da sauri ya matsa, ganin haka yasa Dr ya tsaya batare daya karaso ba ya
kalleta yace "fadama na waye baban ki to" da sauri ta nuna Aaman, kallan kallo daga Aaman
har Dr Aminu sukayi hakan yasa Dr yace "wanan bashine baban kiba, waye Maman ki to?" sake
nuna Aaman tayi, ahankali Dr ya kalli Aaman yace "muje office" yay gaba Aaman ya mike tsaye
da sauri itama ta mike ya kalleta yace "jirani ina zuwa" makemai kafada tayi kaman yarinyar
tafashe da kuka da sauri ya kalli Dr Aminu daya tsaya ya kallesu yace "wai meke damunta ne?"
ajiyar zuciya Dr Aminu ya sauke yace "inhar abinda nake tunani hakane inaga nin sanadiyar
injury data samu akai yasa tasami shafewan kwakwalwa, ma'ana she lost her memory saisa
kaga kaida tafara gani tasani take yarda dashi, yanzu u are her everything kai zaka koya mata
sabawa da yarda da mutane for now kafin mu dubata musan wani treatment zamu daurata
akai".
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




Maman Abd Shakur

63 - 64

Dan juyo dakai yayi ya kalleta nayan sakanni yana nazarin abinda Dr yafada, gashi tawani labe
abayan shi tana wani zazzaro ido, yujawa yayi ya kalli Dr Aminu yace "Man come and examine
her please" ya matsa gefe da sauri tasake binshi kaman zata shige jikinshi hakan yasa ya juyo
da niyar mata masifa ganin yanda take kallonshi yasa yakasa ya nuna mata bed yace "sit" make
mai kafada tayi kaman zatai kuka tana shafa cikinta tana kallonshi da sauri ya dauke kai yace
"menene?" da kyar tace "yunwa" juyo dakai yayi ya kalleta yace "sit lemme get food for you"
zama tayi ya juya zaiyi wajen Dr Aminu daketa kallonsu da gudu ta mike ta bishi hakan yasa ya
tsaya chak tareda juyowa, shagwabe mai fuska tayi Dr Aminu yace "u know something, sata ta
zauna na dubata tukun" baice mata komiba yay wurin gado ya zauna abakin gadon da sauri
itama tabiyo shi ta zauna abakin gadon tana haki, Dr Aminu yadau stethoscope daya ijiye akan
fridge din dakin ya maida wuyan shi yana zuwa wurin su, ihu tayi ta koma kusa dashi sosai ta
rikemai riga da hannu daya tana nuna Dr da hannu daya, ahankali yasa hannu ya fizge rigarshi
data rike da kyar yace "hey calm down" ya mika hannu ya riko Dr Aminu yace "he's my friend,
babu abinda zai miki, Dr kine so don't be afraid okay" gyadamai kai tayi tana kwalalo ido tana
kara mamatso wa kusa dashi, saida ta rike hanun rigarshi gam gam sanan tabari Dr Aminu ya
dudduba tareda cire mata bandejin kanta ya chanza zuwa plasta yasa adaidai wurin ciwon
sanan yay mata murmushi ganin yanda take yatsine fuska alamun zafi yace "wai Barrister zaka

sha aiki anan wlh" yadau byro yana rubuce rubuce sanan ya mikama Aaman, fizge hanunshi
yayi ya mike tsaye da sauri itama ta mike ya karbi takardan, Dr Aminu yace "zaku iya tafiya da
ita na sallame ku, memory loss dinne dai banda haka brain dinta yabugu dan haka zakaga tana
abubuwa sai ahankali, yanzu dai ran Wednesday zaku dawo ranan ne likitan brain din asibitin
nan ke zuwa zai dubata nasan zai mata memory loss test sabida ya gane if long term memory
loss ko short term ne, tasamu daganan saiya daurata akan medications in sha Allah she will be
fine, but u need take extra care of her gaskiya" shiru Aaman yayi yana kallonshi ko motsin kirki
yakasa, ahankali Dr Aminu ya dafashi turo baki tayi tasa hannu ta ture hanun Dr Ameenu daya
daura akan kafadar shi dukansu atare suka kalleta, turo baki tayi tana kallon Dr saikuma ta kalli
Aaman ta washe mai hakora da sauri ya dauke kai ya kalli Dr, Dr Aminu yace "i know wat u are
thinking amma karka damu duk mai taimako baya tabewa, dazaran ta warke saika kaita wajen
iyayen ta kaga yanzu idan ka barta wat if mutanen dasuka so kasheta sukazo suka karasa ta?
Gwara ka tafi da ita chan farm house din for now inyaso ai zaka iya kiran gida chan Abuja
Ummy tazo hutu, nasan kuma Abba zai barta tazo, in yaso saita tayaka kula da ita idan zakaje
site, u can go now buy this drugs for her kabata abinci taci kuma she need it" dan ajiyan zuciya
ya sauke saikuma ya kalleta yanda dogayen kitso guda biyun da wata nurse tamata sabida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login