Showing 45001 words to 48000 words out of 124573 words
Chapter 16 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf
ba yar gidan nan bace ko, bakuwa ce dan
bantaba ganin kiba wlh" gyadamai kai tayi batare data janye idonta daga kan birin daketa
dambe da ayaba ba, shikuma mai aikin sai binta yake da kallo daga sama zuwa kasa yana
wanan kyakkyawan fa haka aranshi. "kai!" atsorace daga shi har ita suka juyo sakamakon wani
irin tsawa daya dakama mai aikin, yana sanye da white singlet daya kama jikinshi sai neon
Beach floral 3 quarter, fuskar nan babu alamun wasa, da hannu yamai alamu yazo, da sauri
jikinshi har rawa yake ya karaso gabanshi kanshi akasa yace "good morning si..." wani wawan
mari Ayaan ya dauke shi dashi azuciye kafin yanunamai hanyar barin garden din yace "u are
fired, out" ganin babu alamun rahama afuskar shi yasa guy din yabar garden din da sauri, arude
sumi sumi jikinta har rawa yake tazo zata wuce ta gefenshi ya damko hanunta ya maida shi
tabaya ya lankwasa ihu tayi "wash Allah na wai mena maka ne nikuma?" juyo da ita yay takusa
fadawa jikinshi da idanunshi dasukai jajir yace "are you trying to seduce my workers" kallonshi
tayi da idanunta dasuka cicciko da kwalla tama kasa magana ya daka mata tsawa. "am talking
to you" hannu tasa ta taushe kunenta sabida yanda dodon kunenta ya amsa tafashe da kuka
sosai fizgan hanunta yy takusa faduwa yajata har side dinshi wanda shine ke tare da garden din
kofar ya bude ya jata ciki wani kamshi da sanyi sukai mata sallama wurgar da ita yay akasa
tafashe da kuka ya maida kofar ya rufe, arude ta mike tsaye tana waige waige, ganin ya
dumfarota da idanunshi da suka chanxa kaman banashi ba yasa ta shige bedroom da gudu
kafin ya iso ta kulle kofar, key data gani ajiki tasaka ta kulle tacire key tana komawa da baya
tana kuka sosai, buga kofar yayi azuciye yace "ke kibude kofar nan tunda ba gidan ubanki
bane, kibude nace" komawa baya tadinga yi harta jingina da jikin wardrobe ta sulale kasa ta
kama kafafuwan ta tana kuka tana kuma addu'a Allah dawo dasu Mami.
Key dataji yasaka a kofar yana murdawa yasa ta mike tsaye da sauri kirjinta na bugawa bude
kofar yayi yawani bugo da gudu ta kwasa zatai bayi taku daya yay ya damkota yajawota jikinshi
tana kokarin fizgewa amma saida ya hadata da kirjinshi ya matse, yanda take nishi kaman zata
mutu ne yasa yace "ke" abakin gado ya zauna har lokacin kanta na kirjinshi tana kuka, cirota
yay daga jikinshi yana wani irin hararan ta, kin kallonshi tayi saima bayan hannu datasa tana
share kwallan daya zubo mata, yanuna ta da yatsa da kakkausar murya yace "wlh duk randa
kika kara fitowa tsakar gida ahaka saina zaneki da belt mara hankali kawai" murya chan ciki
tace "niba mara hankali bace saidai kai" bakinta dayaga yay motsi yasa ya kama hanunta
atsorace ta kallai yace "me kikace?" dauke kai tayi ta turo baki tareda zame hulanta daga kai
tana goge hawayen daya bata fuskarta tace "ni bance komiba" dogon jelar gashin ta yabi da
kallo kafin ya maida kallonshi kan fuskar ta ganin kokarin fizge hanunta take batare data kallai
ba, murya chan kasa yace "hau gado na duba ciwon ki" ko kallonshi batayi ba tace "ai ya warke
baya zafi" dan murmushi yayi ya kalli cikin inda akai aikin kafin yamike tsaye daukar ta yay
hakan yasa ta fasa uban ihu kaman zata tsaga gidan, buge bakinta yay da sauri tai shiru ya
kwantar da ita akan lumtsetsen gadonshi shi da sauri tai yunkura zata tashi ya dakamata tsawa.
"ki natsu" ba karamin tsoron yanayin fuskarshi tajiba hakan yasa ta kulle idonta kam kirjinta na
bugawa, fuskar yadan kalla kafin ahankali yakai hanunshi gun ciwon yadan taba kadan sanan
yacire hannu, flat cikin nata yabi ya kallo kafin ya sauke idanunshi akan kirjinta dake cikin rigar
ya kafesu da ido, jin baya taba cikin yasa tabude ido ahankali karaf suka hada ido da sauri ta
janye nata ganin yanda ya cika mata ido ta tashi zaune ta sauka daga kan gadon duk yana
kallonta, hanyar kofa tai da sauri zata bude tafita, da kakkausar murya yace "ubanwa yabaki
izinin fita" da sauri ta juyo idanunta sun cicciko da kwalla, mai matsalar mutumin nan da itane
wai, da yatsa ya nunamata gadon yace "dawo inda kike" ahankali tafara tafiya tadawo kan
gadon ta zauna nesa dashi tana goge kwalla, mikewa tsaye yayi yaje gaban fridge din dakin ya
bude yaciro farm fresh yogurt ya cika glasscup sanan ya mayar cikin fridge yadau laptop dinshi
dake kan kujeran dakin yadawo bakin gadon ya kalleta yanda taketa share kwalla, wani irin
mugun kallo yamata yace "matsa ciki ke" a tsorace ta matsa cikin gadon ta jingina da bangon
gadon azaune tana share kwalla kirjinta sai bugawa yake, ajiye glasscup da yogurt din ke ciki
yayi akan bedside drawer ya kwanciyar zama yasa pilo akan kafarshi yadaura laptop akai
tareda gyara zaman kanshi a filo biyu daya hada yana daddana laptop din batare daya kalleta
ba yadauko yogurt din yana sipping kadan kadan yana danna laptop da hannu daya, sosai take
share kwalla duk hankalin ta yatashi takara makewa ajikin gadon gashi sanyi takeji sabida
yanda ya kara Ac sosai. Yakai kusan 10mins yana abinda yakeyi kafin yajuyo dakai ya kalleta
har lokacin share hawaye take da bayan hannu ya daure fuska yace "ke" kaman bata jishiba
haka tai hakan yasa ya dakamata tsawa. "ke" arude ta kallai, glasscup din yogurt din da har
yanzu ko rabi bai shaba ya mika mata alamun tazo ta karba girgiza mai kai tayi wasu hawayen
na zubowa, yanda ya kafeta da ido babu alamun wasa yasa taji gabanta yafadi ahankali ta
rarrafo zuwa inda yake ta karba tana kuka mara sauti zata koma inda take yace "ke anan
zakisha" gyada mai kai tayi duk ta rude dan bata saba ganin namiji a singlet ba, kaiwa bakinta
tayi tafara sha duk yana kallonta da gangan yakara daka mata tsawa ganin zata shanye. "ke
nace ki shanye duka ne" da sauri tacire cup din daga baki tana girgiza mai kai ta mikamai cup
din, karba yayi yana kallon yanda yogurt din yama sama lebenta layi kaman gashin baki, zata
koma inda take ya harareta yace "karki sake ki tashi" zama tayi dukta rasa inda zatasa kanta sai
goge kwalla take da bayan hannu, glass cup din yakai bakinshi shima yanashan Yougurt din
data rage yana kallon fuskar ta ya tura hanunshi a aljihu yaciro handky ya mikamata yace
"clean ur mouth" karba tayi ta share bakinta batare data share inda Yougurt din yabata ba ta
mikamai handky din tana kokarin boye hawayen dake shirin zubo mata, karba yayi tareda ijiye
cup din akan bedside drawer ya kalleta da lazy eyes dinshi murya chan ciki yace "baifita ba zo
na share miki" yay maganar yana daura hanunshi abayan ta, arude ta kallai tareda sakin kukan
dayake cinta, hannayen shi biyu ya daura a bayanta ya jawota zuuuiiii tazo jikinshi janye
hanunshi yay daga bayanta lazy eyes dinshi akan lips dinta inda Yougurt yabata, hada goshin
shi yay da nata da sauri tasake kallonshi suka hada ido azabure tafara kokarin mikewa amma
baibata damar ba, hannunshi daya yakai ta bayanta ya janyota ya hadata da jikinshi da kyau
shikuma yay relaxing bayan shi ajikin bangon gado, yasa dayar hannun yakamo habarta yana
kallon yanda ta runtse ido gam tana kuka jinkinta har barbar yake, matso da kanshi yay sosai
saitin fuskar ta dan sunajin numafashin junan su kafin ya fito da harshen shi ahankali ya daura
akan saman upper lips dinta yafara lashe yogurt din.
*inhar kasan baka biyaba ka karanta ban yafeba, dan novel din kudine*
In kanason littafin nan chat me up tanan 07012181461
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
43...
Kokarin juyar dakai tafara jin wani irin zirr zirr da jikinta keyi har kunnuwanta, yasaka hannayen
shi biyu yay cupping fuskarta kafin yakara fito da harshen yafara lasan yogurt din ahankali
ahankali kaman yana tickling dinta har yagama lashewa yakara resting fuskarshi akan nata
yana kallon idonta yanda ta runtse su ta kankame su gamgam hawaye na bubbuluwa ta gefe,
kirjinta na mugun bugawa, dogon hancinshi ya daura akan nata dogon hancin yadan jujjuyar da
kanshi hakan yasa hancin suka bugi juna, tsayawa yay batare daya raba fuskokin suba ya kafe
lips dinta da ido, ahankali ya gangaro da bakinshi ya daura akan lips dinta da sauri ta mayad
dasu ciki ta daure bakinta gamgam tana nishi kaman mai asma, murmushi yay ya saukar da
hannunshi daya yakai gefen cikinta dakeda lpy yamata chakulkule da sauri tasaki bakin zatai
ihu ya kamasu, wani irin kiss ya shiga mata tana mutsu mutsu iya karfin ta ta kwace bakinta
amma takasa kara janta jikinshi yay sosai ya saka hannun ya tunbuke ribon din data kama
gashin kanta dashi ya hargitsa mata gashin gabaki daya, sosai take kuka kaman zata mutu
saidai ba kara sabida bakinta daya kama, mirginowa yay yana kokarin juyawa dauke da ita
ajikinshi sukaji karan laptop bam yafadi akasa, karan yasa ta daddage ta fige bakinta dayake
neman katsawa da kyar tana mugun kuka shikuma ya juya da kyar ya kalli laptop dinshi dake
kan jikinshi daya fadi warwas akasa, dan sakinta yay batare daya cireta daga jikinshi ba ya mika
hannu daya kasa yana kokarin daukan laptop din yaduba dan akwai a whole lot of patient
records aciki, fizge jikinta tai wup da gudu tafita daga dakin tana haki ganin hularta ga gashin ta
duk abarbaje tai waje ahaka yasa ya mike tsaye da kyar yabita, tsaye yaganta tana falo tana
faman murda handle tana kokarin bude kofar yaki buduwa yana gab da isota tasamu tabude
tafice kafin tafita daga balcony din ya cimmata ihu tabude baki zatayi ya daura hannunshi akan
bakinta yana hararan ta tareda jawota jikinshi, tafashe da kuka duk jikinta na rawa ya kafeta da
ido, daidai lokacin Mami da tundazu suka dawo sai nemanta suke basu ganta ba ta tambayi yan
aiki sunce basu ganta ba hakan yasa hankalin ta yatashi tafara zagaye gidan, kaman ance ta
daga kai ta hangosu tsaye Ayaan na kokarin sakamata hula, da sauri ta juya Ayaan daya dago
kai ya ganta yace "gud afternoon Mami na" arude tafara kokarin fita daga jikinshi jin yana gaida
Mami, sakinta yay ta fizge hularta kanta akasa sabida kunya, dan juyowa Mami tai ta kallesu
sau daya kafin tacigaba da tafiya abinta tace "saukar yaushe, daughter kizo kiyi sallama da
Baaba" ta wuce abinta da sauri tabi bayan Mami tana saka hular duk arude, bin yanda take
tafiya yay da kallo kafin yay dan murmushin gefen baki ahankali yace "she has special lips, soft
skin, soft hand" dan tabe baki yayi kafin ya koma ciki ya dauko black shirt yakasa yafito yay
garden dan dubo monkey shi.
Saida ta tsaya ta gyra hularta tamaida gashin ta da kyau ciki kafin ta shiga bangaren kanta
akasa sabida wani irin kunya datake ji, babu kowa afalo hakan yasa tai stairs tafara hawa daidai
lokacin big Mummy itama tafito daga dakin Baaba rike da bowl din fruits da fork tanaci "sannu
da zuwa Mummy" wani irin faduwa gabanta yayi harsaida bowl din fruits din hanunta ya bare da
sauri Bilkisu ta tsugunna tana kokarin tattare fruits din tace "subhanallah" bayanta big Mummy
tabi da kallo ta rasa mesa duk idan taji muryar Bilkisu kokuma ta kalli fuskarta sai gabanta
yafadi, dan murmushi tayi ta dagota tace "ki barshi keda bakida lpy, wuce kitafi wurin Baabar ki
gatachan ta shirya" badan tasoba tatafi.
[7/20, 11:39 AM] +234 803 238 4602: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
44 - 45
Ahankali ta turo kofar, Baaba ce kadai tanata faman daddanna touching screen wayar da Abba
yasai mata tana ganinta ta ijiye tace "zonan tawaje na" harda dan gudun ta tafada kan Baaba
sai kuka, cikin kuka tace "Baaba dan Allah karki tafi ki barni, dan Allah mukoma gida tare
banason mutumin nan" girgiza mata kai Baaba tayi fuskarta ba alamun wasa tace "da auren
akan ki, ai auren kenan, kifara zama dashi kafin ki tantance ko bakison shi yaron me halaye na
gari haka, hakanan zaki daure kindaiga iyayen mijinki yanda suke sonki saiki bisu sau da kafa,
kima mijinki biyayya inya kiraki kije karna karajin kince bakison shi" nan ta shiga yimata wa'azi
mai shiga da ratsa jiki. Mami ce tashigo dakin da sallama tana murmushi ganin yanda Bilkisu ke
kuka ta kankame Baaba tace "wanan kuka haka daughter kiyakuri kinji bagamu nanba" tashi
Baaba tayi tana tureta tace "kinga sakeni nafara latti banison nai dare fa ahanya" tafita da sauri
dan batason tai kukan da takeji, tashi tayi Mami tarike mata hannu tafashe da wani kuka sosai,
hannu Mami tasa ta share mata hawayen tana murmushi tace "daughter nafa jaruma ce, dena
kukan zomuje mumata rakiya" hijabi ta dauka tasaka suka fita sai uban kuka take mara sauti
har waje, tsaye yake kusada Baaba sai magana suke wanda bata iyaji amma fuskarshi dauke
da lallausar murmushi, budema Baaba kofar bayan mota yayi da gudu taje ta kankame Baaba
tana wani irin kuka cirota Baaba tayi daga jikinta tana lallashi tanuna Ayyan dayay kaman bai
gantaba tace "baga mijinki nanba kikema mutane kuka, ke dalla rabu dani karna makeki" Mami
da Big Mum duk suka mata fatan alheri ancika boot da kayan atsaraba takaima yan zaria, ta
kalli Bilkisu data kasa daina kuka ta shafa kumatun ta tace "Allah bada zaman lpy ki rike abinda
nafada miki kinji" ta shiga motar da sauri tana boye kwallan daya zubo mata Ayaan yarufe
motar yanama driver alama yatafi, tanaji tana gani Baaba ta tafi abinta tabarta. Batare daya
sake kallonta ba yay wucewar shi wurin big Mum yace "big Mum yunwa nakeji" murmushi tai
cike dajin dadi tace "muje nabaka abinci my boy" sukai wucewar su sukabar Mami daketa
lallashin ta saida tai shiru sanan suka wuce part dinta.
Apalor suka zauna kanta akasa Mami ta kunna kallo tasa mata zee world tana janta da hira sai
asanan tadan saki jikinta ganin haka yasa Mami tai sama dan akwai kiran datake so tayi.
Kallonta take dudda rabin tunanin ta na gida, dan bawani gane kan film din takeba, yadade
tsaye abakin kofa kafin ya shigo dakin fuskarshi adaure yana tafiya cike da izza, kamshin dataji
yasa ta daga kai da sauri tana ganinshi ta mike tsaye da sauri zatai stairs da hannu ya
nunamata kujeran data tashi gabanta na faduwa takoma ta zauna, Apple yadauka dake kan
hadadden bowl asaman dining table sanan yadawo cikin falon shima akan kujeran ya zauna
yadau remote din da Mami ta ijiye mata akusa da ita ya chanza channel zuwa na wrestling kafin
ya kwanto ya daura kanshi kan cinyarta yana gutsuran apple din dake hanunshi yanaci, dudda
yanajin yanda jikinta ke rawa hakan bai hanashi gyara kwanciya da kyau ba yanacin apple
dinshi batare daya kalli fuskarta ba, stairs ta kalla dan ko kadan bataso Mami tazo ta gansu
ahaka sanan ta kalli fuskarshi ta fashe da kuka tana share kwalla ko kallonta baiyiba, ahankali
Mami ke saukowa daga stairs bayan tagama wayar datake yi da Ummu Haneef tsayawa tai
chak hango Ayaan yanda ya daura kanshi akan cinyar Balkisu yana kallo abinshi girgiza kai tayi
tajuya da sauri rashin kunyan Ayaan ya girmi tunanin ta wlh, bari baban shi yadawo yauyau
dinan zata bashi matar shi sutai gidansu.
Kallon agogon dakin tayi ganin karfe uku kuma tun kafin azahar take dakinshi bataga yay
sallaba yasa ahankali tace "anyi sallan azahar fa" sai a lokacin yadan birkito da kanshi ya
kalleta ya daure fuska tamau yace "ke nakema sallan dama?" girgiza kai tayi atsorace yace
"gud, to banga damar yiba nd u shut d f*ck up kona natsar dake" "daughter" daga sama Mami ta
kwalamata kira ahankali tace "na'am" sanan ta kalleshi ganin baida niyar dagata yasa ta daura
hannuwan ta akanshi ajiyar zuciya ya sauke wanda yasa ta tsorata ta janye hannuwan dan
tazaci dukanta zaiyi, jin Mami takara kiranta nabiyu yasa yadagata tareda lumshe ido da sauri
tamike tai sama da gudu yabita da kallo yana murmushin gefen baki, dakin Mami ta shiga da
sallama kanta akasa, cup Mami ta mika mata tace "shanye wanan ina zuwa" karba tayi Mami ta
tashi tafita daga dakin ahankali ta kafa cup din abaki ta shanye ta zauna akasa tana jiran
shigowan Mami, ba'a jimaba tadawo da dan babban bowl dauke da farfesun kaza dayaji magani
ajiye mata tayi tace "zoki cinye kafin ya huce" murmushi tayi dan wlh tanason kaza kafin
akunyace tazauna akan gadon data ijiye mata tafara ci ahankali Mami kuma nawaya har taci iya
cinta taji tai dam, Mami batare data yanke wayarba ta kalleta tace "idan ya isheki toki shanye
roman tass" gyadakai tayi ta shanye roman kafin ta mike tsaye tafita daga dan kai plate din
kitchen hada ido sukayi da sauri ta dauke kai ganin har lokacin wrestling yake kallo kenan
la'asar ma baiyiba wanan wani irin dan iskan mutum ne, astagafurullah tace ta shiga kitchen ta
ijiye kafin takoma sama dakinta ta shiga kasancewar bata salla yau tai zaman ta tana wasa da
wayarta.
Koda daddare bayan Abba yadawo da Mami tasame shi da maganan abama Ayaan matar shi
sutafi gida bakaramin murna da dadi yajiba, waya yadauka yakira Ayaan dake Part dinshi yazo
itakuma Mami takoma ta shirya Bilkisu cikin wani hadadden lapaya maroon sanan tahada mata
magunguna datace tadinga sha kullum kafin tarike ta takaita falon Abba, hadasu Abba yay
yamusu wa'azi sosai sanan yakara bama Ayaan amanar ta, big Mummy ma tamusu Mami ma
tamusu sanan suka rakosu har mota sai uban kuka take itadai yau tabanu Mamin datake gani
taji dadi ma yanzu tafiya zatayi ta barta kuma gidan wanan mutumun, a motar shi suka sakata
ya kunna motar yabar gidan yana murmushin keta. Ganin tana neman kashemai dodon kunne
da kuka yasa yawani irin taka burki