Showing 66001 words to 69000 words out of 124573 words
Chapter 23 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf
ido, maida handky yayi a aljihu sanan ya dawo da hannun
ya daura akan kumatun ta kafin yadaura forehead dinshi yahada da nata har numfashin su
nahadu wa murya chan ciki yace "ke look up" dago dara daran idanunta tayi ahankali ta sauke
su akan nashi wani irin kasala da gajiya ne yaji ya sauka akanshi, ahankali yafito da tongue
dinshi ya lashi lips dinta kafin yasake mannota ajikinshi sosai murya chan kasa yace "jekima big
Mum sallama am waiting for u" sakinta yayi tareda karban jakan hanunta yana kallon fuskar ta
jiki asanyaye ta juya tai bangaren Mami shikuma ya bude kofar mota ya shiga ya zauna yana
kokarin ciro wayarshi dake ringing.
Sallama tayi daga barander amma ba'a amsaba hakan yasa ta bude kofa ta shiga ciki babu
kowa akatafaren falon, hakan yasa tai stairs tafara takala matattakala jin alamun magana amma
kasa kasa, ahankali tai sallama agaban dakin big Mummy amma shiru hakan yasa ta tsaya tana
waige waige corridor din toko tana part din Mami ne? A'a Mami ai tace tai bakuwa, tuna
bakuwa yasa ta mike corridor din dan zuwa guest room da tun kafin takai takejin muryoyin su na
tashi kasa kasa suna hira harta daga hannu zatai knocking kofar saita tsaya sabida sunan
Ayaan dataji Big Mummy tafada so kawai take takarajin halin mugun nan da kyau saisa batai
knocking ba tai shiru tareda kara kafa kunne ajikin kofan.
Big Mummy tace "saisa nakiraki kizo sabida na aiwatar da plan dina, abubuwa da dama sun
faru bayan kin tafi nijar, kinsan ko lokacin nan da Alaji yatashi wai duka kamfanin shi zai maida
sunan Ayaan, manyan kamfani fa Munari, kina ganinshi haka yanada jirgin ruwan tsatso mai
daga ruwa, idan aka tsatso man chan kampanin shi dake calaba ake kaiwa suna sarrafa man
acire crude oil, acire kerosine, acire diesel, acire petrol, da sauran abubuwa kinsan kudin Alhaji
kuwa Munari? Mutumin dahar shugaban kasa yasan da zaman shi wanima shugaban kasa har
aksashen waje ma fa, shine yatashi wai zai mayar da komi sunan Ayaan zai bashi duka dukiyar,
hankalina yatashi nace wlh baza ai hakaba, idan Alhaji yamutu fa yanzu Firdausi da danta
Ayaan ne zasu kwashi kusan komi na gadon shi saidan kasona danni banda da, ai wlh bazai
yuba, shine bayan kwana biyu nacemai inada biki a kaduna inaso naje, yabarni harda min
kyauta banzame ko inaba sai gidan bokan da kikamin kwatance nan nace mai inaso ahaukata
yaron sanan bayan ya haukace akada shi yabar gidan bama gidan kadai ba yabar kano gabaki
daya ta yanda kinga idan yaron yabace ai bazai maida dukiyar sunanshi ba, sanan dazaran
Ayaan din ya haukacen zansan yanda zanyi da Alhaji kasheshi ba abu mai wuya bane, yariga
ya tsufa dama, mutuwa yau ko gobe, amma kinsan abinda Alhaji yayi kuwa? Dudda yabace
saida ya maida sunanshi hankalina yatashi sosai shikuma yaron bayan wata daya dayan
kwanaki sai gashi yadawo ya warke wanan yar iskan matar tashi damuka gani dazu damuka
shiga shashin Firdausi ubanta ne yamai addu'a ya warke, banda hakama yanzu yamai na tsari
kome namai baya kamashi wlh, amma yanzu na chanza plan gabaki daya saisa ma nace ki
shiryo kizo" dan dariya Munari tayi takara gyara zama akan katafaren kujeran datake kai, Big
Mum tace "zan tura su Bala sumini kidnapping dinshi nariga nasa lawyer na yamini pepopin
kuma na sato wasu documents din ownership of the company daga dakin Alaji, yanzu abinda
nakeso su Bala zansa sumin kidnapping dinshi jibi, kekuma zaki tafi chan gidan dazasu kaishi,
abu daya kawai nake bukata daga wurin shi shine signature, inhar yamini to duka dukiyar ta
dawo tawa daga nan zansa su Bala su kashe min shi shikuma Alaj..." kasa karashe maganan
tayi sabida karan fashewan abu dasuka ji arude duk suka mike tsyae big Mummy da gudu
tabude kofa mace tagani da hijabi tana sauka daga stairs da gudu hakan yasa itama tabi
bayanta, bigewa Bilkisu tayi da kujera hakan yasa tafadi da sauri ta mike sai a lokacin big
Mummy taga fuskarta tace "Bilkisu" kafin takarashe maganan Bilkisu tamike tafita daga dakin da
gudun ta tana fita tai mota ta bude binta yay da kallo yana waya ganin yanda take nishi ta
zazzaro ido, kunna mota yay da hannu daya yay horn aka bude musu suka fita atsorace ta rike
hanunshi da kyar tace "Ya Ayaan" hannu yanuna mata alamun yana zuwa yacigaba da magana
daga hospital ne wata patient tasami complications a surgery da ake mata shine yake fadinma
Dr Ibrahim abinda zaiyi.
Da gudu Munari tafito ta tara da Big Mummy turus agaban kofa ta dafe kai tace "waye ya jimu?"
cikeda bacin rai Big Mum tace "mayyar matar shice, ban wayana da sauri kafin ta batamin plan"
da sauri Munari ta koma sama Big Mum kuma takoma cikin falon tasaka hannu tadau glass
bowl din decoration dake kan center table ta buga shi akasa ya tarwatse, runtse ido tayi da karfi
ta sanya kafar haggun ta akai ta taka wani karami aiko ya yanketa saiga jini da sauri ta zauna
akan kujera tana runtse idon azaba, daidai lokacin Munari ta sauko daga kan bene tana ganin
jini tace "saratu kinada hankali kuwa" murmushi mai ciwo tamata tace "trust me i know wat am
doing" karban wayan tayi tai dailing number Ayaan har lokacin busy yake yana driving yana
magana da Dr Ibrahim sunma kusa gida, Bilkisu dukta damu yagama wayar sai kallonshi take,
saida suka shigo anguwan su sanan ya katse wayar ya ajiye akan cinyarshi yadan kalleta suka
hada ido kafin ya maida hankalinshi kan hanya yay murmushin gefen baki yace "ke kallon fa"
kaman zatai kuka tace "dazu danaj..." wayarshi tai ringing big Mummy daya gani a screen yasa
yace "1min" daukar wayar yayi daga tacan bangaren big Mummy tai wani irin murya tace "Boy
kana ina?" dan murmushi yayi yace "gani nan a anguwan mu bama mukarasa gidaba, missing
me already" yanda yay maganan yasa ta gane bai riga yasan komiba wani irin nishi tayi da sauri
yace "menene are u okay" Munari ta kanne ma ido hakan yasa Munari ta fizge Wayan cike da
tashin hankali Munari tace "Ayaan hawan jininta yatashi jiri ya dibeta ta fadi afalo yanzu hakama
kafarta jini yake ta taka katoton kwalba, she's seriously bleeding, ka ajiye matarka agida kazo
da wuri dan Allah" arude yace "okay okya, ki danne wajen try and stop d bleeding kafin nazo"
katse wayar yayi daidai yakawo kofar gida yay horn mai gadi ya bude ya shiga ciki adan rude ta
kallai tace "ina zaka i want to talk to you" fuskarta ya kalla saikuma ya matso yama lips dinta
kiss murya chan kasa yace "ina zuwa, sauka ki shiga gida big Mum bata da lpy" da sauri ta
girgiza mai kai, tsayawa yayi yana kallonta ganin zatamai kuka yasa yace "ke" a tsorace ta
sauka yatada motar yafita daga gidan, yana fita wayarshi takara ringing ya dauka Munari tace
"kataho kuwa yafaki tsayawa jinin" ahankali yace "nariga nataho inama hanya yanzu, idan
akwai ice a fridge ki dauko kisa" da sauri ta katse wayar ta kalli Big Mummy tace "yariga yabar
gida yafara zuwa" hannu Big Mummy tamika ta karbi wayar batare datama damu da kafarta da
ke jini ba, wani number mai suna Bala naga tai dailing ringing daya ya dauka, anatse tace "ka
kwashi boys dinka yanzu yariga yabar gidan kuje ku dauko yarinyar koma tayaya ne ku kaimin
ita warehouse, tariga tasan secret dina baniso ta tonamin asiri, idan kun daukotan karka kirani
kamini text" shiru tayi tana sauraron meyake cewa kafin ta katse wayar.
Tafi minti goma a wurin kafin tai cikin gida ahankali tana goge hawayen idonta, yanzu dama big
Mummy dake sonshi haka dama bason tsakani ga Allah bane, dama itace ta haukatar dashi
lallai duniya abin tsoro, dama anacewa makashinka yana tare dakai, kuma ma sabida dukiya
take son kashe shi dukiyar banza, to yanzu idan tafadamai ma zai yarda da ita, da tunane
tunanen nan takai dakinta ta shiga bayi tai wanka tafito ta shirya cikin rigan baccinta na
doguwar riga mai kauri tai addu'an bacci ta kwanta tanata tunane tunane toko tamai text?
Tunanin hakan yasa ta tashi zaune tsaki taja tunawa da jakarta dake dauke da wayarta na cikin
motar shi.
Da sauri ya shiga part din big Mummy rike da first aid box tana ganinshi tawani baje a kujera
tana nishi ga kafarta na didduga da jini kadan kadan Munari na fifitata. "subhanallah sorry Big
mum" kafarta ya dauka yay treating kafin ya mike tsaye yadan duko saitin kan big Mum din yace
"ina zuwa bari naje side dina na dauko abin auna BP" yana fadin haka yafita.
Har bacci yafara daukarta taji karan bude kofa sake shigewa tai cikin bargo tai lamo sosai
kaman tana bacci dan karya mata komi ko yazo, taku dataji daban daban sanan anata bude
kofofi yasa tadan bude ido dan wanan ba tafiyan mutum daya bane toko dai dawani yazo ne,
wani irin bugo kofar dakinta da akayi yasa takara bude ido atsorace, Maza ne guda biyar sanye
da bakaken kaya da bakake mask sun rurrufe fuskar su. "hasbunallahu wa ni'imal wakil" kawai
take maimaitawa ta runtse idonta da karfi dan gani take kaman mafarki take yanda suka
tsatsaya sun zagaye gadon suna kallonta da idanunsu tacikin mask, Babban cikinsu ne yawani
irin fizgo hanunta hakan yasa ta fasa wani irin uban ihu wani irin mari ya sakin mata abaki
batare dayace mata ko kala ba, aiko baki sai jini fashewa tayi da kuka tana tirjewa tace "dan
Allah ku sakeni wlh ni banda kudin baku amma kudau kome kukeso" wani irin finciko hanunta
dayayi saida hanunta yay kara yajata tana tirjewa yafita da ita daga dakin sauran hudun suka
rufa musu baya, ihu take sosai. "na shiga uku Ya Ayaan, Wayyo Allah Babana" tutturjewa take
yanajanta akasa hanunta yaja plate din dake kan center table din falon saman daidai sunkai
wurin stairs zai sauka yana janta ta daddage ta mike ta kifamai kwanon akan hanun daya riketa
dashi hakan yasa tai wuf zata koma daki daya daga cikin hudun da suke bayansu yasa kafa
yawani irin tokareta aciki da baya tayi luuuuu tawani irin mugun faduwa a stairs wani irin
wahalallen kara tayi kafin tafara tumble tumble tumble har takusa kai kasa sai kuma kanta yay
wani irin landing da buguwa a karfen stair case din, ko kara bude idonta batayi ba tasume
warwas sai jini dakebin kanta yana zuba a stairs din.
Daidai lokacin ya shigo part din big Mum rike da abin auna Bp dan yadade yana nema baisan
inda ya ijiye ba, wani irin faduwa gabanshi yayi da baisan lokacin daya saki abin auna BP
hanunshi ba yafadi akasa, daura hanunshi yay akan kirjinshi yay shiru, Big Mummy tadan dago
dakai ta kalleshi kaman mara lafiyan gaske tai magana ahankali tace "Boy lafiya zoka dubani
man" sake danne zuciyar shi dake bugawa sosai sanan ya kalli Big Mum, abu yaji yana
gangaro wa daga hancin shi ahankali ya kai hannu yataba yaga jini, da sauri big Mummy tace
"ur nose is bleeding boy" kirjinshi yakara tabawa dake bugawa sosai yace "Big Mum she's not
fine, i can sense it, my heart is telling me" da sauri ya juya yace "am coming" da saurin shi yafita
daga dakin Big mum na kiranshi ya shiga mota yay horn yafita daga gidan dawani irin
azababben gudu hancinshi na jini.
Dayan daya rikota ne tun farko ya fizgo wanda ya tokaretan sai a lokacin yay magana yace
"dan uwarka ance mutaba tane?" tureshi yay da karfi ya sauka suna biye dashi abaya, daukarta
yayi ya sabata akafada gatanan kaman mara rai kanta na diddiga da jini suka fita daga dakin ya
wurgata acikin bakar van din dasuka shigo da ita compound din, daya daga cikin su yay gudu
yaje yabude musu gate yana kallon mai gadin da har yanzu yake asume suna fita ya bisu ya
shiga motar sukabar anguwan da mugun gudu gate din gidan abude.
[7/25, 9:18 PM] 0mmer Farouk: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
61 - 62
Ko parking bai gama yi da kyau ba awaje yafito yana kallon gate din gidansu dako rufewa ba'ayi
da kyau ba, runtse idonshi yay da mugun karfi kirjinshi na wani irin bugawa kaman ba gobe, da
kyar ya iya daga kafan shi daya mugun yimai nauyi ya shiga ciki, da mai gadi yafara cin karo
azube kaman baya numfashi ga fuskarshi dukta kumbura sabida naushi, wani irin bugawa
kirjinshi yayi ya karasa ya tsugunna ya sauri yana duba pulse dinshi ganin he's still alive suma
ne kawai yasa yay reviving dinshi sanan da gudu yay cikin gida, jinin daya gani a stairs yasa
heart dinshi ke wani irin mugun racing da mugun gudu, yay sama yana kallon plate dake kasa
sanan ga dakunan su duk abude, dakinta ya shiga da gudu babu kowa, wani irin mugun
bugawa kirjinshi yayi kaman zai fashe da sauri yabude bayi ya shiga nan ma ba kowa, da gudu
yasake fita kaman mahaukaci ya shiga dakin shi da bayin shi bakowa yasake fitowa da gudu ya
shiga dayan dakin bakowa, yafito yay kitchen ba kowa ya shiga store bakowa, yafita yay garden
bakowa, dawowa falo yayi yana jujjuya wa yana kallon ko'ina amma bakowa, kanshi yawani irin
rike da hannu biyu kafin da bude baki da karfin bala'i yace "Bilkisssssss" yawani irin zube akasa
ya rirrike jikinshi dake wani irin mugun rawa kaman mai farfadiya, da gudu yafita yay inda mai
gadi yake arude ya dauko ruwa ya yayyafa mai hakan yasa yabude ido gabaki daya da sauri ya
dagoshi da idanunshi dasukai jarababen ja muryan shi har bata fita da kyau tsabagen bala'i
yace "me..me..meya...meya faru?" Mai gadin da biyu biyu yake gani da kyar yace "wasu
mutane su biyar sukazo amota sun rufe fuskokin su, suka dakeni sukai cikin gida daga nan
bankara saning meya faruba daga nan ba" Gabaki daya jikinshi rawa yake kokarin ma saita
yanda zuciyar shi ke bugawa yake sabida karya samu heart attack, da kyar ya mike tsaye yana
dafe zuciyar shi yana runtse ido kanshi na juyawa da kyar ya iya ya lalubo waya bama yagani
da kyau ya lalubo number Abba yakira ringing biyu Abba dake kan dadduma yagama shafa'i da
wuturi ya dauka yace "Boy" da kyar ya iya bude baki yace "p...pops kazo" zumbur Abba yamike
daga kan dadduma jin yanda muryar shi ke fita da kyar tana breaking, Mami dake kwance ta
bishi da kallon mamaki, arude yace "Boy are u okay, menene, talk to me Boy, u don't sound like
u, menene?" da kyar yace "Pops Bilkis, an, ban..ban ganta ba..an dauke..." tsabagen yanda
jikinshi ke rawa ma wayar tazame tafadi akasa ta tarwatse, Abba yace "boy, boy" kallon wayar
yay yaga ta yanke, Mami tace "menene ba yanzu nan yabar nan ba bayan yay treating kafar
hajiya baima tsaya ya auna BP taba fa haka Munari takece min" girgiza kai Abba yayi yace
"sako hijabi ki sameni akasa, Boy doesn't sound gud something is wrong" yana maganan yana
fita Mami tadau babbar hijabin ta saka ta bishi abaya, Big Mum suka gani tana dingisawa tana
zuwa sanye da hijabi hanunta rike da plate tana ganin Mami da Alhaji tace "ina zaku haka nida
nazo na debi fruits a fridge nawa ya kare" Mami tace "ga Alhaji nan shinake bi wai Ayaan ba
lpy" arude big mumy ta kalli Abba tace "meya sami Boy Alhaji? Mutafi mutafi mugano danmu"
gaba Abba yayi suna biye dashi Big Mum ta kalli Mami tace "kedai wlh Allah wadaran halinki
Ayaan baida lpy ne shine wai Ayaan" direba Abba yakira ya shiga duk suka shiga aka jasu sai
gidan Ayaan.
Yanayin parking motar Ayaan dasuka gani awajen yasa Abba yacema driver yay parking duk
suka sassauko Abba ne yafara shiga tsakar gidan ko lura damai gadi ma baiyi ba sai Ayaan
daya hango a tsugunne jikinshi nawani irin rawa uncontrollably, da sauri Abba yay kanshi yana
"Boy, Boy" dago shi Abba yay yay cupping fuskarshi, hanun Abba yakama gam gam yarike da
kyar ya bude baki yace "Pops where is mah wife?" hanunshi Abba yakama ganin kaman ma
baya hayyacin shi yay cikin gida dashi yana binshi luuu su Mami suka bisu abaya hankali tashi,
shikuma direba ya taimaka ma mai gadi ya shigar dashi dakinshi ya kwantar dashi yanamai
sannu.
Zaunar dashi Abba yayi yana kallon jinin daya ga a stairs bakinshi na furta "innalillahi wa
innalillahi raji'un" Big Mum tafashe da kuka sosai ya kalli Mami datai shiru tana kallon Ayaan da
jikinshi ke wani irin rawa hancinshi jini na zuba yace "ban ruwa Firdausi, mara sanyi" da sauri
Mami tai kitchen ta dauko goran ever mara sanyi ta bude ta mikamai Abba ya karba da hannu
daya dayan hanun nakan kafadar Ayaan yakai goran bakinshi yana tofamai addu'o'i, Kukan da
big Mum keyi yasa Abba ya dakama ta tsawa akule yace "ke kokimana addu'a kokiyi shiru"
yasama Ayaan goran abaki ya tsiyaya mai ruwan da kyar yasha sanan yadawo kusa dashi ya
zauna ya kwanto dashi yadaura kanshi akan cinyarshi yana kara tofamai addu'an ko jikinshi zai
dena rawan, kafin yaciro wayarshi daga aljihu number governor kano yakira gabaki daya,
ringing biyu gwamna da kanshi da dauka, Abba yamai explaning abinda ke faruwa.
Within 15 good minutes karan motocin police kakeji suna shigowa anguwa, ansace matar da tilo
ga Abdulrasheed Gwanaye ai dole gwamna dakanshi ya turo polisawan, tundaga waje CP
yafara saka team dinshi bincike wasu na interrogating mai gadi daya farfado kafin yazo da
kanshi har bakin kofa yay sallama Mami tabashi izinin shigowa shida wasu manya police guda
uku suka shigo ya tura biyu dake tareda shi sama bincike sanan ya zauna kusa da Abba dake
ma Ayaan dahar lokacin bai dawo daidaiba addu'a, saida Abba ya idar sanan ya nisa yace
"Alhaji naga akwai