Showing 36001 words to 39000 words out of 124573 words

Chapter 13 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

4023

lips dinshi alamun tai shiru hakan yasa ko tai shiru har yakarasa
kofar gidansu, aiko su Abba sukabi motar da kallo parking yay yafito da sauri ya zagayo ta inda
take ya bude mata daidai nan su Walawa dasuka zo wurinta suka fito daga gidansu, murmushi
both Abba da Baba harda Baba Sulaiman duk sukayi hankalin su yakara kwanciya ganin Ayaan
da Bilkisu tare. Fitowa tayi daidai lokacin su Walawa sun iso sai kallonshi suke atare suka
gaidashi "ango ina yini, ina kukaje kaida Amaryan tun dazu mukaxo fa" murmushin dole ya
kakalo ganin su Abba a wajen itakuma wucewa tai cikin gida abinta, su Walawa sai uban surutu
suke mai yana yake daga baya sukamai sallama rapper kudi yaciro yabasu suka karba sukamai
godiya kafin su koma cikin gidan.
Sai bayan azahar suka tafi bayan sun cika gidan da kayan abinci da kudi duk yanda malam
yaso yaki karba kin yarda Abba yayi yace ai yanzu anzama daya kafin su wuce kano
kowanensu rai fess.

**************
Tun tanama su Umma, Mama da Baaba kuku asaurareta ana lallabata har yazo kowa yafita
harkan ta to uban ma me zasu iya aure dai anriga an daura saidai kuma abisu da fatan alheri,
ganin babu mai sauraron ta danhar su Walawa sunfison Ayaan sunce mezatayi da Isyaka daya
wulakan tata ranan daurin aure yace bayaso, tama godema Allah yaro dan gayu yace yanayi,
hakadai ta tattara ta manta da alamarin tacigaba da zuwa school abinta ta dage da karatun
exam, Mami na yawan kiranta ganin haka yasa duk Friday saita turama Mami Friday message

mai dadi da ma'an hakan ko ba karamin faranta ran Mami yakeba.
Cikin iko na ubangiji ta fara zana jarabawan ta abinta sosai ta dage tana karatu ta manta zance
wani Ayaan da Isyaka, inbama su Walawa sun kirata da matar Ayaan ba wanda yanzu shine
sunanta har mantawa ma take ita matan aure ce, kumama wai Matar dan iskan nan maisa
sarka da dan kunne hmm.
Zaune yake akan daya daga cikin kujerun platinum table dake cikin club din wanda aka jerasu
mussam sabida mayan, non alcoholic wine mai sanyi waiter ya zubamai a glass cup
kasancewar sunsan shi bayashan alcohol, gefenshi wasu maza ne hadaddu guda biyu wanda
suke friends dinshi tare sukai school, daya daga cikin sune mai suna Fawaz yace "wai kai
bazaka je ka dubo matar kaba yanzu more than a month kenan da bikin ku da baka gayyace
muba" jan tsaki yayi tareda kara relaxing ajikin kujeran dayake kai yanabin wankan dake tashi a
club din na Drake, dariya su biyun sukayi banda shi daya wani lumshe ido dayan ne mai suna
Paul yace "yo wai tayaya ma wanda zai aureta kace yafasa awurin daurin auren, mekayi
Ayaan? I know u have something to do with him saying bazai aureta ba" sai a lokacin yadan yi
murmushi kadan kafin yawani tabe baki yana girgiza kai yace "nothing much, I just threaten d
poor guy, bayan nasa an kamomin shi na kusan harbinshi da bindiga ya tsorata harda kuka fa
wai bayason ya mutu yanzu he's just 25, yadan ban taudayi so saikuma na cikamai aljihu
shikenan" dariya sukahau yi dukan su Fawaz yace "shege mugun iche, ashedai kana son
yarinyar" da sauri ya kallesu kafin ya murtuke fuska yace "guys banson iskanci, ni" yanuna
kanshi yace "ni, ni, me fa, inso yarinyar nan wanan yar kauyen? God forbid, Allah ya kyauta,
she is not my type infact tamamin kadan as my woman, i did wat i did for Pops, u know he's old
yo, so banison abinda zaisa yay breaking down, i gats make d old man happy now" atare
samarin suka gyada kai suna "yeah hakane, we gats make our Pops happy kam" drinks
dukansu sukai sipping atare Fawaz ya kalleshi yace "wat about ur Meram?" kallonshi yadanyi
kafin ya maida mai da tambayar. "wat about her?" Fawaz yay yar dariya yace "i mean baka
sonta bazaka aureta ba ita? Me relationship din dake tsakanin ku dont u have feelings for her"
tabe baki yay yace "Gee, get this straight nifa aure ko soyayya bayama ajenda na, infact inda
baku tunamin da dat low life girl da Pops yahadani da itaba ninama manta inada wata so called
wife, and Meram, Meram" yakira sunan sau biyu yanadan rolling eyes dinshi saikuma ya tabe
baki yace "ina more rayuwana da ita ne kawai anytime am in d mood, babu komi tsakanina da
ita, she's just a girl dat love giving her self to me okay" dariya duka sukayi Fawaz yaciro
wayarshi yace "lemme call my babe nima" tabe baki yayi kafin ya mike yaje dance floor yafara
rawa abinshi yana sipping wine din glass cup din hanunshi.

Sai gurin sha biyu suka fito daga club din kowa yaja motar shi dan zuwa gida. Abangaren shi
yay parking yafito yana kwance belt din wandon shi ya bude kofa ya shiga daki, zaune yaga
Abba a kujera ga dukkan alamu shiyake jira, dan sosa kai yayi yamaido kofan ya rufo yazo kusa
da Abban daya kafeshi da ido dan murmushi yayi yace "Pops bakayi bacci ba" yay maganan
yana zama tareda daura kanshi akan kafadar Abba, sosai yay niyar mai masifa amma saiya
sassauta murya cikin lallashi yace "Boy lokaci yayi da u will stop clubbing, da nabarka ne sabida
inama kallon yaro but yanzu ai ka girma tunda ma har ka ijiye mata, ehen talking of mata wat do
you mean ne eh? More than a month yanzu bakasan kaje ka duba matar kaba, ina so gobe

goben nan ka shirya kaje" daure fuska yay tamau kaman zai fashe yace "zanje hospital gobe
akwai aikin da zanma wata" "karya kake" Abba yatari maganar shi afadace ya nunashi da yatsa
yace "wlh inhar baka tattara komi ka ijiye gefe ka wuce kadubo matar ka gobe ba saina saba
maka" ya kamo kunnenshi tareda daye dankunen diamond din daya makala da gum kara yayi.
"Pops zafiiii" ya dafe kunen kaman zaiyi kuka Abba ya cillar da dankunen yace "wlh karna kara
ganin ka dasu, wanan shegiyar sarkar ma kacire, kai ai ba mace bane" turo baki yay yace
"sarkan ma ai bana mata bane, baka gani bane Pops namaza ne fa" "I've said my own, first
thing tommorow morning kabar gidan nan kawuce kaje ka dubo matar ka, hakkin ta na kanka be
careful" Abba ya wuce yafita yana masifa.


Da gudu take tafiya danyau ko tsayawa karban waina batayi ba daga wurin Baaba, yaune take
rubuta last paper ta Civic education kuma karfe biyu ranane paper bacci tayi babu wanda ya
tasheta dan Mama da Umma sunje barka, biyu saura minti goma ta tashi hakan yasa ta zabura
tasaka kayan makaranta tafito tana kaiwa bakin titi tasami Bus ta shiga, abinka da bus sauke
dauka ba ita takai makaranta ba wuraren karfe biyu da rabi, sunayen Allah kawai take kira ta
shiga makarantar da gudu tai exam hall atsorace takai bakin class din ta tsaya yan aji sai
kallonta suke su Walawa dake rubutu suna mata alamu data shigo, kallon fuskar invigilator tayi
ganin baice karta shigo ba saima wani kallon wulakanci dayake mata irin na kinyi latti kinkuma
tsaya awaje dinan yasa ta kwasa da mugun sauri tai cikin hall din, tsayawa tasake yi dan tsoron
zuwa ta karbi booklet da question paper take ganin ya mikomata daga inda yake zaune yasa tai
inda yake da saurin ta, zuiiii tai wani irin mugun faduwa sakamakon bawan ayabar dake kasa
data taka wani irin mugun ihu tayi dan saida ajin duka ya dauka sakamakon faduwa datayi
gabaki daya ta saitin ciwonta, dan ciwonne ma yafara buga kasa kafin sauran ilahirin jikinta, da
sauri shi kanshi invigilator ya sauko daga kan kujera su Walawa ma haka duk aka zagaye ta,
Walawa tasamu ta damke da karfin bala'i cikin kuka tace "Walawa na bige ciwona uhm uhm
uhm" wani irin nishi take tana kuka sosai tama kasa magana, invigilator yace "ku kira principal
dinku" da gudu yan ajin aka fita aka kira principal koda tazo tuni Bilkisu tafice hayyacin ta sabida
azaba kuka kawai take da ihu, Keke napep principal tasa aka kira ta dubi dabilan ajin tace
"wayasan gidansu?" su Walawa ne suka daga hannu hakan yasa principal din tace "kuzo ku
maidata gida wurin iyayenta ku dawo yanzun nan sabida kuyi jarabawar ku" kokarin mikar da ita
ake ta kankame Walawa tana ihu "dan Allah dan Allah nace wlh inna tashi fashewa cikin nan
zaiyi" tana maganan tana kukkule ido kaman mai shirin suma, principal tace sudauketa, taruwa
sukayi suka dauketa suka saka a Keke Walawa da Aisha shehu suka bita sai gida.
[7/17, 12:04 PM] +234 814 359 8303: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

35 - 36

Yafi minti biyar da parking a kofar gidan nasu amma yaki fitowa saima kallon kofar gidan yake

daba kowa dan duk almajiran sun tafi bara, yana sanye da dark blue shadda da akamai aikin
hannu mai shrgen kyau, jumper ne rigar danshi ya tsani tazarce, kanshi ba hula saidai gashin
shi dayay lub lub dashi sai uban kamshi yake, tsaki yakara ja ya dunkule hannu ya daki iska
"f*ck! hanayinyar dayaji yasa yadan dago kai, yan mata biyu yagani da fararen hijabi da purple
dankwali da purple wando alamun yan makaranta ne sun tsaya gaban keke suna mika hannu
suna magana alamun da wani akeken dasuke ma magana, daya daga cikin su yaga ta juya ta
shiga gidan su da sauri chan sai gashi tafito da Baba yasa babban kaya kanshi da rawani irin ta
malamai, magana yaga Baba natayi baya iyaji sabida glass din motar arufe suke fararen hannu
yaga an miko daga keken wanda kumbunan hannun ke zagaye dajan lalli dayay jajir, hannun
Baba ya kama, ya kara daya ta bayan wuyan shi da kyar ta sakko da kafa daya kasa saikuma
ta kece dawani irin kuka da shida kanshi saida yaji daga motar, kamota Baba yayi hakan yasa
tafado jikinshi tama kasa mikewa da kyau tana neman yin kasa tana wani irin kuka da sauri su
Walawa suka taya Baba riketa dukansu, hankali tashe Baba ya rikota da taimakon su sukai cikin
gida tana mugun kuka, dan tabe baki yayi kafin yace "wats wrong with her?"


Shimfideta Baba yayi akan tabarman dake dakinshi sabida tsakar gida yajiku dan dazu anyi
yayyafi, Baaba dasu Umma suka zagayeta dan bama su dade da dawowa daga barka ba, ganin
yanda take ihu tana kuka yasa Malam ya tsugunna ya daga hijabin tareda rigar ya janye farar
shimin datasa ya kalli ciwon bugewan datayi yasa wurin yay ja sosai abunku dafara, mikewa
tsaye yay yakalli Mama yace "cire mata kayan nan iska yadan shigeta kotaji dadi, bari naje na
nemo taxi abakin hanya saimu kaita asibiti" to Mama tace jiki asanyaye ta tsugunna tana
kokarin maida hawayen dataji yana kokarin zubomata, cire hijabin da rigar tayi ta barta da farar
shimin kadai sai kuma wandon makaranta jikinta zata mike ta cafko hanunta tana kuka tace "ina
zaki Mama? Dan Allah ki rikeni, Umma, Baba" takirasu duk awahale, dan uban kukan datake
yasa ta galabaita, zuwa wajen Umma tayi ta rike, Baaba kuma dasu Raiyana duk suka tsaya
akanta suna mata addu'a.

Bude mota yay yafito sabida hango Malam dayayi yana shirin fitowa daga gida adan kunyace
ya dukar dakai ganin Baba na kallonshi dudda hankalinshi atashe yake hakan bai boye farin
cikin ganinshi dayayi ba, ahankali yace "ina yini Abba" murmushi Baba yayi yace "barka dazuwa
saukan yaushe? Yasu Alaji da kowa da kowa" ahankali yace "Alhamdulillah sunce agaishe ku"
girgiza kai Baba yayi yace "kaga ikon Allah yanzu hakafa fita zanyi nem mota ahanya, dan
matar takace ba lapiya yanzun nan daga wajen jarabawan tasu ce aka kawota ma, cha nayi
nasamo sai muzo akaita asibiti amma tunda kaga Allah yakawo ka ai sai kadubata" dan
murmushi yayi yace "meke damunta Abba?" ajiyar zuciya Baba yadan yi yace "wanan dai
matsalar cikin dana fada muku tanada shi, wai bawon ayaba ta taka a makaranta shine fa
tafadi, mu shiga ciki ka dubata" gaba Baba yayi yana biye dashi a tsakar gida har dakin nashi,
aiko tundaga zaure yakejin ihun nata tsaki yadanja wanda shi kadai zai iya jin karanta. Sallama
Baba yayi ya shiga dakin daidai lokacin ta kara kankame hannun su Mama kaman zata shide
tace "Mama Mama wlh zafin yakaru kaman wurin zai farke" dan leko dakai yayi tabayan Baba
ya kalleta kitson shiku ne akanta manya da kanana idan akai babba daga sai ayi karami siriri
guda daya, tsawon shikun har bayanta yakai jelar nata lilo sabida yanda take jujjuya kai, dan

makalen dan kunnene akunnenta ja, ya gangaro xuwa jikinta dake cikin farin shimi dayabi jikinta
gabaki daya saikuma purple wandon da farar safan makarantar dake kafarta, gashin gaban
kanta sunbi zufan datakeyi sun kwanta lub lub idanunta sunyi jajir danhar kumbura sunyi
tsabagen kuka, yanda ta kakkame su Mama tarike su kace a nakuda take, ganinshi yasa su
Mama duk suka mike tsaye a kunyace siriki yazo, dukar dakai yay ya gidansu suka amsa
sunamai barka da zuwa kafin duk su fita dakin su ka barta akan tabarman tana uban kuka,
karasawa inda take Baba yayi ya kalli Ayaan da har lokacin yake tsaye a inda yake kai akasa
yace "karaso ka dubata Ayaan" kara fashewa tai dawani sabon kuka jin sunan da Baba yakira,
ahankali ya tako yazo gefen Baba ya tsaya akaro nabiyu ya daga kai ya kalleta aiko suka hada
ido da sauri ya dauke kai, Baba yace "dubata ina zuwa" fashewa tayi da kuka sosai ta damke
babbar rigan Baba tana kuka tace "Baba ni bazai dubani ba nidai ka kaini asibiti Baba zafi
yakeminin sosai wlh" karban babbban rigan shi Baba yayi yace "kagamin shirme keda baki da
lpy kuma kice likita bazai dubaki ba" ya kalli Ayaan yace "karka biye mata dan Allah rakinta
yawa ne dashi wlh, yarinya ba dauriya ko kadan" Baba yay ficewar shi yana korafin halinta.
Ihu tayi da saida ya daura hanunshi akunne. "wayyo Allah na Baba dan Allah kadawo, cikina
Baba, mutuwa zanyi, wayyo Allah na na banu na" kukan ta taciagaba dayi tana jujjuga kai ta
daddaga hannayen ta sama tana yayyarfe su tsabagen raki, ahankali ya daga kai ya kafe
cikinta da ido dake a shafe ta shimi, ta gefen haggunne yaga shimin yadanyi tudu, dan matsawa
yay kusa da ita fuska adaure, duk uban kukan datake da zafin da cikin ke mata bai hanata
tattaro ragowan karfin daya ragemata ba ta matsa baya da sauri cikin kuka tace "mehaka
malam" wani irin wulakantattcen kallo yamata batare daya daga murya ba gudun kar ajisu yace
"ke banason rashin hankali" yakara matsawa kusa da ita matsawa tayi da sauri sai kuma tafasa
uban ihun dayasa ya bugi bakin ta yace "wlh kika karamin irin ihun nan saina fasa miki baki"
yana fadin haka yasa hannu akan shimin jikinta yana wani irin tabe fuska ya yaye shimin zuwa
sama hakan ya bayyanar da shafefen cikin ta fari, wajen ciwon ya dade yana kallo yanda wurin
ya kumbura yay ja kafin ya kalli fuskarta yanda take hawayen ba kakkautawa ga uban zufan da
goshin ta keyi sabida wahala, ahankali ya mika hannu zai taba wurin da sauri ta rike hanunshi
tafashe dawani irin kuka tana kokarin tashi zaune amma takasa ta kalleshi da rinannun idanunta
tareda kara cukwuikuye hanunshi cikin nata tace "dan Allah, dan Allah, karka taba wlh zafi
yakeyi inka taba mutuwa zanyi dan Allah" hanunshi yabi da kallo hakan yasa ta sakeshi
atsorace tana kuka, yabi hanun da kallo yanda zufan hanunta ya jikamai hannu kaman yasa
hannun aruwa, dan ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sanya dayar hanun nashi a aljihu yaciro
handky ya goge zufan sanan yakara maida hanun zai taba wurin cikin kuka sosai tafara kokarin
tare hanunshi kama hannayen nata yayi da hannu daya fuska adaure kafin yakai hannunshi
ahankali ya daura akan wurin, ihu tayi cikin kuka kirjinta na bugawa sosai, shiru yadanyi kaman
mai nazarin abu kafin ya gangaro da hanunshi kasan ciwon kadan ya danne da karfi, wani irin
ihu tayi da saida ta zaburo ta dago kanta ta daura akan fuskarshi dan yadan rankwafo sabida
akwance take, tsabagen azafa yasa tafara jujjuya fuskarta akanshi gabaki daya zuban datai
agoshi da hawayen ta sharemai su tass a fuskarshi tana kuka, cire hannun yay ya tureta da
karfi takoma ta kwanta tana kuka yace "wat d heck! Are u mad" tsaki yayi yamike tsaye yadau
handky yana share fuskarshi dashi, sanan yafita daga dakin rai abace. Ganin su Baba a tsakar
gidan yasa yadan kakalo murmushi, Baba yace "mecece matsala Ayaan?" dan dukar dakai yayi
sabida kunyar Abba dayakeji ahankali yace "Abba tun yaushe take ciwon nan?" karaf Baaba ta

chabe tace "yafi shekara biyu fa tafara har yazo yafara girma kullum inyafara saidai ai addu'a
abata" ahankali ya gyada kai yanadan tunani saikuma ya kalli Abba yace "ina ganin Appendix
ne, yay girma har ya rika haka, yanzu inaso zan tafi da ita asibitin danake aiki a kano zamuje ai
yan gwaje gwaje inhar shine to dole operation za'a mata acire tahuta" salati su Mama keyi
kaman wani baban abu, shi abin ma yaso bashi dariya yadan daure Baba ne ya nisa yace
"shikenan Ayaanu ai matar kace duk yanda kace hakan za'ayi Allah dai ya bata lpy, yasa kuma
muji alheri" Ameen duk sukace yadan kalli Mama yace "wazai bimu dan dole wani yabimu dazai
riketa amota ni ina tuki" Mama da Umma shiru sukayi ina zasu wani iya zuwa gidan surukai
hakan yasa Baaba tace "muje nabiku, bari naje nahado kayana" takalli Mama tace "hada mata
nata itama" da sauri yace "a'a tanada kayanta achan" murmushi kowa yayi, Baba yace "muje
waje sa fito da ita insun shirya" bin Baba yayi sukai waje, nan da nan Baaba taje tahado
kayanta karban jakan yayi yasaka mata a boot itakuma ta shige gida, ba'a jimaba suka fito
dauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login