Showing 18001 words to 21000 words out of 173505 words

Chapter 7 - SO NE DALILIN So Ko Sha'awa By Khadija bee bee

28 Aug 2026

424

uwa zuwa yakeyi yana rarrashinta amma banxa kwance tayi tanata kukanta...., kashe wayarta tayi domin batasan mezatace da Anwar idan yakirata..,domin yanacen yayi tafiya don nemo ixinin neman aurenta ga mahaifinshi...,gata 2hours kawai yarage ad'aura aurenta....,

Iman ansha kwalliya domin gidan kwalliya taje akayomata aburta..,don iya ynx baruwanta da yayartata sbd tafahimta wata mugunyar rayuwa gareta don haka gada ma tadinga 6atamata rai idan taganta hakan yasa tad'auki duk wani abu mai mahimci dazata nema takoma d'ayan d'akin da qawayenta..,acen suke firarsu da hidimar buki domin idan ka wulga bazakaga amaryarba ita kake gani..,hakan yasa duk wanda yasan farha sai yad'auka Iman d'in itace amarya tayi kyau sosai gata yarinya mai qananan shekaru duka Iman iyakarta 18years ynx sbd ynx taqare secondry school bata wuceba dama bari akayi aqare bukin yayar tata sannan saita wuce....

★★★★★

Abdl-jabbar yadamu domin shi tunaninshi har yaqare wlhy ace farha zai aura kuma bayan yasan bata sonshi....,anya babah baijaman musibaba tunda har yasan batasonshi kuma yakeso ya aureta...,bayan auren anasone ayimashi don yasamu lfy...,domin shi yasan tabbas aure yana cikin wata hanya tasamun lfyrshi domin ciwon cikin dayakeyi bana wasabane...sai ga son abunda bayasonshi kuma ya maqale a zuciyarshi.,wanda ya haddasamashi fitina gashi yana fama dashi....,Hakan yasa duk yatuno yaune d'aurin auren nasu sai gabanshi yafad'i sannan yakira Allah yashaidamashi...
"ya allah kasanyaman sanyi a cikin xuciyata da farha domin nasan idan aka d'aura auren inba wani ikon Allah ba itace ajalina ...,amma nasan cewa babah bazaiyiman abunda zai cutanba...,may b yaga abunda hakan zai zamo...,tunda nags umma taje gurinsa amma bataceman komaiba ...allah gani gareka kawai..,gardama ba tawabace...."
Hakan jabbar yawuni da xullumi domin macce ke zullumin aure amma shi ke zullumi bakomai yajamai hakan ba...., *SO NE DALILIN FARUWAR HAKAN* da ace farko bai kamu dasontaba da hakan duk bata faru dashiba...,gashi yanada masoya amma duka ya ture saidai farha d'in gashi ta bad'a mashi toka a ido...,ana neman manage dashi..,kamarshi jarumin namiji yazamo lusari...,a haka abokanshi suka tarar komai baiyiba gashi har anfara taruwa...,abokanshine wayanda sukayi school d'aya dawayanda suke gurin aiki guda motocine naji da fad'i gashi duka abokan nashi kowannesu daga yayan manya sai masuji dakansu...,amma haka sukeji da jabbar sbd qoqarinshi....,gashi sun had'a gagarumin party aftr ankai amarya bayan gudumuwar dasuka bada....,

Wannan tunanin kad'ai yasaka jabbar daburcewa domin ganin yakeyi asirinshi zai tonu ga qawayenshi domin yasan farha bazatajeba...,kuma koh taje bazatayi yadda akasoba...,amma bari yaga yadda za'ayi...,may b zaiyi qarya kawai a fasa partyn.,,da hakan yashirya shap shap...,bashir kawai ke ta'buka masa aikin saka kaya amma shi kad'ai yasan yadda yakeji..,kwatakwata babu farinciki a zuciyarshi koh kad'an...bashir kecemasa....

"Jabbar kanatsu kayi abunda ke gabanka...,totally damuwa ba taka bace farha dai yau takace kuma da yaddar Allah data shigo hannunka dole tayi relax domin sai yadda kaso zatayi...,fatana shine kawai kasaki jiki ayi komai yadda muke zuwa na sauran insha'allah bazamuji kunyaba....passed kawai muje kaji...."

Suka shirya kamar babu abunda ke damunshi yayi kyau iya matuqa..,yafito a Abdl-jabbar d'inshi domin jabbar akwai kyau na haqiqa ga kamala..,amma al-amarin farha na neman hallakashi...., amma ynx tawakkali yafara nutsoshi...

Yashiga motar dasuka tanadar mashi don shiga domin harda kwalliya sukayimata..,sukayi gurin d'aurin aure...,

Ma'aikatar baban farha d'in cen d'aura auren domin mutane ne naji da fad'i kasancewar ynx mahaifinfin nasu yasamu faraga koh mai yanadashi arziqi na shigoshi tako ina...,hakan yasa manyan mutane sun halarci d'aurin auren....

Ummar jabbar taga nawar ad'aura auren domin tasamu taji waye alhj. Yahad'a tillon d'anta dashi wanda shine qinshiqinta naduniya...,zaune take cikin mutane ana hidima amma wlhy kap hankalinta nacen...,sai duba agogo takeyi....,

Gidansu farha kuwa komai na gudana yadda yakamata kasancewar ba nan ake d'aura aurenba shiyassa gidan yasamu fili..., farha dai ta rufe kanta d'aki d'aya sai darzar kuka takeyi takashe wayarta domin batasan mezatacema Anwar d'intaba domin bata cikika alqawalinsuba....;

Iman da qawayenta sai kai kawo takeyi gurin auren yayarta qwalli d'aya...,wadda tafi so duniya saidai ita 'yayar batasan haka ba..., cikin qawayenta take suna shanawa...,sai janta sukeyi da ace yaune ranar aurenta dasuga rashin .m. ...,gashidai auren yayarta sai wani kicifi takeyi...,

Takwashe da dariya ta miqe tsaye..., tayi bala'in kyau..,domin Iman sak komai na kalar halitta anyumata mai kyau..,gata yr 18 years amma yarinyar komai yazauna daram jikinta...,taqara juya manyan idanunta da qaramin bakinta domin suffarsu d'aya da farha saidai farha farace swal...Iman batakai farintaba...,saidai mutane dayawa sunason rayuwar iman domin ita yarinyace mai hankali da natsuwa hakan ta doke yr uwar tata..,kowa Iman kowa Iman dai.... Ga ban dariya da sangarta...,komai zatayi dole kadara...

Tajuyama k'awayenta idanu da baki tace.....

"Kubari ni wlhy naga nawar a kawar da 'ya'ya nima nafara qara'i domin sahibinah ISHAM yana nan yana jiran abashi qofa yashigo...,kinsan mutuwa akeyi nafison najini tsundum gidan aure sannan nawuce shegen karatunnan..., wlhy ke aure nakeso..,banason nadad'e a waje ina soyayya duk da inason luv kamar ruwan cikina amma nafison naji ina gabatar dashi free ba practical b..,shiyassa inason luv amma banyarda da'bata lkchna ba ga soyayyar friendship ta school domin zan 'bata lkchna ni mai digree nakeyi...,ehe..."

Suka kwashe da dariya..., domin dama sunsan Iman hakan take saidai inba acikin qawayentaba bazaka ta'ba cewa tana maganaba....,

"Dama ai ke tadabance iman rayuwarki tayi ALLAH yanunamana namu baki d'aya kuma ALLAH yashiryaki kibar shaid'anar 'boye...,mu ki ishemu da aure kikeso su mamah sudinga d'aukarki saliha...."
Fad'in babbar aminiyarta wato RUMAISAH kenan...,

Iman tajuya mazaunanta tace "ameen inda gsk kikeyi Allah yasa next year ayiman aure😝....,kisha mamakin Iman don nan take zan kawo maku beautiful son or girl...."

Suka rufe baki Iman ta girmi sanin su...,idan bakasan halintaba akacemaka Iman tasan soyayya zakace qaryane...,amma Iman nada saurayi wato ISHAM.., Sunyi 4 month tare gurin bukin qawarta suka fara had'uwa..,kasancewarshi d'an limamin masallacin garinsu gakuma ilmi yasa Iman tayarda da soyayyarshi..,wanda kowa baisaniba bari tayi ayi auren 'ya'yar tatah sannan ta fitar dashi....

Rashin qaunar auren da farha batayi koh RASHEEDA qawarta batasan da yaune d'aurin aurentaba bale wasu ma su sani...,hakadai yau taji tanason taga aminiyyar tata domin 1 week basuyi wayaba kuma sun dad'e basu had'uba...,
Rasheeda tasanar da mahaifiyarta tabata izini tad'auki makullin motarta sai gidansu farha....,anan tatarar da taron mutane...,amma bataji komaiba tashiga gidan...,shigarta gidan taci karo d Iman.....,dagudu tarugo ta rungumeta...,

"Allah sarki 'ya'ya Rasheeda ynx nake cewa nakiraki don Allah kixo..,kinga wayata a hannuna ma...,domin tunda naganki nasan cewa 'ya'ya farha bata kirakiba.., yaune d'aurin aurenta da brox jabbar amma wlhy ko wanka taqi yi..,kuma ta kulle kanta a d'aki batason kowa ya ganta kuka kawai takeyi kuma takashe wayoyinta...."

"Hmm no wonder nanemeta narasa...,dama jabbar ne bataso..? Lallai farha batada hankali..,wazaiqi namuji kamar jabbar yaso banza...., muje nunaman d'akin datake ciki....."

Suka miqi Hanya dazuwa...,Iman ta qwanqwasa ki bud'e babah na nemanki....,jin haka kamar gada tabud'e amma kuma sai ta bud'e koh din tayima Iman masifa akan me take damunta....,bud'ewar dazatayi bataga iman ba sai Rasheeda tsaye...,hakan rasheedan ta shigo ta dubi idanun farha sunyi jawur duk sunfito sbd kuka...,bale abu ga mutun fari..,taqara kallonta tace....

"Wlhy Farha ban ta'ba sanin bakida hankakiba sai yau ban ta'ba tunanin zaki maida rayuwarki ba bakin komaiba...,kisani Anwar bazai aurekiba.., idan kuwa ya aureki to tabbas bazaki mori komaiba sai halaka da danasani...,dama ashe jabbar ne aka baki kikaqi fad'aman..? Kisani Jabbar yafi Anwar komai don wllhy dazai barki ya aureni ni inasonsa so na haqiqa domin duk maccen da tasameshi tasamu namiji..,domin tako ina yayi...,ynx hakan da maganar nazo maki...,tunda naganeshi naji kince yayankune duka lissafina yaqare.., domin nakamu da sonshi...,inada wanda aka tsayarman amma ganin jabbar hankalinshi da natsuwarshi sun jani..,uwa uba ga kyau...,kisani jabbar shi yakamace ki aure ba ganin dukiya ta rud'ekiba farha...."

Tadafata taduqa qasan da take zaune tace...,ki fahimceni wlhy bansan yaune ranar aurenkiba...,kuma nafison jabbar ya aureki domin nasan ban fad'iba kuma nafison hakan..,Anwar koh kad'an bai dace dakeba...."

Duban rasheeda tayi da jajayen idanunta tace....,

"Idan ke yayimaki toh ni baiyimanba...,sonshi ne kawai at baniyi...,yau da iyayenah zasuji sud'aura aurennan da ke danayi farinciki...,don zanfi ganinshi da mutunci na mutuntashi a matsayin 'ya'ya amma duka basu gane kukanah ba ala dole shine zan aura.., wlhy bazai samu kulawar mata agareniba..,har yagaji yasakan......"

"Subhanallh...! Tabbas Anwar bai barki hakanba domin kinfad'a tarkon yaudararshi Allah yafito dake kawai...."
Tasaketa ta miqe tad'auki makullin motar ta takama hanyar fita tajuyo tace.....

"Na fahimci azaki ta'ba gane menake cewaba don haka ni zan tafi Idan hankalinki yadawo bayan ankaiki gidan jabbar zan dawo naqara baki shawara duk da bakiso nabaki shawaraba..."

Kuka farha taqara bud'ewa kamar ranta zai fita..,tariqo Rasheeda alamar gada tatafi...,hakan yasa rasheeda jin tausayin aminiyyarta tadawo tazauna...,domin tasan sharrin zuciyane kuma so sone...,amma wanda farha keso cutane gareta...,kuka farhar keyi tana fad'in......

"'Daurin aurena akatafi da mutumen da baniso badon yayiman komaiba nabani ni fatima...."

Jin gud'a natashi babban parlonsu da yaya mai yawa hakan ya tabbatar and'aura auren..., qara farha tasaki...

"Nabani..! nabani..! Ni fatima shikenan....."

"Baki baniba domin burinki ya cika..., Allah yabawa jabbar auren wadda zatayi biyayya ga iyayenta....,wato mahaifinki ya d'aura auren Iman da Jabbar...,ke kuma kizauna ga gidannan ki tsinci uwar datafi maki auren jabbar....,insha'allah Iman zata zama silar farincikinmu kuma kinyiwa kanki duk burin mahaifinki akanki ya rushe yakoma kan 'yar uwarki....."

Dum Dumm! Gaban farha yafad'i saida tamiqe tsaye..., mahaifiyarta nafad'amata hakan sai wani tunani yazo mata...,amma tarasa menene...,burinta ya cika saidai tunaninta bai ta'bata za'a auramashi Iman ba...,koma menenene burinta yacika dai..., Allah raka taki gona inji farha p....,tanemi hawaye tarasa ga farinciki gabanta na fad'uwa kuma koma meye dai oho......

Rasheeda tace...,
" kinyiwa kanki wlhy..,ni hakanma yayiman dad'i dole naga qanwata domin nasan lbrn hakan yazomata a birkice...,duk da nasan ita mai d'aukar qaddarace amma zan ganta domin ita najin shawara..,kuma dani za'a qarasa bukin insh'allah yau....."

Tafita tabar d'akin...,farha kuma wayarta takunnah..,tafad'a gado tana murna.....


Tunda lbrn d'aurin auren yarisqi Iman sai ta dskare guri d'aya..,dagudu tafad'a d'akin mahaifiyarta tana kuka mai tsanani...,tanacewa....

"Mamah kunsan dai bani brox kesoba kuma kalmar so bata ta'ba shiga tsakaninmuba yazamuyi zaman aure a hakan...,? Mamah burinah na auri wanda kesona ina sonshi...,jabbar kuma da ciwon son 'ya'ya ne zuciyarshi yaushe nawa son zai shiga....?"

Kuka takeyi mai tsanani wanda saida mamar itama tayi qwalla kad'an...,ta riqa Iman d'in....

"sanin cewa zaki iya abunda mukaso yasa muka juyar da buqatarmu gareki kuma munsan zaki samu farinciki Iman..., ynx hakan mahaifinki ke yakeson gani zakuyi magana dashi...,Allah yayimaki albarka..."

Tace "ameen mamah.."

Tasharemata hawaye tace.....,
"muje na wanke maki fuska muje gurin mahaifinki...."

Koh wanne lungun firar wannan d'aurin akeyi...,kowa da abunda yake cewa.....

★★★★
_Nimadai da abunda nace....,domin akwai Chase's gaba....,_
_Kudai kubiyo bee beenku kusha lbrn hakan..,muje zuwadai...,kowa ya ware qafa yasha zam🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀_😝😝


~Ummul Ilham~
*Bee Been masoya*💞
[1/11, 10:48 PM] Bee Been💞 Masoya: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧


©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋

★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★

*_KYAUTAR ZUCIYATA❤ GADUK WANI MAI KARANTA ..,💧SO NE DALILIN HAWAYENAH😭💧.....,INAJINKU IRIN BA KA'DAN'DINNANBA💋....._*

Page...
★1⃣3⃣★

® Farha bud'e wayarta tayi domin ynx free take...,aure kuma alhmdllh tunda ba a d'aura da itaba....koma meye dai ita burinta zai cika...me akeyi da auren cima kwance komai sai iyayenta sunyimata..,shi ayimashi..,yaushe zasuyi nasu nakansu.? Dama Iman ne dai2 shi itada take yarinya baxata gane komaiba...,iya soyayyarshi koh rashin iyawarshi.....,

Da haka fara dilling wayar sahibinta anwar kenan... Bugu ukku sannan ya d'auka...,kalmar da yafara da ita itace.....

"I missing u my... Inata kiran wayarki kashe 6days kenan tunda nayi roaming d'in layina dana sauka jidda kece kawai nafara nema amma shiru....,toh ya meke faruwa ne.....? Duk narasa yazanyi wlhy...."

"Hmmm dear bari dakyar nasha...,wlhy saura kad'an na kufcemaka..,amma nayi yaqin da kowa saida yagane cewa...,abunda za'ayiman b alkhairi bane...ynx dai we're free fa....naqare nawa aiki saura naka.....domin da ance kafito kawai ready kake..."

Tafad'amasa duka abunda yafaru....

"Nima ina nan ina fama da dady nah...,wai banida hankali aure ynx...,shi bai tashi yiman aureba...,nafad'amasa wlhy na isa aure domin a halin ynx komai nasani amma koh kulani baiyiba...,amma momy nah na nan na matsamashi....,nasan sonda takeyiman dole tayi yaqin nemaman yardarshi...,don wlhy idan ban aurekiba wlhy bazan iya auren wataba domin ke kad'ai nayyiman acikin mata vazan bari ki ku'bucemanba....,bazan dawoba sai dady ya yarda...."

Wani sanyi yaratsa zuciyarta domin tasan cewa batayi wahalar banxaba...,tanada madogara kuma tanada wanda takeso...,kuma iyayenta xasuyi mamakin yadda farha zata koma idan taji kud'd'i🙄.....
Tohhh🤔 inji bee bee....

Sukayi sallama da yr soyayyarsu dasuka saba wadda saida farha ta manta da wani baqinciki....

★★★★★

Iman zaune gaban mahaifinta tareda mahaifiyarta...,yayi murmushi tareda...dubanta domin yasan basuyima iman adalciba amma yasan itakad'aice mai sharemasu hawaye kuma ita kad'aice zata gane me suke nufi dasukayimata haka...,ta d'uqe jikin mahaifiyarta sai kuka takeyi domin batasan yaya jabbar zai d'auketaba...,sbd ba ita bace burin ranshi...,kuma tasan tadda yakeson yr uwarta kamar ya mutu..,wanda ciwon da yakeyi *sonta ne dalilin shi* toh yanata sonzai zauna....?
Baban yakira sunanta.....

"Khadijatul iman..! Kafin nace komai inason nabaki haquri akan abunda mukayimaki batareda ixininkiba....,nayi hakan ne domin nasan ke mai biyayyace kuma ke zaki share hawayena kisakani farincikin da banyi zaton zan rasashiba....,yr uwarki ta6atamana rai iya matuqa kuma banason alqawalin da na d'aukarwa mahaifin jabbar na had'a xuri'ata da tashi yazamo bancikashiba ...,inada inda zan nemama jabbar mata amma jinina nakeso nagani tare danashi...,gakan yasa na yanke hukuncin had'aki aure dashi domin nasan ba halinki d'ayaba dana yr uwarki....,inason kidanne komai dake ranki kishare hawayenah Iman kiyi qoqarin mantar da jabbar wani qunci na rayuwa.....,daga tym d'innan inason kisaki jiki kiyi hanquri duk wata hidima dayakamata ace yr uwarki zatayi yadawo kanki gudun gada asamu mtsl...,ynx duk wani abu damukayi dominta yadawo nakine....,kuma mamarku zata ganki gameda komai akan aure domin nasan ke yarinyace bazaki fahimci komaiba tunda koh jami'a baki kaiba...,kuma karatunki zai cigaba insha'allah zakiji dad'in wannan biyayya iman....,ynx zankira jabbar d'in zan shaidamashi duk abunda kema nashaidamaki sai kucigaba da hidimarku dazakuyi....,Allah yayimaku albarka dukanku......"

Mamah ta amsa "ameen.. Kuma ni nasan fargabarta bai wuce tsoron ba itace yafara soba...,toh wannan abune mai sauqi indai inada rayuwa...,kuma nasan iman d'inama ai zata fahimci wani abun..."

Baban yayi dariya itama mamar....,Iman kuma duqe kawai take...,amma itafa har ynx akwai shakku zuciyarta...,auren huce takaici akanta....,yau tabani itada taso ace soyayya ta 'barza kafin tayi aure...,duk da batasan shin me soyayyar kebadawaba...,domin had'uwarta da ISHAM bai dad'eba....,ynx wai ita yau za a kaita gurin wanda koh inasonki ta aure bata had'asuba...,amma wai zama na har abada...,bayarda ta iya dole tayima iyayenta biyayya tabawa marad'a kunya domin tafitar dasu kunya.....

'Daga fuskarta tayi tadubi mahaifinta tace.....

"Baba Allah yabani ikon yimaku biyayya...,saidai fargabata itace brox jabbar bani yakesoba...,kuma bai ta6a furta kalmarso ta aure tsakaninmuba saidai ta d'aukar k'anwa dayakeyiman toh gashi kuma ni bansan yazanyiba har yasoni ... Kutayani addu'a domin bana burin zama da son maso wani....,Allah yabani ikon haqurin zaman dashi....."

"Iman gada kiji komai...,amintarki ta zama matarshi bata razanakiba...,bale karkato hankalinshi....,kedai kawai ALLAH yayimaki albarka..,kisaki jikinki ayi komai a gama kinji.....?"

Haka koh akayi...,suka fito zuwa d'akin mama....,mamar tasa aka kiramata mai kwalliya tasake yimata aftr tayi sallah taroqi alkhairin hakan....
Aka d'auko kayan da akayi domin farha ..,sune iman tasaka domin za'ayi walima....,buki yadawo sabo domin wlhy ynx akeyin buki....,iman tazuba mugun kyau wanda sai ka santa zaka ganeta....,

Jabbar gaban babah...,shima duk abunda yacema iman haka yacemai....saidai yaqara dacewa...

"Jabbar Iman yarinyace kuma wadda akayima abunda batasan dashiba...,nayi haka domin banason alqawalin da nad'aukarwa mahaifinka da farha...,rashin taqi aminta da hakan yasa naga yakamata nayi hakan...kuma zakaji dad'in hakan danayimaka jabbar..."

Murmushi yayi yadubi baban yace....

"Babah wlhy nima naji dad'in hakan domin ina fargaban farha d'in amma ynx hakan yayiman dad'i...,saidai atayani addu'a kawai....,

" insha allah jabbar...,kasaki jikinka domin nasan Iman batada mtsl zaka yaba danamu za'bin..,kuma ina tare dakai komai zaizo normal....kuma kyautar danayi niyya zuwa gareka daren aurenka itace nasayamaka mota kuma da ita xa'a d'auki iman domin kaita gidanka...."

Godiya jabbar yayi harda hawaye...,wanda baban yaji baiso hakanba...domin yad'aukeshi tamkar d'anda ya haifa...,domin shima mahaifinshi yasoshi har yayimashi gata hakan ba komaibane.....

Ahaka suka rabu murna kamar yafad'o sama aji....,dasauri yafita har abokan wasan su Iman na janshi amma bai kulasuba.....,motar bashir ya bud'e yashiga...

"Aboki dad'i bisa dad'i fa....,aqaramani amarya ynx....,domin kuwa baban Iman yabani mota da ita za'a kawota anjima....,amma kasan akwai qalubale gabana koh...? Domin wlhy har ynx banji zan iya d'aukar iman a matar aureba....,sbd yarinyace....,nasan bazata iya d'aukarjarabataba wlhy kasan waye ni pa..., iman yarinyace domin bazata iya kawar da abunda ni zanzo dashiba....,kasan koh likita baikaika sanin mtsltaba....,tausayinta nakeji...,hakan yasa ban ta'ba sha'awar auren yarinyaba wadda batakai ishirinba...,shiyasa naso farha amma sai taqini...,gashi anyiman auren huce takaici.....,saidai Iman bazata iya d'aukataba zan halakata kawai..,domin ni herone wlhy duk maccen dana riqa saitaji jiki....Iman bazan iya yimata komaiba domin tausanta nakeji....."

"Heee aboki kafad'o wlhy domin ni ai nafison yr sha ukku idan zan samu...,karantar da ita kawai zanyi wlhy tasan komai ta warkar dani...,ai kasani yaran dabasu san komaiba sunfi d'ad'in harka....,kasama ranka iman komai zata iya wlhy har tafi yn 25 sanin komai...,kadai zanyima uzuri domin ba itace frst luv d'inkaba amma ku zauna zanga gid'imewa nangaba kad'an....."

"Hmm ana gabas kana yamma...,wannan pa qwailace sosai don koh qarasa kayan harkar batayiba wlhy...,18 years gareta p wannan ai sai takai 20 koh za'a gane komai....kaidai muyita sirri domin gada aji kunya wlhy..,anjima idan ankaita akwai party dasu Ahmad suka shirya koh ga zamu kwashe....?"

Dariya basheer ya'aza mashi kawai...har da bugun sitarin motar....

"Bashir banson wulaqanci katayar da motar muje nasan Umma taga nawar taganan naji nata jawabin kuma...."

Yatayar da motar suka tafi dariya kawai yake yimashi...,domin mamaki jabbar ke bashi...,wai 18years ne qwaila.....😂


✍🏻
*Bee Been masoya*💞
[1/12, 10:10 AM] Bee Been💞 Masoya: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧


©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋

★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★

*_REAL PURE MOMENT WRITTERS✍🏻....,HAPPY ONE YEAR ANNIVERSARY🎂🎂🎂🎂🎂...,ALLAH YAQARA 'DAUKAKU_*❤❤❤❤❤❤❤❤
*_BEE BEEN MASOYA💞 NATAYA ALL MEMBERS NAMU MURNA...,HOPE MORE YEARS IN HAPPINESS...._*
UP
UP
UP
*© REAL PURE MOMENT OF LYF WRITTERS*✍🏻

Page...
★1⃣4⃣★


® Shigarshi harabar gidan sai dangin mahaifinshi da mahaifiyarshi suka taso sunatayimai tsiya....,domin har ynx bakowa ke gane cewa ba IMAN ba itace FARHA ba...,gud'a suke rangad'amashi..,wanda hakan yasanyashi jin wani farinciki...,domin gad'azun fargabar dake zuciyarshi tawuce misali...,amma ynz komai da sauqi..,domin yasan ba za'aji kunyaba...,saidai qawayenshi zasuyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login