Showing 99001 words to 102000 words out of 173505 words
Chapter 34 - SO NE DALILIN So Ko Sha'awa By Khadija bee bee
Farha hanya takama ta waje, sannan ta share hawayenta da suka zubo mata a ido kad'an, shima bayanta yabi, sannan ya bud'e motar ya shiga.
Tafi 5mnt kafin ta shiga motar, sai da taji dama ta mik'amasa Ikram itakuma tashiga napape, amma sanin zata musgunama ikram idan tatashi bata gantaba zatayi kuka, hakan yasa tashiga motar tana share hawayen bak'in ciki wanda batasan ya zatayi maganinshi ba, a yanzu.
Isowarsu gida, farha koh d'akin umma bata shigaba domin tarin damuwar datake ciki, kuma wadda ta manta da ita tun bayan wasu lokutta, amma a yanzu dole ta kawar da ita ta hanyar yafe ikram a rayuwarta, idan dai akan ikram ne? Toh yau zatayi yak'i da zuciyarta akan abun dake ganin shine dai-dai da kwanciyar hankali a zuciyarta insha'allah.
Umma shigowar Abdul-jabbar kawai taji, amma bataji tasu farha ba, fitowa tayi domin jin ya basu dawo ba har yanzu? Abdul-jabbar ya shaidamata sun dawo suna ciki, umma cikin mamakin wucewar farha d'akin ba tare da ta shaidamataba, hakan yasa da sauri ta shiga d'akin nasu don dubata.
Hango farha umma tayi zaune tana sharar hawaye, ga Ikram na barci alamar ta samu sauk'i sosai, shigowa tayi tare da zaunawa gefenta ta dafata tace.....
"Farha lafiya kika dawo kika zauna kika sanya d'iyarki gaba kina kuka?"
Tayar da fuskarta tayi, idanunta cike da hawaye wanda ta runtse idon suka zubo tace.....
"Umma Ayau zanbar gidan nan nakoma gidan Baba insha'allah, domin zan maida ikram hannun mahaifinta, na fahimci zaman Ikram hannuna ba alkhairi bane a rayuwata, domin koh yaushe idan ina neman farinciki, toh a sanadin zamanta hannuna bangaji da jin gori da tunanen bak'in ciki a rayuwata ba, don haka umma zanjawo hak'urin rashin Ikram a rayuwata nasanya juriyar rashinta tare dani, na baiwa mahaifinta ita, nikuma nayi nesa da dukkan rayuwarshi, narok'eki da Allah Umma gada kiga laifina akan hakan, domin hakan shine kad'ai zai kawo zaman lafiya A rayuwata, domin A yau kad'ai rashin mahaifiya ya dawo mani sabo "
Kuka takamayi mai tsuma zuciya, tare da aza kanta bisa kafad'ar umma d'in tana kuka, nan take ran umma ya'bace, domin tagane yadda zancen yake, kuma abun daga Abdul-jabbar yataso, amma kafin taganshi bari tafara jin menene silar hakan?
"Farha dama har yanzu baki d'aukeni a matsayin mahaifiyar data haifekiba? Toh kisani babu inda zakije,kuma babu zancen maidamashi da Ikram A hannunshi,domin Kece kad'ai kikafi cancenta da kirik'e Ikram a hannunki domin dake tafi sabawa, amma barni dashi, kishare hawayenki, ninasan hukuncin da zanyanke akan hakan, kuma kina tare dani har ranar da zakiyi aurenki kihuta, insha'allah Farha bazaki k'ara kuka a rayuwaba, indai kina tare dani Alk'awalin da nad'auka sai yacika insha'allah, kitashi ki wanke fuskarki, sannan kici abinci ina zuwa kinji "
Share hawayen kawai farha tayi, Amma kuma damuwa damk'e a zuciyarta domin tarasa menene zai kawo wannan k'iyayyar ta yanzu da Abdul-jabbar ke yimata, ai koh don darajar Ikram a hannunta yaci ace ya yafe laifinta da tayi mashi farko, ya kalli girman karamci a rayuwarshi, amma abu kusan shekara nawa yak'i ci bale ya cinye, gaskiya tasan tayi laifi farko, amma dazaiyi tunani anan shine yanzu ai tana k'aunarshi sosai, mezaisa kuma yayita yimata hakan yanzu, gaskiya da tace bazatayi aureba, Amma yanzu dole tasamu miji mai aminci tayi auren ta huta, domin shi kad'ai zai kareta da duk wata fitina, gashi dama tana fama da ciwon mara, kuma anshaida mata aure shine maganin hakan, toh gara ta nemi maganin hakan, da wannan waswasin nata, tafurta cewa.....
"Ya Allah, kasadani da miji nak'warai, mai mutunci, mai k'aunata, wanda zai dubi maraicin rayuwata, da girman nadamar laifina na farko, ya Allah kazabaman muji nak'warai "
Da wannan addu'ar takai bakin toilet don yin alwallah tayi sallah.
Umma cikin fushi ta d'auki wayarta domin kiran Alhaji Aliyu, cikin sa'a yad'auka, ta shaidamashi yazo don Allah idan baya komai tana nemanshi anjima kad'an, ya amsa dazaizo insha'allah daya fito gurin aiki zai shigo.
Umma ta ajiye wayar, sannan ta wuce d'akinta batare da tacema Abdul-jabbar k'ala ba.
Baba natasowa aiki ya zarcikke nan gidan, umma takira Abdul-jabbar a waya tace yazo tana nemanshi a cikin gida.
Alhaji Aliyu yace...
"Lafiya kuwa dai koh?"
"Eh dasauk'i dai, inason ne muyi magana dashine akan wani abun, kuma nasan zancen dakai shine dai-dai, don kaxama shaida "
"Toh shikenan umma Abdul bari yak'araso muji "
Rufe bakin baba dai-dai da shigowar Abdul- d'in da sallamarshi, ya gaisa dashi sannan ya zauna k'asa, domin baisan dalilin kiran nashi ba.
Umma ta kalleshi cikin fushi tace....
"Toh uban marasa hak'uri da tawakkalli, inason kafad'aman cewa kai ba ajizi bane, kuma kai baza'a ta'ba yimaka laifi anemi yafuwarka kayafeba, toh kasani A yau ba sai gobe ba Ikram zata dawo hannunka, sai dai wallahi ni bazan rik'ataba, kuma ni bazata zauna a gidanaba, sai dai kayo aure matar tarik'a maka 'yar da kake ikirarin d'iyarkace kai kad'ai, kuma na rantse yau sai Ikram ta kwana hannunka insha'allah "
"Haba! Haba!! Umman Abdul, menene abun rantsuwa akan wannan zancen kuma? Shin idan ya kar'bi Ikram yaje da ita ina kuma? Wanda bashida mata, kuma bashida yar renon rik'ata, kuma hassali Ikram bata yarda da kowa sai farha, idan akayi hakan ai wata damuwace kuma aka tayar mashi da ita fa"
"Hmmm Alhaji wannan dakake gani shine ke tayar da duk wata fitinar da aka manta da ita, toh don haka abashi 'yarshi koh zamu samu sauk'i "
"Umman Abdul, wata matsalarce wadda bansantaba kuma?"
"Eh, nima bansan Abunda yafaruba, amma farha tadawo gidannan da kuka bayan sunje tare gurin kai ikram asbiti, shine take shaidaman zata bashi Ikram domin tasamu kwanciyar hankali akan Abunda yake yimata, toh tunda baisan girman karamci ba, da hak'uri a rayuwarshi ba, toh za'a mik'amasa 'yarsa sai itakuma ta huta, ni na'aza a dalilin sonda 'yarsa keyima farha ya manta da duk wani 'bacin rai na baya, amma duka wannan bai zamo silar hak'irinshi ba, toh gara ta kama kanta abunda zai zama tashin hankali gareta, indai kan 'yarsa ne, toh daga yau babu ikram babu farha, kuma yafitar da matar da zai aura nan da sati biyu, domin koh macce ce shi yafita takabar mutuwa, bale yana d'a namiji "
"Don Allah umma Abdul kiyi masa hak'uri, kitsaya da fad'an mu fuskanci inda wannan al-amari ya dosa, kai Abdul-jabbar menene yafaru hakan ne?"
Duk'ar da kanshi yayi, sannan yafara magana a hankali yace.....
"Umma don Allah kiyi hak'uri, wallahi nima narasa gane kaina akan wannan al-amarin, idan natuno rayuwata ta farko har izuwa yanzu, toh idan nakalli farha wani bak'in ciki nakeji, narasa meyasa hakan,amma ninasan da cewa na dad'e da yafe mata tuntuni kawai dai halin rayuwa ne, dakuma idan na kalleta natuno da k'iyayyar da tayi man farko, amma don Allah atayani da addu'a bazan k'araba,kuma zancen Aure don Allah baba kuyafeman, wallahi babu maccen danake iya ganin zan iya zaman aure da ita a yanzu "
"Koh kak'ara, koh gada ka k'ara, yau dai Ikram gurinka zata kwana, wajibine yau kagano mahimmancin reno a rayuwarka, sannan kuma Aure wajibine kanka tunda mu ba mutanen banza bane "
"Innalillhi wa'inna ilaihirraji'un! umma don Allah kitausayaman banason na bijirema buk'atarku akaina, sai dai kisani zan kar'bi Ikram yau takwana hannuna gobe zan koma, sai nadawo da ita hannunku"
"Umma Abdul kiyi hak'uri, da wannan zafin fad'an akanshi, ni nasan me Abdul keji, domin ni d'a namijine, kekuma bazaki gane nufinsaba, don haka mubi a hankali zai kawo wadda yakeso nan gaba kad'an "
"Hmmm naji, toh tunda hakane, kai kabashi lokaci ya kawo matar don abashi 'yarshi, mu huta da tijararshi, domin itama mai rik'on na 'yar tashi aure zatayi insha'allah "
Anan yabada hak'uri, kuma bazai sake abunda yake yiba, sai dai don Allah ajaye mashi zancen Aure kusa domin duka yanzu matarshi koh shekara batayiba kuma a tayar mashi da zancen Aure, don Allah ak'ara masa lokaci.
Baba zancen Abdul- jabbar dariya yabashi, domin yasan waye Abdul-jabbar a sha'awa tunda itace tata'ba kwantar dashi asibiti, amma wai yanzu kuma bayason Auren bayan ya d'and'ana zancen auren, baba yak'arabawa umma d'in hak'uri akan ta k'aramasa lokaci zuwa wata d'aya, a lokacin idan babu wani zance, toh shi da kanshi zai yimasa hukunci, aka kai k'arshen zancen tare da bada hak'uri akan abun da yafaru, umma tace anjima yazo yad'auki Ikram domin yau dole su kwana tare, baba yace anjima yaxo ya d'auketa domin cika umurnin nata.
Ahaka aks kai k'arshen zancen cewa anbashi 1month ya kawo matar aure, domin su samu lafiya, kowa ya watse, amma zuciyar Abdul-jabbar kamar ta fashe don bak'in cikin rashin matarshi mai sonshi, gashi yanzu an tilastashi kawo abur da baisan inda zai samu kalar wadda yake soba, shidai wallahi tun fara soyayyarshi har yanzu bai samu kwanciyar hankali mai d'aurewa ba, toh koh ya zaiyi yanzu?
A haka ya yini acikin part nashi.
Da dare yaje cika umurnin umma, amma wallahi Ikram tak'i yarda dashi koh kad'an, a hakan yayi dubarar d'aukarta, yafito da ita, sai dai me, Ikram ta hanashi barci bale yazauna ya huta, a yau kuma yagane cewa farha rufin assirice gareshi, koh ba don komai ba, sai don Shak'uwarta da Ikram, Amma wallahi har yanzu koh kad'an bayason ganinta kusa dashi, domin shi kad'ai yadan girman tsanarta a rayuwarshi.
Tunda asuba Abdul-jabbar ya maida Ikram part d'in umma, domin yasan ta wahala da kuka shima ya wahala, don haka bai bari umma ta ganshiba, ya koma ya shirya don barin garin baki d'aya.
★★★★★
*AFTER 5 DAYS*
Doctor Hisham yakawo ziyara gidansu farha, bayan wayar dasukayi da ita, tabashi dama akan Yazo, domin taji k'udurinsa akanta, A hakan ta sanar da umma zuwansa, itama umma tayi farinciki tare da addu'ar dace ciki.
Isowarshi kenan, Farha ta gabatar mashi da kayan ci da sha, sannan ta samu guri ta zauna daga nesa dashi suka gaisa.
Sanye take cikin atamfa doguwar riga,sannan tad'aura d'an kwalinta dai-dai kanta, irin d'aurin zamani wanda farha tasabayi shi tayi, sannan tayi kwalliyarta dai-dai yadda takeyi bata k'ure zuwa ga wadda take haukata 'ya'ya mazaba, domin har ta manta da ita.
"Wooo my best choice, kinyi kyau sosai, koba kwalliya ke ta dabance fatima, bari gada na zurfafa yabon tauraruwar bayan banji _accepted_ d'in _requesting_ d'in nawaba, da farko dai duk da kinsan da sunana amma gara na kammalashi da tarihi na_____
_sunana Hisham Bello Ard'o Gombe, ni d'an asalin gombe ne, sai dai aiki yakawo mahaifinmu nan kuma muma zaman mu yadawo nan kaduna, nayi aure amma munrabu da matar saboda Rashin mutunci nata da kuma izgilancin wulaqanci ga mahaifana, bamu haihu da ita ba, tun lokacin bank'ara sha'awar auren wata macce ba sai ke farha, tunda na ganki naji gabad'aya komai nawa ya sauya,nayi maki magana, kikace ke matar aurece har da d'iya tare dake, daga baya na bincika naga ashe kin rufene don bakison damuwa, wlhy farha gabad'aya akanki komai nawa ya sauya please ki aminta dani, domin na hango zuciyarki da kalar damuwa irin tawa, mubama zukatanmu farincikin da muka rasa, baki haihuba, a binciken da nayi, naji ance yarinyar k'anwarkice da tarasu, please ki aminta dani mu share hawayenmu tare, sai inkuma nine d'in banyi makiba, amma kuma ki tambaya kaf kaduna wallahi babu wanda baisan family namu ba, akwai mutunci da karamci aciki, don haka inajiran sakamakon zancena gareki yanzu"
"Hmmm Oga Hisham, anan banida wani za'bi sai za'bin Alla akaina, kabani 2days insha'allah zakaji result d'inka daga zuciyata, amma yanzu bansan me zance makaba, domin duk abunda zance gaskiya k'arya kawai zanyi, domin babu nazari ciki, amma next 2 morrow da kaina zan kiraka "
Ya aminta, suka d'an ta'ba fira cikin mutunci, tare da tambayar waye Abdul-jabbar agareta halan? Tabashi amsa da yayanta ne, kuma Abban Ikram ne, k'anwarta ya aura wadda ta rasu, daga nan sukayi sallama cikin jin dad'i da alkhairai irin na soyayya ya kawo mata.
★★★★
★ *WAI WAYE ADON TAFIYA, SHIN YA LABARIN ANWAR DA IYAYENSHI?* ★
*Bee Been masoya*💞
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
_Page d'innan duka nakune, Marubuta gidan Hira✍🏻, inayinku ina k'ara yinku😍 kuna saka bee bee nishad'i, a wanne hali take,ta ganku kawai zata fara 😂 *Love you All Gidan Hira*_❤
Page...
★5⃣3⃣★
*~LABARIN ANWAR DA TAWAGARSA.~*
Tun ranar da Anwar yasaki Farha bayan taka masu suna aikata iskancinsu da abokinshi da kuma jamila k'awarta a d'akinta, bai k'ara zama inda mahaifinshi zai ganshiba domin labarin sakin yazo mahaifinshi a kunne,hakan yasa ya had'a duk wani abu nashi mai muhimmanci yabar garin tare da abokan iskancin nashi.
Mahaifiyar Anwar babu yadda batayi da mahaifinshi ba akan ya nemo mata Anwar, domin shi kad'ai ke gareta rayuwar duniya.
Mahaifin Anwar ya nunamata cewa, dama da hannunta a lalacewarshi don haka idan batayi a sannuba har ita zai iya yafeta ba Anwar kad'aiba, hakan hankalinta yayi mugun tashi da wannan furuci, nan take ta gano cewa lallai dadyn Anwar zai iya yin komai Akan hakan, sai takama bakinta tayi shiru, amma kud'd'inta nashan kashi gurin neman Anwar, amma shiru babu Anwar bale labarinshi.
Tunda anwar yabar kaduna, sai ya tare a wani babban hotel da ke garin Abuja, inda yanzu abun nashi yaci gaba, domin yana homosexual ne saboda yasamu kud'd'i.
Ranar da ya tashi barin kaduna bayan ya rabu da farha, ranar ne yabama jamila k'awar farha kud'd'i masu yawa, hakan yasa jamila taji zata iya binsa akoh inane domin itama tak'ara samun kud'd'i, domin akan kud'd'i babu abunda bazata'iya aikatawaba, don haka da ita akayi wannan tafiyar.
Iyayenta sun nemeta har sungaji sunsakama sarautar Allah idanu.
Anwar abun nashi yaci gaba, domin yanzu manyan masu kud'd'in Abuja sune abokan hark'allanshi, hakan yasa sai jamila takoma tamkar matarshi, girkinshi, tayar mashi da sha'awarshi, amma bai yarda da sex da itaba domin baya gabanshi, sai dai usman ke d'an ta'ba mu'amala da ita, duk da hakan ta za'bi zama dasu, domin tasamu mak'uddan kud'i da yawa a k'ark'ashinsu, tunda har motar kanta gareta, hakan yasa ta manta da wata rayuwar kaduna, masha'arsu kawai sukeyi, wanda yanzu gida garesu na kansu, itama da nata miyagun matan a nan gidan suke tasu harkar.
Mahaifin Anwar yabada sak'o a sanar dashi cewa, ya cire Anwar daga tsatsinshi, koh bayan ya mutu Anwar baya gadonshi domin shi ba d'anshi bane a yanzu, idan ya rasu yafi farincikin dukiyarshi a baitil mali da Anwar ya gadeshi, domin ya samu labarin abunda yake aikatawa, mahaifinshi yayi kuka har yagaji domin Anwar shi kad'aine Allah ya mallakamashi a jinin jikinshi Amma gashi yayi yayi yakoma mutumen k'warai yak'i ya koma, domin duk wasu kayan maye da d'an adam kesha su bugar dashi Anwar zaishasu yanzu, hakan yasa mahaifin anwar d'auko d'an yayanshi domin ya cigaba da gudanar da kular mashi da wasu al-amuran da yake aikatawa a nan gida nigeria, gaba d'aya ya manta da tsarin Anwar a rayuwarshi, kuma yaje har gidan mahaifan farha ya basu hak'uri akan abunda ya faru, domin shi baiso hakan ba, koh lokacin da yaji rasuwar mahaifiyar farha saida mahaifin Anwar yazo yayi mashi gaisuwa da yashigo nigeria.
Mahaifiyar Anwar tak'i takoma jidda domin bazata iya tafiya tabar anwar acikin wannan halinba, domin koh ba komai tasan hadda hannunta a lalacewar Anwar d'in tun farko, domin komai yakeso zata tilasta mahaifinshi yayi mashi koh ransa baisoba, don haka dole ta tsaya ta nemi inda Anwar d'in yake.
Wata shidda da faruwar hakan, momynshi ta shirya domin taje abuja ta nemi gurin da yake zaune, bata wahalaba domin wayanda suka sanshi su tanema, taci sa'a yana nan kuma lokacin a cikin halin yake na bad'alar tashi.
Shigowarta gidan taga jamila zaune a shiga ta rashin mutunci, ga 'yan mata nan zazzaune sai firar banza sukeyi, shigowa momyn Anwar tayi da sunan tambayarsu inda Anwar d'in yake, kafin ta fara tambayar sai wata macce dake zaune gefen jamila tafara tambayarta da koh tazo d'aukar watace daga cikinsu? Momyn Anwar kallonsu kawai tayi saboda takaici, sannan tace.....
"Ina Anwar yake?
Sai a lokacin jamila tagane mahaifiyar Anwar ce domin fuskarsu d'aya da Anwar babu bambanci, nan take ta mik'e domin zuwa d'akin da yake, knocking tafarayi sannan yazo ya bud'e domin aikin yakeyi itakuma zata katsemashi jin dad'i, don haka da sauri ya bud'e tare da hasala yafara tambayarta.....
"Wai meye hakan dakike yiman jamila?"
"Anwar ina tunanin mahaifiyarka ce fa tazo gidan nan yanzu?"
"Eyee! Toh wai su meyasa zasu dameni bayan na barmasu gidansu, Amma kuma suna biyar didiqina? Kawai kice mata bananan baki ganniba, kuma ki wuce kibani guri plz"
Jamila takoma tasanar da ita baya nan, itakuma yarda ne batayiba, hakan yasa tabi hanyar da jamila tabi domin gani da kanta idan gaskiyane, k'ofar ta tsaya tare da knocking, nan take yafito da niyyar rashin mutunci amma ganin mahaifiyarshi yasa ya tsayar da hakan.
"Anwar kaza'bi kazauna acikin wannan halin mara amfani daka zauna damu a matsayin iyayenka masu sonka koh?"
"Momy.........
" Dakataman! Anwar akan ka babu wahalar da bansha ba akakan kaji dad'in rayuwarka, na d'auki kud'in mahaifinka bai saniba domin kaji dad'in rayuwa, nayimaka a kud'd'in dake jikina, amma wai karasa zama mutun wanda iyayensa zasuji dad'in k'aruwa da kai, Anwar kasani ni kad'ai yanzu ke sonka domin nice mahaifiyarka, mahaifinka ya dad'e da mantawa da kai a rayuwa saboda aikin da kake aikatawa "
"Momy kikoma