Showing 162001 words to 165000 words out of 173505 words

Chapter 55 - SO NE DALILIN So Ko Sha'awa By Khadija bee bee

28 Aug 2026

441

nishad'i, domin su kashe jikinsu da wasanni masu aminci, shi ya mantar da ita inda take, haka itama ta mantar dashi inda yake, wanda sun kai stage d'inda burinsu kawai su gusar da sha'awar su akan hakan.

K'ok'arin Abdul-jabbar kenan, na ganin ya gamsar da junansu a zuwa babbar k'orama, farha ta taimaka mashi gurin kaiwa inda yake so, domin ta lura hankalinshi baya jikinshi, don haka sai ta taimaka mashi yakai.

Sai dai wani abun al-ajabi da farha tajiya, domin wani zafi taji ya ziyarci jikinta, wanda rabon da taji hakan tun a first night nasu, domin duk randa ya shiga jikinta tana jin dad'i sa'banin yau da take jin zafi sosai.

Tun farha na jurewa har ta kasa, domin tayi juriyar ne don ganin yana jin dad'in hakan, amma baisan iya azabar da take sha ba, domin har k'walla zubarwa take yi, saboda azaba.

Abdul-jabbar jin farha yake yi daban da kullum, domin shi kad'ai yasan yadda yake ji, domin idan zai iya tuno mutuwarshi a wannan lokacin zai iya gane shi wanene, amma kuma ko d'aya domin kwata-kwata ya kasa control na kanshi, hakan yasa ya kasa saurarama farha.
Tun tana hawaye, har takai gaba d'aya kuka take yi, domin azabar ta wuce guri, amma bai tsaya ba, sai da ya gamsu da hakan, sannan ya k'yaleta.

Kukan da yaga farha nayi, ya bashi mamaki, domin shi abunda yake ji,idan zai fad'i, to k'aryatashi kawai za'ayi, don haka ya shiga tambayar ta, me ya faru ne halan?

Anan farha ta shaida mashi zafin da ta ke ji sosai, shi kuma ya fad'a mata yadda ya samu kanshi sosai, mamaki ya kama dukansu, da niyyar gobe zata binciki lafiyar jikinta.

Lallashinta yayi da bata hak'uri, sannan ya taimaka mata gurin ganin ta gasa jikinta da kuma tsalkake jikin nata da kuma kawo ta bisa gado ta kwanta domin yasan ta wahala sosai, shi kuma ya gamsu sosai, domin a daban yaji wannan ni'ima tata.

Tun da safe ta shirya masu kari, tare da gyarama ikram, sannan ta barta gurin su sadiya .
Abdul-jabbar ya fito cikin shirin shi na zuwa gurin aiki, sannan ya zauna sukayi break dashi da ita, cikin kulawa mai kyau.

Suka k'arasa komai, ta barma sadiya sauran aikin, tace sunfita sai sun dawo.

A asibiti, farha ta shiga neman sanin damuwarta, don haka ta tambayi wata k'awar aikinta akan hakan, nan take ta fara yima farha dariya da tambayar ta kamar haka;

"Sistr kin ta'ba haihuwa?"
Farha tace mata "ah ah sistr, yanzu kusan one year kenan da aure na, ko ciwon kai ban ta'ba yi ba, bale kuma amai "

"Yanzu wataninki nawa bakiga period naki ba?"

Sai a lokacin farha ta fara tunanin tun rabonta da period, domin idan bata manta ba, yanzu tayi 4 month bata ga period nata ba, idan wannan watan yazo 5 month kenan, to amma me yasa duk wasu alamomi na masu ciki ita bata dashi? Kai tsaye ta bata amsa da "4month ko 5 month ban ganshi ba, amma kuma sistr ina ganin ba wani ciwo ne dani ba na daban? Domin wallahi ko ciwon kai banayi, kuma duk yadda naga ana yin wahalar masu ciki, ni banida ko d'aya wallahi"

"Sister farha! Ai ba kowa ke wahalar d'aukar ciki ba, hasali yawan barcin da kike yi da kasalar da kikeji duka alamar ciki ne, sannan zancen sex kuma da oga; tabbas wani cikin idan kana dashi, idan ana sex da kai zafi kake ji, shi kuma a lokacin dad'in hakan yake ji, domin duk wasu k'ofofin ni'ima a gareki sun bud'e, sannan zaki k'ara matsewa sosai. Alokacin idan har ya shiga jikinki to dole ya kasa control na kanshi, ke kuma saboda matsewar, sai ki samu kanki cikin jin zafi, duka wannan ba matsala bace, sai dai a rage ba ma cikin wahala, domin zai iya zubewa. Amma duk da hakan, ki k'ara zuwa lab. Kiyi test da kanki ki gani, nafi tsammanin cikine dake sistr farha "

Farha tayi farin ciki da jin hakan, domin tasan hakan zaisa Abdul-jabbar ya gane cewa bata yin komai, domin tasan har yanzu yana shakku akan hakan, fad'ine kawai baiyi ba.

Farha sai yanzu ta k'ara tabbatar da zancen abokiyar aikinta,na cewa ciki ta samu mai sauk'i shiyasa bata gane samunshi da wuri ba.

Da kanta tayi test nata, tagane cewa tana d'auke da ciki, na wata hud'u da da sati biyu, murna ba'a cewa komai a gurinta, bale idan oga yaji hakan.

Bayan antashi daga aiki, ta zauna domin jiranshi, nan take barci ya d'auketa a office nata, don haka yayi kiran wayar har yagaji, sannan ya fito motar don zuwa office nata.
Barcin kuwa ya samu tanayi, a abur sallah d'inda tayi sallah da ita. Bubbugar hannunta yayi tare da jaye wayar ta da ke gefenta, sannan yace....

"Dear kin zama mai ciwon barci yanzu, duba kusan 8 missed call, amma baki san inayi ba, wai lafiya kike kuwa? Irin hakan ai sai a saceka baka sani ba "

Murmushi farha tayi, tare da mik'ewa zaune tana had'a takardun gabanta tana cewa...

"Sata kamar wasu kaya kuma dear?"

"Eh ai ke kaya ne masu muhimmanci, duk wanda ya d'auke ki ai ya huta ko? Kin ko san da anyi bala'i a duniyar nan fa?

" Hmmmm! Kaya a gurin Sirri nah ba, amma wasu me za su yi dani?"

Ta fad'i hakan tana dariya, ta shiga toilet d'in office nasu, ta kurkure bakinta, sannan ta fito ta d'auki jikkar ta shi kuma ya rik'a mata takardun da ta had'a, suka fito.
A hanya ta had'u da d'ayar sistr d'in ta iso yin duty night, suka gaisa sannan suka wuce gurin motar su, suka kama hanyar gida.

Shigarsu gida, farha ta kama hanyar part nata, tare da mi k'ama Abdul-jabbar takardar result d'in test nata, ta ruga da gudu tana dariya.
Abdul-jabbar, kar'bar takardar kawai yayi amma bai d'auki takardar da muhimmanci ba, domin yunwa yake ji. hakan yasa ya ajiye takardar yayi part nashi don watsa ruwa.

Bayan sun saita komai, farha ta sauko domin gyara masu abincin da sadiya ta girka, domin ciyar da mujin ta.

Bayan Abdul-jabbar ya zauna dining, farha cikin farin ciki ta zauna suka fara cin abincin cikin so da k'auna har suka k'arasa.

Abdul-jabbar ya mik'e tsaye, tare da rik'a hannun farha don tayi masa bayanin takardar da ta bashi.

Rufe fuska tayi tare da cewa...
"ka duba ka gani "

Kamota yayi, sannan yace...
"Ke dai zaki fad'aman, ko kuma na koma da ke sama yanzu, tun kafin su ikram su shigo ki fad'aman kawai"

"To ka sakan ka sakar man hannu, kada su shigo su ganni kwance jikin ka "

Sakar mata hannun yayi, amma bai matsa daga inda take ba. Farha mik'ewa tayi, sannan tace....

"Ikram ta samu k'ane ko k'anwa "

Da gudu farha ta shige part nata, domin taji kunya sosai, sannan kuma ba ta son ya rik'ata a falon, tunda su Ikram na nan, tasan halin shi, akan wannan farin cikin babu abun da ba zai iya ba, ko a gaban waye kuma, hakan yasa ta tsere a d'aki.

Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Abdul-jabbar. Da sauri ya d'auki takardar a hannunshi ya bi bayanta yana fad'in....

"Tsaya ki ji sweetheart, me kika ce?"

Fad'awa part d'in nata yayi, sannan ya rufo k'ofar yana dariya..........



*Bee Been Masoya

*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋

★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★

*NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE 'DIN A K'UNGIYATA, WATO:-*
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERSâœðŸ»*
_'Kungiya mai farin jini, k'ungiyar da kowa ke burin shigarta saboda had'in kanta._
*_MY R.P.M.L PARTNER WRITER'S, BEE BEE NA SONKU BAKI 'DAYA😘_*

Page.78


"Farin ciki! Ki tsaya ki fad'aman naji daga bakin ki, da gaske munsamu k'arin baby?"

Ya fad'i haka tare da kamota a gadon.
Farha sai k'ok'arin k'wace kanta take yi, amma ta kasa. Abdul-jabbar k'arasa hawa gadon yayi, tare da kwantawa saman pillown gadon nata, wanda banda k'amshi babu abun da d'akin ke yi.
Jawota yayi ya d'aurata a saman ruwan cikinshi, domin zancen zaifi mashi dad'i a hakan. 'Daura farha yayi daga bayanta, domin kada ya d'aurata a gaban ta danne cikin, domin shima sai yanzu ya tuno irin ni'imar da ya zuk'a a gareta, hakan yaji Iman lokacin da take da cikin Ikram, mantawa kawai yayi, amma yanzu da yaji gaskiyar ciki ne da ita ai ya tuno da Iman d'inshi, wanda sai da yayi shiru na minti ukku domin gabatar da addu'arshi ga Iman, domin ya tuno wani abu daga gareta, sai dai kuma, yana gode ma Allah, domin anyi mashi sakayya da wata irinta, jini guda, kuma rayuwa guda.

Cen sai yayi nishi mai sanyi tare da farin cikin da ya mamaye mashi zuciya, ya azo hannuwanshi duka biyu ya rungumota daga k'irjinta, domin bayason ya matse cikin nata, ya takura babynshi, domin yanzu hakan da ya shafa cikin yaji alamar cikin ya fara fitowa daga k'asan mararta, domin tayi tuli kad'an. Hakan yasa bai yadda ya matse cikin ba, sai dai k'irjinta da ya cika shima, sai suka k'ara yimashi dad'i aza hannun nashi, sannan ya saita muryarshi yace......

"Farin ciki! Tabbas yanzu na yarda ciki ne da ke, amma me ya sa baki fad'aman tun da wuri ba nayi celebration d'ina ba, sai yanzu?"

Farha matsar k'irjin yayi mata yawa, hakan yasa ta yamutsa fuska, tunda tasan ba ganinta zai yi ba tace...

"Allah dear da zafi fa, gashi ni bansan me ya sa suke yiman ciwo haka ba yanzu, amma nasan, wannan ajiyar taka mai wuya, ita ke kawo wannan zafin, gashi jiyama wahalar da nasha bansan me zance ba ma akai, sannan nima yau d'innan nasan da wannan ajiyar, domin bansan da ita jikina ba, saboda bana wahalar komai, sai wannan abun da kake yi kullum "

K'ara matsarta yayi, wanda sai da tayi k'ara sosai, saboda k'eta yayi mata mai yawa gurin, wadda sai da ta wulk'ita da sauri zuwa gadon. Da sauri Abdul-jabbar ya bud'e idonshi tare da rik'eta, kada tayi k'asa ta sashi yayi hasarar abun da ya dad'e yana nema. Farha dariya tayi sannan ta koma jikin nashi da kashedin cewa kada ya k'ara yimata k'eta.ya amince da hakan, sannan ta yarda ta natsu.
Tambayarta yayi "how many month yanzu ga babyn? Saboda naga kamar kin dad'e a yanayin da kike, kuma sai yanzu nake tuno long time da kika d'auka bakiyi period ba, wata nawa suka ce, baby na zai iso?"

"Baka duba result d'in ba?"

Ga ki, me zan yi da takarda?"
Inji Abdul-jabbar.

Hannu farha ta d'aga mashi da cewa...

"Hud'u da sati biyu, yana nufin wata biyar babu sati biyu "

"Haba dear! Wannan wane kalar lissafi ne hakan? Duk don ki ja mani rai ne ko?"

"Sorry sweetheart! 5month ne, result yace "

"Alhmdllh! Na ma rasa me zanyi anan, bayan gode ma Allah da nayi, wajibi na k'ara da raka'a biyu ta godiya ga Allah, sannan na samu dogaron wannan farin cikin anan "

Juyo da farha yayi, tare da jawo da filon da yake kai ya aza farha a saman filon, sannan ya zame k'aramin gyalen da ta d'aura akan nata, ya zuba ma gashin kanta ido, sannan yakai hannunshi tsakiyar gashin nata.
Duk da hakan bai ji godiyar ta isa ba, sai da ya matsa da bakinshi a nata, yafara kissing nata. Nantake zance ya chanja tunda hannunshi yakai ga zip d'in rigarta, domin zipping na rigar yayi tare da saka hannunshi ciki yana wasa da dukiyar da suka rena tare.
Nantake ko wannensu ya shiga faranta ran d'an uwanshi, ba tare da babban al-amarin ya shigo ciki ba, amma sunsha soyayya a gadon aurensu ta murnar samun d'an jinjirin cikin love d'insu.

Kukan Ikram da farha taji a falo, yasata rik'e mashi hannu da ya rungumota tace...

"Dear d'iyata kuka take yi fa, ka sakan naji me ke damunta? Kasan batada rigima, naje naji abun da ke damunta "

Bai saketa ba, kuma bai daina abun da yake yi ba, domin yaji dad'in kasancewar tasu a wannan lokacin kuma zata katseshi. Hakan yasa bai ko kulata ba, sai ce mata kawai yayi..
"Kijira kad'an"
Ya fad'i hakan cikin murya kamar ta mashayi, domin duka jikinshi ya saki baki d'aya.

K'ara jin kukan nata, yasa farha rik'eshi da sauri tace...

"Dear ka dawo hankalinka, kaji fa Ikram ce ke kuka kuma da k'arfi, don Allah ka sakan muje mu gani, kada wani abun ne ya sameta fa"

Sai a lokacin ya fahimci me take cewa, saboda ambaton Ikram da tayi da ko wani abun ne ya sameta, shima shi ya d'aga hankalinshi. Da sauri farha ta jawo rigarta da yayi k'asa da ita, tayi saka hannun rigar tare da saka zip d'in rigar ta jawo gyalen da tayi d'ankwali dashi da d'aura ba tare da ta gyara gashin kanta ba tayo falon da sauri.
Abdul-jabbar shima rigar tashi yake gyarawa, sannan ya fito.

Farha ta hango sadiya goye da Ikram tana rarrashinta, maryam na d'aure hannun nata da wani k'yalen atampa. Da sauri farha tace "maryam meye hakan kuma?"

Sadiya tace....
"Aunty Ikram taje kitchen wallahi ta yanka hannunta da wuk'a, wai zata yanka lemu ne "

"Subhanallah! Bani ita naga hannun"
Fad'in farha kenan da ke shirin duba hannun. Dai-dai nan Abdul-jabbar ya fito da sauri don ganin abun da ke faruwa.

"Ayya my Ikey! Wuk'a bata kyauta ba, zata sha bulala, yi shiru, sorry sorry"

Farha ta d'auketa tayi part nata, tace ma su sadiya suje part nasu, Ikram sai kuka take yi, jinin da ke zuba hannun nata shine take tsoro.

Abdul-jabbar kar'barta yayi hannun farha ya azata saman k'afafunshi, shima yana rarrashinta. Farha d'auko kayan aiki tayi sannan ta saka mata magani ta d'aure hannun ta kar'beta ta bata ruwa, da sweet d'inda take siyo mata ko yaushe. Da haka farha ta d'auki zane da niyyar goyata,Abdul-jabbar ya banko mata wani mugun kallo,sannan ya aza Ikram d'in a kafad'arshi har tayi barci, sai cewa yake yi....

"Tunda ni bani da hankali, zan bari kiyi goyon k'atuwar yarinya ta danne man hancin baby "

"Lah-lah! Yanzu ina hancin yake anan, kuma ina fuskar take anan?"

"Ni nasan inda suke" fad'in Abdul-jabbar da yake ajiye Ikram a kujerar gadon dake d'akin, sannan yace "zanje d'aki zan dawo idan kin gama jinyar "

Farha ta gane nufinshi, don haka dariya kawai tayi masa tare da kashe mashi ido d'aya, ta fad'a toilet tana dariya.
Tun daga ranar, ikram ta hidimar ikram ta dawo hannun farha, sai in zataje aiki sannan take barinta gurin sadiya, tare da shaidamata a kula da ita da kyau.

★★★★★★★

Bayan dawowar su umma daga hajji, su farha suka shirya domin zuwa gaidasu, domin a kaduna suka tashi, anan kuma suka sauka.

Dukansu sukayi tafiyar don yima su umma barka da zuwa da kuma kar'bo tsaraba inji Ikram da ta bada sak'on a siyo mata baby mai magana, don haka ta matsa a tafi kaduna.

Kwanan su 7 da dawowa, su farha suka dira garin. Tunda umma tayi arba da Farha ta gane cewa akwai tsaraba a cikinta zaune, don haka farin ciki bisa farin ciki. Suma farin ciki gurinsu ba a cewa komai, domin su umma sunyi kyau sosai, umma har wani shek'i ake yi. Abdul-jabbar da ya kalli farha sai ya kashe ido da,alamar akwai zance k'asa kenan akan kwanciyar hankalin su umma, farha sai ta kawar da fuskarta domin ya kusa sakata abun kunya a gurin, domin umma zata gane nufinsu da wuri.

Bayan an basu tsarabarsu, sannan suka sha fira, suka kama hanyar masaukinsu na nan kaduna, wanda wannan karon Ikram bata yarda ta rabu da iyayenta ba, duk inda sukayi tana cen.

Satinsu d'aya, suka kama hanyar komawa, inda suka nemi umma da ta barsu su koma da sadiya, domin zata rik'ama farha wani abun, saboda girman da cikin nata ke yi. Umma ta aminta, domin ko basu ce ba, zata yarda su tafi da ita, sai maryam ta tsaya anan. Itama sadiya taji dad'in hakan, domin tanajin dad'in kyautatawar farha gareta, gashi har school an sakata a cen abujar, ikram itama an sakata wata babbar makarantar da sai d'iyan manya ke kai yaransu. Idan suka je tun 7:00 sai 6:00 domin har islamiyya aciki ake yi masu, ga manyan malamai k'wararru a makarantar, hakan yasa tayi zarra a garin abuja.

Kwanakki na tafiya, cikin farha na girma, sai dai yanzu da yakai 8 month sai farha ta d'auki hutu, saboda kunburin da k'afafunta nayyi. Hakan yasa hankalin Abdul-jabbar ya tashi, ya tilasta mata zama gidan duk da bata yin komai, sai fita motsa jiki da sukeyi a harabar gidan ko yaushi. Duk wani abu da ya kamata sadiya ita ke kula da komai, sai dai farha ta zauna daga nesa tana bata umurnin yadda abincin mijin nata zai kasance, domin bata son kowa ya saka mata hannu akan hakan, amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login