Showing 75001 words to 78000 words out of 173505 words
Chapter 26 - SO NE DALILIN So Ko Sha'awa By Khadija bee bee
itaba.
Fitowar farha kenan daga shop d'in assibitin, taje sayen recharge card sbd zata kira rashida tashaida mata rashin lfyr iman.
Sanye take da dogon hijab tajawo fuskar hijab d'in daga gaba,cikin natsuwa take tafiyar ta, jabbar hango farha yayi daga nesa tana qarasowa, kuma tabbas yasan itace duk da rufe rabin fuskarta datayi,amma wlhy bazai iya tambayartaba saidai yabita daga baya, hakan tawuce shima yabiyota daga baya.
Shigarta d'akin,taga Iman nason tashi amma takasa, dasauri tariqata tareda cewa...
"Menene kikeso iman?"
Tanuna mata Ruwa takeso da yatsanta, farha tace...
"Toh kijira xan kira doctor domin yace idan kin falka gada abaki komai sai yazo"
Kallont kawai tayi,sannan farha tagyara mata zama tace tana xuwa.
Dai2 fitarta sukaci karo da jabbar, wanda saida jikinta yabugi jikinshi,d'agowa tayi da sauri domin ganin waye yayimata hakan? Dubanshi tayi da sauri dashirin mayar da magana,amma kuma sai takasa ganin wanda yayimata hakan, gefe tajawo tareda matsamashi hanya yawuce, sai cewa yayi....
"Mtswww!Mara hankali,duk yadda akayimashi magani watarana sai haukar ta motsa"
Yawuce ciki da sauri, farha runtse idonta tayi, domin iya muzanta ya muzantata, kuma da qeta yayimata wannan dukan domin taji banka'dar da yayimata sosai, amma kawai ta share tatafi aiwatar da abunda tayi niyyar yi, takira likitan sannan takoma reception tazauna tasaka kati takira rasheeda domin bazata shiga d'akinba sai yafito ciki.
Shigar jabbar da sauri yaqarasa gurin iman, duk tayi baqi ga rama datayi, nantake hankalinshi yatashi, zaunawa yayi saman gadon daga gefe ya rungumota yace....
"Haskenah, haka kika koma amma aka rufeman ba a fad'aman ba? Subhanallh! Iman jiya kawai ne at bamu tare fa, menene kedamar manke haka Iman?"
Kallonshi kawai tayi talumshe idonta, domin itama batasan mtslrtaba, kawai ganinta kawai tayi a nan kwance, hawaye nat fara cika idonta wanda data rufe idon zai xubo amma kallon jabbar ya hana turufesu,hannunshi yasa ya runtse idon tareda saka hannunta d'ayan hannun nashi ya tare hawayen.
"Har abada bazan bar d'ayan hawayenki ya zuba ba idan muna tare, fad'aman meke damunki?"
"Nima bansaniba, amma nasan ina amai tun shekaranjiya daga nan banqara sanin inda nakeba,ni kabani ruwa nasha maqoshina zai cire "
Dasauri yad'auko robar ruwan yabud'e yabata, tasha ruwan sosai domin takusa shanye roba sannan yajayemata ya ajiye gefe,taji dad'in ruwan sosai,saidai ina bazasu tsayaba,domin d'agowar da jabbar zaiyi gabad'aya ruwan sun dawo mashi jikinshi, bai damuba sbd ganin yadda take kakarin aman kuma babu komai cikinta, tsoro ya kamashi sosai sunan iman yake kira,hawayen wahala ke zuba idon iman riqe kawai yake da ita yarasa me zai yimata, kwantar da ita yayi kawai yana dubanta.
Suna hakan kawai sai yaji turo qofar d'akin, d'aga idonshi yayi sai yaga doctor ne, hakan yasashi miqewa gefe amma bai saki hannuntaba, suka gaisa da doctor d'in sannan doctor d'in yace...
"Amma abokina wani abun akabata taci koh?"
"Ah ah doctor ruwa ne kawai nabata ynx, domin tace tana buqatarsu, wai don Allah meke damunta ne hakan? Doctor kasanar dani nasamu natsuwa "
"Da alama kaine Ogan nata koh? Domin naga damuwar tayi yawa sosai, ga kuma kasha wankan amai a jiki "
"Eh likita nine, don Allah kasanar dani meke damun iman? Domin shine farkon abunda nakeso naji "
"Toh Alhmdullh ba mtslr komai tare da ita sai alkhairi, dama inajiran mahaifinta yazo nabashi result naku amma tunda gaka kaxo, ga result naku, kuma wannan abun datakeyi ba wata mtsl bace zata daina nan gaba kad'an idan tasamu qwarin jikinta, baqon ne naku yaxo da wahalar da maman nashi sai haquri kawai amma wannan bayada magani sai randa stage d'in dainashi yazo, kuma nace gada abata ruwa sai nazo sbd nasan idan tasha hakan zai faru, a dinga bata ruwan da lemon tsami aciki, idan za'a bata ruwan ad'an matsa lemon tsami kad'an ciki domin kawar da gard'in ruwan hakan zaisa aman yarage, amma babu komai akwai wayanda sukafita wahala sosai, ita somewa kawai tayi, wasu idan suka fara hakan bazasu samu sauqiba har sai sun haihu, Toh ALLAH ya inganta yabada mai albarka "
Wani farin ciki ya cika cikin jabbar, wanda banda jikinshi babu kyau daya rungume likitan, amma koh ynx alhmdllh.
Duban doctor d'in yayi tareda murmushi ya bud'e result d'in yafara dubawa yayi murmushi yace...
"Alhmdllh, Alhmdllh,doctor nagodema Allah dajin wannan result da ganinshi,amma doctor babu wani abu daza'ayi gameda mtslr wannan data keyi? Duba yadda take wahala "
Murmushi likitan yayi sannan yace...
"Ba wata mtsl,domin zata daina a hankali,kuma anyimata allurorin range aman,ynx qarfin jiki kawai yarage zuwa anjima sai kuwuce gida, sai dai kaima fa ynx sai ka rage yawan ziyara domin kaga baiyyi qwariba za'a iya samun mtsl a yawan takurashi, sbd gaga 3weeks ne da kwanakki sama baiyyi qwariba "
Murmushi jabbar yayi tareda godiya, kuma yacire 10k aljunshi yace don Allah yasaka recharge yagode da kulawa.
Fitar doctor d'inne, jabbar yakoma gurin iman tareda d'agota jikinshi yace...
"My everything mun girma, nauyin jarumtarmu da soyayyar mu ta haifar muna dasamun baby,ina cen nadamu naji menene damuwarki ashe ajiyata ce ke wahalar dake, iman bansan wanne irin farin ciki nake cikiba a ynx, ni na yarda cewa ni mai sa'a ne a duniya, baby nah zai iso lkchn da nake cikin wadata ta, ina murnar qara girma gurin aiki,sai ga murnar qaruwar da nahaifar muna sanadiyar soyayyar damuka gina dashi.
Iman jinsa kawai takeyi, domin ita abunda yadameta ya isheta, bacika gane me yake fad'iba takeyi,dubansa tayi da alamar tambaya ta bud'e baki dakyar tace....
" waye ya haihu kake kiran kun samu baby?"
"Ban haihuba, amma nakusa haihuwar,domin iman nad'auke da baby nah a cikinta wanda ni nabada ajiyarshi kafin natafi, ynx kuma sai gashi shine yadawo dani domin yace nazo yana wahalar da momyn shi, qarshe dai iman kina d'auke da cikin baby nah natsawon 1month ynx hakan shine silar ciwonki "
Wani yunquri tayi, zata tashi da sauri ya riqeta tareda rungumeta,hawaye tafarayi tace...
"Toh ynx yaushe zanji sauqi?"
"Ance sai yafara qwari nanda yakai 4month koh 3month, komai zai koma normal "
Matseshi tayi sannan tatura kanta qirjinshi tace...
"Nidai wlhy vazan iyaba,mutuwa zanyi 3days dubi yadda nakoma kuma ni kad'ai nasan menakeji jikina, sannan ace sai nayi 4month zan daina amai? Nidai gsky acire babyn kawai nasamu sauqi wlhy wahala bazan iyaba"
"Haba, haba iman, dabakinki kike cewa bakiso acire? Kituna sakamakon k'aunar mune yafito, kuma ai kowa haka yayyi koh? Wannan babyn shine gudan jininmu wanda muke fatar samu koh yaushe mai albarka, insha'allah komai zai zamo normal nan gaba kad'an"
Kallonsa kawai tayi,domin bazai gane me takeji bane shiyassa,hakan takan yasa bata cemashi komaiba sai hawaye dake fita idonta,shikuma yana goge mata da hannunshi, yana shafa bayanta.
Dai2 nan su umma suka shigo baki d'ayansu har da farha, wadda ta tsaya daga bakin qofa, Iman qowarin tashi takeyi jikinshi amma ya hanata domin ya riqemata hannu yana matsawa ta gefe, mama dubansu kawai tayi, sai tayi murmushi, itakuma umma cewa tayi...
"Kai kuma yaushe kadawo? Toh ka saketa mana mutane sunzo ganinta, kabi ka wani daddafeta hakan tanaji da kanta "
Qala baice mataba, domin dama yasan umma zatayi hakan, mutun da matarshi a takurashi ta'bata bayan kuma batada lfy, Runtse idonta iman tayi domin iya kunya tajita anganta saman k'afafunshi, bai jayeta jikinshiba saida yaji sallamar babansu iman d'in sannan ya yi dubarar jawo pillow ya ajeta sannan ya tashi yana shafar kai.
Gefe yakoma yatsaya, tareda takardar result d'in hannunshi, baba mamakin ganinshi yaka mashi domin yace gada yazo amma sai da yazo, duqawa yayi yagayar dasu baki d'ayan su, sannan jabbar ya miqama baba result d'in yakoma gefe.
Farha nace gefe, domin motsin arziqi ma batayi, domin bata mance da haukar da jabbar yakira mataba,bada dad'ewa ba, hakan yasata ciro wayarta tana duba wani abu ciki, duka iyayen basu damu da yanayin da farha d'in ke cikiba domin ynx sunsan shiru aikinta ne, inba ace itaba bazata tamka mutunba.
Baba yayi hamdala, sannan yafad'amasu cewa "iman nad'auke da juna biyune" wanda kowa saida yayi murnar jin hakan, iman najinsu amma takasa cewa komai.
Farha kuma hawaye nat biyo tacikin idonta wanda bakowa xai gansuba sbd hijab da yakare fuskar tata baki d'aya, kukan xuci takeyi wanda ita kad'ai tasan me take cewa, dubi yadda kowa ke farinciki domin samun jika, da ynx itace hakan yafaru da ita, amma gashi kowa ta iman yakeyi.
Ana haka dukansu suka fita domin bawa iman guri tasamu barci, sai akace amma farha ta tsaya gudun gada abarta ita kad'ai, jin hakan jabbar shima jabbar yaqi fita,domin yayi niyyar fita ya changer kaya, amma dagajin ance farha taxauna da iman sai yaqi tafiya, hakan yakoma gefen gadon yazauna, anan yafara kiran abokanshi yana sanar dasu dad'i bisa dad'i, ga aiki ga baby dakuma wadda yafi qauna aduniyya Allah yabasu babyn.
Duka fa da gangan jabbar keyi domin yaga farha zaune,harda kiran basheer yayi yace...
"Aboki kaga ikon Allah koh? Gashi gaba kawai nakeyi, ga aiki babba kuma ga baby nasamu da k'wailata takawo mana baby, kasan aduniya babu abunda nafi k'auna kamar iman da abunda ke cikinta, idan kacire umma dake uwa, don haka dole naje da matata abuja don samun kulawa "
Duk wannan zancen dayake zubama basheer martani ne yake maidawa farha, kamar kuma yasan cewa abun ya hau sosai, domin farha tasan da ita yake, hakan yasata fasa kuka mai qarfi wanda saida iman tatashi daga barcin datakeyi.
Dasauri ya daka mata tsawa yace....
"Ah ah don Allah yi waje gada kisa muyi hassarar ribar damuka samu, ba k'aunar uban babyn kikeyiba zaki iya illata babynshi, gada kitayar mata da hankali nashiga wani yanayi "
Aguje farha tayi waje tana kuka, iman ta riqe hannunshi tareda zubar da hawayenshi tace...
"Hakane yafitar dakakira kayi domin ni? Kasani 'batawa yaya farha kamar ka 'bataman rayuwane, kyautata mata kamar ka kyauta taman ne, yaya jabbar yadda kake d'aukar yaya farha ada a ynx ba haka takeba, duk da bansan a wanne hali nazo assibitiba amma tunda na falka nake ganin kukan yaya farha akan ciwon dake damuna, bata barci bata cin abinci duk sbd sanadin ciwon dakake iqirarin soyayyar dakake yiman ne ya haddasa samunshi, toh kasani farha yr uwatace uwa d'aya uba d'aya wadda ita kad'aice gudan jinin damuka fito ciki guda, yaya jabbar inasonka sonda bansan adadin shiba, kuma kasan bazan iya rayuwa babu kaiba, saidai zan iya za'bar ganin mutuwata akan abunda kakeyima yaya farha"
Miqewa tayi da alamar fita taje gurin farha d'in, duk da juwar da ke d'ibarta amma zataje gurinta tadawo da ita ciki,kuka takeyi mai tsanani wanda hakan yasa hankalin jabbar tashi sosai.
Hanata tashi yayi tareda rungumeta yace........
*Bee Been masoya*๐
๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH๐ญ๐ญ*
๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
ยฉยฎ
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
๐๐๐๐๐
โ
TRUE LYF STORYโ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
Page...
โ
4โฃ1โฃโ
ยฎ mayar da ita yayi kwance, sannan shima ya bita kwance yayi mata rumfa da jikinshi yace....
"Iman ina zakije?"
Shiru tayi tana kallon sa, idonta na zubar da hawaye sosai, domin taji zafin tsawar da yayima farha,hakan yasata juyar da idonta gefe tace....
"My honesty, dama baka yafewa yaya farha ba,ka 'boye man kace kayafeta har abada?"
"Ah ah haskenah, wlhy na yafeta, amma kinsan maida martani akaina gsky ne a rayuwata akan farha koh? Domin irin wannan lkchn shine lkchn da yakamata nafara bata amsar tambayoyinta akaina, farha taceman matsiyaci, yau gani cikin wadata, farha taceman batasona, yau gani jikin mai sona, Iman idan ban fad'amata tajiba, yaushe zata san cewa ni jabbar nafi qarfin ajinta ynx? Nayafe abunda tayiman, kamar ciwon da yakamani domin ta, amma mayar da amsar ne ban yafeba dole na fad'a mata ita "
"Yaya jabbar! Yaya farha tagane laifinta, tagane kuskurenta na farko, kuma ta nemi afuwan akan laifinta, don Allah kamanta komai da yafaru tunda har kasamu madadin hakan a guna, idan kanason babyn dakake murnarsa samunsa yazo lfy, toh kasama man kwanciyar hankali anan, domin shine cikon samun natsuwata bayan kai"
Murmushi yayi tareda kai bakinshi cikin nata ya datse, yasaka hannunshi cikin nata ya matse,sannan yad'ago yakai halshenshi fuskarta ya lashe hawayen da keda saura, sannan yakoma bakinta yad'an samu relief kad'an, sai yaji duk 'bacin ranshi kuma yatafi yadubeta a cikin lumshe idonshi yafara kiran sunanta a natse yace...
"Khadijah, wannan kad'ai ya'bata maki rai? Toh kiyi haquri,zan kwatanta mantawa, amma kinsan abune mai wuyar mantawa koh? Toh duk da hakan zan kwatanta yin nesa da farha, domin ganinta kad'ai nasakani jin tsanarta, amma idan bana ganinta may b na mance, kiyiman lamuni iman, kinsan banda nake mai imani da yawa da a lokacin nakashe kaina, amma duka na haqure,sbd tsananin azabar data sakani ciki,amma ynx insha'allah komai zai wuce, idan nasamu baby nah a hannu, amma kiyiman murmushi nagani, inason naje na changr kaya, me kikeso nazo maki dashi?"
Murmushin tayi, sannan tace...
"Ni banason komai,amma agwaluma nakeso kawai kasiyoman "
"Tafd'i! Menene agwaluma kuma? Kuma ina xan sameta?"
"Oho nidai tambayata kayi, nabaka amsar buqatata"
Dariya yayi tareda d'an shafa cikin nata a hankali har zuwa qirjinta ya matsa kad'an kuma bai sauke hannunba saida yace...
"Nayi missing naku,sannan ga dear baby yanason takura mu,amma babu komai zamu dinga ganawa kad'an kad'an "
Riqemashi hannu tayi tareda ya mutsa fuska tace....
"A assibiti muke fa, sannan kowa zai iya shigowa,plx barci nakeji,kuma kaina ciwo "
"Sorry zan tafi, amma ba don mutaneba,domin bana tsoron kowa akan matata,sai dai don tayi barci"
Iman murmushi kawai tayi, itafa kad'ai tasan me take ji, daurewa kawai takeyi koh magana bata so sosai,sbd shine take amsawa.
Miqewa yayi tareda riqe hannun nata yace...
"Zan tafi, anjima xan dawo maki da abunda kikeso"
Iman murmushi tayi, har yabar d'akin baki d'aya,sannan tajuya don gyara kwanciyarta, nishad'in son mijinta har qarshen zuciyarta..................
_Afuwan banajin dad'i,mutane sun daman koh kad'an ne toh gashi arage fira_
*Bee Been masoya*๐
๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH๐ญ๐ญ*
๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
ยฉยฎ
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
๐๐๐๐๐
โ
TRUE LYF STORYโ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
๐ฟ *WASU MATAN*๐ฟ (a wannan zamanin)
NA
*~RUKEY HAROUN~*
*_masha'allah mmn nour, ina ta yaki murnanr k'arasa buk naki, ALLAH yaqara d'auka ka da zaqin hannu, ALLAH yaba da ikon sambad'o mana wani,ya kuma sauke ki lfy._*๐๐ป
Page...
โ
4โฃ3โฃโ
ยฎ Da sauri jabbar ya jawo rigar shi yasaka tare da, qara jawota jikin shi, duk ya rud'e sosai.
"Iman fad'aman me yasa mu cikin naji?"
Cen iman ta qara riqe cikin cikin kuka tace...
"Marata zata 'balle, wani zafi take yiman, ciwo wlhy "
"Subhanall! Iman nine koh? Wayyo nabani, idan cikin nan yasa mu mtsl bazan ta'ba yafuwar kaina ba, nara sa hankali na ne wlhy, ban san inda kai na yaje ba, ina son na k'yaleki amma na kasa, dana tuno halin da kike ciki sai kuma na manta, Ina zuwa kad'an "
Da sauri ya fita don zuwa fallow d'auko wayar shi, doctor habib ya kira, nan take ya d'auka tare da cewa....
"Engineer har ka iso kenan?"
"Eh doctor, akwai mtsl fa! Don Allah kana assibiti koh gida?"
"Ah ah nata shi aiki, gani gaban madam, wani abu ne?"
"Eh doctor marar iman ke ciwo, plz ina zan sameka?"
"Ok ba mtsl, kujirani kad'an gani zuwa, amma tambayar ta jini bai fara zuba ba koh?"
Yajuya yafara tambayar ta, kai kawai ta d'aga mashi alamar babu komai.
"Eh tace babu komai, na jira anan koh?"
"Eh gani zuwa"
Kashe wayar jabbar yayi tare da jefar da wayar gefe, ya jawo doguwar riga ya saka ma iman, ya zauna gefen ta tare da kwanto da kanta k'afafun shi, sai sannu yake yimata, tare da shafa marar a hankali.
Jin isowar mota harabar gidan nasu, yasa jabbar saka ma iman hijab tare da d'aukar ta domin bazata iya tafiya ba, yakaita kujerar ya kwanta sai wani lumshe idon bala'i take yi, bud'e qofar yayi doctor d'in yashigo, sannan ya fara yimashi bayanin abunda ya faru.
Nan take likitan ya gano mtsl da takawo hakan, allura yayi mata ba don ta so ba,sannan yace a kwantar da ita zai daina ynx nan, suka fita tare, anan yake bashi shawarar yadaina da muwar cikin cen, domin har ynx bai yi qwarin da za'ayi mashi bankar da yake yimashi ba, domin daga kalar wancen ciwon marar sai jini ya 'balle mata , daga nan sai cikin ya fad'o.
Sukayi sallama, jabbar ya gode Allah da hakan bata faru ba, kuma insha'allah zai jure har xuwa lkchn da cikin zai girma, duk da wata barazanace a rayuwar shi, bale yau da ya d'an d'ana yadda ni'imar mai ciki take,amma zai daure.
Komawa yayi ciki, yayi mata sannu, domin abun ya lafa, d'aukar ta yayi, sai toilet domin tsalkake jikin su, izuwa yin sallar magariba,anan yace ta kwanta yana zuwa, tea ya had'o mata tare da tayar da ita yabata a baki sannan yace ta kwanta, shikuma yafita don saita fallow d'in da kuma cin abinci, sannan ya zauna yin wani aiki nashi.
โ
โ
โ
โ
Ahaka rayuwar tayi ta tafiya, idan jabbar baya gari, iman na gidan umma, duka kulawar ta ta rataya hannun farha, duk da pant farha ke wanke ma iman, sbd cikin ynx ya girma ba ko mai take iya waba.
Acikin wannan lokacin ne farha ta nemi da a taimaka abarta takoma makaranta domin zaman ba wani umfani zai yimata ba, ga rasheeda har tafara aiki.
A hakan sai iyayen suka ga dacewar yin hakan, mahaifinta shi yayi mata komai, sai dai Nursing school tashiga domin tun farko under healt ta fara karantawa a university d'in su,hakan ya sanya ta koma mkrnt tare da kulawa.
kafin tafita zuwa mkrnta sai ta tabbata iman bata buk'atar komai sannan zata fita, wannan kulawar kawai da takeyi ma iman yasa iyayen ynx suka fara k'aunarta ba kamar umma ita dake tare da su tana ganin halayen kowannensu. iya ynx tasan cewa jabbar koh kallon banxa farha bata isheshi ba, hakan yasa ummar bata tsaurara mashi ba domin tasan cewa ynx farha ba zama take yi ba, shima kuma baya koh gari sai in ya shigo.
Farha na tafiyar da karatun ta yadda ya kamata, tunda farha ta fara zuwa makaranta koh yaushe cikin shiga ta alfarma wadda hijab take sakawa har k'asa, tare da niqab a fuskarta, tun da take zuwa school d'in ba ruwanta da kowa koh yaushe ita kad'ai take zaune tana karatunta, duk gefen da tasan zata had'u da maza tana