Showing 18001 words to 21000 words out of 55052 words

Chapter 7 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE by FATIMA ZAHRA

28 May 2026

26

daddy bai siya min ba,




' Qarya kakeyi kana da Ita, wacce kaba yaya ya ajiye ma rannan.... ka tuna? kaje kace yaya yabaka bindigarka muyi Wasa.






Pherty🎤👯


Babana da mijina.....




©fertymerh Xarah 💞




20




Da kyar ya iya saita numfashin sa gurin Iman ya kawar da jinsa gurin su fauxie amma hankalinsa a matuqar tashe,




Ya kasa furta mata ko wace irin kalma, baisan yanda xai bayyanata a cikin mutane cewar wadda xai aura ce,




Ganin haka Iman ta ďauke idanuwanta akansu ta maida kallonta ga su fauxie dan samawa xuciyarta sassauci kuka ma xata iya a Wannan lokacin, mijinta ya kawo mata wata mace a gida shiyasa bai damu da bata haqqintaba saboda yana da wasu matan a waje ta sauke ajiyar xuciya, salima ta kasa haquri cos Macece Mai xafin kishin tsiya,




'ita Kuma Wannan Wacece Ahmed, dai dai lokacin fauxie ta qaraso tana faďin,


'yaya wai Adnan ka bashi bindigarsa xamuyi wasa,




'Kuje ina tashi xn ďauko masa,




'wace bindiga kuma? Cewar salima tana kallonsu,




'toy gun ce na siyo masa ranar ita take mgn cewar Deedah cikin dakewa?




'Malama ke wacece wai kinxo kin xauna gidan mutane,




Saudah ta dubeta cikin basarwa,
'ki tambayeshi mana shi da yaxo dani,




Sa'eed yace ba ruwanki salima matarsa bata tambayesa ba sai ke,




'wallahi sai na tambaya ai ni aminiyarta ce dole na tambayar mata, kayi mgn Ahmed,




Deedah ya kasa mgn ganin yanda Iman ta ďauke fuska daga gareshi yanayin fuskarta ma kesa hankalinsa daďa tashi,




Saudah tace tunda kin matsa kiji koni wacece to budurwarsa ce, yace naxo naga matarsa bata lfy,




Sa'eed na jin haka ya tashi yana kiran su Adnan ya dubi salima tashi muje gida, daga kallon yanayin sa xaka karanci bacin rai a tare da fuskarsa yasa kai ya fice,




'Amma ke Anyi wawiyar mace inda xaki biyo namiji har gidan aurensa wai kinxo gaida matarsa, kina budurwa ko kunya bakyaji koda yake ba abin mamaki bane tunda mutuncin ya riga ya xube a titi, ta dubi Iman dake sauke numfashi da kyar,




Fatyma sai kinyi a hankali fa saboda cutar xamani.... tasa kai tafice tana faďa sosai ranta ya baci,


Suna ficewa Iman ta tashi taja hannun fauxie sukayi ďakin ta,




Saman gadon fauxie ta xauna ta saki wani irin kuka mai cike da qunar xucci, fauxie tayi shiru tana kallon yayarta kafin taje ta kwanta a bayanta,




'Anty kiyi haquri, anty kiyi haquri shine kawai abinda take faďa har Deedah na shigo ďakin, yanayin da ya same su yayi matuqar tausaya masu sai yake nadamar xuwa da saudah amma bayajin xai iya fasa aurenta a yanda yake son yara ynxu ballantana saudah tace xata bashi soyayya mai cike da kulawa.....


A wanna lokacin faďa sukayi sosai dashi, borin kunya yakeyi dan me xata wulaqanta baquwarsa, itama rufe idanuwanta tayi ta Hausa da faďa sosai,






Wannan yana ďaya daga cikin tarihinta rayuwar aurensu basu taba faďa ba sai yau Kuma mai tsanani, fauxie na daga gefe tana kallonsu ta tsurawa bakin Deedah ido tana ganin ynda yakewa fatyma faďa sosai sai ta soma jin haushinsa ta qara matsawa jikin yayarta ta kwanta sosai tana kuka domin a ruďe take da sabon canjin da tagani tsakanin yayarta da yayanta, ita kuka Iman kuka ba mai rarrashin wani har ya gama fadansa yasa kai ya fice, ta rungume fauxie sosai a jikinta kamar wani xai kwace mata ita,




Ta karbi wannan jarabawar da Allah ke mata da hannu biyu tasan watarana sai labari amma ta rasa gane kan mahaifinta da mijinta me suke nufi da ita?




Tun daga lokacin daga ita har Deedah suka ďauki fushi mai tsananin gaske da junansu,


Baxai shigo gidan ba sai gab da asuba, wanka kawai xaiyi ya fice daga gidan, abinci ma ya daina ci a gidan tunda yanada saudah a ynxu,




Iman ma bata taba nemansa ba qoqarinta a ynxu na ganin ta Kula da rayuwar qanwarta Sau da ke Dama fauxie kan tambayeta ina yaya.... ina yaya,




Takan xauna ita kaďai tayi tunanin rayuwar da take ciki sai dai tayi mgn a xuciyarta, inada mahaifi kamar bani dashi Muna rayuwa a gida ďaya amma baxan iya kaimashi kuka na ya sharemin ba, nasani akwai wani lokaci da xaixo Wanda *babana da mijina* xasu kasance cikin tsananin nadama kan abinda suka min,




Har tsawon sati uku ba wani canji daga gareshi duk da shima kawar da kaine kawai yakeyi amma yasan fatyma itace rayuwarsa wannan Faďan da sukayi yafi kowa damuwa,




A yau ta shirya tarbon mijinta, xata sauke duk wani fushi dake kanta ta bashi haquri tunda yace ta kasance mai laifi a garesa ta wulaqanta budurwarsa, ko ba komai mijintane, mahaďin rayuwarta kuma aljannarta tana tsananin buqatar mijinta a yau, tana wannan tunanin take haďa masa abincinsa a dinning tanayi tana share kwalla dan batada tabbacin xaici ko baxai ci ba,




Anashi bangare shima haka, ya gaji da wannan fushin na matarsa, ko yana tare da saudah bayajin daďi kamar yanda yake tare da Iman, yasan shi mai laifine a gurinta na kawo mata budurwarsa har cikin gida Sannan ya rufeta da faďa, dole xai ďauke girman kansa yaje ya nemi yafiyar matarsa,




Da Wannan tunanin ya qaraso cikin falo, tana xaune tayi kyau cikin wata atampha,sai ya tsinci kansa cikin jin kunya da nauyinta ya kasa qarasawa cikin falon,




Qamshin turarensa ya sanarda ita xuwansa tana juyawa Kuwa ta ganshi tsaye,murmushi ta sakar masa kamar ba abinda ya taba hadasu ta taso kamar yanda ta saba taryarsa,




Tsananin mamaki da jin daďi suka hana masa motsi daga inda yake tsaye musamman lokacin da yaji ta rungumesa haďe da sumbatarsa a goshi, sai ya riqota sosai yana sauke numfashi da sauri da sauri,




Ta jasa suka nufi sama, ruwan wanka ta haďa masa bayan ya fito ta taimaka masa ya shirya cikin kayan barci kana suka nufi dining da kanta take ciyar dashi bayan sun gama ta soma bashi haquri yayi Saurin rufe mata bakinta,




'Ni ya kamata na baki haquri Iman, ki yafemin ni nasan Mai laifine agareki a koda yaushe, murmushi kawai tayi,




Ranar sun jima suna hira fauxie dama tuni ta dade da yin barci,




Bayan wani lokaci suka nufi bedroom ďinsu ga mamakinta Deedah addua kawai yayi ya kwanta, sai ta kasa haquri ta fara masa qorafin fitar da yakeyi a da ynxu ya maidata ina yake xuwa kwanakinnan Kuma meyasa baya nemanta?






Ya tashi xaune yana kallonta,


'inaji mun gama solving wannan issue dake tuntuni kan fita ta, aiki nake xuwa Kuma training nake xuwa and what else did you want to know, idan ban fita na nemo ba so kike na xauna a gida ina bata lokacina a banxa ko Kinsan yanda na sami aikin, kinsan wahalar danayi kafin na sami aikin? Ki gayamin menene bana miki tun daga ci, sha sutura da sauransu, dame na rageki a gidan nan fatyma?




Tsananin tsoro da kaďuwa yasa tana kallonsa da mamakin jin furucinsa, yau Deedah call her with her real name, meke faruwa kada ya daina son tane a ynxu, nan da nan jikinta na soma rawa da kyar ta iya buďa baki tayi mgn,




'xaman ka dani shine bata lokaci Deedah? Idan ban rasa ci da sha a gidan ka ba na rasa soyayya da kulawarka, nima xn iya Kula da kaina da qanwata ta qarfin aikina ko babu kai da babana Deedah..... ta soma hawaye sosai,




'har sai yaushe xaka xauna dani kaji damuwata idan har kai baxaka iya gayamin taka ba, tell me Deedah kasan matsalata a Yanxu da Abinda ke damuna? You are my life partner idan ban xauna dakai na gayama damuwata ba dawa kake so na xauna, babana ya gujeni nida qanwata banda kowa a duniyarnan da xan kalla naji daďi kamar kai, nayi xaton bayan miji da yaya xaka xame mana uwa uba nida Fauxiya, (kuka take sosai)




'Baka xama damu, haqqina ma baka bani, zina kake so nayi kome? Ko wani namiji kakeso naje na nema a waje, auren soyayya mukayi bana qiyayya ba har sai yaushe xn sami kulawarka, kasanya neman kuďi a xuciyarka kana so ka manta ko kai waye, tell me miye amfanin Kuďin da babu kwanciyar hankali akai, ka kwashe dukiyar ka bana so kulawarka nakeso, I want you to know am not satisfied with you....... buďar bakinsa sai cewa yayi




'Ashe baki da kunya Iman, ni kike ma tsawa, are you shouting on me or what? to baxan ajiye aikina saboda ke ba.....




Xatayi mgn kenan kuka yaci qarfinta sai ta juya da sauri tabar ďakin ta nufi ďakin fauxie tana kuka sosai Kamar ranta.




Pherty🎤👯


BABANA DA MIJINA.......




©Fertymerh Xarah 💞






21






Kukan ta da hawayenta ba qaramin ďaga masa hankali yayi ba sai ya sauko ya bita shima,




Gab da xata sauka step ďin ya rungumeta sosai Kamar xai tsaga kirjinsa ya sanyata ciki Mai yiwuwa Sannan ne xai xamo contented, ya juyo da Ita yana fuskantarta,




Did I hurt you Iman? tayi masa shiru sai sheshshekar kukanta,




Shikenan naji xn gyara, xan cnxa xn rage fitar na xauna na kula dake, xn riqa baki haqqinki akai akai idan su kaďai ne damuwarki amma ni banason Wannan Kukan naki,




tayi shiru batare da ta tanka ba idan da sabo ta saba da jin Wannan Mgnr kullum xn cnxa kullum xn cnxa har yau bai cnxa ba ta lumshe idanuwanta cikin qunar xucci,




A hankali yakai bakinsa dai dai nata yasanya harshensa akan labbanta yana xagayawa dashi har ya isa cikin bakinta,




Shikansa yayi missing ďin ta he don't know sai yanxu daya ruďe yana kiciniyar rabata da kayanta da sauri ta riqe masa hannu tana son janye jikinta daga garesa har ynxu xuciyarta bata huce akansa ba,


A yanda ta lura idanunsa sunyi jawur ya soma fita hayyacinsa baxai iya kyaletaba, itama a buqace take sai ta saduda ya ďauketa ya nufi ďaki da Ita....




Washe gari har yaso ya makara koda ya tashi bata ďakin, bata tayarda shi ba saboda har ynxu bata huce ba, ya lura da hakan tunda asuba da xasuyi sallah, ya tashi a gurguje ya nufi toilet,




Koda ya shirya ya fito daga ita har fauxie ba kowa a gidan, tayi gurin aiki fauxie Kuwa tayi Skul, ya jinjina kansa lallai abin Iman babbane,




Tun da taje asibiti aikin komai batayi ba, tana daga xaune iyakarta da patient rubuta magani ko dubasa amma bataje karban haihuwa ba kamar yanda ta saba a kullum,






Bayan wasu awanni likitocin suka dawo duk aka haďu a consultant nan aka fara barkwanci kamar yanda suka saba ana dariya, Iman na xaune komai batace ba illah idanu da ta xuba masu tana kallonsu ďaya bayan ďaya,


A tsarin halittar ďan adam personality tana cikin rukunin al'ummar da ake kira introvert da wuya kaga haqoranta sai idan likitocin sun kaure da rigima tayi murmushi tana kallonsu wani sa'in kuma tasa baki, she is simple batada hayaniya,




Yanxu ma murmushin take tana kallonsu duk mata ne yan uwanta likitoci, basu damu da rashin sanya bakinta a ciki ba cos sun santa sunsan halinta,




Tashi tayi tana harhaďa kayanta da alama tafiya xatayi,




Dr Hauwa ta dubeta tana faďin, idan gida xakije Dr fatyma taimaka ki saukeni a hanya,




'ba gida xnje ba, banki nakeson biyawa na fiddo Kuďin Skul fees ďin fauxie,




Tace shikenan Bari Dr Fulani ta saukeni, yau bada Mota na xo ba,




Iman tayi masu Sallama ta fice, bata taba biyawa fauxie Skul fees ba sai wannan karon da mahaifinsu ya yafe su yamaida responsibility ďin fauxie hannunta Kuma she accept xata Kula da qanwarta duk abinda take so xata iya mata a rayuwa indai baifi qarfinta ba,






Akan hanyarta ta xuwa take wannan xancen xucci harta iso bankin da Deedah ke aiki,




Sai da ta gama Abinda take tukunna ta nufi office ďinsa, batayi tunanin neman Sa'eed ba, batare da tunanin komai ba ta shiga office ďin yana xaune da laptop a gabansa sai faman dannata yakeyi, sallama tayi ta qarasa shiga,




Muryarta kawai yaji ya ďago da sauri yana kallonta,


Ta qaraso ta xauna kujerar dake fuskantarsa fuskarta ba walwala,




'Sannu da aiki yayan fauxie, bai amsa mata ba da alama baiyi farin cikin xuwanta a Wannan lokacin ba duk da bata taba xuwa office ďin sa ba tun bayan auren su,




'Iman wannan tafiyar ta baxata fa, me kika xo yi? tayi masa wani kallo




'tambayata kake dan naxo naga mijina, ko laifine Deedah? ya girgixa kansa yana murmushin yaqe




'ba laifi bane kuma naji daďi sosai amma naga baki taba kawomin irin wannan xiyara ba,




'tace hakane, skul fees ďin fauxie na....... bata qarasa ba aka buďe qofar office ďin aka shigo,




'cwty you have been waiting da kyar umma tabarni na fito,




Yayi shiru bai amsa ba hankalinsa inyayi dubu ya tashi, Iman ta juya tana kallon wacce ta Kira Deedah da cwty, saudah ce rataje da qaramar jakarta cikin doguwar riga ta atampha, bata lura da Iman xaune a gurin ba ta isa inda yake ta sumbacesa a goshi,




'da sauri ya ture ta cikin borin kunya, me kike yi haka Ashe baki da kunya....




Ta ware idanu tana masa kallon mamaki sai alokacin ta lura da Iman dake xaune tana kallonsu,




'oh no wonder shiyasa xakayi rejecting ďina, kace rival ďita ce a banki, ta juya tana kallon Iman,




'sannu anty ya aiki, Iman ta amsa da




'Alhamdulillah cikin basarwa, saudah ta sami guri ta xauna,




'wannan yanayin yafi komai yimin daďi gani ga uwargidanka, ka gayamata matsayina na amaryarka,




Deedah ya dubeta, get out of my office saudah, ban taba sanin baki da tarbiya ba sai yau, duk iskancin ki ya tsaya kaina kada ya kai ga matata,




Dariya tayi ta gyara xamanta, Iman kallonsu kawai take kafin ta tabe bakinta ta tashi da Jakarta a hannu ta fice,




Tana fitowa sukaci Karo da Sa'eed shima ya fito nasa office, a tare suka sakarwa juna murmushi bayan sun gaisa sai suka jero tare suka fito farfajiyar bankin xuwa inda tayi parking, tun basu qarasa ba taga fitowar saudah a fusace, Sa'eed ya dubeta




'yau ina qawar rakiya fauxie bn ganku tare ba,




'fauxie na skul, school fees ďin ta naxo fiddawa gobe nake son naje na biya mata,




Yace hakane, nima Adnan gobe nakeson biya masa,




Tace ko na baka na fauxie ka haďa ka biya masu pls, ta ciro Kuďin daga jakarta ta miqa masa,




'nawa ne Kuďin,
'65,000
'barsu hannunki a Yanxu idan na tashi aiki kafin naje gida xn biya na karba gobe ina biya sai na kawo maki receipt ďin,




'shikenan Nagode sosai ta maida Kuďin jaka akan idon wasu matasa su kusan shidda da alama yan fashi ne,




'Nine da godiya, kinga Deedah kuwa? ta yatsina fuskarta




'naganshi, bara na tafi Sa'eed sai kaxo,






Sukayi Sallama ta shiga motarta ya juya cikin banki,






Tun da ta fito daga banki taga alamar kamar wata Mota na bin bayanta, ta glass take tsinkayosu motar cike take da maxa harda bindiga tana gani, hankalinta yayi matuqar tashi ta qara gudun motar sosai sai taga suma sun qara gudu,






Gudu take shararawa kan titi kamar xata tashi sama suna biye da Ita, su kansu dake cikin motar suna mamakin yanda ta iya Mota haka gashi sun kusa shiga gari xasuyi missing Kuďin da suka gani hannunta,






'world best ko asakarwa motar bullet ne, yarinyar ta kware wurin Mota sosai,




'A'a kada ku harbeta an shigo gari, asirin mu xai iya tonuwa kawai mubita muga gidan anjima muje mu karbi kason mu,






Tana shigowa layin su ta soma horn sosai tun kafin taxo gate an buďe mata ta shiga,




'kai gidan ďan siyasar nan ne Alhaji Abdallah fa,




'abin yaxo dai dai ai, muyi shiri sosai muxo gidan kasan akwai kuďi fa anan, muyi qoqari muci nasara dan naga harda yan sanda ke gadin gidan da alama Mai gidan na gari, in sunyi gardama ayi watsin alburushi kowa ma akashe.....




Sukayi dariya haďe da jan motarsu da sauri suka bar layin,






My Wattpad Phertymerh1


Babana da mijina.......




©fertymerh Xarah 💞




22






Harabar gidan maqil take da maxa da mata yan siyasa haka ya tabbatar mata da cewa baba yana gari,




Da kyar ta iya samun guri tayi parking kasancewar motocin dake gurin birjik, har lokacin jikinta bai daina rawa ba,




Taron siyasa suka gama da alama, taga suna watsewa suna shiga motarsu ďaya bayan ďaya,




Ta fito daga cikin tata motar ďauke da jakarta, ta rufe motar tayi hanyar gidanta anan taci Karo da baba ko ta ďaga fuska ta kallesa ballantana ta gaidasa, fuskarta a ďaure tamau tabi ta gabansa ta wuce batare da ta kallesa ba,




Kallo yabi ta dashi haďe da cixon labbansa cikin jin xafin halin ko inkula da ta nuna garesa a gaban mutane,






Tun kafin ta qarasa gidan take jiyo Kukan fauxie, ta duba agogon dake maqale a hannunta 11am baa isa tashi Skul ba to meya maida fauxie gida, ta hanxarta da sauri domin yanda take jiyo kukanta har cikin kanta Kuma ta tabbata baba ma yanajin Kukan yarinyar amma bai damu ba,




Tana shiga falon ta ganta jikin adama tana jijjigata sai kuka take tana kiran anty, anty,




Da sauri ta qarasa gurin adama tana tambayar meya sameta,




'hajiya tun ďaxu malamar su ta kawota batada lfy sai kuka take, Iman ta karbeta jikinta xafi sosai idanunta a lumshe da alama ta jima tana kuka yanda idanun suka kumbura fuskar tayi jawur, ta kalli adama




'amma shine kin san da haka bakimin waya kin sanarda ni ba, inda bn dawo ynxu bafa, kina nufin sai kibarta tayi ta kuka,




'kiyi haquri hajiya nagayawa yallabai babanta yace inje kawai nayi xaton xai xo ne shinake jira tun ďaxu shiru, Mtseww Iman taja tsaki ta xauna rungume da Ita tana kiran sunanta a hankali,




Sai ta buďe ido luuuu sai sukoma su rufe, taji kanta yafi xafi sosai, ta cire mata uniform ďinta tana faďin,




'ďauko min wata riga na sanya mata adama, ta juya bata jima ba sai gata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login