Showing 39001 words to 42000 words out of 55052 words
Chapter 14 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE by FATIMA ZAHRA
Wasa da ita suje yawo ba, shikenan baxasu qara cin abinci tare ba, baxata qara ganinsa ba itada anty, ta juya tana kallonsu duk sunyi shiru, ta gigice ta fita daga ďakin haďe da fashewa da irin Kukan nan Mai qara irin na yara, da ka ganta kasan a gigice take batasan inda xataje ba,
A tsorace ta farfado daga barcin da take, xuciyarta na tsananta bugawa ta tuna Deedah da yanda ta barshi, ta sauko daga Saman gadon da sauri haďe da fisge drip ďin da ake sanyamata a hannu,
Mararta a qule take har lokacin tafiya take a hankali ba takalmi ba mayafi sai kallabi akanta, kallon xararra ake mata a asibitin ga Waďanda basu Santa ba duk inda tabi sai an kalleta, kai da kaganta kasan haihuwa tayi saboda xaninta duk jinine,
Nurses ďin da suka Santa suka biyo bayanta da sauri suna kiran sunanta, tanaji ta kyalesu sai ta qara Saurin qafafunta musamman ynxu da take jiyo Kukan fauxie sai ta qara ruďewa,
Tun daga nesa ta tsinkayo fauxie na kuka a jikin Dr Deen, tana qarasowa ana fitowa da gawar baba,
Ta tsaya cak tana maida Numfashi da kyar kamar wata zakanya jikinta sai karkarwa yake, juyowar da xatayi taga anfito da Deedah, Sa'eed na bayansu yana sharar kwalla Idanunsa sunyi matuqar ja,
Fauxie na ganin an fito dashi ta qara fasa ihu a gigice tana neman kwacewa jikin Deen, iman Kuwa qarasawa tayi ta riqe gawar,
'meyasa kuka rufesa ai bai mutu ba, ku duba suma ne yayi, Deedah baxai mutu ya barni ba, wannan lokacin Kukan da take harda majina ta xama wata xautacciya,
Duk qarfin hali irin na mutum idan yaga halin da Iman take ciki a Wannan lokacin sai ya xubar da kwalla,
'Deedah ka tashi sugani su San cewa Baka mutu ba, Deedah ka tashi kaga yaron da muka haifa, meyasa xakaje ka barmu a lokacin da muke tsananin buqatar ka,
Taje ta riqe Merah,
'kace su dawo dashi acigaba da kula dashi anan, Deedah bai mutu sai idan kune xaku kashe shi,
Fulani ta qaraso da jaririn a hannunta har lokacin kuka yake kamar yasan abinda ke faruwa, tunda ya faďo duniya yake kuka,
Kukan yaron har cikin kanta take jinsa, ga Kukan fauxie dake qara rikita kwakwalwarta, tana ganin lokacin da suka sanyasu a mota ta tabbata lallai gida xa'a je dasu ayi masu wanka da sallah akaisu makwancinsu, shikenan Deedah yaje yabarta.....
Cak numfashinta na ďauke, sai ta xube gurin a sume....
My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina*
©Fertymerh Xarah 💞
34
*Masu turo ta'aziyar Deedah, iman na godiya sosai, saqonku ya iso*.
Tana xubewa gurin su Dr Umayma sukayi kanta, fauxie na ganin lokacin da ta faďi ta soma neman saukowa jikin Deen tana kuka amma ya riqe ta tamau sosai a jikinsa,
Aka sanya gawarsu a motar Sa'eed, shi yaja motar su Merah na bi bayansa da nasu motocin,
Iman Kuwa motar Dr Deen aka sanyata tare da sauran likitocin fauxie na kusa da ita fuskarta ta qara kumbura tayi jawur ga ciwo ga kuka, kanta har nauyi yake mata ga wani Xaxxabi da take ji wannan karon baxata sami kulawar Iman ba cos ita kanta bata cikin hayyacinta, mutuwar mahaifi da miji a lokaci ďaya (it's the greatest loss of all losses),
A Wannan ranar xo kaga jama'a, mutane kamar me, nan da nan gari na ďauka mutuwar Alhaji Abdallah abinka da ďan siyasa sananne a gari,
Mutuwar taxowa mutane a baxata daga shi har Deedah ba Wanda aka yiwa tsammanin mutuwa a ynxu,
Abokan Deedah suna cikin ruďani da tsoron Allah, duk Wanda yace shine yau ba shi bane gobe, mutuwar sa ta girgixa shi idan suka tuna jiyama suna tare dashi a office, ya sami kyakkyawar Shaida daga garesu,
Ma'aikatan gidan maza da mata tamkar sune akayiwa mutuwar, kuka suke sosai sun san qarshen barin su gidan yaxo, ba uban gidansu to Waye xai riqa biyansu Waye xai riqa ciyar dasu, wasu ma da gidan suka dogara,
Sa'eed da kansa yaje part din baba ya rufe ďakunan sa na dukiya, mutanen ynxu basu da amana wani baxaiji tsoron ana cikin wannan tashin hankali ba suje yiwa marayu sata wannan ne dalilin dayasa ya rufe,
Anje yiwa gawarwakinsu wanka, a Wannan lokacin fauxie na rakube a bed side kanta a langabe, barci take daga xaune tana gyangyaďawa kamar xata faďi,
Iman Kuwa tana xaune da jinjirin a hannunta tana bashi mamma, ance kuka ma rahama ne Wannan Karon kam Kukan yaqi ya xo xuciyarta a bushe take, kallon jaririn take,
Yaxo a MARAYA, yaxo duniya babanshi yabar duniya, kakanshi ma yabar duniyar, duk da haka yaronta baxai taso cikin maraici da rashin gata ba, xata bashi tarbiya ta kula dashi shida fauxie tamkar Iyayen su na raye, bata da sauran buri a rayuwarta ynxu na ganin ta Kula da marayun biyu, ta sauke nauyin dake kanta akansu, aure baxata sanyoshi gaba ba aynxu a tsorace take da kowane namiji da halayyarsa, xata cigaba da rayuwarta a hakan, Wanda take so ya tafi yabarta tana roqon Allah ya sa shine mijinta ko a lahira,
Sai a lokacin hawaye na samu xubowa daga idanuwanta ta rumtse idanuwanta suka xubo akan fuskar jaririn Wanda ke barci tuntuni,
Fulani ta karbi yaron ta goya, sai Iman ta maida kanta jikin cinyoyinta tana kuka sosai,
Sanda aka gama masu wanka aka Kira Iman tayi masu addua, kuma tayi cikin jarumta da dakewa irin tata, ba Wanda batayiwa addua ba acikinsu, tana gani aka ďauki gawarsu,
Sai ta bisu da ido idanunta taf da hawaye fuskarta ďauke da murmushi,
'I know Deedah must come back to me, ni nasan bai mutu ba, nasan Deedah baxai je yabarni ba, bayan yace xamuyi rayuwa tare mu raini jaririn mu tare,
Xuciyarta ta cigaba da bugawa lokacin da aka fita dasu, taga yawan jama'ar da suka cika gidan sai taja jikinta ta koma ta xauna, tana bin mutanen dake falon da ido tana kallonsu suna kuka,
Bataga dalilinsu na kuka ba, Wanda suke wa kuka xai dawo tasan xai dawo, xai dawo..... xai dawo haka kwakwalwarta ke bata
Sai ta fashe da dariya, duk gurin aka juyo ana kallonta, ko miye abin dariya ga Wanda akayiwa mutuwa?
'lafiyar ki kuwa? Cewar salima tana kallonta cikin tsananin mamaki,
'tor miye amfanin Kukan da kuke, baba ne kawai ya mutu banda mijina, nasan Deedah yana raye, ynxu xaku ganshi ya dawo xaiyi wanka yayi shirin xuwa masallaci bara naje na fidda mashi kayan da xai sanya a yau, ta tashi tayi ďakin sa,
Mutanen falon suka kalli juna cikin tsananin mamaki, Fulani tabi bayanta da sauri,
Ta juyo da kafadunta suna fuskantar juna,
'Kinsan me kikeyi fatyma, me kike son nunawa mutane, baki yarda da qaddara bane keba musulma bace?
'my husband is alive Dr Fulani, Kune keson kashe sa, jiya fa muna tare, yau ma munyi mgn dashi, ya roqeni gafara Kuma na yafe masa, shine fa ya suma kuke kiran ya mutu,
'Wanda ya mutu baya dawowa Iman, kada ki ruďar da kanki, ki nutsu dan Allah kada wani abu ya sami kwakwalwarki, dan Allah fatyma kixo muje falo kicigaba da yi masu addua, kinga ga yan uwanku ma suna ta xuwa.
Iman tayi shiru Kamar mai naxari sai Kuma ta dubeta,
'tell me Fulani idan Marhoom ne ya mutu me xakiji?
Sai da xuciyarta na buga ta gyara goyonta tana kallonta,
'me ya kawo wannan mgnr Kuma? Idan ma mutuwa yayi haquri xanyi nayi tawakkali ga Allah, nasan yafini sonsa Kuma nasan yafiye masa duniya daďi,
Iman ta girgixa kanta,
'you are not saying the truth Dr fulani, baxaki iya jurewa ba, bakisan xafin dana keji a xuciyata ba, bakisan ciwon da Mace take ji idan ta rasa abokin rayuwarta ba, ballantana irin nawa rashi na *babana da mijina* a lokaci ďaya, ta soma hawaye sosai,
ta juya tana ciro kayan Deedah,
'ni nasan bai mutu ba xaki ganshi sun dawo dashi,
Fulani tayi shiru tana kallonta cikin tausayawa, itama ta tsinci kanta cikin kuka sosai ta fice daga ďakin da sauri.
Haka Iman ta fito da kayansa, juyowar da xatayi tayi arba da tangamemen hotonsu dake manne a ďakin, yana rungume da Ita suna yiwa juna murmushi, sai ta saki murmushi tana faďin,
'Haba taya ma xasu ce Deedah na ya mutu, nasan xaka dawo kaxo kabasu mamaki su san cewa kana raye......
An kaisu makwancinsu an rufesu daga su sai halayyarsu sai abinda suka shuka a duniya, in hairan hairan in shairan shairan, wani abin tsakaninka ne da mahaliccinka, idan ka kasance mai tuba agaresa,
Duniya kenan....
Babu dukiya aciki, babu gida mai tsada, babu mota mai tsada, babu abinci mai tsada, babu lallausar katifa mai taushi da tsada, babu Mulkin da ake taqama dashi,
An kaika inda xaka xamo abinci ga tsutsoci, qasar da kake taki da takalmi yau kaine acikinta timbir, babu mai ceton ka aciki sai Allah, sai aikin da ka aikata a duniya, ya Allah ka tsare mu da azabar kabari, kasa muyi kyakkyawan qarshe mucika da imani Amin.
Sa'eed kuka yake sosai Idanunsa sunyi jawur, shikenan Deedah yaje ya barsu, baxasu qara ganin Deedah ba, yayi rashin aboki, Allah ka gafartawa Deedah ka Kai haske a kabarinsa kamar yanda goshinsa yayi haske lokacin da suke masa wanka,
Suna dawowa jana'iza suka nufi gidan, tun daga waje suka fara gaisuwa ga mutane birjik an shimfida Manya Manya tabarma saboda masu gaisuwa, yan uwan su Iman ne a waje da suka xo,
Kai tsaye su Dr Merah suka nufi falon Iman domin yi mata ta'aziya, tana ganinsu ta tashi da sauri ta nufesu, sai leqen bayansu take burinta taga Deedah a bayansu amma wayam,
Ta dubi Dr Merah, Dr Deen, Dr Bakori, Sa'eed, sai taga suna hawaye kowane na jin nauyin haďa ido da ita a yau, bakinsu yayi nauyi ga duk kalmar da xata fito bakinsu,
'Banga Deedah ba likita, ina kuka barshi?
Merah yayi qarfin halin mgn, Idanunsa akan nata,
'Dama Wanda ya mutu yana dawowa ne Iman? Deedah is dead, Deedah has gone and he will never come back, ya tafi ya barmu dole haquri xamuyi da wannan rashin Allah ya fimu sonsa mutuwa na kan kowa,
'wace mgn kakeyi likita, Kada kace min da gaske Deedah na ya mutu, ya tafi ya barni nida qanwata, ya tafi yabar jinjirinsa, dan Allah kace masa ya dawo, yaxo ga kayanshi ya Sanya yaje jumma'a, ta juya tana neman inda ta ajiye kayan,
Kai da kaganta kasan bata hayyacinta a ruďe take, inbashi ba, mace kamar Iman Mai kunya da kawaici, Mai haquri da tawakkali, Mai hankali da nutsuwa, yasan da hankalinta baxata tsaya gabansa tana wannan mgn ba ynda take matuqar girmamashi,
Gabaki ďaya falon suka ďauki kuka, Dr Deen ya fita da sauri shida Sa'eed baxasu jure ganinta a Wannan halin ba,
'ki nutsu fatyma, Merah ke gabanki, baxan maki qarya dan na cutar dake ba kinsani, Deedah ya tafi inda baxai dawo ba Kinsan miye mutuwa please pray for your father yana buqatar addua sosai akan Deedah, Deedah ya tafi cikin kyakkyawan qarshe fuskarsa kaďai xata Shaida hakan da ynda jikinsa yayi kyau, ki roqa masu gafara ki masu addua, please fatyma ki nutsu,
Nan da nan jikinta na soma rawa sai karkarwa take sai ga hawaye sharrrrr,
Shikenan da gaske Deedah ya tafi,
Bakinta na rawa ta nemi gurin xama da kyar tana faďin,
'Allah ya jiqansu, Allah ya gafarta masu, Allah ya haskaka kabarinsu,
Duk falon aka ďauki Amin, wasu Kuwa suka fashe da kuka......
*Babana da mijina*
©Fertymerh Xarah 💞
36
_Congratulations for the completion of ur book Rabi'atu Sk Mashi, MATATA CE, ko ina xanga Rabi'atul Adawiya? Nagode da qaunarki,_
_mistake page 35 in babana da mijina, ban sani ba ko tsananin ruďewa ce tasanya Iman sallah bayan ta haihu, it's a mistake pls._
Da kyar yaja qafafunsa yabar gidan, duk jikinsa a sanyaye yake har ya iso gidansa,
Sai da yaje ya duba mahaifinsa har lokacin barci yake kafin ya koma side ďin sa, kwanciya tayi haďe da lumshe idanuwansa, fuskarta yake gani, murmushinta wani abu ne mai girma a xuciyarsa, da alama tana matuqar son yaron ya gani a kwayar idonta don haka yayi alqawarin Kula da Ita da yaron kamar shi ya haifesa, da Wannan tunanin barci ya ďauke sa,
Sa'eed Kuwa yana xuwa gida ya sameta xaune a falonsa tana jiransa, cikin wasu irin shu'uman kayan barci, rabonta da sanyasu yana ji tun farkon aurensu, ya ďauke kansa cikin basarwa kamar bai ganta ba yayi hanyar ďakinsa ta biyosa tana faďin,
'ina kaje da wannan daren Abban Adnan,
Yau kuma har wani Abban Adnan ya samu ya raya hakan a xuciyarsa shi da ake kira da xallar sunansa Sa'eed,
Bai dubeta ba bai Kuma tankata ba ya hau gadonsa yayi kwanciyarsa fuskarsa ba walwala hakan yasa take tsoron tunkararsa Kada ya sauke fushin akanta, sai ta soma mgn a hankali,
'Dan Allah ina kaje, Allah yasa ba gurin wata kaje ba dan bansan yanda xnyi da xuciyataba,
A fakaice ya ďan dubeta cikin mamaki bai bari sun haďa ido ba ya ďauke kansa, tana sonsa ne bata iya Kula da shi,
Ganin baxai tankata ba ta kwanta a qirjinsa, da sauri ya juya mata baya haďe da Jan dogon tsaki, Hakan da yayi hankalinta yayi matuqar tashi tasan idan Sa'eed yayi mata haka to yana fushi da itane,
'kayi haquri ďaxu wasa nake ma xnyima tausa ďin,
'karki kuskura ki tabamin jiki, inba haka ba ranki xai baci... duk wannan mgnr da yake fuskarsa ba walwala,
Nan da nan ta soma hawaye tayi xaune xuruu tana kallonsa, tana gani ya tashi ya kashe wutar ďakin Kafin ya dawo ya kwanta batare da ya kalleta ba, hankalinta ya tashi sosai ta tashi tabar ďakin ta nufi nata, ranar barci a idonta sai dai barawo....
Sa'eed Kuwa barcinsa duk na Iman ne, yana tare da Iman, ya tashi yana adduar Allah ya bashi Iman su kasance tare cikin farinciki da kula da junansu.
Iman Kuwa tana shiga ďaki ta shimfide yaron, ta gyarawa fauxie kwanciyarta anan taji jikinta xafi rau, ta manta da taci abinci batasha magani ba, gefen fuskarta ma ya fara ďebe kumburi, tausayin yarinyar ya kamata,
Taya akayi fauxie ta fita wayo da dabara, Ashe surutunta bana banxa bane, sai komai yake dawo mata sabo, lallai fauxie ba qaramin namijin qoqari tayi ba dan da baba bai gayamasu komai kafin ya mutu ba da baxatasan komai ba,
Ashe da gskyr Deedah da yace fauxie ce ajalin baba, sanda yayi furucin taso ta tambayesa dalili amma ta manta, Ashe Deedah yasan baba matsafine amma bai taba gayamata ba sai Faďan da sukayi na qarshe dashi inda yake cewa, *gwanda xama da barawo akan xama da matsafi..*,
Inama Deedah ta xai dawo, xata xauna dashi a matsayinsa na barawo, tana son mijinta fiye da tunanin mai karatu,
*Babana da mijina* sune jigon rayuwata, yau babu su daga ita sai qanwarta da ďanta... ta soma waige waige a ďakin kamar xataga Deedah, dama a irin wannan lokacin yake dawowa gida, ta tashi da sauri tana kallo ta window gani take xataga motar mahaifinta ya dawo, xuciyarta ta kasa amincewa da mutuwarsu, meyiwuwa xasu dawo Gobe a tunaninta sunyi tafiya ne tadawo cikin ďakin har lokacin hawaye take,
Magani ta ďauko da ruwa taxo ta tayar da fauxie,
Kuka ta fara, tayi saurin toshe mata baki da hannu gudun kada ta tayarda jaririn,
'yi shiru karki tayarda baby, magani xaki sha sai ki koma barcin,
'anty baxan sha ba.... ta qara kwanciya idanunta a lumshe, Iman ta riqo hannunta haďe da sunkuyawa dai dai fuskarta,
'please babyn yaya, idan kinsha magani yaya will be happy, kuma xakiji sauqi kafin ki koma Skul fuskarki xata dawo dai dai, your friends will not laugh at you,
Ta buďe idanunta a hankali tana kallon Iman itama kallonta take, sai ta tashi xaune, Iman ta bata maganin tasha tana yatsina fuska kamar xatayi kuka bata barta ta kwanta ba sai da ta tabbatar ya kwanta mata, fauxie taje kusa da yaron ta riqo hannunsa ta riqa da nata,
'Anty shi hannunshi yana da laushi, yaushe xaiyi girma kamar ni muyi wasa,
'kiyi barci ba surutu na tayarda ke kiyiba, fauxie tayi shiru haďe da rufe idanuwanta bata saki hannun yaron ba, Iman ta kwanta a kusa dasu tana kallonsu, barcinta a ranar sama sama ne sai ta fara ta tashi a firgice.
*
Washe garin ranar Dr Deen tare da mahaifinsa baffa, nan yake bashi lbrn Iman, sosai ya tausayamasu sai yaji inama Xahradeen xai aureta ya kula da yaronta da qanwarta sai ya tuntubesa da Mgnr,
Dr Deen yayi shiru kafin ya dubi baffa,
'xamuyi Mgnr wani lokaci baffa, ya tashi ya fice cikin shirinsa na xuwa asibiti,
Sa'eed ma yana shirin xuwa bank salima ta shigo, ta gaidashi ya amsa fuskarsa ba walwala,
'breakfast ďin fa,
'na qoshi,
'Dan Allah kayi haquri ka yafemin,
Ya ďauki jakarsa yasa kai ya fice batare daya dubeta ba, tabisa da kallo ranta a bace tabbas idan har wata mace kesa yana mata Wulaqanci a ynxu wallahi ko Wacece sai taga bayanta.....
Tunda sassafe Iman ta shiga wankan ruwan xafi, yaran basu tashi ba harta gama ta fito, sai taji daďin jikinta sosai, tana shirinta take jiyo hayaniyar mutane tasan baxai wuce yan uwansu bane da suka xo, ita batason xaman makokin nan da duk yawanci Munapurci ake, sai ayita qananan maganganu kan mamaci, sun maida gidan kamar gidan biki ba mutuwa ba, sai fita ake da abinci da juice, jiya kaďai tana lura da yanda yanayin gidan ke tafiya, almubazzarancin yayi yawa.
Wata dattijuwace tayi Sallama ta shigo ďakin,
Iman ta amsa sallamar tana kallonta bayan sun gaisa,
'Tace Inna ai bai tashi daga barci ba,
'banda abinki fatyma shi jariri ai baya tashi barci karkiyi mamaki ma ynxu har ayi wankan a gama bai tashi daga barci ba, bani shi nan ki gani, Iman ta ďauki yaron tana kallonsa kafin ta miqa mata shi,
Tana xaune tana shan kunun kanwa fauxie ta tashi barci lokacin