Showing 42001 words to 45000 words out of 55052 words

Chapter 15 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE by FATIMA ZAHRA

28 May 2026

40

har angama yiwa yaron wanka ana gasa masa cibiya,


'anty nima ayimin wanka cikin robar baby,


'a'a kije dijeh tayi maki a toilet ke bakisan kin girma ba kinaso Inna taga jikinkine,


Ta make kafada kamar xatayi kuka,


'ni banaso anan nake so,
'yi haquri aje toilet ayi maki kinji, keda akewa a Jacuzzi 🛀 Ina ruwanki da robar wankan jariri,


Ta soma cire kayanta Iman bata ankaraba sai ganinta tayi cikin robar, Inna ta soma dariya, iman bata ce komai ba har dijeh taxo ta ďauketa da robar tayi toilet da ita sai daďi takeji,


Angama wankan tafito komai sai na jariri xa'a shafa mata,


Lokaci ďaya Sa'eed da Dr Deen suka xo, ta fita suka gaisa dasu kafin su wuce gurin aikinsu,


Dr Merah ma na qoqari akansu har akayi adduar qarshe, ranar komai ya dawowa Iman sabo da kyar Merah ya kwantar da hankalinta harta yi shiru,




Ranar suna yaron yaci sunan mahaifin sa Ahmed, Dr Deen, Sa'eed da Dr Merah sosai sunyi namijin qoqari gurin sunan yaron tamkar Deedah na raye, ba abinda suke nema suka rasa daga ita har jaririn da qanwarta, ba abinda xata cewa waďannan maza uku sai godiya da fatan alkhairi a rayuwarsu,


Haka rayuwa ke cigaba da tafiya, Dr Deen da Sa'eed na iya qoqarinsu na ganin sun kula da Ita tare da nuna mata soyayya,


Ba wannan ne a gabanta ba a ynxu, ba wanda takeji a xuciyarta, ba wanda take ita ba lokacinta a cikinsu bayan qanwarta da ďanta,


Sai addua Sa'eed da Deen keyi a xukatansu na ganin ta amince da soyayyarsu a shirye suke da su bata farin cikin da ta rasa a baya,


Xuwa wannan lokacin iman tasan ta rasa Deedah ďinta, ta rasa wanda takeso, farincikinta, a ynxu da ta jima bata ganshi ba bataji ďumin jikinsaba ta yarda ya mutu ya barta har abada, xuciyar musulunci ce kawai ke riqe da Ita a yanxu,


Hankici tasa tana ďauke hawayen fuskarta cikin tausayin kanta,


Tunda ta iya ta karbi rashin Deedah, na wanene baxata iya karba ba a ynxu? But it's still painful.... Yeah so painful!




Bata burin mai kuďi ko wane irin mutum ne shi, tafison talaka xama da Wanda bashi da meyiwuwa hakan xaisa xuciyarta ta xamo so contacted, kuďi basu amfana ta da komai ba illah baqin ciki a rayuwa,


Wannan dalilin ne ma yasa ba abinda ke burgeta a duniya balle ya sanyata nishaďi, haka take xaune ba doguwar magana, babu hope, no future, babu xabi acikin rayuwarta, duk yanda Allah yayi da rayuwarta dai dai ne.


A yau ta tuno da Deedah kan abubuwa da yawa, baxai barta cikin damuwa ba, hawayenta kaďai xai gani gigicewa xaiyi da tarairaya concern da emotional pity amma ynxu babu shi,


Ba Wanda xai rarrasheta, ba wanda xai sanyata a jikinsa ya nuna damuwarsa akanta, babu wannan Deedah dake son farin cikinta Wanda xai iya barin komai na rayuwarsa dan yaga ya faranta tata rayuwar,


Wasu irin hawaye masu ďumi suka barko daga idanunta, a hankali bakinta ya soma motsi,




_"This life has changed... and we go our separate ways Deedah... but you'll still be in my heart till my dying days... my world has never meet a person like you..... I love you Deedah."_






My wattpad Phertymerh1
*Babana da Mijina*




©Fertymerh Xarah 💞




38




_dis page is for you Faxyfashion_






Ta ďauke kanta daga kallonsa ta maida hankalinta kacokan Kan abincin da take ci,




Fauxie taxo da gudu ta rungumesa tana dariya,


'Mrng yaya...
'Mrng little angel, bakije Skul ba,
'ina jiran driver bai xo ba,


Ya ďauki little yana yi masa wasa, yaron sai dariya yake daka ganshi kaga Deedah photocopy sak....


Adama ta shigo da kayan kai tsaye ďakin Iman ta nufa dasu duk da batasan ko menene acikiba amma bata ďebe tsammani ga kayan Iman ne,


Driver yaxo fauxie ta fice tana yi masu bye bye,


Iman ma Acikin shirin fita aiki take tana gama kalaci ta taso ta karbi little yaqi xuwa ya liqewa Deen,


Ta rataya Jakarta tana faďin,
'xan barka anan kuwa inda adama tunda yau ni kakewa quya,


Dr Deen ya juya dashi tabi bayansa, motarta ta shiga shima ya shiga tasa tare da little,


Itace ta fara fita da motarta yana bayanta, tafiya suke akan titi hankalinta na gunsu, yanda ya biyota abaya ya tuna mata da Deedah, Allah ya jiqan Deedah ta faďa a hankali.


Tana isowa kai tsaye office ďinta ta nufa shima bai kulataba yayi nasa office da little....


Haka rayuwarsu ta cigabada tafiya tsawon shekara ďaya kenan Iman ta kasa tsaida xuciyarta akansu, Dr Merah yayi iya qoqarinsa akanta taqi sai ya xuba mata ido yana kallonta yasan komai daren daďewa dole xata xabi ďaya acikinsu Sa'eed ko Deen ta aura.




Shaquwa ta musamman ta shiga tsakanin little, fauxie da baffa, akoda yaushe suna can sun maidashi kakansu shi kansa yana jin daďin kasancewa tare dasu badan komai ba dan shima ba yara ba jikoki daga shi sai masu yi masa aiki sai Deen Idan yana gidan bai fita aiki ba.


A yanda ta lura yaran a ynxu sunfi son xama da baffa akan ta, bata yaye little ba yana shekara ďaya da wata biyar idan ka ganshi xakayi tsammanin ya tasamma shekara biyu saboda girmansa da wayonsa ko ina xuwa yake gashi da rigima sosai, sau tari ba'a gidan suke kwana ba sai inda baffa, yanda suke sonsa yasanyata qaunar tsohon itama akai akai take xuwa gaidashi ta daukeshi da girma haka take ganinsa Kamar mahaifinta kamar yanda ya ďauketa ya',


Idan tayi ba dai dai ba yakan xaunar da Ita yayi mata faďa Kamar yanda xaiyiwa Deen, haka duk wani abu daya shige mata duhu na rayuwa shike warware mata, sai ta daukesa tabashi wani matsayi a xuciyarta na UBA, a Yanxu tana samun kulawar da bata samu a baya, ga yaranta suna jin daďin kasancewa dashi ba abinda xata cewa wannan tsohon bayan yi masa addua a tsawon rayuwarta.




A nata ganin Sa'eed yafi dacewa da aurenta, yafi kowa sanin halinta da mijinta sannan tasan halinsa fiye da halin Deen, miskilancin Deen kesa take qinsa komai yana yinsa cikin nuna isa da gadara, ta tambayi Dr Merah xabi acikinsu ya xaba mata Dr Deen Wanda Sam bata amince da wannan xabin ba, sai taje ga baffa tana tsammanin xaice ta auri yaronsa Deen ga mamakinta sai ji tayi yace,


'fatyma ki auri Wanda xuciyarki tafi amince maki dashi, Wanda kike gani yafi kusanci gareki inda hankalinki xaifi kwanciya kiyi xaman aure, ki kuma kula da yarannan guda biyu da suke amana agareki,


Sai taji kunyarsa da nauyinsa, akwai kawaici a gareta baxata iya fitowa ta gayamasa Sa'eed xuciyarta tafi aminta da ta aura ba, sai ta kawar da mgnr ta ďauko wani xancen suka cigaba da hira kamar ya' da uba....


Akwai wani lokaci da lauyoyin babanta dana Deedah suka xo gareta domin dukiyar mamanta dake hannunsu suna so su rabu da Ita,


Tayi mamakin dukiyar da Deedah ya bari, bar mgnr Waďanda ke cikin account ďinsa, bata taba sanin yanada irin waďanna kuďin ba, sai ta boye mamakinta lokacin da taga dukiyar baba, kusan tsoro da ruďewa tayi a inda take xaune,


Files files dake xube a gabanta na kamfani, gidajensa, filaye da shagunansa bata san iya Karsu ba, ga makullayen motocin da aka xube mata a qalla xasu kai ashirin inma basu haura hakan ba, anan gida ma tanajin makullan motarsa dake hannunta sun kai bakwai, na Deedah biyar ne Kuma tasan suka ďai ne motocinsa a duniya Gashi kuma taga xahiri sai ta qara yarda da mijinta akan babanta,


Ta dubi Sa'eed kafin ta maida dubanta ga Deen domin sune shaidarta sai lauyoyin, idanunta sukayi rau bakinta har rawa yake kamar xatayi kuka data tuna Deedah,



'Dukiyar Deedah na yafewa ďan mu Ahmed, ku shaidane ko bayan mutuwata idan ya girma xaku iya bashi, in kuma ina raye Alhamdulillah,


'sai dukiyar baba a raba biyu dani da qanwata, a ajiye mata nata daban, Acikin nawa xan sallami yan uwanmu da duka ma'aikatan gidan nan, sauran kuďin xn kaisu gidan marayu da asibiti saboda masu buqata, xan gina masa makarantar islamiya shida Deedah domin lada ta kai garesu Allah ya gafarta masu,


'banajin xn iyacin dukiyar baba koda kwandalace a ynxu danasan da jinin mahaifiyata da yayyuna da qannena aka tara wannan dukiyar, kuka take sosai


'Allah ya gafartawa baba, Allah ka yafewa baba, Allah ka yafe kuskurensa daya aikata,


Suka amsa da Amin suna kallonta cikin tausayawa....ta tsurawa dukiyar ido, xuciyarta ta taushe ta dacewa,


'duniya ba komai bace tamkar matafiyi ne akan tafarki, baba kaďai ya isheta misali, Waye baisan baba a Nigeria ba shahararren ďan siyasa mai ji da dukiya, a yau yana ina? ya tafi yabar kuďin a inda ya samesu, ya tafi inda abinda ka shuka shine jarinka, bai tafi da gidajen ba bai tafi da motocin ba, bai tafi qasashen da yake xuwa ba, qarqashin qasa ya tafi cikin yadin likkafani dai dai dana kowa, babu AC babu katifa mai taushi, sauran al'amarin tsakaninsa da ubangijinsa ne, to haka kowa fa xai mutu yabar wannan dukiyar dayake taqama da Ita, dukiyar nan da ake tarawa ana hana talakawa da masu buqata, dukiyar da ake kashe bayin Allah saboda ita, dukiyarda xaka ga yan uwa suna faďa suna gaba saboda ita, duk xa'a mutu abarta Allah ya gafartamana Amin.


2 months later ~~~




Tana xaune a falo cikin Atampha mai qarshen tsada, kanta babu kallabi ta matse gashinta a tsakiyar kanta, farin glass dake idanunta ya qara ma fuskarta ilhami da kwarjini tana naxarin wani littafin ilimin halin ďan adam Wanda a fakaice ba komai bane aciki ba sai applied Christianity, malaman kimiyar halin ďan adam ke amfani dashi jami'oi matsayin hanyoyin gyara mu'amalar xamantakewar ďan adam tana tsintar na tsinta tana xubar dana xubarwa, sunan littafin 'The power of positive thinking'.


Da Sallama ya shiga falon ya bayyana cikin kyakkyawar suit (Japanese) da baqin gilashin Prada a idanunshi, falon ya gauraye da qamshin Dior addict daka ganshi kaga gogaggen ďan boko.


Kallo ďaya tayi masa taji xuciyarta ta buga a yau, kamar yau tafara ganinsa, bawai yau ta fara ganinsa ba sai dai bata fiye yiwa mutum kyakyawan kallo ba, yau ta ganshine sosai a gabanta yayi mata kyau, shima gabansane ya faďi sakamakon ganin Iman yau a ainihinta ba cikin mayafi da labcoat ba kamar kullum,


Ta lalubi ďan kwalinta ta ďaura ta xare gilashin idanunta tayi mishi barka da xuwa,


Shiru ya ratsa na wani daqiqai wani chemistry mai ban mamaki na aiki a zuciyoyinsu da kwayoyin idanunsu yana shiga cikin xukatansu dai dai lokacin fauxie ta shigo da gudu da ball a hannunta little na biye da Ita yana kuka akan tabashi taqi sai dariya take masa,


Suna ganin Dr Deen duk sukayi kansa suka rungumesa suna dariya,


'ďanki kike hanawa ball fauxie, bakiji kunya ba yana kuka yana biye dake,


Ta soma dariya tana kallonsa kafin ta bawa little ball ďin,


'amma shine ya jefomin ita a goshi ina assignment,


'Kiyi haquri kidaina sashi kuka kinji,


Little ya dubesa yana gauranci da alama ya kawo qarar fauxie ne, daga shi har Iman suka kwashe da dariya yanda yake Mgnr komai baxaka fahimta aciki ba amma yanayin fuskarsa xaka gane da faďa yake Mgnr, Deen ya rarrashesa haďe da bashi ball ďin ya fice da gudu,


'yaya yau xakaje damu inda baffa,


'kujirani a waje gani fitowa ynxu sai muje, ta fita da gudu itama,


Deen ya dubeta wannan karon ba walwala a fuskarsa,


'inason nasan matsayina a gunki fatyma,


'Sa'eed na xaba, shi nake ganin yafi kowa sanina da halin dana fuskanta a baya, nasanshi ya sanni,


Ya dubeta da tsananin mamaki,


'kina tunanin har akwai wani abu daya shafi rayuwarki a baya wanda ban sani ba, fiye da shekara muna tare kina nufin bakisan hali na bakisan ko waye niba, ban taba roqon mace ta soni ba sai akan ki Iman, kinsan yawan matan dake bibiyata domin na auresu naqi saboda kece a xuciyata Kuma baffa yafi amincewa dake, mecece ribar aurenki da mai mata kije masa da qanwarki da yaronki....


'Acikin yan matan dake bibiyarka ka xabi ďaya ka aura Dr Deen, qanwata da yarona ko bada aure ba xn iya Kula dasu domin Nafison rayuwarsu akan tawa Nafison farin cikinsu akan nawa,


Wannan Karon ya harzuqa and he mean it, ya haqura da Iman a ynxu bai taba rarrashin mace ko roqonta akan taso Shiba sai akanta kuma take wulaqantashi, duk girmansa da ajinsa,


'Na tabbata ďan halak fatyma, kije gaki ga Sa'eed, ya tashi ya fice batare daya qara kallonta ba,


Nan take taji xuciyarta ta buga tabisa da kallo kada dai ya haqura da itane?


Daga inda take xaune tana jinsa yana kiran little akan yaxo su tafi,


She knows it Dr Deen yana sonta, kuma shi yafi dacewa data aura, shine baida mata shi kaďai xai iya riqe yaranta ba tsangwama gashi yaran sunyi sabo sosai da baffa, amma Sa'eed fa?


Shima yana sonta shima xai iya riqa yaranta haka shima yana buqatar kulawar Mace tunda bai samu agurin matar saba.....


Har dare yaran basu dawo ba tasan baxai wuce acan xasu kwana ba, ita a ynxu yaye little xatayi ta huta tunda dama bai damu dashan mamma ba, idan ba Ita ta matseshi tabashi ba baxai nema ba yanacin abincinsa sosai ga bakinsa ya saba dacin daďi kamar irin na fauxie duk kalar kwalama xaka Deen ya siyo ya kawowa yaran harma Sa'eed.


Kwana biyu bata qara sanya Deen a ido ba ko a asibiti sun daina haďuwa, ya daina kiranta a waya sai tayi qoqarin kiransa sai ta fasa kada dai da gaske yake ya haqura da ita,


A xahirin damuwarta a ynxu Iman na wani hali na soyayya, Wanda ita kanta batasan cewar soyayyar ce ke dawainiya da xuciyarta ba, soyayyar Dr Deen Wanda a halin ynxu batasan halin da yake ciki ba, ita dashi sai gani a nesa ko idan yaxo maida little shima daga gate,


Soyayyarsa a xuciyarta sai qara linkuwa take Kamar ana iza wuta, ta tuna ranar rabuwarsu ta qarshe,


_'Na tabbata ďan halak fatyma kije gaki ga Sa'eed._


Sautin dake ta mata kururuwa a kunne kenan a duk lokacin data xauna ita kaďai, wanda ke qara ruruta wutar nadamarta, irin nadamar da RAIHAN yayi a SALIMA MAKAUNIYA (shima littafin Pherty ne), to amma rabuwar ta xamo mata jifa'i...dai dai wannan halin data tsinci xuciyarta da ruhinta aciki na bege daso da qaunar gabaki ďaya,


Ta yarda harshe mugun abu ne, ya Allah kabamu linxaminshi a hannunmu, harshe yana kaimu ga wuta, yana kaimu sa'ira Kuma yana kaimu aljanna, again yana lalata mana rayuwa, mu dinga riqeshi ta hanyar tauna magana kafin mu faďeta,


Idan ya furta baya taba mayarda ita komai daďinta ko ďacinta, da Hausa (harshe), da turanci (tongue) da larabci (Lisan), wata tsokace mai amfani daban daban da Allah ya halitta a cikin bakinmu wadda in muka iya controlling ďinta xamu iya controlling ďin duka al'amuran rayuwarmu,


Me xatayi tayi repenting kuskuren data tafka a baya, Dr Merah ya kamata ta tunkara ko baffa? Waye xabinta a ciki, Dr Deen ko Sa'eed?......




My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina*




©Fertymerh Xarah 💞




39






Yinin yau duk suna tare da Sa'eed, yana xaune a office ďinta tana duba patient, little kuwa yana gun Deen tun jiya da yaje dashi bai dawo mata da shi ba,


Deen yaga xuwan Sa'eed asibitin bai damu ba a ynxu da yake yaqi da xuciyarsa na ganin ya fiddata a ransa,


Sanda Sa'eed xai tafi taje ta rakasa ta dawo kenan ta tsinkayo Dr Deen da wata budurwa a tsaye tana ďauke da little, yanayin ynda suke tafiya murmushi a fuskarsu kaďai xai nuna ma masoya ne, nan take taji wani abu ya taso ya tokare qirjinta,


Kai tsaye ta nufesu, little dake hannun yarinyar ta fisge, budurwar tayi tsaye tana kallonta da mamaki little kuwa kuka ya fara yana qoqarin sauka jikinta tare da miqowa Dr Deen hannunsa alamar ya karbesa,


Dukkansu an rasa mai bakin mgn har ta nufi office ďinta, Deen yayiwa budurwar Sallama ya fice da sauri yabi bayanta,


A office sai qoqarin goya yaron take amma yaqi, ya miqe mata a baya sai kuka yake,


Cikin xafin nama ya fisgo yaron daga bayanta haďe da hankaďata gefe, yaron ya qanqameshi sai ajiyar xuciya yake,


Sosai little ya saba da Deen fiye da mahaifiyarsa, yasan Deen sosai ko muryarsa yaji da gudu yake tunkararsa yana dariya,


Shi yake kallo a matsayin mahaifinsa, bai kuma aje shi nan kusa a xuciyarsa ba, Don ko kuka yakewa uwar idan bai sa baki ya rarrashesa ba baxai yi shiru ba, haka inya qi cin cereal ko abinci a hannunta indai yana gidan shike bashi,


Ta dubesa ranta a bace,
'kabani yarona,
Bai tankataba sai yaga little nason xuwa inda take da alama mamma yake son ta bashi, ba musu ya miqa mata yaron ta karbesa a fusace ta ajiye akan sofa kana ta xagaya ta xauna inda take duba patient, har lokacin kuma bai daina kuka ba,


Yasan baxata bashi ya sha ba yanda yaga ranta yake a bace to miye dalilin wannan fushin nata?


Fushin bai sauka daga fuskarsa ba amma ya sassauta murya,


'Kiyi haquri ki manta komai ki daukesa kibashi abinci,


Cikin bala'i tace
'idan kai ka haifar min shi sai kagayamin haqqinsa dake kanka, Yanxu incire inbaka abinka,


Yayi murmushi ya ďauki yaron yaje ya ďora a jikinta,


'naji bani na haifesa ba, nima Kuma bn fidda rai ba inaji a jikina Allah xai bani nawa,


Sai taga idanunshi sun juye sun koma luv colour wani irin situation ne da baxata iya mantawa da shi ba,irin halin da Deedah ke shiga kenan idan yana biďarta ba sai yayi mgn ba take ganewa, dan haka sai taji tsoron shayar dashi a gabansa ballantana ma tun jiya ta yayeshi, sai ta ďauko empty feeder tasa masa a baki yaqi karba, ta dubesa a raunane Idanunsa akanta cikin bacin rai,


'tun jiya na yayeshi..
'what? Kin yayeshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login