Showing 3001 words to 6000 words out of 55052 words

Chapter 2 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE by FATIMA ZAHRA

28 May 2026

23

kafin ya rakasu har dakinsu da kanshi, yana labe yana kallon sanda suke game suna shan yoghurt Wanda a ciki yayi siddabarun sa, basu jima ba Kuwa suka xube gurin suna kakaki kumfa na soma Fita bakinsu, yaje da sauri ya ďauke yoghurt ďin ya musanya shi da Wanda baida komai ya fice, idan xakayi masa kallon natsuwa a Wannan lokacin xaka fahimci baya cikin hayyacinsa ko kaďan....


Mami ta fito daga ďakinta Kai tsaye study room ta nufa ta sami fatyma da tulin takardu a gabanta, gefenta kofin coffee ne da take korawa akai akai...


Iman ya kamata ki riqa bawa kanki hutu ki samawa xuciyarki sauqi, wannan karatun yayi yawa haka ke kullum akan takarda....


ta ďago idanunta da kyar tana kallon mahaifiyarta idanunta sunyi jawur sosai sun nuna kalar barci,


Mami you won't understand,karatun likita is quite different da sauran karatun, kibari nan da shekara ďaya na kammala karatuna na xama cikakkiyar likita xn fara maki surgery..


Surgery? ta tambaya da mamaki tana kallonta, surgery akan me?


Tayi far da ido tana kallon ta cikin shigar wasa irin ta ya'da uwa,
Tace Mami har ma sai na gaya miki kibari lokacin yaxo xaki sani...


Mami tayi dariya tana tattara littafan dake gabanta,
Ko Alhuda huda yana samawa xuciyarsa sauqi Iman, ki tashi kije ki kwanta,


Ta tashi tana miqa, a tare suka fito suna tafe suna hira, baba na ďakinsa yana jinsu hr lokacin da yaji Faty na fadin,


Mami Ina ya'yanki ko sunyi barci bnji hayaniyar game ba,


Me yiwuwa haka ne, amma bara na dubasu, ta nufi ďakin Faty na bayanta, yana daga window yana kallonsu har suka shiga, basu jima ba ya jiyo qarar fatyma tana kiran baba... ya koma yayi kwanciyarsa kamar mai barcin gaske,


Iya ruďewa sun ruďe bama kamar Mami da ta xama mutum mutum, batasan meke faruwa akan ya'yan taba, suna haka baba ya shigo cikin yanayin barci sosai ya nuna damuwarsa hrda kuka yayi.....


Tun daga lokacin abubuwa sun soma faruwa, walwala da jin daďi sun rageshi a gidan, ga kuďi kamar me, basu taba xargin sa akan Kuďin da yanda yake kashe dukiya ba saboda sun San dan siyasa ne,


Iman da Fauxiya ne kaďai suka rage masu a ynxu duniya, yana son su fiye da xaton mai karatu haka yake ji komai xai iya dan ganin farin cikinsu....


2 years later


Siyasa ta tashi sai faman xabe ake ana campaign, baba yaje wa Sima da buqatar Wannan Karon yana son matsayinsa na mataimakin gwamna kowane mutum ne yaci gwamna a birnin kebbi yana so yaxama mataimakinsa, wani xabe mai xuwa yana so ya fito takarar shugaban qasa....


Sosai sima tayi dariya wadda tayi matuqar raxana su,


Buqatar ka xata biya Abdallah, xakaci siyasa idan har xaka bada jinin matar ka......


Sosai ya raxana da jin kalamanta, bai taba xaton akwai abinda xai rabashi da Mami a ynxu ba saboda ta xamo ginshiqin rayuwarsa,


Auren soyayya sukayi, tun saurayi da budurwa, yana sonta tana sonsa.....


har ya dawo gida bashida sukuni tunaninsa yanda xai bada jinin Mami, ya kasa barci sai faman juye juye yake akan gado, duk abinnan da yake akan idonta tana kwance tana kallonsa,


Ta matso a hankali xuwa garesa,
Meke damun ka alhaji, yayi firgigit yana kallonta da mamaki,


Kada dai hr ynxu kana tunanin su musa ne? Ya girgixa kansa hawaye suka xubo masa, hankalinta yayi matuqar tashi,


Meke faruwa meke damunka? Ya janyota sosai jikinsa ya rungumeta...
Ki yafe min, ki yafe min Amina,


Jikinta ya ďauki rawa,
Ba abinda kayimin a xamana dakai, inma kayi na yafe ma nima ka yafemin,


Ya sauke ajiyar xuciya yana qanqame da ita yana jin sonta har cikin ransa Kuma har lokacin bai daina hawaye ba,


Ta maida kanta qirjinsa hankalinta ya kasa kwanciya da yanayin mijinta tabbas akwai abinda ke damunsa yake boye mata, Gobe da safe xata tuntubesa ya gaya mata damuwarsa....


Suna haka hr barci ya ďauke ta, ya sumbaceta sosai kafin ya janyo wani Jan kyalle qarqashin pillow ďinsa....


BABANA DA MIJINA


©Fertymerh Xarah 💞


5


Rumtse idanuwansa yayi kafin ya ďora mata kyallen a jikinta,


A hankali ta buďe idanuwanta tana kallon sa sakamakon wani raďaďi da taji a xuciyarta,


A hankali bakinta Na soma motsi kafin idanun su rufe dai dai lokacin numfashinta na ďauke,


Cikin wani irin yanayi ya rungumota jikinsa haďe da fashewa da wani irin kuka mai tsuma xuciya,


Mutuwar Mami sosai ta girgixa mutane, yan uwa da abokan arxiki bama kamar fatyma da fauxiya,


Shi kansa baba idan ya shiga gidan ya sami Fauxiya jikin fatyma sai hankalinsa ya tashi saboda tsananin tausayinsu da tausayin kansa, a lokacin Fauxiya is 6yrs, sun xama marayu.....


Ma'aikatan gidan ya qara saboda kula dasu, basu da wani aiki a gidan daga ci sai kallo sai barci, Fatin ce batada hutu saboda karatu...


Bayan wani lokaci akayi xaben siyasa Kuma yaci, sai ya Gina masu wani qaton gida mai hawan bene guda biyu kowane da gate ďinsa sai aka xagaye gidajen aka maida shi gate ďaya as 2 in 1,


Cikin ďaya suka tare sai ďayan ya ajiye idan fatyma xatayi aure su tare a gidan saboda bayaso tayi nesa dashi ko kaďan,


Sosai taji daďin haka ynda takeji a xuciyarta baxata iya barin qanwarta da mahaifinta ba, she is happy with the house, sai ta rungume mahaifinta cikin farinciki shima sai ya tsinci kansa cikin nishaďi ganin fatyma taji daďi...


*


Ahmad Deedah bayan rasuwar mahaifiyarsa, ya karbi tayin oga nas suna xuwa wurare da dama sata, ya kware ya iya bama kamar harbin bindiga, baya kissa kamar sauran abokansa sai dai ya tsoratar da bindiga, haka Kuma idan police sun masu taurin kai wajen bibiyarsu yakan harbi mutum a hannu ko qafa,


Cikin lokaci qanqani yayi fice ya xama gwarxo aciki Wanda oga nas ke alfahari dashi, duk suka fita operation sai sunci nasara wannan shine dalilin dayasa oga nas yabawa Deedah matsayi babba a cikinsu Kuma yakeji dashi and again yana tsoronsa domin mutum ne kaifi ďaya idan yace eh ko A'a ba Wanda ya isa ya lankwasa sa,


Bayan wani lokaci ya nemi aikin banki kai tsaye ya samu cos kuďi ke mgn Kuma ya bada,


Ya kanje aiki tunda sassafe baxai dawo ba sai marece, idan yayi wanka yaci abinci xai fice inda sauran abokansa inhar baxasuje sata ba a Wannan ranar,


Idan ka ganshi Kaga kamillin mutum, qasaitaccen namiji mai ji da kyau da kuďi, bafillatanin gaske, baya neman mata xina,baya shan giya matsalar ďaya ce DAN FASHI.....


Haďuwar sa da fatyma ya samo asaline a bank, taje verification,


Daga yanayin tafiyarta xaka gane nutsuwarta da kamalarta sai dai kallo ďaya xaka mata ka fahimci baa hayyacinta take ba, kai tsaye ta shiga bankin hannuwanta duka Acikin Jakarta da alama abu take nema tana tafe tana dubawa,


dai dai lokacin ya fito daga office ďinsa, sanye da baqaqen suit, hannuwansa da laptop yana tafe shima yana latsa ta cikin sauri...


Kicibis sukayi karo da juna, daga shi hr ita kayan dake hannuwansu suka xube a qasa, laptop ďin ta ďauke wuta,


Ya salam... ta furta a hankali bayan ta sunkuya daukar laptop ďin bata damu da nata kayan ba, ta ďago tana kallonsa yana tsaye Idanunsa sanye da farin glass daga kallo ďaya xaka fahimci bacin rai sosai kwance a fuskarsa, sai ta tsinci kanta cikin ruďewa Abinda bata tabayi ba,


Am sorry please, ya karbi laptop ďin haďe da Jan dogon tsaki ya fice tabi bayansa da kallo xuciyarta na bugawa kafin ta maido hankalinta ga kayanta dake xube a qasa, ta sunkuya ta haďa kayanta ta fice....


Ta jima sosai a bankin kafin ta gama verification ďinta, tana gab da fitowa wayarta ta ďauki qara, ta ciro ta Jakarta Dr.hadixa, sai a lokacin ta tuna da Kuďin dake Jakarta xata tura mata,


Oh sorry Dr. Ina banki ynxu xn turo maki Kuďin.... ta faďa bayan ta ďauki Wayar,


Ta juya da sauri,inda ta fito ta koma tayi masa bayani, ya nuna mata office ďin, tayi godiya ta juya ta fice...


Da Sallama ta shiga office ďin, yana xaune Wannan Karon ba glass idanuwansa ya xubawa Mai gyaran laptop ďin ido, tsoronsa kada taqi tashi saboda muhimman abubuwan dake ciki,


Sallamarta ta janyo hankalinsa gareta,
ita ďin ce, me taxo yi office ďinsa, itama tayi mamakin ganinsa jikinta yayi sanyi ganin ana gyaran laptop ďin, ta maida kallonta garesa hr lokacin fuskarsa ba walwala,


Dama na xone na baka haquri, it seems like na bata ma rai, ni bnganka ba ban San yanda akayi Hakan ta faru ba kayi haquri,


Ya sauke ajiyar xuciya,
Is ok ba komai, is not your fault is mine..


Tace A'a laifina ne...
Yace laifina ne..
Tace shikenan Nagode ta juya xata fice ya tsaidata,


Ba Wannan ya kawo ki ba, menene, sai a lokacin ta tuna ta ciro Kuďin Jakarta ta miqa masa,dai dai lokacin da aka gama gyaran laptop ďin sosai yaji daďi,


Nan ma bata jima ba ta fice da sauri xuwa asibiti...


My wattpad Phertymer


BABANA DA MIJINA


©Fertymerh Xarah 💞


6


2 days....


Ta fito cikin shirinta na xuwa aiki, Fauxy na bayanta sai rigima take mata yau sai taje da Ita asibiti,


Idan naje dake, skul ďin ki fa, Sannan bakyaji ne baxaki xauna inda xan xaunar dake ba, xakije...... tayi Saurin katseta,


Anty kije dani dan Allah, I will be a good girl,


Ta sanya Labcoat ďinta ta dubi Dijeh Mai kula da Fauxy,
Tace dijeh ki ďauki uwar rainonki ba inda xanje da Ita kisanya mata uniform ďinta kada tayi late.... idanun Fauxiya sukayi rau sai ga hawaye


Please Anty kije dani, bana son Skul yau,


Fatyma ta fice da sauri dan bata son ganin hawayenta, Fauxiya Kuwa ta soma Kuka sosai...


Harta xo asibiti Kukan Fauxy ke mata yawo akai, office ďinta ta nufa ta ajiye kayanta kana taje duba patient ďinta data bari a jiya,


Gynaec suka haďu da Dr. Merah,
Morning Dr.
Morning inlaw (yanda yake kiranta saboda Fauxy da ďansa Sultan) you are late today,


Am sorry, fitinar Fauxiya ce tana so naxo da Ita,


Fauxie uwayen rigima itada sultan, ya miqa mata file dake hannunsa Dead Case ne, Matar ta mutu after delivering amma yaron da ransa,


Ta Karbi file ďin tana dubawa, a tare suka juya inda ya cigaba da mata bayani jiya cikin dare an kawo wani patient accident case, ya xubar da jini da yawa, xnje gida shiyasa na damqawa Bakori case ďinsa, ku kula dashi Pls,


Shikenan ta faďa, ya fice, a hanya suka haďu da Dr Hadixa suna tafe suna hira har suka iso A&E....


She was shocked to see him, mutumin da suka haďu a banki, garin ya haka ta faru she don't know, sai ta tsinci kanta cikin tausayinsa, shima kallon mamaki yake mata is she a doctor? tambayar da yayiwa kansa,


Ya jikin ta faďa tana kallonsa,
Alhamdulillah ya faďa a sanyaye....


A ranar ita ta kula dashi saboda Bakori is busy


Sosai Ahmad yaji daďi,


Oga nas da yaransa sunxo dubiyarsa, idanu fatyma ke binsu dashi cikin shigarsu ta mutunci baxaka taba gane ko su Waye ba, sosai sun birgeta ynda suke mutunta junansu sai dai abu ďaya na ďaure mata kai ba Wanda yaxo daga gefen Ahmad uwa ko sister kamar xata tambayeshi sai tayi shiru wannan ba hurumin ta bane,


2:00pm


Lokacin tashinta aiki yayi ta soma harhaďa kayanta, hrta shiga mota ta tuna da patient ďinta, taje ta sanardashi she is going....


Ya tsura mata ido hr lokacin baisan sunan taba and he need to know....


Hr ta juya sai Kuma ta kallesa,
Sorry to ask, ba wani naka da xaixo ya xauna da kaine kafin Dr. Umayma taxo ita ke on duty,


Ya girgixa kansa,
Babu, NI MARAYA NE..... ya faďa Idanunsa akanta, bnda kowa bayan abokaina,


Sosai ta tausaya masa ta gyara tsayuwarta,
Ka Kira ďaya daga cikin abokanka ya tsaya da kai, ba amfanin barinka kai kaďai cos nurses baxasuyi jinyarka ba,


Hakane I will Insha Allah, tnx for your care, ta gyada Kai ta juya yayi Saurin tsaidata,


Your name Pls....
Dr. Fatyma Abdallah,
Sunan Mai daraja da muhimmanci a rayuwata, sunan mahaifiyata nake kiranta da Inna, xn iya kiranki da Ummi?


Ta girgixa Kai tana kallonsa cikin tausayawa jikinta na soma rawa data tuna Mami, ta share hawayen idanunta,


Nima na rasa mahaifiyata da yan'uwana, am alone with my sister sai mahaifina, ka kirani da Iman shine laqamina,


Allah ya gafarta masu, tace Amin ta soma share hawayenta abinda ya faďa ya sanyata juyowa da sauri tana kallonsa,


Ki aureni Iman.... Tsananin mamaki ya sanyata furta komai Illa idanu data xuba masa shima kallonta yake, she is not dat beauty tana da nata dai dai ita, haskenta shi ya qara mata kyau Wanda xakayi tunanin ita wata muguwar kyakkyawa ce, sanyin halinta da nutsuwarta yaji yana raayinta.....


Batare data tankaba tasa kai tabar ďakin yabita da kallo..


Harta iso gida bata da sukuni muryarsa ke mata yawo akai, ki aureni, ki aure ni....


Da kyar ta fito daga motarta, ta juya tana kallon harabar gidan birjik da securities, ina little sister ta shiga.. Oh Allah ta tuna ita Mai laifi ce a gareta yau baxata xo yimata oyoyo ba tana fushi da Ita,


Da sauri ta qarasa cikin gidan tana kiran fauxie, shiru bata amsa ba harta iso qaton falon su ga mamakinta sai ta sameta xaune akan sofa da skulbag ďinta tana ciro littafanta da alama assignment xatayi,


Ta ajiye kayanta ta qaraso inda take,
Kinaji Ina kiranki kika min banxa, is not the right thing fauxie,


Ta tunxure bakinta ta maida kanta gefe, ta xauna kusa da ita tace da kika je Skul are you not happy, kinga friends ďin ki, you play and eat together,


Ni banyi wasa ba,
Tor meyasa? Ta nuna ta da yatsa idanunta sun kawo kwalla, ta rungumeta don't cry, gobe dake xanje, kinci abinci,


Yes sister, dijeh tayi min wanka,
Yayi kyau, ta buďe littafinta tana duba class work ďinta,


Subhanallah Fauxiya me kikeyi a class har kika faďi haka, 2/5
Tayi shiru tana kallonta, sosai ta ďaure mata fuska,
Xamu bata dake, silly girl, simple questions baxaki iya amsawa ba,


Tace Anty ni ban iya ba ku.... ta katseta cikin fushi,


Shut up, ta tashi a harxuqe itama Fauxiya tabi bayanta,
'Anty kiyi haquri, koda naje nayi kuka shine banyi ba,


Har suka iso ďaki tana roqarta,
Anty kiyi haquri karki gayawa baba, ta juyo tana kallonta
Baba kike tsoro kenan, ai Kuwa xn gaya masa,


Ta soma bubbuga qafafuwanta,
Dan Allah anty baxan qara ba, I promise you.....


Da dare ta kasa barci sai juye juye take, idan ta rumtse idanuwanta kyakkyawar fuskarshi take gani, maganarsa nayi mata kururuwa a kunne.....


NI MARAYA NE KI AURENI.....


BABANA DA MIJINA


©fertymerh Xarah 💞


7


Ta rumtse idanuwanta,
Yh is true as her age ya kamata ace tana da aure yanxu, baba will be happy duk da baya mata Mgnr auren tasan yana so ne,


Duk Acikin likitocin ita kaďai ce budurwa bayan nurses da yawa sun girmeta wasu Kuma age mate ďin tane, tana da maneman aure da yawa but she don't have interest on them, ta kunna fitilar ďakin tana kallon fauxie,


Abubuwa da yawa take tunawa game da rayuwarta da qanwarta, komai suke so suna samu kuďi da jin daďi, haka komai yi masu akeyi, tun daga kan girki, wanki, shara, kula da gidan da komai ma baba ya Sanya masu yi masu, sai dai sun rasa kulawarsa basu samun Isashen lokaci daga garesa, kullum yana hanyar tafiya baya ďebe masu kewar UWA, hawaye suka sumulyo mata, ta qanqame qanwarta dole tayi aure kodan farin cikinta da qanwarta, dole tayi aure ko damuwarta xata ragu ta sami soyayyar miji tunda bata sami ta iyaye ba.......


Washe gari tare da Fauxiya suka nufi asibiti, sai tsalle take tana jin daďi, nurses ďin dana Santa suka soma murmushi,


Yau Fauxiya a asibiti, Ashe akwai rigima..
Fatyma murmushi kawai take hr suka iso office ďinta, ta ajiye Jakarta juyowar da xatayi ba Fauxiya ba dalilinta, dama tasan a rina,


Ta xauna tana duba files ďin patient ďin da xata duba na ranar, sosai ta dade akansu kafin ta gama, shiru ba alamar fauxie, ta tashi tabi bayanta inda take xato nan ta sameta office ďin Dr Merah tana xaune a gefensa da sweet a hannunta sai surutu take masa yana duba patient ďinsa, sai kayi xaton yar sa ce ta cikinsa


Bata Bari ta ganta ba ta juya da sauri ta nufi a&e,


Su biyu ne aciki shida abokinsa Sa'eed gurin aikin su ďaya a bank,


Da Sallama ta shiga idanunta sanye cikin farin glass, hannuwanta a aljihun Labcoat ďinta, sosai tayi kyau,


Suka amsa sallamar suna kallonta, bata yarda sun haďa ido ba, drip ta xubawa idanu tana tambayar ya Mai jiki,


Sa'eed ya amsa da jiki Alhamdulillah, ta maida hankalinta kan haďa masa magani,


Sa'eed ya tashi yana fadin,
Aboki is olmost tym, by 8 xn dawo, ya gyada Kai yana kallonsa kafin ya fice,


Dr. Save a life.... taji ya faďa daga inda yake kwance, kusan faďuwa ta tashi yi, batasan meke damun patient ďin ta ba, hr lokacin bata tanka ba sai ma qoqarin yaqi da xuciyarta takeyi, ta juyo haďe da miqa masa magani ya karba, ta ďauko masa swan ta bashi hr lokacin bata kallesa ba shikuma Idanunsa akanta, bayan ya gama sha, ta duba file ďin sa yana da sauran allura uku, ta dafe goshinta da hannunta.....


A duniya idan akwai abinda Deedah ya tsana allura, indai akan allura ne yana da rakin wannan, bai tsoron bindiga kamar yanda yake tsoronta..


Yana Ganin ta ďauko allura ya tashi xaune, wannan Karon fuskarsa a yamutse,


Ummi bana son allura, na roqeki karki min, ta juyo da mamaki tana kallonsa Abinda ta gani a idanuwansa ya nuna mata yes he mean it, baya son allura, batayi mamaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login