Showing 15001 words to 18000 words out of 55052 words

Chapter 6 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE by FATIMA ZAHRA

28 May 2026

30

ba,




'meyasa baxata cnxa miki ba? tayi shiru ba amsa,




'yace shikenan anjima xn turo a cnxa maki,


'baba pink nake so,


'tor shikenan, sai me kuma?
'yaushe xaka dawo?
'bayan 2 days Auta, kinaso kiganni?
'eh,
'ki gaida Iman ya tsinke Wayar,


Cikin jin daďi ta nufi bangarensu,




5:pm


Iman na xaune a falo taga ana shigowa da kaya fauxie ce a gaba tana nuna masu ďakin ta,




Matuqar mamaki xaka gani bayyane a fuskar Iman, ina tasamu kayan, kai tsaye ta tambayi daya daga cikin mutanen dake shigowa da kaya,




'Alhaji ya Kira aje ta xabi kayan da takeso a sanya mata a ďaki,


Iman tayi shiru tana jinjina abin, daga inda take xaune tana jiyo ynda fauxie ďin ke basu direction yanda xasuyi, ita ynxu yarinyar ta fara bata tsoro,






Tana xaune suka gama haďa ďakin komai pink har tedy ďin ta da komai, sai murna take xata Kira ihsan taxo taga ďakin ta itama yayi kyau,






Masu aiki sai xuwa kallo ake tsofin kayanta ta raba masu, duk Iman na xaune tana jiyo ynda suke mata godiya, wannan idan tayi sake kayan gidan ma xata kyautar duka,




Da gudu ta shigo falon tana kallon Iman cikin murna,
'Anty xo kiga ďakina yafi naki kyau, nan da nan ta ďaure fuska,


'xo nan fauxie, tayi shiru tana kallonta bata je ba
'ko bakya jine,
'Anty kiyi haquri,
'idan kika Bari na tashi daga inda nake xaune sai kin raina wayonki, xo nace... ba musu taje jikinta a sanyaye Iman ta jawo ta, ta xaunar da Ita kusa da ita,




'gayamin yanda akayi baba yace a cnxa miki ďaki,


'a wayar mai wanki nakira na gayamasa,


'tunda ni baxan miki ba sai kika kirasa ko, idan ya dawo xaki barmin gidana kije duk abinda bana miki yayi maki, buďar bakin fauxie sai cewa tayi,




'Anty ai baba yafiki kuďi, yana dasu da yawa a ďakin sa,


Iman tayi shiru tana kallon yarinyar, dole xata kai xuciyarta nesa akan yarinyar saboda qurciya komai sai da rarrashi,




'ke kinga kin kyau ta kenan kin Kira baba ya cnxa miki kayan ďaki, ga maqotanki na neman abinda xasu ci, kina gani duk wata ina raba abinci a gabanki ake xuwa min godiya amma ke baki taba tunanin Kice baba ya siye abinci a basu ba sai dai kawai ke akashe maki kuďi,




Fauxie tayi shiru hankalinta na gun sabon dakin ta,


'anty kixo kiga ďakina,


'baxan je ba ina miki mgn kina min wata mgn, gayamin yaushe kika ga baba yana shan sobo a kwarya mutumin da ko sobo bayasha, fauxie ta buďe bakinta tana kallonta,




'Anty yana sha fa ai na gansa yana sha sau biyu ya koreni Kuma yaqi bani nasha Kuma...




'yimin shiru shashasha tashi ki ban wuri karna miki wawan bugu, ta tashi tana tsalle tayi ďakinta...




Iman na xaune maganganun fauxie na mata yawo akai dole ta sanya ido akan mahaifinta kamar da qamshin gsky a mgnr qanwata amma batason tunaninta ya xama gsky idan Kuwa hakane xata iya yafe babanta tayi tafiyarta da qanwarta,






Yau ka Sa'eed yaxo gidan sun jima suna hira kafin ya tashi ya fice har lokacin Deedah bai dawo gidan ba, a Yanxu shima ta soma xarginsa Dan meyasa Sa'eed ke dawo wurin aiki da wuri amma shi bnda shi bayan gurin aikinsu daya da Sa'eed ďin?




Har 12 na dare bai dawo gidan ba tagaji da xama tayi sama tabar fauxie na xaman jiransa tana da abubuwa da yawa da xata gayawa yayanta,




Anty ta dake ta, Kuma an cnxa mata kayan ďaki,




Tana xaune tana kallon cartoon ya shigo da gudu taje ta rungumesa hannunta dai dai gurin aljihunsa bindiga ce aciki,




Ta sake shi da sauri tana ja da baya hannunta akan bakinta,


Lah yaya.........


BABANA DA MIJINA.....




©fertymerh Xarah 💞




18








Sosai ya buďe ido yana kallonta, ganin fauxie a ynxu masifa ne atare dashi, ya duba ba kowa falon yaja hannunta da sauri yana fadin,




'xo muje kiji, ďaxu naga wata qatuwar tedy har xn siyo maki sai na manta, da murmushi take kallonsa




'da gaske yaya...


'e mana Kuma mai kyau da Ita,


'yaushe xaka siya min yaya inaso,


'sai gobe xan siya maki amma idan baki gayawa anty kinga bindiga ba,...... Sai a lokacin ta tuna ta gefen idanunta take kallon aljihunsa tana kallon bindigar da bata qarasa shigewa ciki ba shima ya lura da kallon da take masa ya ciro bindigar bayan sun shiga ďakin ta,






'wannan bafa bindigata bace, ta Adnan ce yaron yaya Sa'eed, kin tuna shi?




'oh yes exactly yaya yaxo da Ita ranar mukayi wasa xaka aramin wannan? Da sauri ya maidata aljihunsa dabarar sa tayi,




'A'a gobe xan maida masa yabani ajiya ne, yabi ďakin da kallo,




'wow baby waya gyara maki ďakin haka, ta soma dariya tana tsalle,




'baba ne ya gyaramin yayi kyau yaya?




'sosai ma har yafi na anty, pink & white,




'yaya anty yau ta dakeni a bayana Kuma ta jefeni da bottle,




'me kika mata?
'wai na fiye surutu,
'ai da gskyrta fauxie surutun naki Kuma bamai amfani ba, abinda baa tambayeki ba shikike mgn dan Allah ki Bari kinji,




'na bari yaya xaka siyamin tedy ďin ko?


'xn siyamaki, ina dijeh taxo ku kwanta dare yayi, ta tunxuro baki




'yaya ni baxata kwanta min a new room ba, ai na bata gadona yana can a dakin su,




'ke kaďai xaki kwanta a ďakin ne? ta gyada kai




'noo kibarta taxo sai ta kwanta a qasa, ta soma buga qafafunta qasa idanunta sunyi rau kamar xatayi kuka,




'Ni yaya bana son ta nikaďai xn kwanta,




'shikenan karkiyi kuka, ya ďauketa ya kwantar da ita a Saman gadonta yaja blanket ya lulluba mata,




'ki tabbatar da kinyi addua fa, ta gyada Kai tana kallonsa da murmushi,


'gudnyt bro
'night baby, ya fita daga ďakin yana sauke numfashi wannan ai security ce acikin gida, ďakinsa ya nufa sai da yagama abinda yake kafin ya nufi ďakin Iman tuni ta dade da yin barci, toilet ya nufa yayi wanka kana ya hau internet yanayi yana kallon gefen Iman dake kwance, sabuwar budurwar sa na online sai abin yayi masa daďi yau suka haďu a banki sosai tafi fatyma kyau sai dai hasken da fati xata nuna mata, aurenta yake son yi koxai samu Ya'ya kamar yanda yake buri a rayuwarsa, sunan ta Saudah......






2days~




Baba ya dawo daga tafiyarsa Wannan Karon xai ďan jima Nigeria kafin ya ďaga, Iman taje yi masa sannu da xuwa sai kallon cikinta yake don son tabbatar da Mgnr Sima idan da gske tana da ciki, baiga komai ba saboda bai fito ba,




Ya miqa mata wasu ruwa acikin cup,


'kisha maganin tsarine na karbo maki Iman,


Ta karba tana kallonsa,


'Fauxiya fa? sai da gabansa na faďi,


'nabata tasha ďaxu.... dai dai lokacin da fauxie ta shigo a guje tana dariya muxuru ne a bayanta ya biyota sai kiransa take tana nuna masa Naman dake hannunta, batare da tunanin komai ba ta faďa jikin Iman ta qanqameta cup ďin dake hannunta ya subulce ya faďi maganin ya xube qasa,




A fusacce ya fisgo fauxie daga jikin Iman haďe da ďauke fuskarta da mari,bai taba kai hannunsa akantaba sai wannan karon, hakan yayi matuqar bawa Iman mamaki, ďif numfashin ta na ďauke ta faďi ragwab a jikin Iman, da sauri ta riqata hankalinta a matuqar tashe take kallon mahaifinta da qanwarta, hawaye har sun fara xuba a idanuwanta,




'baba meyasa ka mareta, metayi?


'bakiga asarar da tayi min ba, kinsan maganin miye Kinsan ynda na samesa?




Sai alokacin Iman ta fahimci dalilinsa na dukan fauxie, but why? Saboda ta xubar da magani xai mata wannan duka? Ta fashe da kuka mai tsanani bayan ta ďauki fauxie ta fito da Ita, hankalinta bai tashi ba a matsayinta na doctor tasan suma ne tayi, babban tashin hankalinta bacin rai da tagani kwance a fuskar mahaifinta saboda fauxie ta xubar da wannan maganin, kada hasashenta ya xama gsky,




Tana fitowa taci Karo da motar Sa'eed a waje tasan yana ciki yana jiranta sai tayi bangarenta,




Daga inda yake xaune yake jiyo Kukan Iman, ya tashi hankalinsa a tashe a falo sukayi kicibis da juna fuskarta sharkaf da hawaye, duk yaji jikinsa yayi sanyi gwiwoyinsa sun sage,




Ya salam..... ya furta a hankali bayan ya karbi fauxie hannunta da sauri ta nufi kitchen ta ďebo ruwa a cup ta fito, yayyafa mata ruwan suka shiga yi,bata đauki wani lokaci ba ta sauke ajiyar xuciya amma idanuwanta a lumshe, gefen fuskarta yayi jawur sosai gwani bn tausayi,




Sa'eed yace meya sameta haka?
'baba ya mare ta,
'Mari? taya xai daki wannan yarinya metayi masa haka? Nan tayi masa bayanin komai yayi shiru cike da tunani iri iri, wannan wane irin maganine,




Tunda ta farfado take kuka qanqame a jikin Iman sai rarrashinta takeyi,


'Anty meyasa baba ya dakeni, tell him i hate him, Anty Kice masa bana sonsa yaya nakeso, yaya baya dukana, I don't like baba,




Iman ta qara rungumeta a jikinta,
'is ok fauxie kinyiwa baba laifi, kin xubar da maganinshi shiyasa ya dake ki, don't hate your father,


Kuka take sosai ba kakkautawa, numfashinta har sarqewa yake, idanunta sunyi jawur sun kumbura, idan Iman ta kalleta itama sai taji hawaye na xubo mata, fauxie bata taba kasancewa a irin Wannan yanayi ba, abinda ta jima batayi mata ba dan tayi shiru sai ta ďauketa ta goyata tana rarrashinta,


Fauxie ta kwantar da kanta a bayanta hannuwanta qanqame da Ita hartayi barci bata daina sauke ajiyar xuciya da qarfi ba,




A hankali Iman ta kwantar da Ita kan sofa tana kallon yanda fuskar ta kumbura, kanta yayi xafi sosai dama tasan Wannan Kukan sai ya janyo mata ciwon kai,


Tana son sanin dalilin mahaifinta na dukan fauxie akan magani,


Meyasa ya fifita maganin akanta? Wannan Karon xata tunkaresa da Mgnr sai idan itama xai daketa,




Ban yarda da cikar imanin mahaifina ba, tabbas akwai wani boyayyen al'amari game da rayuwarsa shida Deedah, akwai abinda suke boyemin Wanda ya kamata na sanya ido akai na gano ko menene, tabbas a yau na kasance mai xargin *babana da mijina* ban sani ba ko Allah xai iya yafemin xargin dana ke masu? Ta soma kuka sosai Mai narkarda xuciya,




Tana cikin ruďani, Tana neman mafita, tana cikin tsoron halin da suke ciki ita da qanwarta,




Sa'eed na xaune yana kallonta xuciyarsa ba daďi shima kamar xaiyi Kukan a yanda yakeji a xuciyarsa, domin Iman ta xama wani bangare na xuciyarsa duk da tana matar abokinsa yana jinta a xuciyarsa tare da tsananin tausayinta,




Irin Kukan da take mai raguwar xuciya baxai iya daurewa ba sai ya tayata, _and he don't want to be among, he dunno why her cry weakness him, he want to turn this sadness to joy...._,




Abinda yasa a ranshi yana son bata farincikin da ta rasa gurin mijinta, yana so yabata kulawa irin wacce mace ke buqata a gurin mijinta kamar yanda shima bai sami kulawar gurin matarsa salima ba, _he want to make these tears to smile_.




Amma ta wace hanya?


Babana da mijina.....




©fertymerh Xarah




19




Tashi yayi ya fice daga gidan baki ďaya, cikin mamakin Deedah inda yake xuwa yabar matarsa a Wannan halin.....






Salima na xaune da qawarta ya shigo, cikin girmamawa qawar ke gaidashi amma banda salima ta ďauke kanta wani gefe tana taunar cingam,






ďakin sa ya nufa,
Qawar ta dubeta,
'bara na tafi salima mijinki ya dawo sai wani lokaci,


'Haba habbi idan ya dawo me xanyi masa, kiyi xamanki Musha hira, Mai aiki xata Kula da shi,




'Chabďi lallai salima Ashe har ynxu kina nan da halinki, shiyasa naga ya shigo ko sannu da xuwa baki masa ba, bansan meke damun rayuwarki ba, baki Kula da mijinki bakya kyautata masa, kina da miji mai kyau da kuďi ďan gayu dashi.....




'kiyi shiru habbi bana son haka, ba ruwanki da kyawun mijina,




'au kishi kike yi, kina sonsa kike masa haka, ai wallahi Sa'eed yafi qarfin ajinki kema kinsani darajar ya'yan ki kike ci ina gaya miki gsky a matsayina na aminiyarki ki canxa halinki ki rungumi mijinki,




'Naji sai anjima habbi,
'ki koreni ynxu tunda na gaya miki gasky, ta tashi sabe da jakarta ta fice bako sallama, salima na bita da kallo,




Duk Mgnr da suke akan kunnuwan Sa'eed, yasan halin salima baxata taba canxawa ba yana mamakin xuciya irin tata, yasan inda xai kamata,






Yana xaune mai aikin ta shigo da kaya a hannunta ta ajiye a gabansa ta fita, bata jima ba sai gata ďauke da ruwa da lemu, ta xauna haďe da tankwashe qafafuwanta tana xuba masa abinci a plate, shiru yayi kawai yana kallon yarinya aikin da take yafi albashin da ake bata, dole xai qara mata kuďi, ya ďauko Mai aiki saboda wanke wanke, mopping da kula da yara, sai gashi mai aikin ita ke kula da komai tun daga gidan, yaran har Mai gidan komai itace,




Tana gama xuba masa ta tashi ta fice da sauri batare da ta kallesa ba Kamar yanda matar gidan ta gargaďeta.




2day~




Tun daga ranar fauxie bata qara xuwa gurin baba ba hassalima muryarshi idan taji guduwa take ta boye bayanda Iman batayi da Ita ba, ta riga ta sanya tsoronsa a xuciyarta,




Shima baba yana tsananin nadamar Marin da yayi mata dan gashi fatyma tana xarginsa da wani abu akai, baya manta sanda taxo ta sameshi da Mgnr dan me xai Mari fauxie akan magani,




'saboda tayi min asara,
'wannan wace irin asara ce da tafi lafiyar fauxie baba?
'banason Mgnr banxa fatyma, Fauxiya ya'ta ce I have the right in mata duk abinda naga dama a duniyar nan bamai cewa dan mi saboda ni na haifeta,




'Ni xn tambayeka dan mi saboda qanwatace, ita kaďai nake da a duniyarnan, amana ce a gurina idan na Bari aka cutar da Ita gobe Allah xai iya kamani, Inaso na bata farin cikin da bata samu a gurin UWA ba, fauxie na min kallon wani bangare na rayuwarta jin daďin ta da komai,




'Ashe baki da tarbiya Iman, ni xaki xauna kina gayawa mgn haka, kina nufin bana baku farin cikin da mahaifiyarku xata baku idan tana raye ko me? Kije gaki gata indai nine sai naga bayanku...... Sosai ta buďe ido tana masa kallon mamaki da jin furucinsa shi kansa baisan ya furta ba sai a ynxu sai yayi Saurin gyara mgnrsa,




'Ina nufin kije gaki ga Fauxiya ki xame mata uwa duk abinda takeso ki mata,ki ďauki duk wani responsibility nata, na yafe maki ita kome xai same ku daga ke har ita baruwana da lamarinku,




Batare da tayi mgn ba ta fice tana kuka sosai, Kukan maraici da rashin gata a ynxu....




Tun daga lokacin ta daina xuwa gaidasa kamar yanda Yace ba ruwansa dasu haka suma ba ruwansu dashi, sai dai kallo daga nesa ko idan sun jiyo jiniyar motocinsa,






Tana xaune a falo taga jini na bin qafafunta, ba ciwon mara ba komai jini ya soma fito mata, da sauri ta nufi toilet ta duba, bleeding takeyi sosai kenan cikin xubewa xaiyi ta faďa a xuciyarta sai ga hawaye na bin kuncinta ta fito da sauri jikinta har rawa yake, tun daga Sama har qasa duk inda tabi jini ne, tana kuka ta Kira adama ta gyara gidan xataje asibiti,




Sosai masu aikin sun tausayamata, abinda suka lura da rayuwarta akwai kuďi a tare dasu amma ba kwanciyar hankali.




Tana fitowa Sa'eed na shigowa, yanda ya ganta ya sanyashi fitowa ba shiri,




Key ďin motar ta ta bashi dan batason ta bata motarsa,


'muje asibiti Sa'eed, bleeding nakeyi ka taimaka ka kaini Kada cikin ya xube Ina matuqar son sa,


Yakai Idanunsa qafafuwanta sosai ya rikice yace ta shiga tashi motar,


FMC suka nufa suna isowa ko parking bai gama ba ta fita da sauri, sai ynxu takejin ciwon mara amma bata damu ba, Sa'eed na bayanta shima hankalinsa a tashe suka nufi Gynaec,


Tayi Sa'a Dr Fulani na gurin ita ta dubata ta gaya mata cikin ya lalace ya riga ya xube wata biyu,




Wani irin kuka ta soma yi gwani ban tausayi Fulani na rarrashinta da bata baki sai dai tana mamakin yanda cikin fatyma ke xubewa akai akai bayan ko ynxu ta dubata batada matsalar komai a tare da Ita,


A Wannan lokacin sai fatyma ta yanke hukuncin xata soma planning meyiwuwa bata da rabo a duniya sai ta huta da wannan wahala da take taji da wahalar dake damunta, itama Fulani sai tabata kwarin gwiwa akan haka,




Sa'eed ya Kira Deedah ya gaya masa halin da ake ciki,


Sanda ya xo sosai xaka ga damuwa a fuskarshi, yana tsananin tausayin matarshi musamman irin kukan da take mai ratsa xuciya, daga shi har Sa'eed sai suka fice daga ďakin dan baxasu iya jure jin kukanta ba.






Dariya suke ba kakkautawa, irin dariyar da ko ina ke amsawa idan anayinta, sima da mutanenta kenan,




Burin ka ya kusa cika Abdallah idan kaci gaba da bamu jinin fatyma muna sha, muna jin daďin sa kaima kana jin daďin mu, akwai kuďi na can na jiranka a ďakin ka, ya sunkuya




Godiya nake ya shugabata, suka ďauki wata dariya....




Bayan sun dawo asibiti suna xaune a falo har salima matar Sa'eed da ya'yan su Adnan da Khadija,




Fauxie suna gefe suna Wasa da Adnan abinka da yaro bata damu ba sai dariya take tana xagaye falon ita da Adnan,




Deedah ya shigo da sallama a bayansa wata kyakyawar budurwace ta shigo,




Kallo ďaya Iman tayi masa xuciyarta na soma bugawa fal fal ko sallamar bata amsa ba ganin ynda Deedah ke rawar jiki akan yarinyar ita kuma Wacece,




Budurwar ta xauna tana gaidasu duk cikin su salima kawai na amsa, Sa'eed ma kallon mamaki yake masu, Deedah ya soma mgn






Uhm....uhm... Iman ga saudah ta xo ta gaidaki ta miki ya jiki, mgnr da ta fito bakinta da wadda yaji fauxie nayi nayi matuqar ruďashi,




'ita wacece, daga ina.... dai dai lokacin da yaji fauxie na cewa,


'Adnan ina bindigar ka muyi wasa?


'yace ni banda bindiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login