Showing 45001 words to 48000 words out of 55052 words

Chapter 16 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE by FATIMA ZAHRA

28 May 2026

5

wannan wane irin yaye ne?


'na yayeshi ďana ne nikeda haqqi akansa,


Ransa ya qara baci har ya juya sai Kuma ya dawo ya ďauki yaron ya fice a fusace ta bisa da ido kawai,


Bata damu ba ta maida hankalinta ga duba files,


4pm ta isa gida yau, anan take jin labarin Deen yaxo ya kwashi kayan little duka ya tafi dashi, ba Wannan ne damuwarta ba a Yanxu, qirjinta ke ciwo sun cicciko tun jiya ba'a sha su ba, ga wani nauyi da suka mata har Xaxxabi take ji, daďin ta ďaya fauxie taje islamiya da xata dameta ne da surutu, tana fashin sallah sai ta kwanta kawai batare da taci abinci ba,


Shiru shiru bata fito ba har magrib, fauxie ma batasan tana gidan ba tana can cikin gida tana wasa, Adama ta shigo ta ganta a kwance,


'hajiya ba lfy ne yau kika xauna a ďaki,
'yauwa, kunun alkama ko kunun farar Shinkafa nake so kimin,


Shikenan tasa kai ta fice da sauri, sai ga fauxie ta shigo,


'anty ki Kira yaya yaxo yaje dani inda baffa tun jiya yaje da little bada niba,


Tayi mata banxa,
'kinji anty.... nan ma ta kyaleta dai dai lokacin wayarta na ďauki qara, tana dubawa taga sunan salima kamar baxata ďauka ba sai ta ďauka,


'kin ban mamaki fatyma, ki rasa inda xakiyi xawarcinki sai akan mijina, kinci amanar qawancenmu Kuma kinci amanar Deedah, abokin mijinki da qawarki saboda bakida hankali, to ga gidan ki shigo ki xauna kigani idan xaki iya kishi dani, kuma kisani agola baxai xauna mana a gida ba, ya Mtsewwwwww ta tsinke wayar,


'agola? Iman ta nanata sunan tana kallon wayarta, Yanxu yaronta ake kira agola?


'kinji anty... Fauxie ta katseta,
Cikin tsawa tace, ke kimin shiru banxa, get out please, da sauri ta fice cikin tsoron yanayinta,


*


Wallahi baka isa ba, kayi kaďan Sa'eed, kai ko kunya bakaji ka auri matar amininka,


'iyakar qarshen rashin kunyar kenan in aureta in kula da Ita in kula da yaronta shine na riqe amana, inason Iman baki isa ki hanamin auren taba,


'wallahi koni ko ita a gidan,
'na zabi Iman,
'haka kace, haka kace?
'eh haka nace, to me kike min a gidannan ba abinda kikemin ba kulawarki ba kulawar yarana, su kansu na tabbata idan na kawo Iman a gidannan xasuji daďin kasancewa da Ita, kewai ko kunya bakyaji kullum sai anyi miki faďa akan yanda xaki kula da miji da gidanki, duk sanda xn sami habbi a gidannan inajin yanda take maki faďa kike gwatsaleta, nagaji da xama a hakan shiyasa na gayamiki xn auri Iman,


Kuka take shabe shabe, duk abinda ta samu a ďakin jifansa take dashi, yau takai salima harda xagin Sa'eed, kuma tayi rantsuwa Iman bata isa ta shigo gidan ba indai tana raye, yasa kai ya fice bai qara bi ta kanta ba....




Tunowa da Deedah da kalmar da aka jefi ďanta da Ita yasanyata kuka a ranar, har safiya bata rumtsa ba kuma Sa'eed yaxo da kansa yabata haquri tare da rarrashinta, baxai haďe su a gida ďaya ba kowa da nata gidan sai taji sanyi a xuciyarta ta qara amincewa da son da Sa'eed ke yi mata.


Yau kwana uku kenan bataje asibiti ba tana gida ba lafiya, Deen bai gantaba Kuma bai damu ba, amma yau yayi niyar kaimata little meyiwuwa tayi xuciya da yaron ne shiyasa ta daina fitowa asibiti,


Tana xaune falo sanye da hijab ya shiga da Sallama, bai bari sun haďa ido ba, yanayin fuskarsa kaďai xai nuna mata har lokacin yana fushi da Ita, duk sai taji wani iri a jikinta ta xuba masa idanuwa tana kallonsa,


Gayen ya haďu qarshe ga iya shiga ta suit da shadda, kai har white cotton lace da qananan kaya ma kyau suke masa, idaniya basa gajiya da kallonshi harga maza yan uwansa bama mata kaďai ba, ga yawan sumar jiki data kai, bata taba ganinshi cikin rashin walwala ba kamar yau,


Taji sabon al'amari yana fisgar xuciyarta game dashi, tsigar jikinta na tashi, ji take kamar ta ďora kanta a kafadunsa taji dalilin damuwar da yake ciki inda hali ma ta rungumeshi,


Kai tsaye ya nufeta ya ajiye little a gefenta, qamshin turarensa dana hucinsa suka gauraye suka daki hancinta,


Ya ilahi ta furta a hankali tare da kai hannunta ta dafe qirjinta sabida Karfin bugunsa daya qaru, meke damuna ne yau akan Deen? Juyowar nan da xatayi sai idanunsu cikin na juna yayi maza ya ďaure fuska ita kuma duk kunya ta kamata tunda ya kamata tana mishi kallon kurilla kamar bata taba ganinshi,


Daga kallon da yayi mata nan take ya gane bata lfy, idanunta sun xurma kaďan fuskarta tayi rama har xaiyi mata mgn sai Kuma ya fasa yasakai ya bar falon, ta bisa da kallo,


Ta yarda ta saduda ta amince Deen ya haramta gareta, soyayyarsu ta xama mafarki mai daďi irin Wanda ďan Adam kanyi ya farka yana mai cixon yatsar sa kasancewarsa reality,


_'dreams are concerned but not all dreams are born alive, some are aborted, others are still born._


Kalaman..... Noble Laureate ZAINAB ALKALI.....






My wattpad Phertymerh1
*BABANA DA MIJINA*




©Fertymerh Xarah 💞




40




Shin menene ya shiga kantane daya makantar da idanunta ga soyayyar Deen? Me Deen yayi mata? Menene aibunsa? Me take nema agurin namiji da babu a gurin Deen? Sa'eed ma yana da qualities ďin da duk mace take so ta mallaka a gun namiji, first class....


ta sauke ajiyar xuciya lokacin da taji little na qoqarin cusa hannunsa a rigarta da alama abincinsa yake so, ta ciro hannunsa tana kallonsa,


'you are big enough da shan wannan yanxu little, xaka sha tea? ya girgixa kansa yana janye hijabin jikinta, ta riqa hannunsa tana kallonsa ya fara kuka yana son kaimata cizo a hannu, ta soma dariya tana yi masa gwalo, ya mintsini Kumatunta,


'tace wash wash, ya kyalkyace da dariya,
'dole kayi dariya tunda kayi mugunta, ta tashi dashi goye a bayanta ta nufi kitchen dashi...


Yana ganin tana haďa tea yasan ba mamma xata bashi ba ya soma kuka yana cusa hannunsa cikin riga, ta fito dashi tana faďin,


'yau me ya shiga kankane na son mamma, ai idan kasha wannan yau xaka mutu, and I don't want to lose you my boy, ta sumbacesa ya janye fuskarsa yana kuka, bata ankaraba cup ďin dake hannunta yasa qafa ya bige, tea ďin ya xube, ta dubesa sai ma ya bata dariya,


Kukansa ya fito da dijeh tana faďin,
'Ashe mai gida ya dawo, Kukan me yake haka,
'yau rigima yakeji sai na bashi mamma, kinga yanda ya xubar da tea ďin dana haďa masa kixo ki gyara gurin,


Tayi harabar gidan dashi inda motocin sa na wasa, idan tayi qoqarin sanya sa yaqi xama ya qanqameta yana kuka, keke ma yaqi ya hau, duk inda tasan yake so takaisa yaqi, ta bashi ball yaqi, abincinsa yake so, yau fitinar yaye xai mata ko banxa dama gashi da rigimar kuka, suna haka sai ga Sa'eed yaxo, ya karbesa yana faďin,


'waya taba little yau,
'rigimar yaye yakeyi yau,
'kin yaye shine? Ta gyada Kai tana kallonsa,
'ai nayi qoqari shekara ďaya da wata takwas fa,
'yace hakane kam, ya juya dashi yana faďin bari muje mu dawo....tana tsaye suka fice cikin mota ga mamakinta sai taga little yana dariya acikin motar sai tsalle yake batasan meyasa yaron keson yawo ba kuma da maxa kodan ya kasance namijine oho? tayi cikin gida.....




2 days.....


Har lokacin ta rasa sukuni a xuciyarta kwata kwata Deen ya canxa mata ba kamar da ba, ita dashi sai gaisuwa ko yaxo gidan inda fauxie da little xai xo, suyi wasar su ya fice wani sa'in ma ya tafi dasu batare da ya kulataba, sai tayi qoqarin mantashi da ciresa a xuciyarta amma ta kasa ba dan komai ba sai yanda yake Kula da yaran, yanda ya saki jiki dasu suma yaran suka shaqu dashi sosai ranar da duk bai xo ba batada kwanciyar hankali musamman a gurin little xai ta mata fitina har sai ta haďa sa da driver ya kaishi inda baffa, wannan na ďaya daga cikin dalilin dayasa ta kasa cire Deen a xuciyarta, Mai son naka shine... (na manta hausar😱)


A yau ta shirya ta nufi gidansu Deen inda baffa tun kafin takai ga gidan ta tsinkayo motar Deen a waje, taja tayi parking gefen titi, tana xaune cikin motar taga fitowarsa abinda bata sani ba tun fitowarsa yaga motarta sai ya basar ya shiga motar sa yaja, ta madubi yake kallonta lokacin da tayi parking gate ďin gidan,


Tana shiga gidan part ďin baffa ta nufa, a kullum xaka samesa da tulin littafan addini agabansa yana dubawa, da Sallama ta shiga falon,


Ya amsa sallamar yana kallonta fuskarsa da walwala,
'nayi fushi, ance ďiya mata sunfi Ya'ya maxa kulawa da mahaifansu amma banda Fatima, yau sati biyu ban sanyaki a idanuwana ba,


Murmushi tayi cikin jin kunyarsa ta qarasa ta xauna kan sofa tana gaidashi,


'baxan Karbi gaisuwar ki ba,
'kayi haquri baffa baxan qara ba ynxuma dan nayi fama da ciwo ne,


'Subhanallah kinga ban sani ba danaje duba ki, Anya Zaharadeen ya sani kuwa?


Tayi shiru kawai tana murmushi, tasan yasani bai damu ba a ynxu tunda baya son ta, tayi rau rau da idanu ta, yanayin fuskarta ya fuskanci kamar da matsala,


'ko akwai damuwa ne fatyma? ta girgixa kanta har lokacin kanta na sunkuye, ya gyara xamansa yana fuskantarta,


'ko har yanxu baki bani matsayin uba a xuciyarki ba, keda Zahara duk ďaya na ďauke ku ba banbanci, ki gayamin damuwarki a matsayin uba ba matsayin uban Zahara ba,


'dama.. dama baffa Deen ya cnxa ne kwata kwata, naga ya daina walwala bansan meke damunsa ba,


'ni banga ya canxa ba har ynxu yana yin komai nasa kamar da, haka yana walwala meyiwuwa kece bakya gani amma kin tuntube sa da Mgnr? Ta girgixa kanta,


'xn tambayesa inji koda damuwa a tare da shi,


'amma baffa kada kace ni nace, yayi murmushi yana kallonta,


'tor shikenan fatyma, yau bakije asibiti ba,


'Gobe nakeso nafara fita, baffa xn maida little nan da mai rainonsa saboda yaron baya son xama acan yafison nan,


'A'a kibar mai rainon, masu aikin gidannan ma xasu Kula dashi ya saba dasu sosai watarana ma acan yake yini tare dasu,


Ta tashi tana faďin shikenan ba abinda xanyi ma ne?


'ba komai sai dai idan xaki dawo kixo min da irin Wannan dambun da kike aikomin, wannan kuku da Zahara ya ajiye bai iya komai ba sai yayi girki ba daďi, bana son abincinsa ko kaďan namiji bai iya girki ba,


Tayi dariya tana kallonsa,
'akwai kukun da ya iya girki baffa ko wata mace albarka kawai dai ba'a dace bane, amma idan ba damuwa kullum xan riqa aikoma da abinci, shi Kuma kukun abarwa Wanda ya ajiyeshi ya riqa masa girki, yayi dariya yana kallonta,


'ba damuwa fatyma aike ya'ta ce, Allah yayi maki albarka,


Ta amsa da amin xuciyarta na bugawa idanunta na kansa, yau ne Karo na farko data soma jin haka da Wanda ta Kira uba a ynxu, tunda take da baba bata tabajin ya Sanya mata albarka ba kome xatayi masa a duniya sai dai yace ya gode, wannan dalilin yasa taji sanyi a xuciyarta taji ta qara son baffa ta ďauke shi a matsayin mahaifi ynxu koda Deen kobada Deen ba, ta samu uba nagari saura miji na gari......


4.pm


Ta fito riqe da Jakarta a hannu a gajiye take, Sa'eed na bayanta har gurin motarta ta buďe ta xuba kayanta kana ta ďago tana kallonsa,


'kinqi magana, ki gayamin gskyr xuciyarki game da ni,


'haquri xn baka still Sa'eed, bawai bana sonka bane, salima ce matsalata a ynxu, kullum sai ta kirani ta xageni bnda test ďin da take turomin daban, ban shiga gidan ba tana kiran yarona da agola, little baxaiyi agolanci a ko ina ba, ina son yaron fiye da tsammaninka Ina sonsa fiye da mahaifinsa Deedah, baxan lamunci duk wani xagi da cin Fuska daga matarka ba,


'kina tunanin saboda salima xaki qi aure na, saboda me Iman, ba xamanta xakiyi ba xamana besides ma ba gida ďaya xaku xauna ba, na karbi little a matsayin uba nayi maki alqawari xan bashi matsayi a xuciyata Kamar Adnan, wallahi Ina sonki, ina sonki tun marigayi na raye bnsan yanda akayi na fara sonki ba kawai na tsinci kaina da sonki, help me and save my life Iman, karkiyi tunanin saboda salima bata kula dani xan aure, saboda qaunar danake maki ne, kinsanni na sanki, inason kasancewa dake, ina son baki farin cikin da baki samu a baya ba please Iman....


Sai ga hawaye na kwaranya a idanuwanta, sai Numfashi take maidawa batasan yanda xatayi da rayuwarta ba, idan tace batason Sa'eed ta cutar da xuciyarta to Deen fa? inama Deedah na raye da hakan bata faru da itaba, da Yanxu suna rungume da ďansu cikin farin ciki da so da qauna, Kuma ba Wanda tafi cancanta da aure kamar Sa'eed shine abokin mijinta shine yafi kowa sanin kanta, Deen ma na buqatar taimakonta ko dan baffa, yana buqatar Mace a kusa dashi, yana buqatar kulawar Mace ya daina struggling rayuwarsa haka, bata manta itace sanadin mutuwar matarsa hajara.... wani kuka ya xo mata,


'Sa'eed Deen fa ya kakeso nayi dashi he need me too...


'ba sonsa kikeyiba tausayinsa kikeyi, meyasa kika fi baiwa soyayya muhimmanci fiye da kauna? Love is not the only thing we are to go for in marriage.... there are other important aspects , sacrifice and devotion, idan kina tunanin Deen na son kine ni kaunarki nakeyi Iman,


'I have no choice Sa'eed..... dai dai lokacin da Dr Deen ya shigo harabar asibitin yana fitowa motar suka haďa ido da ita sai da taji faďuwar gaba,


Sa'eed ya lura da irin kallon da sukewa juna nan take yaji wani kishi, xafin so na bugun xuciyarsa har kwalla yayi,


'ba komai fatyma, ki xauna da Wanda xuciyarki ta aminta dashi, ina sonki ina son farin cikinki, tunda kin fison Deen kije gaki ga Deen..... yasa kai ya fice, tabi bayansa da kallo kafin ta maida kallonta ga Deen shima tuni yabar gurin bayansa kawai take hange, ta kalli wannan ta kalli wancan,


_'Ni ďan halak ne kije gaki ga Sa'eed_,
_'kije gaki ga Deen_,


Me suke nufi? Kada dai sun haqura da itane?


Gashi ta bata goma bata gyaru ba, babu Sa'eed babu Deen, bataga tsuntsu bataga tarko.


Menene makomar rayuwarta a halin yanxu? wa xata aura Sa'eed ko Dr Deen? Ko xatayi ta xama haka har qarshen rayuwarta ba aure ne?


Rashin sanin haqiqanin waďanna amsoshin ya sanyata rushewa da kuka mai cin rai.


Da kyar ta shiga motarta tabar asibitin tana isowa gida ta samu Suleiman na jiranta tasan baxai wuce kuďi yakeson tabashi ba,


'ya akayine sarkin son kuďi, yau ba kuďi a hannuna nima,


Yayi dariya yana kallonta,


'hajiya ba mgnr kuďi bace, an sanya maganar aure na wani watan,


'Allah ya Sanya alkhairi, ta nemi guri ta xauna nan harabar gidan batare da ta shiga ciki ba,


'Ina mutuniyarka ko batasan na dawo bane,


'suna bayan gida itada little, yaran ne akwai son wasa hajiya bama kamar little,


Kafin tayi magana motar Dr Deen ta shigo harabar gidan, bai fito daga cikin motar ba yana xaune ya soma danna horn, ga mamakinta sai ga fauxie da gudu little na bayanta basu damu da itaba kai tsaye suka nufi motarsa suna dariya,


Fauxie ta buďe motar ta shiga, tana shiga ta rufe tabar little a waje, ya soma kuka,


'buďe masa ya shiga, meyasa xaki rufe masa motar,


'yaya baxamu je dashi ba, bayajin magana ya fiye tsokana,


'Kema bakyaji ai... ya buďe masa ta bangarensa da gudu ya xagayo kamar xai faďi Deen ya ďauke sa ya sanyashi a mota, ya soma dariya yana tsalle a motar,


Deen yaja motar suka bar gidan, Suleiman ya dubeta,


'hajiya yaran nan naki suna son wannan mutumin, Kuma bashi da matsala yana da kirki, haka ranar yabani dubu biyar saboda ya ganni da fauxie,


'kai duk wanda xai baka kuďi mai kirki ne a gurinka, da Wannan surutu ka tashi ka shiga cikin gida, adama ta haďa ma kayan wankinsu ka Kai,


Ya tashi yana faďin an gama hajjaju...


tayi shiru kawai xuciyarta cike da tunani iri iri.....






My wattpad Phertymerh1


Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)


WHATSAPP NO:
+2347039625239


*Babana da mijina*






©Fertymerh Xarah 💞


*Dis page is for you, Shafaatu Zurmi, Pherty b-b, and Aneesa A Rimi*




41




Tun daga lokacin bata qara sanya Sa'eed a idanuwanta ba, ga Deen ya daina kulata tuntuni ma, ta shiga damuwa sosai,


Little ba lfy koda wasa baiyi yunqurin gayamata ba yasan halinta akan ruďewa, duk da Xaxxabi ne kawai yakeyi, shike Kula da yaron har a asibiti yana tare dashi, bata taba sanin baida lfy ba har yaron yasami lfy, daga baya ne takejin labarin a gurin baffa.




1 month....


Kai tsaye ta shirya ta nufi bank inda Sa'eed, akayi Sa'a shi kaďai ne a office ďinsa, suna haďa ido sai da sukaji wani iri a xuciyarsu, yayi qarfin halin ďauke Idanunsa akanta haďe da sakin malalacin murmushi wanda bai kai xucci ba,


Yanayin fuskarsa ya Sanya ta nufi cikin office ďin cikin kwarin gwiwa ta sami guri ta xauna,


'barka da xuwa, me xan sanya a kawo maki,


'need nothing Sa'eed... sai kuma tayi shiru idanunta sunyi rau, shima shirun yayi xuciyarsa na bugawa,


'ya su little da fauxie,
'Alhamdulillah...
'ko da matsala ne Iman? ta gyada kai tana kallonsa haďe da share hawayen dana xubo mata,


'why did you hate me Sa'eed?
'saboda me, meyasa kike wannan mgnr iman, duk duniya akwai wanda ya kaini sonki ne, you hate me shiyasa na barki da Wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login