Showing 54001 words to 55052 words out of 55052 words

Chapter 19 - BABANA DA MIJINA BOOK COMPLETE by FATIMA ZAHRA

28 May 2026

34

Zaharadeen......








My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina*






©Fertymerh Xarah 💞






*Dedicated dis buk to Rabi'atu Sk Mhs, Serdia Lawal bala & Aysher Gambo*






46










A gurguje


Rayuwa ta miqa, so da shaquwa sai daďa qaruwa take tsakanin Su,




Xuwa Yanxu Iman ta gama sanin ko Waye mijinta Zaharadeen , ta yarda ita kaďaice a xuciyarsa,


Mutum ne dayasan ciwon kansa, ya kuma San mutuncin ďan Adam da kuma darajar aure,


Haka Kuma mutum ne da ya San soyayya mai tsayawa mutum a qoqon rai, barta kyawun halittarsa Deen is Classique da kowacce ďiya mace da tasan ciwon kanta xata yiwa kanta burin mallakarsa,


Xuwa ynxu soyayyar mijinta ta ratsa kowacce jijiya mai gudanar da jini a jikinta ta ratsa qashi da bargo,




Duk dukiyar da suke da bai damu ba, ba ruwanshi da dukiyarsu burinsa ya sauke haqqinsu dake kanta,


Iman knows her husband for now, tasan waye shi tasan aikinsa, ta bashi amana da yarda 99% tasan baxai cutar da rayuwarta ba,


Daga Deen har mahaifinsa tafisu kuďi amma basa barinta taba dukiyarta sai dai suyi amfani da tasu, hankalinta da xuciyarta sunfi kwantawa a ynxu she loves Deen tana masa wani irin son da bata taba yiwa wani namiji irin sa ba,


A da ta ďauka Deedah kaďai ne a xuciyarta, Deedah kaďai xata so har qarshen rayuwarta, Deedah ne masoyinta amma ynxu Deen ya mamaye wannan gurbin na Deedah, idan tana tare da Deen harta Kan manta kanta da wani Deedah, sai dai idan ta kalli little tayi masa addua,




Ko a ynxu xata iya shaidawa duniya she have the best father and husband a ynxu, mutanen nan biyu tana alfahari dasu a ko ina and she will never forget them in her life, presently *Babana da mijina*, tayi murmushi tana kallon baffa dake tsokanar fauxie,


'matar sultan, matar sultan, yarinya tun tana qarama anyi mata kamen miji...


'ni ba matar sa bace baffa, bana sonsa..... ya soma yi mata dariya,


'shikenan irin auren nan da akeyi a da shi xa'a yiwa wata, Wayyo bata san mijinta ba sai dai a ďauketa akai masa, kinma ji daďi xakije gidan sarauta, akwai Wanda yafiki Sa'a Kuwa na kasancewarki surukar Dr Merah,




Kuka take sosai ta faďa jikin Iman, daga baffa har iman dariya suke mata ganin da gaske kuka take suka kyaleta, akwai bidiri kenan a *Sultan Merah*,




Ko ina kuka hango min salima🤔


Salima Yanxu ta xama cikakkiyar mace wace ko wane namiji yake alfaharin samun irinta,


Believe me Sa'eed har cewa yake da haka take tun farko da ba'a abinda xai sanyashi auren habbi, duk da haka baya regretting na auren habbi itace sanadiyar shiriyar salima,


Xama suke na amana duk da baxaa rasa irin kishin nan namu na mata ba, (kamar Serdiyer Lawal bala) suna ďan tattatabawa watarana amma ba kullum ba,


Kowace tana kula da mijinta da ganin ta kyautatamasa, kowacce tana son tafi yar uwarta a xuciyar mijinta, yana sonsu Kuma yana kwatanta adalci tsakaninsu gwargwado iyawarsa.....




Ta fito sanye da doguwar riga ta shadda, cikinta ya turo sosai Kamar yau xata haihu, Deen na bayanta da plate ďin sinasir ďayan hannunsa juice ya riqo, rarrashinta yake akan taci abincin taqi, duk inda tayi yana biye da Ita,


Suna isowa falon ya ajiye kayan ya juyo yana kallonta lokacin take qoqarin xama,


'har sai yaushe xaki daina wahalar dani, idan baki ci abinci ba taya kike tunanin nima xn iya cin nawa, ta tsuke baki tana kallonsa, ya xauna kusa da ita haďe da ďora hannunsa akan nata hannu,


'Bari na baka kaci tukunna, bana son kana xama da yunwa saboda ni likitana, all I have is you.... taja dogon hancinsa tana murmushi, yayi murmushi ya janyo sinasir ďin yana kallonta,


'sai kinci xnci, kina so baby na ya xama raggo baida kuxari ko, to baxan yarda ba ďure xn maki a ynxu, ta kwanta a kafadarsa tana murmushi,


'Baban little kana so ka nuna min kafison babyn dani... yayi shiru bai tanka ba ya soma cin sinasir ďin,


'kinga ni ki Kyaleni Kada ki dameni tunda baxakici abinci ba kuma ba ruwanki dani munyi faďa,


Dariya tayi haďe da sanya hannunta a plate ďin suka soma ci tare....


Watan haihuwar ta na shigowa suka ďauki annual leave a asibiti sukayi Dubai, acan ta haihu ta sami baby girl,


Rayuwa suke mai daďi wacce aka gina ginshiqin ta da soyayya ta gaskiya da amana, irin wacce tayi qaranci a Wannan xamanin, rayuwace mai cike da qauna da soyayya yarda da girmama juna, babu abinda suka sanya a gaba daga aikinsu, sai Kula da yaransu da kuma junansu,


Kwanciyar hankali da jin daďi tare da Iman a ynxu, ko yaushe xaka ganta fuskarta da farinciki sabanin da, bata da damuwa ynxu ko fargabar rayuwa,


Dr Deen shi ya taimakamata wajen ganin ta gina qatuwar islamiya mai ďauke da sunan baba da Deedah, adduarta ladar ta isa garesu a koda yaushe kuma Allah ya yafe masu kurakurensu,


Lokaci lokaci take masu sadaka, bata manta da waďannan mutanen biyu masu muhimmanci a rayuwarta ba komai kin daďin da take ciki, suna nan maqale a xuciyarta Kuma tana yi masu addua a koda yaushe,




Allah yaji qan maxan jiya ta faďa fuskarta da murmushi tana kallon Deen,


Ya amsa mata da amin, yana cigaba da danna laptop ďinsa, ta kwanta ta bayansa haďe da lumshe idanuwanta,


'Ina son mijina, ina alfahari da mijina, ko a ynxu xan iya bawa duniya labarin *Babana da mijina*, ba abinda xance sai Allah ya saka masu da gidan aljanna,


'wannan adduar tare dake fatyma, bani da mata a aljanna sai ke da hajara, kun bani farinciki a rayuwata bn taba dana sanin auren ku ba, the best wife's in the world, proudly to have you,


Ta qanqameshi sosai,
'my husband is the best too.. Suka rungume juna cikin tsantsan farin ciki da qaunar junansu.




Masha Allah lakuwwata illah billah!, Anan na kawo qarshen littafin *BABANA DA MIJINA*, kuskuren dake ciki Allah ya yafemin,


Ina Godiya ga duk makarantar littafan *Pherty*, Allah ya sada mu da alherinsa Amin.


Kuyi haquri da yanda qarshen littafin ya xo maku, a gurguje nayi komai exam Monday....


Sai mun haďu a *Sultan Merah* dan jin qarshen rayuwar fauxy,


*Sultan Merah* yana referring kowanne motion ďin sa akan *Mulki ko Sarauta* kamar mahaifinsa Dr Merah, ko ya rayuwarsu xata kasance tsakaninsa da fauxie?




*love you all*




My wattpad Phertymerh1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login