Showing 21001 words to 24000 words out of 47415 words

Chapter 8 - GOJE Book 1 Hausa Novels By Binta Umar Abbale.pdf

09 Jun 2025

1715

ya sake mai da idonsa gareshi yace." Inaso naji cikakken
sunanka gami da jin asalin tarihin rayuwarka."?




*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da
wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* katin mov ko airtal.
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊ï¸í ½í³š_*
_____________________


FREE PEGE



*19&20*
Cikin tsantsar tashin hankali! da gigita suka gurfana a gabansa kafin su sheda masa abinda
yake faruwa.............."Ya wani mike a fusace! tare da mi'ka tafkaken hannunsa wanda yatsun
ke cike da zabban zinare da azirfa! wani irin bahagon mari! ya dinga kifa musu kafin ya sanya
kafarsa ya tunkudesu duka suka fadi wanwar! a gurin. gabadaya suka Sunkuyar da kansu, jikinsu in banda rawa babu abinda yake.

Ya takarkare! da karfi! ya kurma uban ihu!!! lokaci k'ank'ani gabadaya kaf yaransa suka
kewayeshi! ya goya hannu a baya yana kai kawo a gurun!

Tsit! gurin yayi babu mai kwak'wk'waran motsi a cikinsu.

Lokacin da yake kai kawo a gurin kallonshi nake ina mamakin muninsa! baki ne sosai gashi
gajere dab da kasa, yana da katon kai da tafkekiyar fuska, gabadaya hallitunsa masu girma ne
bayan gajartar da yake da ita, bakinsa kato haka nan hancinsa kwala-kwala idonsa kadai ya
isa firgita yaro! jajawur! dasu, kasumba tayi kaca-kaca a fuskarsa babu kyawun gani! kallo guda za kayi masa ka tabbatar da rashin imaninsa.!

Cikin kaushin murya! ya fara magana kamar haka." A jinin jikina naji cewar akwai ayarin da
suka shirya min! Yau tsayin sati guda kenan idan na kwanta bacci nake ganinsu a idona!
babu wani shirinsu da zai firgatani! na shiryawa zuwansu! na kuma yiwa kaina alkawari cewa
duk yawansu sai naga bayansu! babu wani mahalukin daya isa ya tunkari inda nake ba tare da
she'kashi barzahu ba! nafi karfin hukuma! ballanatana wani dan adam! saboda haka
dukkunanin ku na umarceku da cewa ku zauna cikin shiri babu wanda zai fita da rai a cikinsu."!
jiki na tsuma! yake maganar yana wani irin huci! gabadaya ya burkice sakamakon jin abin da
yazo masa a bazata!


********
Saboda tsabar kwarjin da yayi musu sam sun kasa hada ido dashi, suna gurfane a gabansa,
yayin da shi kuma ke kai kawo a tsakaninsu kafin yaja tunga ya tsaya a gabansu, hannuwansa
ya goya a baya, babu wasa ya fara magana kamar haka." "Ya sunanku."?
babu wanda yayi magana a cikinsu. Ya sake maimaita maganarsa! uffan basu ce ba.
Ya juya baya yana kallon jama'arsa dake tsatstaye kowanne a cikin shiri.

"Alba bani wannan dorinar." yafada yana kallonsa.
Da saurin gaske ya ciro bulalar daga cikin gidanta, kaurinta ya isa! nayi imanin za ta iya dauke
fatar mutum.

Ya gyara rikonta a hannunsa, cikin wani irin hargagi! wanda yasa gurin amsawa! yace."Ba zaku
bude baki kuyi magana ba ko."? Duk da sun tsorata da yanayinsa, amma hakan besa sun
magantu ba.

Ya zabura! ya juya tare da kiran Alba! yana zuwa ya umarceshi da ya cire musu kayan jikinsu
kaf!
Alba yabi umarni!

Ya kai ya kawo ya gurin jikinsa na wani irin karkarwa! tsumin ne ya tashi! ganin haka ya sanya
wasu daga cikin yaranshi suka bara buga gangi!!! da bushe-bushe? Ya sake rikicewa! wani irin
tafka! yake musu! suna ihu! da birgima a gurin!
Birgima suke a gurin suna gurnani! yana binsu da tafkekiyar dorinar dake hannunsa yana tafka
musu, wanda ya janyo tsiyayewar idon daya daga cikinsu.

Hankalinta a masifar tashi taje tana kokarin rike masa hannu kuka take kariris! tana bashi hakuri

sunyi bala'in bata tausayi! bata san bashi da imani ba sai yau!

Tureta yayi ta fad'i kasa ta rirrike kafafunsa "Kayi hakuri wannan rashin imani ne, ka zubar masa
da ruwan ido ga jini yana fita a jikinsu kada kayi kisan kai." Wannan maganganun nata besa ya
fasa abinda yake ba, ya sanya kafarsa ya taka gwiwar wanda yake kokarin gudu! ya murza da
karfin gaske! wani marayan ihu! ya saki kafin ya zube a gurin yana karkarwa jiki yace." Yi hakuri
kada ka kasheni zanyi ma bayani."

Ba tare da cire kafarsa ba, ya buga musu tsawa! da fadin" Ya sunanka."? baki na rawa yace."
sunana Yakubu ." Ya kalli dayan da yake matagugu a kwance "Kai fa."? Yace." Sunana
Sulaiman."

Kafarsa ya cire yana wani huci! ya barsu a gurin.......Saman wani icce! ya zauna! wasu daga
cikin yaranshi suka bishi! da ruwa...

Wasu na masa fifita wasu kuma na kara kambaba darajarsa!

Nad'in kansa ya warware kafin ya sunkuya tare da bada umarnin a zuba masa ruwa a saman
kan.

Ya dago kan yana girgije ruwan sumarshi mai laushi tabi ta kwanta tana digar da ruwa. Alba
yasa abu yana tsane masa ruwan.

Har yanxu babu sassauci a tare dashi, idonshi na tsaye a inda suke. tana tsaye a gabansu,
magana a suke a tsakaninsu amma basa iya jin abinda suke cewa.

Ranshi ya baci da ganin abinda take, yarinyar ta nema ta lalata masa aiki. mikewa yayi da
bulalar a hannunsa ya karasa gurin, kallon mara imani take masa, za tayi magana kenan, a
zabure! yayi kanta da bulalar!! ta matsa gefe da sauri! gabanta na bugawa! jajayen
idanuwansa ya tsira mata cikin mashahuriyar tsawar data kusa sanyata sakin fitsari yace."
Wuce ki bani guri."! kafafunta na rawa ta bar gurin, bai ta'ba firgitata ba kamar yau.

Ya kallesu kafin yace." Ku tashi tsaye! suka yunkura da kyar suka tashi! gabadaya jikinsu ya
sauya kama saboda duka! yayi musu wani kallo kafin ya juya da basu umarnin bin bayansa.


Ba tare da iya kallon fuskarsa ba ya fara yi magana kamar haka "Aikinmu shine ta'addanci!
rai ba abakin komai yake ba a gurunmu, sannan muna tarewa jama'a hanya cikin dare mu
farauci dukkanin guzirinsu, muna rabasu da matansu da 'ya'yansu, mu kwanta dasu, kamar
matan auranmu daga 'karshe mu 'kona gawarwakinsu ko kuma mu fito dasu kan hanyar mu
yasar! duk wanda ya shiga komarmu bama saurara masa muna da muggan makamai kuma
muna da daurin gindi daga sama, kamar yanda ka sani cewa masana sunyi hasashen cewa
gurin da muke rayuwa akwai albarkar kasa, to tabbas hakane akwai! amma maigidanmu yaci

alwashin cewa babu wani mahalukin daya isa ya amfana da albarkar dake wannan guri sai shi
da ayarinsa, yawancin mu musulmai ne magoya bayanshi, amma ya haramta mana ibadah!
bama sallah bama salati da duk wani abu da ya cancanta, burin mu ako yaushe mu kashe duk
wanda yayi yunkurin shiga gonarmu, maigidanmu yaci alwashi mai zafi! akan duk wanda yayi
yu'kurin ganin bayan rayuwasa." Ya k'are maganar tare da sake risinar da kanshi kasa.

Beyi mamakin da jin wannan jawabi ba, hausawa sukace da dan gari akan cin gari, a jawabin
da sukayi masa ya fahimci cewa gabadayansu musulmai ne amma suka yarda suka bada
goyon bayan ta'addanci a kasa.

Ya girgiza kanshi da fadin." Yakubu-Sule daku aka hada baki wani wawa! zindiqi! mushiriki! ya
addabi! kasa da al'ummar dake cikinta, shin me kuke nema a duniya da har kuka mayar da
zubar da jini! abin banza? a matsayinku na Musulmai masu amsa sunayen annabawa! shin ya
cancanta ku aikata wannan ta'addanci."!
Gabadaya suka shiga girgiza, jikinsu yayi wani irin laushi, yaja numfashii ya fesar! kafin ya
cigaba da cewa." Dukkaninku baku cancanta da cigaba da rayuwa a duniya ba domin barin
irinku a ban 'kasa had'ari ne."!

Jin abinda ke fitowa daga bakinsa ya firgitasu, a tsoroce! suka shiga bashi hakuri suna kiran
sun tuba!!

Wani mugun mari! ya kifa wa daya da jikinsu, 'yar hantsile yayi ya kifa yaci da kasa! tsaye ya
mike! yana zagaye a kansu. gabadaya sun tsorata da yanayinsa, su kansu yaran shi basu
taba ganinshi a cikin irin wannan yanayin ba, jikinsa in banda tsuma! babu abunda yake, Zinat
kuwa addua take a zuciyarta kada Allah yasa ya aikata kisan kai!
Da jan ido ya kallesu, da fadin." *Ni! ne zan kawo karshen ta'addancinsa! *GOJE!!* *Nake mai
maganin wani takadiri! Nayi tawa! nayi ta wasu! wannan haka yake! ba'a zubawa dani a
kwashe lafiya! *Billahil-lazi hurramanu!* *nayi wa kaina alkawarin ganin bayansah"!* Yanda
yake maganar yana zazzare ido shi tabbatar da abinda yake cikin zuciyarsa hakan yake babu
'karya!

Shar'bebiyar wukar dake rataye a kafad'arsa ya fizgo! daga gidanta, wani masifaffan ihu! ya
kurma!!! kafin ya fara dadura! wukar a wuyansa!!
Tashin hankali kenan! gabad'aya gurin ya kacame! dan yaran sa ma manyan wukake! suka fito
dashi suna gurzawa a kowane sassa na jikinsu! . shi kuwa a wuyansa yasa wukar ya zage
karfi sosai! yake gurzawa.!

kuka wiwi! ta dinga yi tana kallon badakalar dake afkuwa, ita tsoronta kada su kashe kansu, ta
rasa ya za tayi da rayuwarta a cikin wannan mashahurin dajin!

Tana kuka na fitar hayyaci ta karasa inda yake gabanta na lugudan duka! hannu na karkarwa

take kokarin rike damtsan hannunsa, "Ka bari don Allah! ka daina! ka umarci yaranka su daina
kada ku kashe kanku."!!
Ko sauraranta beyi ba ya cigaba da abinda yake, jikinta na wani irin rawa ta rumgumeshi tsam!
tana kuka tare da dukan bayanshi. wannan ya janyo sadudarsa! ya cake! wukar! a gurin tare da
danneta da tafin hannunsa!
Numfarfashi kawai yake gumi na yankowa daga kowane sassa na jikinsa!

Tsit! gurin yayi sakamakon umarnin da ya basu, suka mayar da wukaken jikin jikinsu.

Har yanzu tana manne a kirjinsa ta kam'kamshi shi da yayi wani motsi zata kai masa duka!
kuma bata fasan kukan ba.

Hannu yasa ya d'ago fuskarta, suka tsirawa juna ido! ya jima yana kallonta kafin yasa hannu
ya goge mata hawayen da suke ta zuba! yayi namijin kokarin cireta daga jikinsa! ta sake
kokarin rungumeshi! duk a kokarinta na hanashi aikata wani abun.
Hannu ya daga mata da ido! ya gargade ta, sai ta sunkuyar da kai! amma har yanzu bata
dawo daidai ba.


Ya kalli Alba da fadin." Bani abun rubutu."

Da sauri ya fito da takarda da biro! ya mika masa.
A takaice ya rubuta."


_*(KA SHIRYA YAKI DA MAKASHINKA!!!)*_


Wanda yake da d'an sauran kuzari ya mikawa takardar da fadin." Sa'kona ne wannan kana isa
ka bashi, cewa daga ni *MAKASHIN MAZA!*

Da kyar! ya mike ya kama hanya yana tafiya tare da waiwayen d'an uwanshi dake kwance cikin
halin rai da rayuwa!


Koda ya karanta wasikar sai kawai ya fashe! da wata mahaukaciyar dariya! da mike tsaye tare
da dukan! girkakken dutsen dake gabansa!

Hannuwansa yasa ya tallefe 'keyarsa! tare da sunkuyar da kanshi kasa!

Ya jima a haka kafin ya d'ago yana kallon yaranshi dake kewaye dashi, gabad'ayansu suma
jikinsu yayi sanyi da wannan al'amarin.

Ya kalli Nuhu dake rakube! gabadaya kammaninsa sun sauya saboda wuyar da yasha, ranshi
ya sake 'baci! kawai ba tare da kowa ya ankara ba, ya fille wuka! tana! walwali a wuya ya
burma masa! a take ya fara shure-shure a gurin jini sai tsartuwa yake, kafin wani lokaci rai yayi
halinsa!
Ya juyo kansu a sukwane! yana kallonsu da kwala-kwalan idanuwansa! Sun tsorata mutuka
gaya da ganin tashin hankalin maigidansu.

*"Cike da cin laya yace."Kamar yanda na soke! wuyan wannan shashashan! to haka zan soke!
wuyan wannan marakunyar yaron daya tunkari inda nake! Ni! nayiwa kaina wannan alkawari!!
saboda haka zamuyi kwankwance! kafin mu afka inda suke da yak'i."*

Suka hada baki gurin fadin."Yanda kayi shine daidai maigida muna goyon bayanka ako wane
yanayi."

****
Tun bayan tafiyar Nuhu! babu wani abu daya gilma, hakan besa sun saki jikinsu a gurin ba, sai
da duhun dare ya shiga sannan suka fara neman abinda za su ci.

Ita dai 'ya'yan itacuwa kad'ai ta iyaci, tana zaune tana kallonsu sun tada wuta sai
gashe-gashe sukeyi da kallon ikon Allah! da kudirarsa, ace wai mutum ya gasa majici gafiya
da sauran dabbobi marasa kyau yana ci a cikinsa.

K'auri da karni! duk ya cika gurin! dole ta tashi domin sauya gurin zama, domin mutukar tana
shak'ar hayaki da kaurin dake tashi agurin zata iya amayar da abinda taci.

Ido ya bita dashi! be dauke ba har sai da ta samu guri ta zauna can nesa dasu, inda Allah ya
takaita akwai hasken farin wata a gurin.

Ta jima a zaune a gurin tana sakawa da kwancewa! sai yanzu ta san ya rayuwa take, ta taso
cikin kulawa da gata da komai na jin dadin rayuwa, tunda take bata ta'ba tsammanin cewa
akwai ranar da za tayi rayuwa mai muni irin wannan ba! babban tashin hankalinta rayuwa da
d'an ta'addah! irin wannan, duk abinda yake a kanta bai janyo masa 'kima da mutunci ba,
domin kuwa shine mutum na farko wanda yayi sanadiyar tagayyara rayuwarta, hakika ta
tsorota da rayuwa da duniyar ma gabad'aya, A yanzu babban burinta ta samu ku'bta daga
cikin wannan dajin, sannan tayi wa kanta al'kawarin ganin ta jefa rayuwarsa cikin kunci da
tashin hankali kwantankwacin yanda yayi mata.


Saukar wani abu taji saman wuyanta, da sauri tasa hannu ta buge! ta mike tsaye! wata
lafceciyar tsutsa ce ta fado daga saman bishiya.

Rintse ido! tayi tana kiran sunan Allah! kafin taji zirrrrrr a kan kafarta, tayi tsalle ta matsa gefe

tana kallon gurin, ashe gabadaya gurin tsutsutsine suke yawo.

Jiki na wani irin rawa ta bar gurin, tana isa inda suke ta iske sunyi shimfida sun gatange gurin
da itacuwa tare da rufe gurin da Net!

Tsayawa tayi a gurin ta kasa shiga, domin gabad'ayansu mugun haushinsu takeji! daga nesa
ta hangoshi ya nufo gurin, d'auke kanta tayi tare da jan tsaki a cikin zuciyarta.


Koda ya iso gurin bece mata komai ba, ya kama hannunta! kallonshi tayi kamar za tayi magana
sai dai tayi shuru, jan hannunta yayi suka shiga gurin.

Guri guda ya zaunar da ita, muryar rarrashi da kwantar da hankali ya aro yace." Ki kwanta
anan gurin nayi miki alkawai cewa babu abinda zan bari ya sami rayuwarki."

A maimakon hakan ya faranta mata sai kawai taja masa tsaki! ta kawar da kanta tana zumbura
baki!

Hakan da tayi ya bata masa rai amma sai ya danne! be dauki mataki ba ya fara kokarin barin
gurin, ta bude baki da fadin." Mamugunci! insha Allah sai naga karshenka."

Maganar ta bashi mamaki mutuka! sai ya juyo da wani irin murmushi a fuskarsa ya nuna kirjinsa
da fadin." Me yasa kike so ki kaga bayana."?

Ta zabura! da fadin." Saboda kai din azzalimi ne macuci.!!

Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta" Saboda kai din azzalimi ne macuci."! to wai shin da
take kiransa da wannan sunayen wane irin zalinci yayi mata tun farkon had'uwarsu?

Still murmushin ya sake kafin ya furzar da iskar bakinshi, cikin gaggawa ya fita ya bata guri
domin yana ji idan ya kara second a gurun zai iya nakastata.

Ya jima yana fesar da hayaki kafin ya samu sassauci a zuciyarsa, zazzafar ajiyar zuciya ya
sauke! yana me sake jin sautin muryarta na amsa kuwwa! a kunnanta a cikin kunnuwansa,
tunda ya taso lokacin kuruciya da girma gwargwamaya yake da *Maza!* bai ta'ba sanya mata a
cikin al'amuranshi ba, saboda sanin hallayarsu! yana da tausayi mussaman akansu amma baya
yarda da raini daga garesu, mace daya ce yake jinta a cikin zuciyarsa, domin duk ta tara
abinda yake da bukata, hankali nutsuwa ilimi tarbiya da sauransu, ita kad'ai! yake ji a zuciyarsa
zai rayuwa mai tsayi da ita, ya kai ma'kura a gurin iskancin da yarinyar nan take masa, yana
tausaya mata amma ya lura ita bata gani ta daukeshi a matsayin macuci! to yana ganin zai fita
daga harkata domin ya samu zaman lafiya. tare da gudanar da aikin dake gabanshi.

*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da
wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin Mov ko airtal
a
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊ï¸í ½í³š_*
_____________________



*JAMILA MUHAMMAD-ALI*
_(( (MMN BOBO💞) )_
Ina gaisuwa gami da fatan alkairi, Nagode sosai da kulawa da shawarwari Allah ya raya zuria,
ya jikan MAMA yai mata rahamaí ½í¹í ¼í¿»


FREE PEGE
*27&28*
Ya jima kansa a 'kasa tun bayan 'kare maganar Asp din yake cikin nazari da tunani, kafin ya
d'ago kanshi ya fara magana kamar haka............Sunana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login