Showing 39001 words to 42000 words out of 47415 words
Chapter 14 - GOJE Book 1 Hausa Novels By Binta Umar Abbale.pdf
rigarshi, yace." Na dawo my dear nagaji ne shiyasa ban leka gurinku ba, ina so nayi wanka na
huta tukkuna."
Cike da kulawa tace." Sannu ya aikin? bari na had'a ma ruwan wanka ko."? yana kokarin cire
rigar daga jikinshi yace." Godiya nake Allah yayi miki albarka." Cike da jin dadi ta amsa, kafin
da sauri ta kama hanyar dakinsa, ido ya bita dashi har ta shiga dakin ya girgiza kai a fili yace."
Wannan itace matar aure mai cikakkiyar tarbiya nutsuwa sanin ya kamata yayi imani ko zuria
ya had'a da wannan yarinyar ba zaiyi kaico ba.
Ta fito falon ta sameshi daga shi sai vest wacce ta matse shi da gajeran wando domin ya cire
gabadaya kayan jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta kunyar had'a ido take dashi, ganin haka
yasa yayi murmushi ya tashi ya bar gurin, da sauri ta dauki inform din ta kai masa daki ta
rataye masa kafin ta bude wardrobe ta dauko masa 'kananun kayan shan iska, ta ajiye saman
gado da sauri ta fita daga dakin. tana jin wata annushuwa a cikin ranta, yau ta d'an fara ganin
alamun sonta acikin 'kwayar idanuwansa....
*Free pege zai 'kare a pege 40 ga masu bukatar wannan littafin suyi payment domin karanta
littafin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kada mugunta!/hassada!/ ganin k'yashi! ya hana ku
biya, ku jira na sata ku karanta, wallahi tallahi hakkin wani masifa ne! bala'i ne! muyi kokarin
nesanta kanmu da haram! duk kankantarta!*
*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp
da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number....
22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!!í ¼í¿¹*
í ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURNí ½í²«í ½í±‘)_
*BINTA UMAR ABBALEí ¼í½’*
*MANAZARTA WRITER'S*
*ASSOCIATIONí ½í³ší ½í¶Šï¸*
____________________
*37&38*
Da yake ta sheda fuskarsa suna shiga ta ganeshi, cike da farin ciki take masa barka da zuwa,
ta nuna masa gurin zama da fadin." Ashe tare kake da yaran naka sannu da zuwa ga guri zo
zauna." Asp ya zauna kusa da ita yana amsawa ya dora da fadin." Tare muke tafe dasu ai
nace su zo su gaisheki sannan kuma ita ZINATU tayi miki bankwana domin gobe idan Allah ya
nufa zamuje mu kaita gida da yardar Allah."
Tace."Eh ta sheda min hakan har na bada sakon gaisuwata ga manyan nata, ina fatan Allah ya
kai ku lafiya ya kuma dawo daku lafiya."
Gabad'aya suka amsa da ameeen ya Allah.
Falon yayi shuru na minti biyu kafin tace."Duk ya iyalin naka ina fatan kowa lafiya." ?
Yace."Kowa lafiya lou insha Allah gabadaya zasu zo su gaisheki." Cike da jin dadi tace."To
shikkenan ina nan jina jiran zuwansu."
Tun shigowarsu shida Asp din yake a tsaye a gefen kujerar da take zaune, be kalleta ba
ballantana ya fahimci yanayin da take ciki wanda tsayuwarsa a kanta ya janyo mata, k'amshin
turaran jikinsa ne yake fizgarta take jin wani irin azababben feelings! ta rasa wace irin masifa ce
wannan duk sanda zai kusanceta hankalinta ya kan tashi, gabadaya jikinta ya mutu ta dinga
matse 'kafafunta wani irin sanyi ta keji a cikin jikinta, cikin zuciyarta take wasu irin
tunane-tunane marasa kan gado............Gyaran murya yayi gabadaya suka kalleshi amma
banda ita, Ya dubi Uwale da fadin.'' Ina Hamra'u ne."? Tace."Yanzu-yanzu ta shiga daki
watakila ko tana wani uzuri ne."
Ya kalli Asp da d'an murmushi a fuskarsa yace." Yana da kyau kafin ka wuce ku gaisa da
matata da yardar Allah."
Jin abinda yace yasa Asp din yin 'yar dariya ya bashi hannu suka tafa da fadin'' Gaskiya ne
abokina hakan yayi ya kamata ta fito mu gaisa." Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba
ya nufi dakin nata.
Cikin tsantsar fad'uwar gabada gami da jin wani abu mai bala'in d'aci a wuya ta bishi da kallo a
lokacin da yake kokarin bude dakin, ba ta janye idonta daga kansa ba har sai daya shiga dakin,
sannan ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya wacce ta janyo hankalinsu kanta, sunkuyar da
kanta tayi 'kasa tana 'kokarin saisaita yanayin da take ciki, halin da ta shiga a lokacin da yake
maganar ta kasa fassara shi shin wai me hakan yake nufi?
Cikin yanayi na damuwa ya sameta, ya kira sunanta ta dago kai tana kallonsa , nan ya hango
b'acin rai cikin 'kwayar idonta, cike da kulawa yace."Menene yake damunki."? da yake a kusa
take kuma kishi yana cin zuciyarta, sai kawai ta fashe da kuka harda shashsheka!
Hankalinsa ya tashi ya zauna kusa da ita yana rarrashinta, da kyar tayi shuru sai ajiyar zuciya
take saukewa, ya rike hannunta da fadin." Waye ya ta'ba min ke."? shuru tayi ba tace komai ba,
yace." Ba zaki fad'a min ba ko baki da lafiya."?
Kai ta girgiza alamun a'a. Yace."Babu daya daga ciki amma kike kuka gaskiya ban yarda ba
kada ki boye min abinda ke damunki kinji my dear."
Zuciyarta ta sake karyewa kawai sai ta tsinci kanta da fadin." Yanana don Allah Menene
tsakaninka da ita."?
Yayi jim yana kallonta kafin yace." Wa kenan."?
Ta kalleshi hawaye na karakaina a saman fuskarta, hannu yasa yana goge mata tare da girgiza
kai alamun ta daina.
Cikin shashshekar kuka tace." Kada ka gujeni na riga na makance akan sonka ba zan iya
rayuwa da kowa ba idan ba kai ba, zuciyata tana wasiwahsi cewa zaka maye gurbina da wacce
'yar sarkin daka taimaka wannan shine dalilin daya sani zubar da hawaye."
Da murmushi a fuskarsa yake girgiza kansa har yanzu hannunta na cikin nasa yace." Babu
wata alaka da take tsakanina da ita, ki cire faruwar hakan a cikin ranki, bani da matar aure sai
ke, domin duk kin tara abunda nake da bukata, insha Allahu kece uwar 'ya'yana."
Wani sanyi ya ratsa zuciyarta, cikin tsantsar farin ciki ta kalleshi da fadin." Nagode masoyina
ina fatan Allah ya tabbatar da alkairin da yake tsakaninmu." Ya amsa da "ameen ya Allah."
A 'kalla ya kai minti ashirin da shiga dakin shiru bai fito ba, shi kansa Asp din ya 'kosa
ballanatana ita da take jin kamar taje ta sha'ko wuyansa ko uwar me yake a dakin oho!
A cunkushe! ta kalli Asp din da fadin " Ranka ya dade ya kamata mu tashi mu tafi wannan
mutumin ya mayar damu shashashai! ya shige daki ya bar mu a zaune zaman jiransa."
Ya kalli agogon dake daure a hannunsa da fadin." Hakane nima nayi mamakin jimawarsa amma
bari na kira wayarsa naji."
Uwale kuwa gyangyadi take bata ma san ma abunda ke faruwa ba.
Yana kokarin kiran wayar tasa, suka fito a tare hannunta na cikin nasa.
Har suka zauna bata kallesu ba, cika kawai take tana batsewa! wani mugun abu mai nauyi ya
tsaya mata a wuya.
Gwiwa a kasa Hamra'u ta gaishe da Asp, ya amsa da fuska a sake yana janta da wasa,
murmushi kawai take ta kasa hada ido dashi, gabadaya farin ciki ya mamaye zuciyarta, tayi
mamakin yanda akayi ya santa har yake kiranta da amarya hakan ya sanya ta sake gazgata
maganarsa.
Tashi tayi kawai ta kama hanyar fita ba tare da ta tankawa kowa ba, Nabilan ta kalli
mahaifinta nata da fadin." Daddy bari muje kawai sai ka shigo." Ya mike da fadin.'' Aa ku jira ni
mana saurin me kuke." duk da taji abunda yace hakan besa ta tsaya ba, ta bude kofa ta fita,
ita Nabilan ita ta jira mahaifin nata har sukayi sallama cikin girma da mutunta juna.
*****
Washe gari da wuri suka shirya tafiyar, bahaushe yace sabo turken wawa, 'yan kwanakin da tayi
a tare dasu ya sanya duk jikinsu yayi sanyi har dashi Asp din kawai ya daure ne domin ya san
dole watarana yarinyar zata bar hannunsa, Madam dai kasa hakuri tayi sai share hawaye take a
fakaice.
Al'amarin ya bata mamaki mutuka! ta rasa wane irin so matar take mata, gabadaya sai jikinta
ya mutu ta rungumeta da fadin." Mommy kiyi hakuri ba mu rabu da juna ba insha Allah zan
dinga ziyartar ki, bayan haka kuma zamu dinga gaisawa ta waya ki daina kuka." tana maganar
tana share mata hawaye.
Hannunta ta rike da fadin" Idan kin isa gida lafiya kice ina gaishe da mamanki kuma insha Allah
idan an kwana biyu zamu kawo muku ziyara dani da Nabila."
A sanyaye tace."To shikkenan in Allah ya yarda zan sheda mata sa'kon ki daga zarar na isa ."
Nabila ta fito daga daki ta same su cikin damuwa, a sanyaye ta zauna kan kujera tana kokarin
magana ya k'araso gurin yana duba agogon dake hannunsa, ya kalleta da fadin." Tashi muje
ko." Ta mike tana gyara mayafin jikinta, Nabila ta kalleshi da fadin." Dady zan je nima." kai ya
girgiza da fadin." Ki bari idan an kwana biyu zaku shirya zuwa keda Madam." Kamar za tayi
kuka tace." Dady ni nafi so naje yau." be saurareta ba ya kama hanyar fita, itama da sauri tabi
bayansa domin bata so ta tsaya dogowar magana zuciyarta ta karye, gabadaya suka bita da
kallo cike da alhinin rabuwa da ita.
Wayarsa ya kira ya sheda masa cewa sun fito suna jiransa.
Da yake tuntuni ya shirya tafiya sai kawai ya fito daga gurinsa kai tsaye bangaran su Uwale
ya nufa domin yi musu sallama.
Fitowarsa ta dauki hankalinsu daga ita har Asp din......Yana sanye da kayan mu na hausawa
shadda milk colour dinkin tazarce har kasa, sai yayi amfani da hula zannar bukar mai duhun
zare, kafafunsa sanye da bakin takalimi mai gidan yatsa, agogon dake d'aure a hannunsa ma
baki ne, yayi kyau sosai fuskarsa tayi kar! sai fitar da annuri take.
Kasa janye idonta tayi daga kansa suna magana da Asp yana tsokanarsa cewa yayi kyau a
cikin dogwayen kaya, murmushi kawai yayi kafin ya fara duba cikin motar, sai suka had'a ido
da sauri ya janye nasa yana gyara yanayin fuskarsa, babu fara'a a fuskarsa ya kalleshi da
fadin." Ya za'ayi tafiyar ne."?
Asp din na 'ko'karin magana direban da zai jasu ya iso gurin, gaisuwa ya mi'ka kafin ya bude
motar ya shiga Asp din yayi saurin zama a kusa dashi, ya kalleshi cike da mamakin abinda
yayi wato yana nufin shine zai zauna kusa da yarinyar.
Ba tare daya shiga motar ba ya kalleshi da fadin.'' Ni yafi kamata na zauna anan gurin." Ya
kalleshi da murmushi a fuskarsa yace."Akwai dalilin da yasa nayi hakan kai dai kawai shiga
mota mu, tafi."
Ya jima yana kallonsa gami da hasaso dalilin da yasa zai ce dole ya kusanci yarinyar, ajiyar
zuciya ya sauke bada son rai ba ya bud'e motar ya shiga da bisimillah a bakinsa.
Duk maganganun da suke tana jinsu, itama taji haushin abinda Asp d'in yayi kome yake nufi
oho! dalilin da yasa kenan yana shiga motar ta kawar da kanta tana ya mutse fuskarta.
Shima bai ce mata komai ba ya mayar da hankalinshi gurin tasbihin da yake ja da carbin dake
yatsan shi a ma'kale.
Jefi-jefi suke hira a tsakaninsu kafin Asp din ya juyo ya kalleta da fadin." ZINATU yau sai
kwanan gida ko."?
Baki ta ta'be kafin tayi masa wani irin kallo mai kama da harara! kamar wanda yayi mata laifi, ta
d'auke kanta uffan ba tace ba.
A maimakon hakan da tayi masa ya 'bata masa rai sai kawai ya fashe da dariya yana kallonta
da fadin." Ke kam kin zama hukuma! sai rarrashi abu kad'an ke tunzura zuciyarki kamar ba
d'azu ki ka gama kuka ba okey mu yanzu dai ba za kiyi kukan rabuwa damu ba kenan."
Ta kalleshi still dai bakin ta tabe kafin tace." Ranka ya dade meye had'a ni daku da zan zauna
ina kukan rabuwa daku ni burina ma nayi nesa daku."
Ya dinga girgiza kanshi yana mamakin furuncinta, yace." Ni dai na san a'iya zaman da mukayi
dake banyi miki wani abu ba ballanatana ki k'ullaceni, meye duniyar ma da kuke gaba da
junanku dalilin da yasa na shirya zamanku a kujera daya domin ku gaisa da junanku duka ku
yafi junanku, duk da ba wani laifi kukayi wa junanku ba amma duk kun tsangwami kanku da
kanku, ke ZINATU kece 'karama ya kama kiyi wa abokin zamanki sallama ki gashe shi sannan
kiyi godiya akan alkairin da yayi miki wannan shine zaman duniya."
Ta dinga kallon Asp din tana jin takaicin maganarsa, a maimakon tayi abinda ya umarceta kawai
sai ta juya tana galla masa harara! wacce ta sanya shi juyowa yana kallonta ido suka hada
hakan besa ta daina hararsa ba...........Yanayin fuskarsa kawai ya gyara ba tare da yace mata
komai ba ya janye idonsa.
Hakan da yayi ya 'bata mata rai sosai! wato ya ma mayar da ita mahaukaciya, tsaki taja mai
tsayi ta kawar da fuskarta.
Beyi niyyar kula taba amma tsakin da tayi masa yasa ya kalleta cikin shan mur! yace." Wa
kikewa tsaki."?
Kallon gefen ido tayi masa ta sake jan wani tsakin! ba zato! ya matseta jikin motar! lebunan ya
kama ya shiga ligwigiwitasu! hawayen azaba! suka fara sauka saman fuskarta, Asp ya kalleshi
da fadin." Ka kyaleta haka mana."
Be kalleta shi ba ballanatana yaji maganarsa ya cigaba da ligwigwita leban! hannunta tasa kan
nasa tana kokarin cirewa ya rike sosai! yace." Yau zanga karshen rashin kunyarki."
Asp yace." Ka janye haka tayi kuskure tana neman afuwa."
Yace."Da bakinta nakeso ta nemi afuwar idan ba hakaba to zamuje a haka ban damu ba."
Asp din ya kalleta tayi wujiga-wujiga! ta shiga hannun maza! hawaye harda majina!! dariya ta
kusa kubce masa ya danne ya kalleta da fadin ." Ni zan zama sheda idan zaki bada hakuri."
Kanta ta d'aga alamun ta yarda. Ya kalleshi da fadin." Ta yarda zata bada hakurin ka saketa."
Ba lokaci guda ya saketa ba sai da ya niyya tukkuna sannan ya saketa! kawai sai ta kifa kanta
jikin motar tana wani irin kuka na tsantsar takaici da bakin ciki.
Asp ya kalleshi da fadin." Baka kyauta ba, nida na had'a ku zama guri daya nayi hakan ne da
kyakykyawar munufa dana san abunda za kayi kenan da ban zaunar da kai a kusa da ita ba.
Ta'be baki yayi bece komai ba ya cigaba da jan carbin dake hannunsa.
Motar tayi shuru na 'yan mintina 'kasa-'kasa sautin kukanta yake tashi tare da ajiyar zuciya.
Asp yace." Kiyi hakuri kinji ki bar kukan kada mu sauka a haka wasu su dauka wani abu ne.
Hannu ta dora saman lebanta da yayi tudu ya kumbura saboda ligwigiwatar daya sha ta
kalleshi da fadin." Asp ni zaku yiwa haka ko? shikkenan yau zaku ga gatana."
Asp yace."Aa ni meye laifi na babu ruwana wanda yayi laifi ai ya san kansa duk hukuncin da ya
kamata kiyi masa daidai ne amma kema ki kiyaye ki dinga girmama na gaba dake."
Bata iya ce masa komai ba taja mayafin jikinta ta rufe fuskarta dashi, gabad'aya jikinta laushi
bakinta sai zafi yake, bata tsammanci rashin imaninsa ya kai hakaba ya ligwigwice mata le'be
saboda tsabar mugunta har sai dai ya kumbura! wallahi ko za'a mutu ba zata bashi hakuri ba.
Shima ganin yanda ta galabaita yasa beyi wata magana ba, yana dai jin yanda take sauke
ajiyar zuciya dalilin kukan da taci, har suka isa masarautar bata sake magana ba, a maimakon
tayi farin cikin dawowarta mahaifarta, kawai sai ta shiga kumbure-kumburen kiris take jira ta
fashe da kuka.
Maimartaba da kanshi ya fito domin yi musu barka da zuwa, direba yana parking ta bude motar
ta fito, ba tabi ta kan kowa ba ta wani fashe da da kuka kamar wata kan'kanuwar yarinya taje
ta rungumeshi tana shashshaka! shi kam fuskarta ya dago yana goge mata hawaye tare da
rarrashinta, Aunty Maijidda ce ta jan hannunta suka nufi sashenta tare, hakan beyi wa Safah
d'adi ba, ganin yanda yarinyar tayi kamar bata gansu a gurin ba, koda yake daman dole hakan
ya faru tunda ita din ta kasance mai yi mata fada gami da nuna mata kuskuranta.
Bata iya barin gurin ba sai da ta tabbatar da cewa an sauki bakin a guri mai kyau da kuma
dukkan abun bukata.
Gimbiya Aysha kuwa kunya da kawaici ya hana ta fitowa tarar su, amma tana zaune labarin
abinda yarinyar tayi ya isa kunanta daga bakin 'yan uwanta Hassana da Husaina wanda su d'in
ma ta nuna tamkar ba jininta koda yake inda sabo sun saba da halinta amma dai abunda tayi
musu a yanzu ya 'bata musu rai mutu'ka!
Sosai suka samu kulawa mai kyau kafin maimartaba ya bukaci zama dasu sai da sukaci abinci
suka gabatar da sallar la'asar tukkuna sannan suka sameshi a fada shi kad'ai domin akwai
maganar da yake so suyi a tsakaninsu.
Gaisuwa suka sake mikawa a gareshi kafin shi da kansa ya mika godiya a garesu akan alkairin
da sukayi masa.
Asp yace."Ranka ya dade ai babu godiya a tsakaninmu da kai, domin kai uba ne a gurin mu, ka
cancanta da abunda yafi haka, bayan