Showing 42001 words to 45000 words out of 47415 words

Chapter 15 - GOJE Book 1 Hausa Novels By Binta Umar Abbale.pdf

09 Jun 2025

1724

hakan kuma kulawar da mukayi akan yarinyar nan
hakkinmu ne tunda aikin mu ne kare rayukan al'umma."

Ya girgiza kanshi da fadin." Tabbas maganarka haka take Asp amma dole nayi godiya domin
samun irinku masu tsoron Allah da kishin 'kasa zaiyi mutukar wahala wannan dalilin yasa na
jima ina nazari da tunanin irin alkairin da zanyi muku."

Kafin Asp din yayi magana ya riga shi da fadin." Ranka ya dade kada ka damu kanka akan
wannan al'amari wallahi ni abunda nayi akan yarinyar nan don Allah nayi bana bukatar komai a
gurinka face addua."

Murmushi yayi yana sake jin kaunar yaron a cikin zuciyarsa, yace." UMARU kenan addua kam
zan cigaba dayi muku har karshen numfashina amma ba kaji bahaushe yana cewa (yaba
kyauta tukwici ba) ba don kada nace na baka auran yarinyar nan ka dawo min da kyautata ba

to dana baka ita sakamakon alkairin da kayi min."

Fadar tayi shuru sakamakon maganar.

Kasa d'ago kansa yayi ballanatana ya nuna rashin amincewarsa da kyautar da akayi
masa..............Jin beyi magana ba yasa yace." UMARU kodai baka kar'bi wannan kyautar tawa
bane."? Asp da sauri yace." Aa haba dai! ranka ya dad'e wane mutum! kyautar mutum ba
karamin al'amari bane sosai ni naji dadin wannan al'amari kuma kayi kyautar akan ga'ba domin
dama bashi da aure a halin yanzu mungode sosai da wannan karamcin."

Fuskarsa cike da annuri yace." Asp ka ari bakinsa kaci masa albasa amma yanayinsa ya nuna
kamar beyi na'am da wannan kyautatar tawa ba."

Yayi namijin 'ko'karin kawar da damuwarsa kansa ya dago tare da kokarin aro walwala da farin
ciki yace." Ranka ya dade farin ciki ne ya hana ni iya magana, tabbas abunda abokina ya fada
hakane kayi min kyauta akan ga'ba kuma na kar'ba hannu biyu nagode kwarai da wannan
karamcin."
Ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Alhamdullihi Allah abin godiya, lallai babu shakka ZINATU
tayi dace da miji irin wanda yake da wahalar samu ina rokon Allah ya tabbatar da alkairin dake
cikin wannan al'amarin." Gabad'aya suka amsa da "ameen ya Allah."



*Free pege zai 'kare a pege 40 masu payment kawai nake da bukata idan kin san na siyan
littafin nan za kiyi ba kada kiyi min maganaí ½í¹í ¼í¿»*




*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number....
22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!!🏹*
🐕â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITER'S*
*ASSOCIATION📚🖊ï¸*
____________________

*1-NANA KHADIJA*
*2-YARO DA KUDI*
*3-GIMBIYA BALARABA*
*4-BABBAN YARO*
*5- MASHAHURI*
*6- LADIDI KWADAGA*
*7-TSANTSAR BUTULCI*
*8-SADAUKI OMAR*
*9-NIDA YAYA SADAM*
*10- 'YAR BANGAR SIYASA*
*11-DA WATA A KASA*
*12- MADADI*
*13-KWARA TABI KWARYA*
*14-GA RINTA NAN*
*15- MATSALARMU A YAU!*
*16-RUWAN DARE*
*17-GOJE!!*

_Littatafai na kenan ga duk mai bukatar karanta daya daga ciki zai samu damar karantawa cikin
saukin farashi, wanda zai iya siya nake da bukata, don Allah idan ba siya za kiyi ba kada ki
dauki number ta kiyi min magana NAGODE sosai masoyaí ½í²ží ½í¹í ¼í¿»_



*SHAFIN NA YAU NAKU NE 'YA'YAN ALBARKA.*

_DAUGHTER💞_
*ZEEY KUMURYA*
_MARUBUCIYAR_
*(NEHAL)*💫
*DA*
_MAMAN TEDDY💞_
*MARUBUCITAR*
_LITTAFIN_
*WALI-JAM🐄* *BAFULATAN RUGA*
_DA SAURANSU_

Allah ya kara muku basira da haza'ka, NAGODE 'kwarai! Allah yayi muku albarka.í ½í¹í ¼í¿»
________

LAST FREE PEGE
*39&40*
A takaice dai basu bar masarautar ba sai da duk suka gaisa da duk wanda ya kamata, sun tafi
da mamakin mutumci da dattakon mutanan, hakika kaf famliy din yarinyar nagartattun mutane
ne masu hankali da sanin ya kamata, ita kadai ce ta fita zakka a cikinsu, koda yake dama haka
Allah yake ikonsa, amma duk da hakan itama ba za'a rasa wani abu mai kyau daga cikin
dabi'unta ba.

Maimartaba ya basu kyautar dawakai lafiyyayu gami da kayan sarauta kwatankwacin irin
wanda yake amfani dasu, mussaman yasa aka kawo masa kayan farauta daban-daban domin
ya gwangwajeshi, aikuwa duk cikin kyautukan da yayi musu yafi farin ciki da kayan farautar
domin dama yana da bukatarsu, a ganinsa koda zai cika d'aki guda da irinsu ba matsala bace a
gurinsa.

Wannan karon gabad'aya a kujerar baya suka zauna, sai da sukayi nisa da tafiya sannan Asp
ya fara maganar da tuntuni take cin zuciyarsa.

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi da fadin." Asp kwata-kwata fa ni wannan al'amari be kwanta
min a rai ba, kawai dai na amsa masa ne amma bana jin zan kar'bi auran yarinyar nan."

Asp ya 'bata fuska da fadin." Kada ka zama k'aramin mutum mana, ko dai har ka manta da
wanda kayi magana, ba fa gurin wasan yara mukeje ba, ya za'ayi ka amsa masa cewa ka kar'bi
kyautarsa daga baya kuma ka shigo da wata magana''

Kallonsa yayi babu farin ciki a fuskarsa yace." Kunyarsa ce ta sanya na amince na kar'bi
kyautarsa amma kai kanka kasan tafiyarmu ba zata zo d'aya da yarinyar nan ba, naji takaici a
lokaci da yayi maganar har kake cewa dashi bani da aure alhalin jiyan nan, na nuna maka
yarinyar da zan aura a lokacin daka shigo gidana, tabbas ka shigo masa da maganarta ina
ganin ba zai k'arfafa maganarsa ba."

Yace."UMARU mace hudu Allah ya halasta maka mutu'kar za kayi adalci a tsakaninsu, wannan
dalilin yasa lokacin daya fadi maganar na k'arfafa masa gwiwa, haba mutumina ai da kunya a
gabansa ka nuna k'yamarka akan jininsa, kayi hakuri da katsalandan din da nayi maka domin
ni kaina nasan da cewa yarinyar akwai matsala a tattare da ita, bata da tarbiya ko kadan, to
amma hakan ba zai hana a aureta ba tunda wannan matsalar kawai gareta ina ganin idan ta
hadu da jajurtacce namiji kamarka to cikin sauki rayuwarta zata sauya.

Ya jima yana nazarin maganganun Asp din kafin yace." Kasan Allah a tsarina bani da ra'ayi tara
mata amma ina ganin hakan ba zai samu ba, Asp ina jin tsoron auran yarinyar nan ta hana ni
kwanciyar hankali, wannan dalilin yasa gabadaya al'amarin be kwanta min a raina ba.

Ya dan doki kafadarsa da fadin." Haba mutumina kai da saba gwagwarmaya da maza mai zai
sanya lamarin mata ya dinga baka tsoro! wallahi babu wani abun fargaba da tsoro a cikin
al'amarinsu daga zarar ka gane hallayarsu shikkenan zaka zauna dasu lafiya saboda ka cire
shakku akan hakan mutumina ba tun yau ba nasha fada maka cewa mace hud'u ce ta dace da
kai haba *jan wuya* kada ka bani kunya mana."

Dariya ya d'anyi ya bashi hannu suka tafa kafin ya girgiza kanshi da fadin." Asp ba zaka gane
ba ne amma shikkenan kawai mu bar maganar Allah ya tabbatar da alkairi."

Yace." Yauwa abunda nakeso naji kace kenan abokina insha Allahu za kayi fari ciki da wannan
al'amari.


To har bayan magariba ZINATU na tare da aunty Maijidda komai anan ta gabatar wanka cin
abinci da sauransu, hankalinta da tunaninta gabadaya baya kan uwar da ta haifeta ba
ballantana kuma wani, hakan yayiwa ita Maijiddan dadi dama babban burinta ta cusa bakin ciki
a zuciyar Safah domin itace abokiyar gabarta tun sanda ta fahimci cewa gimbiya Ayshan tayi
mata nisa, sai ta mayar bakin kishinta kan Safara'u wacce ita kuma ta mayar da ita shashasha
domin duk abunda take na rashin hankali bata biye mata su taru su lalace gabadaya.

Ta dinga bugar cikinta tana bata labarin abubuwan da suka faru, da rayuwar ta a dajin gami da
irin wahalhalun da tasha, da labarin zamanta a gidan Asp babu abunda ta rage, sai dai koda
wasa bata fada mata irin namijin kokari da kulawar da yayi akanta ba, duk abinda zata a fad'a a
kansa sharri ne, har da k'azafin fyad'e kamar yanda tayi masa a gurin Asp, gabad'aya suka
had'u suna zaginsa, Aunty Maijiddan ita ke fadin." Zata shedawa maimartaba komai domin abi
mata hakkinta, hakan yayi mata dadi a ranta domin ta san mahaifin nata yana saurarar
maganar auntyn nata.

B'angaran Gimbiya Aysha kuwa ganin har bayan isha'i yarinyar bata shigo ba, sai ta kalli
sauran yaran nata dake zaune a gabanta tace." Wannan zaman da kuke bashi da amfani domin
dai kune kuka damu da yarinyar nan amma ita bata damu daku ba, da ta damu daku to da
yanzu ta nemi inda kuke saboda haka ku tashi ku tafi gidajenku hakan shi yafi ku rabu da ita da
mugun halinta, sannan kada wacce tayi yunkurin kiran wayarta ku 'kyaleta taje tayi rayuwa da
wacce ta za'ba a madadi na da kuma ku."
Cikin rashin jin dadin abinda 'yar uwar tasu tayi kowacce ta tafi gidanta da bacin ran abun a
cikin ranta.

Da yake aunty Maijiddan ce da girki a daran ta zauna tana shirya masa k'arya da gaskiya har da
cewa ya dauki mataki mai tsauri a kan yaron domin yarinyar ta sheda mata cewa a yayin
zamansu a dajin ya keta mata haddi."

Duk cikin maganganunta wannan ce kadai ta dauki hankalinsa, hankalinsa ya tashi da jin
maganar saboda ya san hakan na iya faruwa idan shad'en ya ratsa, to amma wannan maganar

ba zata sanya ya janye manufarsa ta alkairi ba, kamar hakan ma shine rufin asirinsu, duk da
hakan zai tuntubi yaran domin tabbatar da gaskiyar magana.


Washe gari da safe kafin ya zauna a fada ya nufi b'angaran matayen nasa domin dubasu,
gabadaya ya samesu ba yanda ya saba ganinsu ba, Safah dai tayi kokarin kawar da
damuwarta har ya dan zauna sukayi hira, bangaran Gimbiya Aysha kam rigima suka tafka irin
wacce sukayi shekara da shekaru ba suyi irinta ba.
Cikin tsananin 'bacin rai yace."Aysha yau ni kike nunawa da yatsa akan wani dalili naki na
banza da wofi shin wai me Maijidda tayi miki kika dauki karan tsana kika dora mata, baki da
kawaici akan 'ya'ya Aysha baki tausaya mata cewa ita bata dashi meye laifinta anan don ta
nuna kauna akan zuriarki."
Ido jawur! tace." Bana bukatar ta a cikin al'amarina kuma ba tun yau ba na tabbatar da cewa
kaine kake daure mata gindi take mana duk abunda takeso, shin itace ta haifar min 'yar da zata
nuna min iko a kanta! na haifi 'yata ta lalata min ita duk hakan be isheta ba sai da ta san yanda
tayi ta shiga tsakanina da ita da 'yan uwanta! bayan dawowarta har yanzu bata tako kafarta nan
ba ballanatana taje gurin 'yar uwata, haka nan jiya 'yan uwanta suka gaji suka tafi gidan
auransu bata shigo ba, shin kai a ganinka hakan shine dai-dai? duk abunda yarinyar nan take
aikatawa da sanya hannun Matarka a ciki amma kullum sai ka dinga nuna cewa baka gane ba,
to ni gaskiya na gaji da wannan al'amari zan kuma dauki mataki."!

Ganin yanda take numfarfashi! ya sanya shi sauke nasa fushin, hannunta ya rike ya jata suka
zauna gefen gado a tare.

Cikin sigar rarrashi yace."Yi hakuri ki samu nutsuwa muyi magana da fahimta.'' ta kalleshi da
fadin." Wane irin nutsuwa zan samu a cikin irin wannan yanayin."? hannun ya sake rikewa da
fadin." Na yarda da gaskiyarki, Aysha amma kada b'acin rai ya sanya k'ima da mutuncinki ya
zube kada fa ki manta kece babba a gidanan kowa yana ganin darajarki kada kuma kiyi wani
abun da zai sanya mutuncin ki ya zube a idanun jama'ar dake cikin gidan nan, kibi komai a
sannu a hankali."

A raunane tace." To wai yanzu ya kake so nayi? kana so na bari Matarka ta samu nasara a
kaina kenan."

Ya girgiza kansa da fadin." Maijidda baza ta samu nasara a kanki ba Aysha kin zama murucin
kan dutse a ko'ina kece a gaba."

Ta girgiza kai da fadin." Ban da gurinka domin yanzu Maijidda ce ke tsara maka komai kuma
idan ta fadi magana dai-dai ne a gurina."

Murmushi yayi yana kallonta, ya san kawai ta fadi wannan maganar ne saboda kishi amma shi

duk cikin matansa babu wacce ke tsara masa magana yayi amfani da ita gwanda ma ita takan
bashi shawarwari yayi amfani dasu, amma don ya kwantar mata da hankali sai yace." Na
amince da maganarki kuma zanyi wa tufkar hanci banji dad'in abunda suka aikata ba, kuma da
kaina zan samesu na nuna musu kuskuransu."
Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Shikkenan tunda kace haka amma dai duk da haka ina so kayi
min tsakani da matarka babu abunda ya shafeta dani da kuma zuria'ta."

Domin a zauna lafiya yace."Kada ki damu zanyi mata magana ta kiyaye shikkenan kowa ya
zauna a matsayinsa." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin.'' Hakan shine abinda ya dace.

To atakaice dai bai samu damar zaman fada ba sai da ya tabbatar da cewa ya kashe wutar da
take kokarin ruruwa, ya kuma yi namijin kokari gurin nunawa Maijidda kuskuranta duk irin
hujjojin data kawo masa be saurareta ba, yace."Idan ita ZINATU tayi aikin kuruciya ke ya
kamata ki nuna mata hanyar dai-dai, cewa taje gurin mahaifiyarta da 'yan uwanta da suka damu
da rashinta, amma kema sai ki ka aikata aiki irin na k'ananun yara abunda ki kayi sam be dace
ba."

Kuka ta shiga yi tana fadin." An nuna mata iyakarta akan abinda take ganin tana da iko dashi,
kuma ba tayi hakan da wata manufa ba amma tunda sun juya al'amarin da wata siga daban
shikkenan zata cire hannunta daga kan 'ya'yansu."

Maganganun da tayi besa yaji tausayinta ba domin idan da sabo ya riga ya saba da jin irinsu
kawai dai shi ya nuna mata kuskuranta ne.

Da kanshi kuma ya shiga dakin ZINAT din tana bacci ya tasheta sosai ya rufeta da fad'a irin
wannan be ta'ba yi mata irinsa ba, a take a lokacin ya bata umarnin kan cewa tayi maza taje ta
nemi afuwa a gurin mahaifiyarta.

Tana share hawaye ta shirya, ya sanya ta a gaba sai da ya tabbatar da cewa ta shiga sashen
sannan ya nufi fadarsa.


Da sallama a bakinta ta shiga, ta amsa tare da tsira mata ido har ta 'karaso inda take ta zube
k'asan kafet kawai sai ta rushe da kuka tana takure jikinta.

Zuba mata ido kawai tayi tana mugun takaicin sangartar da take sai kace yarinya k'ankanuwa!

Tsawa! ta buga mata da fadin." Za kiyi min shuru ko kuwa shashashar banza shashashar wofi."!

Kokarin hana kanta kukan take amma hakan ya gagara yi take ita kanta takasa tantance me
dalilin yin sa.

Tace." To tunda haka ki ka za'ba bani da magana dake ki tashi ki koma inda kika fito."?

Kasa tashi tayi sai dai tayi kokarin rage sautin kukan ya cigaba da fita kasa-kasa.


Taja tsaki da fadin." Kullum kina girma amma kina cin 'kasa! Zinatu ban san lokacin da za kiyi
hankali ba, ya kamata ace wannan abunda ya faru dake ya zama izina a gareki amma sai
gashi kamar kin 'karo wani iskancin a inda ki kaje, to don baki mutun tani ba sai me? Allah dai
yasa bake kad'ai na haifa ba ballanatana bakin cikinki ya kasheni! ina da wasu bayan ke kuma
zan iya yafewa Maijidda ke babu abunda ya dameni."

Cikin reshin kuka tace." Mammah don Allah kiyi hakuri wallahi duk abunda ya faru dani
tsautsayi ne, kuma ina jin tsoron zuwa a gurinki kiyi min fada shiyasa na zauna gurin aunty
Maijidda."

Tace."Don Ubanki tsautsayi ko son zuciya? na dauka ranar da al'amarin zai faru sai da kowa ya
hanaki fita amma ki ka fakaici idanuwanmu ki kama hanya ki ka fita ai naso wa'inda suka sace
ki sun kasheki kowa ya huta."

Ta dago kai tana kallon mahaifiyarta da mamakin jin furucinta.

Tace."Eh ki kalleni da kyau! ni nayi wannan furucin saboda duk wani wanda zai zama annoba a
cikin al'ummah to bashi da wani amfani a duniya rashinsa shi yafi alkairi."

Yanzu take kukan gaske hawaye masu tsananin zafi suka shiga sharara a saman fuskarta!
tunda take da mahaifiyarta bata ta'ba ganin bacin rainta ba irin na yau ba, har tana mummunan
fata a kanta da rayuwarta gabadaya duk sai jikinta yayi sanyi.

Numfashi ta sauke kafin ta cigaba da cewa." Shekarunki ashirin da hudu a duniya ya kyautu ace
yanzu kin nutsu kinyi hankali kin fuskanci abunda yake gabanki amma kullum ke kina daukar
kanki yarinya saboda mahaifinki yana sonki yana biye miki da dukkan abunda kike so, kin
zauna shirme da shashanci 'yan uwanki na dakin mazajensu har da zuriarsu, 'kawayenki wasu
daga ciki duk sunyi aure suna zaune lafiya da mazajensu, ke kuwa hakan baya burgeki kullum
burinki ki sanya suttura masu tsada kiyi ado da gwalagwala ki shiga motar da kike so ki zaga
duk inda kike so kina takamar cewa ke 'yar mulki ce duk mazan da suka zo da niyyar auranki ki
sai ki kore su to me zai sanya mutane ba zasu d'ora ayar tambaya a kanki ba."?

Shuru tayi tana auna maganar mahaifiyartata, tabbas duk abunda ta fada a kanta gaskiya ne
babu abunda tayi mata kazafi a ciki, manya mutune masu kudi da muk'amai daban-daban sun
zo da niyyar auranta amma duk ta koresu saboda ta ganin kamar auran zai tauye mata
rayuwarta, a yanzu kuma maganganun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login