Showing 12001 words to 15000 words out of 47415 words
Chapter 5 - GOJE Book 1 Hausa Novels By Binta Umar Abbale.pdf
idan an samu zaki jini."
Bayan fitar Rakiya daga gidan itama Uwale kayan dillancinta ta dauka ta fita, ya rage saura ita
kadai a gidan, ta jima tana sakawa da kwancewa kafin ta tashi cikin sanyi jiki ta gyara gidan tsaf
ta kulle da kwado, gidan Tasallah ta shiga ta bayar da mukkulin kafin ta kama hanyar gidansu,
salo-salo take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki........."Hamra'u." da sauri ta juya jin
muryar kawarta Zabbah, taja ta tsaya tana wasa da karan dake hannunta har ta karaso gurin da
faratin goro da lemon tsami a kanta.
Zabbah ta karaso inda take da fadin." Daga ina kike haka naga duk jikin a sanyaye."?
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Daga gidan yayar mahaifina nake kullum ina zuwa nayi mata
aiki kafin ta fita.
Zabbah ta fashe da dariya irin ta shakiyanci kafin tace."Hamrau kenan wai kenan kina kamun
kafa ko? wallahi kina wahalar da rayuwarki domin kaf cikar karkarar nan banga wata mace da
zata ja ra'ayin *GOJE! ba*
Tace." To ke Zabbah waye ya fada miki ina kamun kafa da Uwale a matsayin uwa take a
gurina laifi ne don naje gidanta."
Zabbah ta tabe baki da fadin." Hamra'u bari na fada miki abunda baki sani ba, kaf 'yan matan
garinan babu wacce bata san halin da kike ciki akan *GOJE!* ba kowa ya san kece kike sonsa
baya sonki kullum sai kinji kinyiwa kakarsa aikace-aikace sai kace baiwa bayan haka ance idan
yana gari kece kike masa wankin kayansa ki goge ki wanke masa takalma saboda rashin
hankali irin naki kin mayar da kanki yar aiki bayan baki da tabbacin zai aureki.
Tace."Zabbah! duk abinda kika fada hakane babu karya ina san UMARU kuma ina rokon Allah
yasa ya zama uban 'ya'ya na, bayan haka kuma duk wata bauta da nake masa ra'ayi na duk
surutun da jama'a za suyi akan hakan bai dameni ba."
Ta girgiza kai da fadin." Shikkenan ai tunda kinyi nisa duk abinda zan fada miki a yanzu ba zaki
fahimta ba, saboda haka muna zuba ido muga yanda za'ayi wannan auran.
Shuru kawai tayi bata sake magana ba, ita Zabbah ce keta surutu tana bata labarin saurayinta
wanda zata aura uffan bata ce ba har suka rabu da juna.
Cikin kunci da damuwa ta shiga gidansu, nan ma ta iske wani bacin ran don mahaifiyarta fada
ta rufeta dashi sosai tace."Ina ji ina gani kinfi karfina Hamra'u! saboda kulafucin namiji kullum da
gari ya waye hankalinki na wani guri kisa kafa ki fita ki barni da aikin gida, kina can kina bauta a
wani gurin, to wallahi nagaji ba zan hanaki ba tunda ke ki kasa kanki amma ba zaki kara fita ba
sai kin gama min aikin gida."
Daki kawai ta shige tana kokarin danne kukan dake kokarin kufce mata, wai shin da wane
bala'in za taji? ko'ina babu sassauci, bata samun nutsuwa da kwanciyar hankali sai a gurin
Uwale ita kadai ce ke kwantar mata da hankali, amma ita kanta wacce ta haifeta kullum habaici
take mata akan wanda ta kwallafawa rai! kowa yana ganin laifinta bayan itama ba ita tayi kanta
ba, Allah ne ya halliceta ya sanya mata soyayyar wanda bai san ta nayi ba, dole idan ya dawo
ta cire kunya ta sameshi da maganar ko ta san matsayinta..
*Don Allah idan ba sayan littafi zaki ba kada ki dauki number ta Nagodeí ½í¹í ¼í¿»*
*Ga mai bukatar Sadauki Omar 1k zai tura domin samun damar karanta littafi biyu Goje sadauki
Omar return*
*#500 via 0542382124......Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da
wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari Katin airtal ko Mov
Aa
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*í ¼í¿¹
í ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURNí ½í±‘í ½í²«_)
*BINTA UMAR ABBALEí ¼í½’*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONí ½í¶Šï¸í ½í³š_*
_____________________
_*INA MAFITA?*_
_*Matsalar dai guda daya ce data addabi tsakanin ma'aurata rashin hakuri da juna, wanda
shike haddasa fitintinu masu yawa, ma'aurata shifa aure gabad'ayansa ibadah ne, jin dadinsa
kadan ne, to mai yasa ba za'ayi hakuri da juna a mayar da hankali gurin ribatar ladan dake cikin
auran ba*_
*WA YAFI LAIFI*?
_*Shin wa yafi laifi a tsakanin ma'aurata biyu wato mace da namiji? ni dai ba zance ga wanda
yafi laifi a tsakanin ma'aurata ba, saboda i dan akayi duba na tsanaki za'a fahimci cewa
kowanne bangare da nasa laifin. a matsayina na mace bana goyon bayan 'yan uwana mata
akan matsalar data shafi zamantakewar aure wanda kullum ta Allah sai na samu sakon da ya
danganci wannan maganar da nake a yanzu, hankalina ya kan tashi idan naji yarinya karama
auran fari haihuwa daya biyu kai wata ma auran beyi shekara ba zata kira waya ko ta turo sako
tana kuka a taimaka mata da shawarwari yanda zata zauna lafiya a gidan auranta, haka zalika
daga b'angaran mazan ma ina samun irin wannan sakkonin cewa baiwar Allah matata tana
karanta littatafai na hausa amma bata daukar darasin komai karshe ma tarbiyar tace take
lalacewa sakamakon karance-karance littafan da kuke rubutawa. ire-iren wannan sakkonin ba
zasu lissafu ba, shin wai ta yaya marubuci zai lalata tarbiya? a ganina marubuci har in dai ya
san abinda yake bai cancanta da a kirashi da mai aikata 'barna ba."*_
FREE PEGE
*11&12*
Tun bayan tafiyarsa farauta, Uwale ta samu 'kafar yawo, wanda idan yana gari ko nan da can
baya bari taje a cewarsa ta tsufa abinda yafi cancanta a gareta ta zauna a gida ta huta, tunda
shi yana iyakacin bakin kokarinsa gurin daukar dawaniyarta da duk wani abu da take bukata
na yau da gobe.
Ita kuma a nata bangaran haushin abinda yake mata take, ta dingi mita da surutai tana fadin
ba zata zauna zuciyarta ta mutu ba sai ta fita ta nemi kudi kodan bada gudumawa idan sabga
dangi ta tashi,
Hakan ya sanyashi
yanke hukunci a duk sanda zai fita sai ya sakar mata kare a gidan ya rufe kofar daga waje
yayi tafiyarsa.
A ranar yini take d'aki bata fitowa saboda yanda Allah ya zuba mata tsoron kare a rayuwarta,
idan ya dawo gidan sai ta fashe da kuka tana fadin." *UMARU* saboda bani na haifeka shine
kake azabtar dani, ka san sarai bana san kare amma saboda mugunta zaka sa min kare
sannan ka rufe kofa ka tafi yawo to babu shakka wata rana zaka dawo ka samu gawata."
Sai yace."Uwale idan kina so mu shirya dake ki daina dillanci domin kuwa kina zubar min da
mutunci a gari, ni mutum ne mai zuciya da gudun magana bana son jama'a na ganin gazawata
a kanki."
*"UMARU* Ba zan daina dillaci ba saboda itace sana'ar data ci da kai ta shayar da kai har ka
kai munzali, sannan kuma kana maganar zagin jama'a kai yanzu *UMARU* wane irin zagi ne
jama'ar gari ba suyi maka irinshi ba, babu fa wanda yake maka kallon mutumin kwarai mai
daraja, kowa yana maka kallon banza tare da kiranka da sunaye masu muni! *B'arawo* *'Dan
ta'addah!* duk saboda wannan harkar daka jefa kanka a cikinta, Mahaifinka da bakin cikin
hakan ya mutu dalili irin zagi da habaice-habaicen da mutanan gari ke masa, bana rana dayan
biyu bakin cikinka ne ya kasheshi."
Duk sanda zata fad'i wannan maganar hankalinsa yana tashi mutu'ka, shi fa har yanzu bai ga
illar abinda yake aikatawa ba, na farko bai ta'ba tare wani a hanya ya k'waci abunsa ba, na biyu
tunda yake ba'a ta'ba kamashi ya haura wani gida yayi sata ba, na uku bai ta'ba yiwa yarinyar
wani fyade ba, abu na karshe shine baya muggan! shaye-shayen da zai janyo masa zubewar
kima da mutunci, abunda ya sani shine yana busa Sigari sa'i da lokaci sai shan Shisha da ya
zame masa masifa, wannan abu biyun sune abunda ya san yanayi bayan haka azimi sallah
akan lokaci basa wuceshi, a ganinsa zagin da jama'ar gari ke masa k'in gaskiya ne, babban
abin mamaki kuma duk sanda yayi nisan kiwo dashi da jama'arsa ma'ana suka fita farauta, to
duk sanda ya dawo gari da yawa masu zagin nasa sune suke zuwa su gurfana a gabansa
domin kar'bar maganin sanyin da yake guzurin zuwa dashi.
Ita kanta Uwalen matan da suke zuwa gurinta kar'bar magani suna da yawa, wani sa'in yana
kallo zata zabga kudi masu yawan gaske sai sun nemi alfarma a gurinsa sannan take sassauta
musu, amma shi anasa b'angaran 'karamar sadaka yake kar'ba wani sa'in ma kyauta yake
bayarwa yace sadaka ayi wa Annabi Salati dubu, Uwale tayi ta jin haushin hakan, idan ya fita
sai ta samu buhu mai zurfi ta shiga dakinsa ta kwashe rabin maganin ta boye a karkashin
gadonta, idan ta samu sarari ta fita cikin gari ta siyar akan kudi masu yawan gaske.
Wannan dabi'ar ta kakar tashi tana b'ata masa rai, mutuka idan yana so ya tsoratar da ita akan
ta daina abinda take sai yace." Uwale shifa aljani ba'a wasa dashi kuma wannan magungunan
da nake zuwa dasu ba a banza nake samu ba, musulman aljanu ne suka lamunce min da
hakan domin kin san kowane bawa da hanyar abincinsa to nima bani sukayi domin na taimaki
jama'a idan kika wuce gona da iri zan barki dasu."
Sai ta tsorata ta dinga rokansa kan cewa ya basu hakuri ta daina abinda take, yace shi babu
ruwansa taje ta nemi inda suke ta basu hakuri ba maganarsa bace, kuka irin na tsofaffi take
sawa ta rikeshi ta hanashi fita tace lallai sai ya basu hakuri sannan zai futa. sai ya fahimci tayi
laushi sannan sai yace tayi shuru ya basu hakuri sun hakura amma kada ta sake aikatawa,
Zata amsa da cewa ba zata sake ba, amma cikin ikon Allah idan aka kwana biyu zata manta ta
cigaba da sayar da magani da tsada tana boye kudin a cikin adaka a cewarta da kudin zata
hada masa lefen auransa.
***********
Kishingide suka sameshi a gurin hutawarsa, ya mike zaune tare dan gyara zama ido ya tsira
musu har suka samu guri suka zauna kafin su gaisheshi, ya amsa still idonshi na tsaye a kansu
mussaman mutuniyar tashi da yake hango rashin walwala a tare da ita, koda yake tunda
al'amarin ya faru gabadaya walwala da farin cikinsu ya gushe duk abinda suke karfin hali ne.
Gyaran murya yayi kafin yace." Idan kaga wata to za kaga zarah Aysha Safara'u wannan
tafiyar taku tana burgeni."
Babu wacce ta saki fuska a cikinsu, domin kuwa suna ciki dashi sakamakon hade kai da yayi da
matarsa suna daukarsu a matsayin marasa tawakkali.
D'aya daga cikin hadimanta ne yaje ya sheda mata cewa yanzu - yanzu ya gansu sun nufi gurin
hutawar Maimartaba
Da saurin gaske ta shiga daki ta shiryo ta fito kai tsaye can ta nufa, tana sauri taje ta riski
abinda ya kai su bayan itace da girki.
Tunda ta doshi gurin take hangoshi gabadaya hankalinsa yana kan wacce ta tsana a cikin
matan nasa fuskarsa akwai alamun sassauci da rarrashi, gabadaya ma kamar ita kadai ce a
gurin babu Safah.
Ta isa gurin da sallama wacce bata fito sosai ba.
Ya amsa yana kallonta kafin ya kallesu da fadin." Kuna ji 'yar uwarku na muku sallama kunyi
shuru."
Safah ta amsa a ciki Aysha kam ko kallonsa ba tayi ba ballanatana 'yar koran nasa.
Ta samu guri ta zauna tana ya mutse fuska da fadin." Ranka shi dade barka da dare."
Ya amsa "Barka dai Maijidda ya hidima." Ta amsa "Alhamdullhi."
Gurin yayi shuru na 'yan mintina kafin gimbiyar ta kalleshi babu fara'a tace."Ranka ya dade
wannan magana iyakacin nida kai da 'yar uwata muka tattauna bana son wani yaji abinda ya
shafeni da zuriata."
Ya 'bata rai da fadin." Aysha wannan wace irin magana ce? shin ita Maijiddan bare ce a
cikinmu."?
Ta d'aga masa hannu da fadin." Allah shi gafarta maka tunda na fara maganata kaji sunan
Maijidda a bakina."?
Ransa ya baci mutuka, yace." Ki sauke hannunki idan ba hakana ranki ya b'aci zaki nuna min
abinda zanyi ne? ko kuma zaki hanani iko da abinda na haifa? dake da ita Zinat din da ita Safa
da Maijiddan duk ikona ne to ke baki isa ki tsara min yanda zanyi ba."
Maijidda ta fashe da kuka da fadin." Ranka ya dade na rasa me yasa har yanzu matarka bata
kaunata, meye laifina ? me kuma nayi mata? haihuwa dai Allah ke bayarwa ba wani ba, nima
ban cire rai ba."
Tausayinta ya rufeshi, sassauta murya yayi yace." Maijidda kada ki sanya damuwa a ranki nida
na aureki nafi kowa sanin halinki babu wanda zai kawo min jita-jita a kanki na dauki maganarsa,
maganar haihuwa kuma kada ki cire tsammani, zaki haihuwa da izinin Allah, bayan haka kuma
baki da shamaki da zuriata zaki iya yanke hukunci akansu ba tare da na daga kai na kalleki ba."
Gabad'aya suka kalleshi a lokacin da yake wannan maganar, Aysha gaza hakuri tayi tace." Ba
zai yuwu ba ranka ya dade ana duba nagarta da cancanta kafin a yanke hukunci babu wani
d'a da zan haifa na amince ya dauki wannan matarka taka a matsayin me kaunarsa duk
mutumin da ya fito da kiyayyarsa a sarari a kanka be kamata kayi rayuwa dashi ba.
Gabadaya sai suka rasa inda maganarta ta dosa, ta mike tsaye tana gyara lifayar dake nade a
jikinta, sunkuyawa tayi da fadin." A tashi lafiya." Bakinsa ne ya mutu kawai ya bisu da kallo a
lokacin da suka kama hanyar fita, Ya girgiza kai yana jimanta al'amarin wato dai har yanzu Safa
taki zama cikkakiyar mai 'yanci a gidan auranta, tana biyewa Aysha suna zuwa har gabanshi
suna masa rashin kunya, to babu shakka zai sa kafar wando guda dasu.
***********
Washe garin ranar da ciwon ciki ya tashi, yaransa suka kewayeshi suna masa sannu, yana
kwance idanuwansa a lumshe yake amsawa, daya daga cikin rayan nashi, yace." Allah ya
taimaki *Mai dawa!* ga magani na had'a maka." A hankali ya bude idonshi ya dora kan
'kwaryar maganin dake hannunsa, ya mutse fuska yayi ya mayar da idonsa ya rufe da fadin."
Alba ka ajiye wannan maganin ka matsa min lemon tsami guda shida."
Da sauri yace." An gama ranka ya dade.
Ya dan sauke numfashi tare da sake rintse idonsa shi kadai yasan irin ciwon da marar shi ke
masa.
Alba ya k'araso gurin cike da bin umarni yace." Allah yaja zamaninka ga abinda ka bukata.
Ba tare da ya bude ido ba yace." Nagode Alba kuna iya tafiya Allah ya bada sa'a." Suka amsa
da ameen kafin su bar gurin sai da sukayi yi masa kirari kamar yanda suka saba.
Kimanin minti biyar da tafiyarsu ya tashi da kyar, ya jima yana yamutse-yamutse kafin ya dauki
matsatstsan lemon tsamin ya shanye tas, ya ajiye ya koma ya kwanta, yana danne saman
cikinsa.
Tayi mamaki da gari ya waye be zo ya dubata kamar koda yaushe ba, kawai tashi tayi a bacci
ta samu ruwa cikin kwarya da asuwaki sai manya manya ayaba da mangwaro a gabanta.
Ta wanke bakinta da fuskarta, dama can ibadah bata dameta ba domin data dameta da duk
yanda za tayi sai tayi ta gabatar da sallolin da suke kanta.
Yunwar da takeji bata tsammanin Ayaba da mangwaro zasu kawar da ita, taja tsaki tana
harare-harare a gurin da babu motsin kowa sai ikon Allah.
Jikinta ta duba tayi fututu! fatar jikinta duk ta bushe tayi datti! ta dubi qunar da duk ta bushe
tana mata kaikayi, ruwan hawaye ta goge tana tunanin jin dadi da irin rayuwar da take ciki
amma lokaci kankanki rayuwa ta juya mata baya.
Kullum idan za ta kirashi da *'Barawo* zai kalubanceta kan cewa shi ba *'Barawo!* bane to
idan ba haka ba waye silar zuwanta wannan kasurgumin dajin."?
Ta girgiza kai cikin qunar zuciya ta kudiri aniyar irin rashin mutuncin da za tayi mata huce
takaicinta.
Ayaban kadai ta iya ci ta dauki kwaryar ruwan ta shiga tsakanin bishiyu kayanta jikinta ta cire
tas ta wanke jikinta, gurin wankan ta jike rigar data zame mata garkuwa, bata damu ba kawai
tasa breziyya ta mayar da wandonta ta fito a haka, taja ta tsaya tana dube-dube a gurin.
Babu motsin mutum sai kukan tsintsaye da alama yau ma sun fita sun barta a dajin ita kad'ai.
Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke taja tsumman zanin ta dan daure tsakain cinyoyinta kafin ta
nemi saman wani kuttuturun icce ta zauna tana tunanin halin da iyayenta ke ciki na rashinta, ta
san mahaifinta sai yafi kowa shiga tashin hankali rashinta a kusa dashi.
Ya kai minti arba'in cikin halin ni 'yasu kafin Allah ya sassauta masa, ya mike zaune da kyar!
duk da halin da yake ciki hankalinsa na kanta burinshi ya tashi yaje ya duba halin da take ciki.
Ya mike babu kuzari a jikinsa, kai tsaye gurin da take ya nufa...................Rintse idonsa yayi da
karfi yana Auziya a fili sakamakon ganin da yayi