Showing 27001 words to 30000 words out of 47415 words

Chapter 10 - GOJE Book 1 Hausa Novels By Binta Umar Abbale.pdf

09 Jun 2025

1720

hakan."
Ya girgiza kai da fadin." Kayi kokari sosai kuma ka aikata sunnah Allah ya baka ikon yim adalci
a tsakaninsu."

Ya amsa da "Ameen ya Allah ina fatan kai ma kayi koyi dani."

Girgiza kai kawai yai baya tsammanin hakan domin baya san damuwa ba lallai sai ka tara mata
a gidanka za'a tabbatar da jarumtarka ba, shi a ra'ayinsa zai iya 'kare rayuwarsa da mace
daya, sai dai kuma duk yanda Allah ya shirya masa rayuwa to zai kar'ba hannu biyu tare da
godiya a gareshi.

****
Ke'bantacen guri aka ajiyeshi shi kad'ai ba tare da da sauran yaran sa ba, sai dai su an
tattarasu guri guda da sauran masu laifi gama gari. wannan karamcin da Asp din yayi masa ya
tsaya masa mutuka a rai yayi ta tunanin irin alkairin da zai saka masa.


***
Uwale duk atamfofin da take k'uzu tana tarawa a cikin adaka fito dasu tayi ta siyar. ta dinga bin
tsangaya-tsangaya tana bayar da sadaka domin almajiran suyi mata saukar al'kur'ani akan

bukatarta, Allah maji rokon bawansa addua ta kar'bu.


Washe garin ranar da ita da Mahaifin Hamra'u da ita Hamra'un suka yanke shawarar zuwa
headquarter 'yan sandan domin samun cikkenan bayani.

Sun jima a tsaye kafin wani jami'i ya sauraresu, Malam Hafi'i mahaifin Hamra'u shine yayi
masa bayanin abinda yake tafe dasu.

Yayi jim! yana kallonsu kafin yaja tsaki ya barsu a gurin......Uwale da sauri taje tari gabansa
kuka ta fashe dashi ta zube gwiwa biyu a gabansa tana rokonsa, hakan ya janyo hankalin
ma'aikatan dake gurin suka fara tambayar ba'asi.

Cikin kuka tace." Me yasa dukkaninku baku da imani ne? tunda muka zo gurin nan babu wanda
yayi mana kallon mutunci Allah da Annabi sunfi karfin wasa amma gabadayanku bakwa tsoron
Allah."!

Daya daga cikin musulman dake tsaye gurin ne yace." Tayi masa bayani abinda yake tafe da
ita.

Hanci ta fyace kafin." Tace "Mun zo gurin UMARU wanda ku ka d'aure kuna zarginsa da
ta'addanci bayan ba haka gaskiya take ba."

Yace." Yi shuru ki kwantar da hankalinki ki daina kuka zanyi miki kokari yanzu." Ta mike tsaye
tana gyara yafan mayafinta, tace."Nagode sosai Allah yayi maka albarka." Ya amsa da 'ameen
kafin ya umarcesu da suje su zauna a wata rumfa.

Sai da yaga zamansu sannan ya bar gurin, kai tsaye ofis din Asp ya nufa domin sheda masa
abinda ke faruwa.
Ya k'ame da sarawa kafin ya sheda masa abinda ke da akwai, kai tsaye ya bashi umarnin
shigowa dasu.

Da kanshi ya nuna musu gurin zama yana musu sannu, Malam Shafi'i da 'yarsa suka zauna
kamar yanda ya umarcesu Uwale kuwa kai tsaye kujerarsa ta nufa, ya dinga kallonta har ta iso
inda yake ta zube gabansa kawai sai ta fashe da kuka tare da rirrike masa kafafu! kuka take
sosai tana bashi hakuri.
Tausayi ya rufeshi da kyar ya iya mik'ewa tsaye sakamakon rikon da tayi masa, ya sunkuya tare
da sanya hannu ya dago ta ta mike tsaye, rungumeta yayi yana rarrashin gami da bata hakuri.

Ita kuma fadi take." Ku za'a bawa hakuri ku dubi girman Allah kuyi adalci kada ku yanke
hukunci akan wanda bashi laifi bashi ne wanda kuke zargi ba.

Hankici ya ciro daga jikinshi, ya goge mata hawaye yana sake kwantar mata da hankali, sai da
ya tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya umarcesu da cewa subi bayan shi.


Kai tsaye ke'bantaccan gurin da aka ajiye shi suka nufa...........Aps din a gaba suna bayansa,
yana shiga sai ya basu hanya. gabadaya suka hada ido dashi yana zaune kasan kafet da tire
din abinci a gabansa tsaf dashi da nutuswa a tare dashi bashi da wata matsala bayan sararin!
dake daure da kafafunsa
Hamra'u da gudu ta iske inda yake, kawai sai ta fad'a kansa tana wani irin kuka! wanda yake
nuna tsantsar tashin hankalinta, itama Uwalen da kuka ta karasa gurin duk da ganin da sukayi
masa cikin nutsuwa hakan be gamsar dasu ba.

Asp ya juya ya fita yana jimamin al'amarin.

Tun bayan data fad'i jikinsa yasa hannu a bayanta yana dan bubbugawa, a Hankali cikin taushin
murya yake rarrashinta, ta dago kai tana kallonsa hawaye sai ambaliya yake a saman fuskarta,
kai yake girgizawa alamun ta daina kukan, yasa hannu ya goge mata fuskar sosai yake
mamakin irin k'aunar da yarinyar take masa, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sai dai har
yanzu bata saki hannunsa ba ta rike tsam a hannunta.


Ya d'ora idonshi kan Uwale da ta dage tana kuka sai kace wacce aka nuna mata gawarsa.

Murmushi yayi tare da mika hannunshi kan fuskarta hawayen ya share mata da fad'in." Kukan
bashi da Fa'idah Uwale addua zaki min."

Tace."UMARU kukan shi yake kansa yin kuma shine samun salama, amma a zahirin gaskiya
muna cikin tashin hankali bamu da kowa sai Allah shine kuma zai fitar damu."

Yace."Kin gama magana tunda ki kace Allah, kuma gaskiya tayi halinta tun kafin tafiya tai nisa
gaskiya ta bayyana cewa wanda suke zargi bani bane nima kuma na san da hakan saboda
haka ku kwantar da hankalinku insha Allah zan fito lafiya na cigaba da rayuwa da ikon Allah."

Tace."Idan hakane mai yasa basu kwance maka wannan d'aurin ba, duba fa yanda kafafunka
suke daure.

Yace."Akwai dalilin da ya sanya hakan wannan ba matsala bace kada hakan ya daga muku
hankali."

Kusan a tare suka sauke zuciya da jin furucinsa suka shiga godewa Allah da abinda yayi
musu.

Har yamma suna tare ya saki jikinsa sosai yana basu labarin irin gwagwarmar suka sha a dajin!
tace."Kaga Umaru shiyasa kwata-kwata hankalina bai kwanta da wannan harkar ba mahaifinka
har ya mutu da abun a cikin ransa saboda haka idan Allah yasa ka kubta to dole ka ajiye
wannan sana'ar ka nemi wata domin hakan shine samun nutsuwarmu baki daya.
Domin ya kwantar mata da hankali sai ya amsa mata akan abinda take so, taji dadin hakan
kuwa tay tai masa addua da fatan samun nasara akan dukkan abinda ya sanya a gaba.


*****
Ta jima a toilet din tana durje jikinta da sabulai iri-iri kafin ta dauro towel ta fito. idonta ya sauka
kan tufafi wanda aka ajiye mata su kan gado komai sabo underwears sai riga da siket na wani
material mai taushi, goge jikinta tayi kafin ta zauna gaban mudubi tana kokarin duba man da
zata shafa a jikinta, tsaki taja tana hararar tarin kayan kwalliyan dake dressing mirror din duk
ciki babu kalar man da yayi mata ballantana ta shafa a jikinta........wani lotoin ta dauka tana
jujjuyashi a hannunta sai ya mutse fuska.

Ta turo kofar dakin ta shigo da sallama a bakinta kallo guda kayi mata zaka fahimci cewa tana
daga cikin jerin mutane masu sauki kai da daukar rayuwa a sannu, tana da fara'a sosai domin
da wuya kaga bacin ranta sai in tura ta kai bango.

Fuskarta yalwace da fara'a ta 'karasa shiga dakin da fadin." Yawwa kin fito ko ga kaya nan na
ajiye miki na san za suyi miki dadin sawa.''

Shuru tayi bata tanka ba. Ta kalleta da fadin." Ko dai na sauya miki wasu wannan ba suyi miki
ba."?

Tsaki taja da fadin." Don Allah kin cikani da surutu haka na duba na gani okey nagode."

Ranta ya 'baci da abinda tayi mata amma sai ta danne ko alama bata nuna a fuska ba tace."
Okey to shikkenan idan kin shirya sai ki fito muci abinci ."

Ta'be bakinta tayi ba tace komai ba ta cigaba da jujjuya abinda ke hannunta.

Juyawa tayi da niyyar fita daga dakin. sai ta dakatar da ita, ta tsaya tana sauraranta.

A yatsine tace." Wannan tarkacen mayukan shafawar taki ba zan iya shafawa ko daya a jikina
ba domin ni ba irinsu nake shafawa ba.

Cike da mamaki take kallonta tana mamakin furucinta, tarkace!!! duk man da take shafawa
babu na kasa da dubu biyar sai sama amma shine har take magana cewa ita tafi karfin ta shafa
a jikinta.

Jinjina al'amarin tayi kafin tayi 'yar dariya da fadin." Lallai 'kawata kina ji da gayu amma idan ba
haka ba meye laifin mayuka na ko wannan na hannunki kika shafa ya isheki." Cike da wasa ta
karashe maganar..........Sai ta fusata! ta mike tsaye tare da buga mata tsawa! da fadin." Ke kin
san wacece ni kuwa? da har kike min wannan banzar maganar."? Ta'be bakinta tayi tace." Ina
zan sani hajiya ni dai Daddy ya kira ni a waya ya sheda min cewa zanyi b'akuwa shiyasa nake
karramaki bahaushe yace." bakon ka Annabin ka."

Dogon tsaki! taja kafin ta koma ta zauna..........Ita kuma da sauri ta bude kofar dakin ta fita tana
mamakin al'amarin.


Zama tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ta kalleta da fadin.'' Ya akayi ne? bata gama shiryawa
bane."?

Baki ta dan ta'be kafin tayi 'yar dariya da fadin." Na isketa ta fito daga wanka tana nazari man
da zata shafa."

Cike da mamaki tace." Kamar yaya nazari duk cikin mayukan shafawar taki babu wanda yayi
mata."?

Tace."Hakan take nufi."

Tana kokarin magana motsin fitowarta ya katseta duk sai suka juya suna kallonta tayi kyau
sosai a cikin material din sai dai siket din ya matseta dalili tana da kwankwaso mai fadi da cika
sakamakon mai kayan da nata bai kai hakan ba.

Da murmushi a fuskar matar gidan tace." Kin fito."? "Umm." tace kawai ta nemi kujera ta zauna
sai wani basarwa take.

Ta kalleta da fadin." Nabila mai yasa ki ka bata wannan kayan kamar sun matseta ki tashi ki
dauko mata wasu."

Tace."Mommy kin san duk kayana riga da siket ne kuma bai zama dole suyi mata yanda takeso
ba tunda ta fini kiba."

Ta kalleta da fadin." Zinatu baki takura ba dai ko."?

Girgiza kai tayi da fadin." Kada ki damu hakan yayi min daidai domin yawancin kayana haka
suke." Tace." To masha Allah ku tashi muje muci abinci." kusan a tare suka mike kai tsaye
gurin cin abincin suka nufa.

To duk wasu bayanai da ya kamata ace gwamnati ta san dasu Asp ya harhad'a komai ya
turawa maigirma governor domin ya saurara dashi da wa'inda da ke da alhakin hakan, sai dai
ya sheda masa cewa ranar asabar shi da wanda ake zargi da aikata ta'addancin zasu shiga
sansanin domin binkice akan sassan sannun da zai tabbatar da gaskiyar magana. maigirma
governor yayi na'am da maganar ya kuma bada goyon baya akan tafiyar.


*'Yan jarida mane ma labarai suka samu abun yayatawa a gari! gidajen redio da television
gami da jaridu labarin abinda suke nunawa kenan cewa ashe wanda ake zargi da *UBAN
DABA!* *bashi da ala'ka da zargin da ake masa asali ma shine mutum na farko wanda ya fara
karya alkadarin d'an ta'addan da ya addabi kasa da al'ummar dake cikinta, domin tabbatar da
gaskiyar magana kakakin rundunar 'yan sanda wato Asp Musa Baharu zai jagoranci shi wanda
ake zargi domin gudanar da binkicen sassan hannun wanda ake nema ruwa a
jallo...........Sannan kakakin rundunar 'yan sandan ya shedawa mane ma labarai cewa yanzu
haka akwai d'iyar Sarkin Kano mai suna Zinatu wanda ake zargin cewa wasu 'bata gari sunyi
kidnapping d'inta domin samun kudi daga gurin mahaifinta, amma ha'kan su bai cimma ruwa ba
sakamakon zuwan shi wanda ake zargi da ta'addanci mai suna UMARU wanda jama'a suka fi
sanin sa da GOJE!* *shine wanda ya zama garkuwa a gareta har yayi nasarar tallafar rayuwarta
bayan ya samu nasara akan wa'inda sukayi garkuwa da ita............Wannan shine cikakken
rahoton da ya cika garin Katsina dama kewayanta.*


Duk wanda ya danganci masarautar yana cikin farin ciki sakamakon samun cikkaken labarin
bayyanuwar ta............Fada ta cika da jama'a masu zuwa taya murna da fatan alkairi maimarta
da 'yan uwansa fuskokinsu tamkar gonar auduga saboda tsantsar farin cikin da suke ciki a ranar
yini cir masarautar babu masaka tsinke mata da maza wannan ya fita wannan ya shiga.
Gimbiya Aysha da 'yar uwata tare da 'ya'yansu su ka kasance cikin farin ciki mara misaltuwa,
Maijidda ma tayi nata murnar daidai gwargwado amma ta ciki na ciki domin kasa zama tayi cikin
'yan uwanta ta nufi b'angaranta jikinta duk a sanyaye yanzu babbar damuwarta kada asiri ya
tonu sunanta ya fito shine abinda yafi tsaya mata a rai....


*Hello my fans A hanzarta biyan kudi domin yanzu zamu shiga cikin labarin akwai kuraa!! �
kada ki sake ayi bbu ke 'yar uwata kada ganin k'yashi ya hanaki biya ki zauna jiran na sata
wallahi tallahi! hakkin wani masifa ne!! mai girman gaske!! yi kokarin gudun haram! komai
kankantarta!!!*

*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da
wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin mov ko airtal

[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊ï¸í ½í³š_*
_____________________


FREE PEGE

*29&30*
Kusan a tare suka d'auke idonsu daga barin kallonta, Asp din yayi magana amma shi uffan
bece ba har ta gama harare-harare! ta fita daga ofis din. Ya d'an ja k'aramin tsaki da fadin."
Yarinya nan babu tarbiya a tattare da ita duk kuwa da cewa ta fito daga tsatso mai kyau, ba ta
gaji dattako da karamci irin na mahaifinta ba, duk da ba a garin kano muke zaune ba muna da
labarin dattakon mahaifinta mutum ne mai karamci da mutunci yana aiki da hankali da ilimi yana
kuma gudanar da mulki a bisa tsari na isalama."

Beso ya tanka a cikin al'amarin yarinyar ba amma ganin yanda Asp din yake jaddada maganar
yasa yace." Akwai irinsu da yawa wa'inda suka dauki mulki wata tsiya idan akace mahaifinsu
nada sarauta ko wani muk'ami sai su dauki girman kai su dora a kansu suna ganin babu wanda
ya isa dasu, hakane maganarka mutumin kwarai yana iya haifar baragurbi acikin al'umma
jarabtace kawai daga Allah.'' Yace." Kwarai kuwa wannan haka yake sai dai kawai mu roki
Allah ya shirya mana zuria baki d'aya." Ya amsa da ameeen ya Allah.

Shuru na minti biyu ya ratsa gurin, cikin 'yar tsokana Asp din yace." Akwai abinda na manta ban
tambayi *MAI DAWA!* ba."?
Murmushi yayi da fadin." Akwai sauran tambayoyi kenan."? Girgiza kai yayi da fadin." Tambaya
daya ce shin kana da iyali kuwa.''?

Girgiza kai yayi gami da dan ta'be bakinsa.........Asp ya dan zare ido da fadin." Kana nufin babu
iyali kenan."
Kai ya daga masa still da murmushi a fuskarsa.

Sai kawai ya shiga girgiza kansa da fadin." Gaskiyar magana yanda kake jarumin namiji mata
hudu suka cancanta da kai amma ace ma ko daya babu." cike da alhini ya kare maganar.

Sai abun ya bashi dariya ya dan dara kafin yace." Asp matsalar mata nada yawa shiyasa nayi
zamana a haka ba wai don bani da bukata ba, kawai nafi bukatar kwanciyar hankalina nayi duk
abinda nake so ba tare da wani ya caza min kai ba.''

Yace." To ai hakan nan ake hakuri dasu da matsalarsu Umaru kowane maigida yana da
matsalar iyali mussaman idan mace fiye da d'aya yake da ita, dole ba zaka rasa shi da matsala
ba, nima matana biyu sai dai kowacce da gidanta kuma yanzu haka ina shirin yin ta uku da
yardar Allah sai na cike domin ina da ra'ayin hakan."
Ya girgiza kai da fadin." Kayi kokari sosai kuma ka aikata sunnah Allah ya baka ikon yim adalci
a tsakaninsu."

Ya amsa da "Ameen ya Allah ina fatan kai ma kayi koyi dani."

Girgiza kai kawai yai baya tsammanin hakan domin baya san damuwa ba lallai sai ka tara mata
a gidanka za'a tabbatar da jarumtarka ba, shi a ra'ayinsa zai iya 'kare rayuwarsa da mace
daya, sai dai kuma duk yanda Allah ya shirya masa rayuwa to zai kar'ba hannu biyu tare da
godiya a gareshi.

****
Ke'bantacen guri aka ajiyeshi shi kad'ai ba tare da da sauran yaran sa ba, sai dai su an
tattarasu guri guda da sauran masu laifi gama gari. wannan karamcin da Asp din yayi masa ya
tsaya masa mutuka a rai yayi ta tunanin irin alkairin da zai saka masa.


***
Uwale duk atamfofin da take k'uzu tana tarawa a cikin adaka fito dasu tayi ta siyar. ta dinga bin
tsangaya-tsangaya tana bayar da sadaka domin almajiran suyi mata saukar al'kur'ani akan
bukatarta, Allah maji rokon bawansa addua ta kar'bu.


Washe garin ranar da ita da Mahaifin Hamra'u da ita Hamra'un suka yanke shawarar zuwa
headquarter 'yan sandan domin samun cikkenan bayani.

Sun jima a tsaye kafin wani jami'i ya sauraresu, Malam Hafi'i mahaifin Hamra'u shine yayi
masa bayanin abinda yake tafe dasu.

Yayi jim! yana kallonsu kafin yaja tsaki ya barsu a gurin......Uwale da sauri taje tari gabansa
kuka ta fashe dashi ta zube gwiwa biyu a gabansa tana rokonsa, hakan ya janyo hankalin
ma'aikatan dake gurin suka fara tambayar ba'asi.

Cikin kuka tace." Me yasa dukkaninku baku da imani ne? tunda muka zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login