Showing 6001 words to 9000 words out of 47415 words

Chapter 3 - GOJE Book 1 Hausa Novels By Binta Umar Abbale.pdf

09 Jun 2025

1711

mummunar magana akaina sai na
illataki."!
Shuru tayi jikinta yayi bala'in mutuwa ganin yanda hancinta ke zubar da uban jini shine abinda
yafi zaburar da ita.

Ta kalleshi, yana safa da marwa a gurin, tace." A kan me ba zan kira ka da wannan suna ba? ka
sato ni a gaban iyayena domin su baka kudi. akan me ba zan kiraka da *'Barawo* ba me kake
bukata? da ka kawoni daji ka ajiye kana azbtar dani, kamar ni *Zinatu* wacce ta gaji sarauta
gabada da baya ina rayuwa a wannan kazantaccen gurin, tare da kai makaskanci to saurara
kaji da kyau! wannan jinin da ya zuba, be zuba a banza ba, wallahi sai kayi daka sanin zubar
dashi."!

Hannu d'aya yasa cikin aljihun jins din dake jikinsa, ya dan sunkuya tare da dogare gwiwarsa,
fuskarta ya dago da hannunsa, yana kallonta tana kallonsa, yace."Daga wace masarauta kika
fito naga kina girmama kanki kina mutunta kanki, duk wanda ya gaji saurata baya kambaba
kanshi kamar yanda ke kike, ina so ki sani zargin da kike a kaina kar ki gazgata, Allah ya
kawoni ne tareda jama'ata domin na taimakeki, kuma zan taimakaki bakin kokarina, amma ni
zan koya miki tarbiya.

Magana za tayi ya sanya yatsunsa biyu ya murje fatar bakin...........tsam! ya rike lebunan yana
ligwigiwitawa, kukan zucci kawai take, jikinta yayi mugun sanyi, yana sakin bakin ta silale a
gurin, yaja tsaki da furta "kalankasa kawai."!

Zanin dake nannad'e a jikinta ya janye duk tana jin abinda yake amma tsabar yanda jikinta
yayi tubus, ta kasa hanashi sarrafata.

Bai damu da kallon wasu sassan na jikinta ba, domin gabad'aya babu wani feelings a tare
dashi, tunda yake sai yace babu ranar da wata mace ta ta'ba tayar masa da hankali duk zubi da
kirar dake gareta, Asalima yakan jima bai shiga yanayi na bukata ba, shiyasa auran baya
gabanshi, wanda uwar rikonshi wato kakarsa Uwale keyi masa surutu akan hakan.

Da kanshi ya lalubi inda kunamar! ta harbeta ya shefe gurin da magani, ganin duk yaran nashi
sun bar gurin yasa ya bude mata jikin domin qunar tasha iska.

Har ya gama abinda yake a gurin bata daina zubar da hawayen takaici ba, tayi turr! da wannan
rayuwar da take ciki, a tunaninta hanya ba zata iya had'awa dashi ba, sai gashi w *Kazami-
Bagidaje!* irin sa yana ganin sirrin jikinta. tana ganin wannan ko hadimanta (masu yi mata
bauta) sun fishi kyawun gani sai gashi a banza yana yin yanda yake so a kanta ya tatta'ba
jikinta babu tsoro ko shakka a tare dashi hawaye masu zafi ta goge tana jimanta al'amarin.


Taji dadin maganin sosai domin tana tsaka da tunanin hanyar da zata bi domin kubutar da
rayuwarta bacci mai nauyi ya dauketa.

*****
Kana ganinta kaga bafulatana, doguwa ce sambal kyakykyawa a fuska, gata fara tas! ta tara
duk wasu abubuwa da da namiji ke bukata amma hausawa sukace wai Dan Adam tara yake be
cika goma ba, Hamra'u bata da cikkar kirji hakanan kuma babu baya a tsaye take kamar
muciya da zani, sai dai akwai tarbiya da kunya irin ta fulani.
A nutse tayi sallama a gidan, Uwale dake uwar daki ta amsa, da fadin.'' 'Yar halak yanzu nake
maganarki a zuciyata.

Murmushi tayi ta cire takalminta, ta shiga dakin, Uwale na kurbar kunu ta mika mata kofin da
fadin " Bisimillah."
Girgiza kai tayi tana murmushi tace." Ai daga gida nake kuma sai dana karya kafin na fito.

Dariya tayi irin ta tsoffi tace." Hamra'u kenan wai me yasa duk sanda zan baki abu sai kice daga
gida kike ko dai kankyamina kike ne."?

Da sauri tace."Aa Wallahi ba haka bane Uwale na koshi."

Tace."To ai shikkenan duk ya mutan gidan."? Tace."Suna nan lafiya lou alhamdullhi babanmu
yace a gaisheki da kyau.''

Tace."Ina amsawa ai a cikin satin nan nake so nazo gidanku mu gaisa sai kuma *UMARU* Yayi
tafiya gashi zai dauki sati guda bai dawo ba.

A sanyaye tace."Yanzu fa nake shirin tambayarki ina yake shine zakice yayi tafiya kuma sai yayi
sati zai dawo."


Tace."Eh haka yace min da zai tafi kin san dai yanayin al'amuranshi, wani sa'in ma har wata

guda ya kanyi yana gwagwarmaya a daji"

A raunane tace." Ni wallahi ba naso yana irin wannan yawace-yawacen tsoro nake kada 'yan
fashi su kasheshi ko kuma namun daji su cinyeshi."

'Yar dariya tayi tana sud'e kofin kunun data gama sha tace."Sai dai kiyi hakuri Hamra'u wannan
mijin naki yayi nisa addua kawai zaki dinga yi masa.

Tace."Kullum inayi masa addua tare da sauran jama'a." Tace."yawwa hakan yana da kyau,
sannan ki cigaba da hakuri insha Allahu, hankalinsa zai karkato kanki."

Idonta ya cika da ruwan hawaye, tace."Uwale sai nake ganin kamar baya sona tausayina kawai
nake gani a kwayoyin idonshi.

Tace." To in banda abinki Hamara'u ai sai da so ake tausayi, da baya sonki ba zai tausaya miki
ba."

Shuru tayi tana nazarin maganar, itafa tunda take dashi babu wata kalmar so daya taba furta
mata, asalima yana kiranta da kanwata, amma bai taba cewa Hamra'u ina sonki ba, sai dai
yana tsananin bata kulawa komai take bukata idan tayi masa magana kai tsaye yake mata,
wannan dalilin yasa iyayenta da ita Uwalen suke ganin kamar sonta yake, ajiyar zuciya ta
sauke ta kudire a ranta cewa idan ya dawo zata cire kunya ta tambayeshi matsayinta a
zuciyarsa.

Hamra'u 'yar kanin Uwale ce, tun tana yarinya Allah yasa mata so dakaunar Goje tun be
fahinta ba har Allah ya fahintar dashi, be ajiyeta a wani matsayi na daban ba face wanda take
dashi a zuciyarsa, gabadaya tunda ya taso baya da ra'ayin soyayya, shiyasa baya fahimtar
tarin 'yan matan dake k'aunarsa, Samari da yawa a karkarar tasu suna kishi dashi, a cewarsu
sai kace shi kadai ne namiji ko wacce budurwa bata da magana sai tasa, ransu yana baci
mutuka, suna kuma bala'in kishi a kan haka, ita kanta Hamra'un akwai wanda yake mutuwar
sonta amma fafur taki amince masa ita dai Umaru takeso wanda bata da tabbas a
kansa..............

Uwale, kayan dillacinta ta dauko ta nada gammo ta dora aka, tana gyara yafan mayafi take
fadin."Hamra'u ni zan fita dama a irin wannan lokacin nake samu na nemi halalina idan kin
gama gyara min gidan ga kwado ( dan mukulli) akan taga ki kulle gidan ki bawa Tasallah ta
ajiye min."
Tace."Uwale inace Yayana ya hanaki yawon dillaci nan kuma kin san Babana ma baya so me
kike bukata ne a duniyar nan."

Tsaki taja da fadin." Sai kiyi kuma kinga tafiya ni babu wanda zai hanani neman kudi." tana
gama maganarta tasa kai ta fita daga gidan.

Hamra'u girgiza kanta kawai tayi idan da sabo ta saba da hakan , a nutse ta mike ta fara
ayyukan dake gabanta....

***********
*WAIWAYE*
K'allo d'aya nayi masa na fahimci wanene a gabana, ko da yake koda zanyi shekara d'ari ba
tare da na sanyashi a idona ba to ba zan mance kammaninsa ba, *Sadauki Omar* kenan
Sarkin dake kan karagar mulki a jahar *Kano* Adalin sarki wanda al'ummarsa ke jin dadin
mulkinsa.
Yana nan a yanda kuka san shi tsayayye! kuma jarumin namiji! kamanninsa suna nan sai dai
alamun girma da ya baibayeshi amma a tsaye yake da jarumta babu abunda ya samu nakasu
a cikin halayensa da d'abi'unsa.

Yana tsaye a tsakiyar babban falonshi hannuwansa goye a banyanshi yana kai kawo a gurin,
kallo daya kayi masa zaka fahimci yana cikin damuwa.


Cikin nutsuwa da kamala tayi sallama be juyo ba ballantana ya amsa sallamarta,
kai tsaye inda yake ta nufa, sai na bita da kallo, ina hasashen a inda na san fuskarta,
Gimbiya *Aysha ce fa* zuciya tayi saurin tuna min ita

Cike da dumbun mamaki nake kallonta tana sanye cikin laffaya milk color da adon zaiba kafarta
sanye da takalmi rufaffe irin na sarauta, ban hango wata tawaya a tare da ita ba domin kuwa
jikinta ya nuna alamun hutu da jin dadi sai dai alamun shekaru sun tura hakan ma sai ka 'kura
ido a kanta sannan zaka fahimci cewa ta kwana biyu a duniya.
Hannunta ta d'ora kan kafadarsa, a nutse ta kira sunanshi *"Jarumi."* be juyo ba ballantana ya
kalleta, sai ta dora kanta kan kafad'arsa, hawayen da take boyewa suka kufce, wai shin ya za
suyi da wannan ibtila'in da yake kokarin ruguza musu farin cikin da suke ciki na tsayin shekaru
masu yawa................



*Ga wanda bai samu damar karanta Sadauki Omar ba, zai tura 1k domin samun damar karanta
littafi biyu tare da Goje! Sadauki Omar return*



*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da
wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* Mutanan Nijar zaku turo min katin Mov ko airtal na Dala dari.

[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊ï¸í ½í³š_*
_____________________


FREE PEGE

*15&16*
Sosai ta kwanta jinya sakamakon artabun da sukayi ita dashi, jikinta yayi mugun tsami! ta
shar'be! a guri guda da kyar take iya motsa hannu saboda tsabar sanyi da jikinta yayi, al'amarin
bai tashi tsananta ba sai da dare ya tsala tukkuna, ta kasa rintsawa gabadaya jikinta ya dauki
ciwo! ga wani irin kaikayi da ciwukan jikinta keyi. Kuka ta dinga yi tana jan hanci! ita kam wannan bala'i bata san ina zata kai shi ba.

Can cikin baccin daya dan fizgeshi ya dinga jin shashshekar kukanta, zumbur ya mike zaune,
dama babu wata tazara a tsakaninsu, ya d'auki fitilar dake gefansa ya kunna yana daga inda
yake zaune yake haska gurin da take.

Hannu tasa ta kare fuskarta ta sake takure jikinta tana cigaba da zubar da hawayen azabah!.

Ya karaso gurin da fitilar a hannunsa, ya dudduba ko'ina babu wani abu. tsugunawa yayi a
gabanta yana duba fuskarta, hannu tasa ta doke fitilar ta fadi. a take ta mutu gurin yayi duhu!
ya lalubi fitilar yana kokarin gyara batir din, amma ina ta rikice! yayi-yayi ta kama taki, haka ya
hakura ya ajiyeta kafin yace." Kukan me kikeyi ko wani guri yana miki ciwo a jikinki."? Shuru tayi
masa, ya sake maimaita maganarsa, uffan ba tace masa ba.

Sai ya yun'kura da niyyar barin gurin tayi saurin rike gefan rigarsa, a rikice tace."Jikina ne duk
yake ciwo ko'ina babu dadi."

Yanda yaji tana magana a rikice da alamun kuka ya sanya ya gazgata maganarta, bece komai
ba ya sake yunk'urin tashi. Ta rike gefan rigarsa da kyau! yaja! taja! sai ya juyo yana kallonta,
da k'yar ta mike zaune kafin tace."Kada ka tafi kayi wani abu wallahi zan iya mutuwa."

Yana da tsananin tsausayi mussaman akan 'ya mace! sai duk jikinsa ya mutu, ya koma ya
tsugana yana dan ganin shatin fuskarta duk tayi wani iri idonta yayi jajawur! fuskar duk ta
kumbura!.

Be iya tausasa murya ba, amma sai ya tsinci kansa da sassaita muryasa yace."Yi hakuri ki sake

min rigar na samo miki magani."!

Hanci taja kafin ta sakar mai rigar ya tashi, tabi inuwarsa da kallo tana sauke ajiyar zuciyar
wahala.

'Daya daga cikin yaranshi ya umarta daya had'a masa maganin ciwon jiki, da yake duk suna
tafe da guzurinsu, ba tare da anja dogon lokaci ba, ya harhad'a komai ya nufi inda take dashi a
hannunsa.

Samun ta yayi tana rawar d'ari, domin lokacin sanyi asubah ya fara sai zazzabi yake kokarin
rufeta, sai datse hakoran bakinta take.

Cikin wani irin yanayi ya mika mata maganin da fadin." Kar'bi kisha wannan za kiji sasaauci
sannan zaki samu bacci."

Kasa kar'ba tayi saboda halin da take ciki kawai ido ta tsirawa fuskarsa hawaye na sharara!
jikinta gabadaya yaki tsayuwa a guri daya saboda karkarwa!.


Ya ajiye maganin hannunta ya lalubo ya rike a cikin nasa, nan yaji zafi rau!! ya sake shiga
damuwa da ya fahimci zazzabi ne a jikinta.

Sosai ya zauna a gurun ya kama dukkanin hannunta cikin kokarin sassaita muryarsa da sigar
rarrashi yace."Zazzabi ne ko."?


Sai ta fashe da kuka! mai karfi! kamar me jiran kiris! da sauri yasa hannu ya rufe mata baki yana
girgiza mata kai!

Hannunsa ta cire tana me cigaba da janyo kukan dake cin zuciyarta.

Kawai sai ya tsinci kansa da janyota jikinsa, ya sata cikin katuwar rigar dake jikinsa, ya san
nauyin rigar zai zame mata garkuwa gurin karkarwar da take.

Da yake taimako take nema ba tayi wani turjiya ba mussaman da taji ta kan faffadan kirjinsa
dake cike da gargasa ga wani irin dumi da ya fara ratsa jikinta, luf tayi ta kwanta sosai tare da
sanya hannu a bayansa ta rikeshi kam! tana sauke ajiyar zuciya daki-daki.


Sai da ya fara jin saukar numfashinta a hankali sannan ya dan gyara zaman shi, cikin wannan
muryar daya aro yace." *GIMBIYA!* Yanda ya kira sunan yayi masifar kassara mata gabobin
jikinta.

Taji shi sarai! tayi shuru motsin kirki ta kasa mamakin ma take yanda akayi ta saki jikinta a
kirjinsa ba tayi tsammanin zata yarda numfashinta da nasa ya hadu ba sai gata a kwance a
kirjinsa male-male maimakon taji wari! ko wani abu makamancin haka na fita a jikinsa sai taji
akasin haka, jikinshi baya fitar da wari! ko kad'an sai ma wani irin dumi! da takeji na ratsa ta,
nutsuwa da kwanciyar hankali na sauka a sassan jikinta.

*"GIMBIYA."* Ya sake kiran sunan daya sanya mata a lokacin, koda yake daman Gimbiyar ce
shiyasa shima ya ara ya yafa.

Dan motsi tayi amma bata amsa ba, kuma bata sakeshi ba, ya dan ja numfashi, jin yanayinsa
yana sauyawa, ya fara kokarin cireta daga jikinsa. Ta dage! harda gyara kwanciya kamar
wacce take kan katifa.

Mamaki sosai ya rufeshi, tunda yaji tayi shuru kuma numfashinta ya daidaita ya san ta samu
sassauci bayan haka kuma jikinta ya daina karkarwa da alamar zazzabin yayi nasa a guri,
amma meye amfanin abinda take.

Namijin kokari yayi ya cireta daga jikinsa, babu kunya ta zuba masa ido kamar wanda yayi mata
laifi.

Ya saisaita yanayinsa kafin yace."Sannu kina bukatar magani ko."?

Shuru tai na minti biyu kafin ta kalli hannunsa, maganin ne yake kokarin sanya mata a baki.
Tasa hannu ta buge kwaryar maganin gabadaya ya zube kasan gurin da jikinsa

Cike da takaici da bacin rai yake kallonta, ta 'bata rai da fadin.'' Wane irin magani ne wannan
me wari zaka sa min a baki."

Ya hadiye b'acin ransa wannan karan bai sassauta murya ba da yanayin maganarsa yace."
Ke ki kace jikinki na ciwo maganin karfin jiki ne."

Ta'be baki tayi da fadin." Bana bukata." Bece komai ba ya tashi daga gurin tare da jin takaicin
abinda tayi.

Ta kalleshi da fadin." Ka bani aron wannan rigar ta jikinka na rufe jikina da ita tana da d'umi."

Uffan bece mata ba ya bar gurin, minti uku ya dawo da irin rigar a hannunsa. Ya mika mata, ta
kalleshi da fadin." Ta jikinka nake so."? Yace."Duk daya ce da wannan din."

A yamutse tasa hannu ta kar'ba tana kokarin sawa a jikinta ya bar gurin .

Sai kace suddabaru! hankalinta ya gaza kwanciya koda tasa rigar ta kwanta domin jin d'umi
kasa nutsuwa tayi ta tashi zaune tana rawar jiki.......Me yasa ta kasa samun abunda takeso a

jikin rigar! ita a tunanin kaurin rigar ne ya saukar mata da nutsuwa sai taga akasin haka. "Ba
rigar bace mai rigar ne yasa miki nutsuwa da kwanciyar hankali."
zuciyarta ce take mata wannan maganar.

Da sauri ta k'aryata zuciyarta ta sake rurrufe jikinta da rigar tana korar abinda zuciyarta ke raya
mata, babu yanda za'ayi ta amince da cewa wannan gantallalan ne zai zama garkuwa a gareta.

Daya daga cikin yaranshi ne ya kawo mata ruwa da asuwaki da abin kari. ganin yanda
maigidansu yake bata kulawa ya sanyashi gaisheta, bata amsa ba sai wukalantaccan kallon da
take masa shida tarkacen da ya ajiye a gabanta. Girgiza kansa yayi baki a cije! ya bar gurun ba
don kar ya dauki mataki akan yarinyar ya samu matsala da maigidansa ba, da sai ya fasa
mata baki domin yaji ciwon kallon banza da tayi masa.

Har gari yayi haske sosai tana takure cikin rigar har yanzu ta kasa tantance a wane iri
yanayi take,

Can ta hangoshi yana zuwa inda take, ido kawai ta tsira masa babu kiftawa sosai take
mamakin tsananin kamar da yake da jarumi(Barbahs) tana bala'in son jarumin saboda
jarumtarsa da iya soyayyarsa idan yana abu a film kamar gaske, zazzafar ajiyar zuciya ta
sauke tana kokarin karyata abinda zuciyarta ke raya mata a kansa.
Tsaf yake cikin shirin fita, ya sauya rigar jikinsa doguwar jallabiya ce browan mai gajeran hannu
sai ya sanya dogon wadon jens kanshi nannad'e da bakin yadi yayi gammo sosai! idanuwan
nan rad'au! da bakin kwalli! kafad'unshi rakwacam! da tarin kayan farauta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login