Showing 36001 words to 39000 words out of 47415 words

Chapter 13 - GOJE Book 1 Hausa Novels By Binta Umar Abbale.pdf

09 Jun 2025

1761

6) kai tsaye can ya nufa yayi parking a inda aka ta nada kafin ya
fito da sauri ya bude musu mota.

Tun sa'ilin da Asp din ya kira wayarsa ya sheda masa zuwansa ya fito ya tsaya domin
tsumayinsa sai dai ganinshi tare da yarinyar ya d'an sosa zuciyarsa, amma be nuna hakan a
fuskarsa ba, cikin wani irin taku na gwaraza! ya isa bakin motar gabadaya hannuwansa goye a
bayansa. Hannu ya mika masa sukayi musabaha ga juna, Nabila da saurin gaske ta gaisheshi har tana
kiran shi da Uncle, ya dan saki fuskarsa ya amsa shima ya darajata kamar yanda tayi masa ya
'boye asalin sunanta ya maye gurbin sa da daughter ina godiya." Murmushi kawai tayi tana

sunkuyar da kanta.............Kamar yanda ya watsar da lamarinta ita itama haka ta watsar dashi,
ta dinga cika tana batsewa tana banka musu harara! tabbas da ta san gidansa ne da tuntuni ta
sauka a hanya domin bata bukatar abinda zai had'ata dashi.

Asp ya juyo cikin tsare gira ya kalleta da fadin." Ku shiga ciki ku gaisa da mutan gidan, sannan
ke Zinatu sai kiyi mata bayanin kanki."

Ta kalleshi da niyyar caccakarsa, yanda ya sha kunu! yasa ta d'an ji shakkarsa domin ta fahimci
shima dan had'in takaici ne mybe tana iya magana ya buga mata tsawa! a gaban mak'iyinta
wannan dalilin yasa tayi shuru amma a fuskarta zaka tabbatar da cewa ranta a b'ace yake,
Nabila ce tayi gaba, kafin tabi bayanta tana d'acin rai!

Barin su gurin yasa gabadaya suka sauke ajiyar zuciya, suna shakkarta tana shakkarsu, tana
da wata baiwa wacce ita kanta bata san tana da ita ba, koda yake jinin saurata gaba da baya
yana yawo a jikinta, dole takewa mutane kwarjini a ido, dan dai ta had'u da jajurtattu ne.

A wasu kujeru suka zauna kafin su shiga tattauna abinda ya had'asu a gurin.


Da yake ta sheda fuskarta a tv da jarida yasa suna shiga ta sheda ta, fuskarta a sake take
musu lale marhabun tana nuna musu gurin zama, Uwale ba dai karrama mutane ba.

Nabila ce kadai take amsawa, ita kuwa kamar kurma! uffan ba tace ba ta nemi kujera ta zauna
tana bin falon da kallo, komai akwai tamkar falon shahararan mutumin daya amsa sunansa.
hotonansa dake kafe falon sune suka dauki hankalinsa, uku ne d'aya yana sanye da inform
wanda yayi masa bala'in kyau! biyun kuma kayan farauta ne rakwacam! a jikinsa hannunsa
rike da wata gora mai lankwasa! kansa nannad'e da wani bakin yadi, gabad'aya jikinsa babu
masaka tsinke damtsen hannuwansa daddaure da wasu igiyoyi! hoton ya dauki hankalinta
mutuka sai kawai ta tsinci kanta da tunanin rayuwarsu a daji! tsigar jikinta gabadaya ta tashi
sa'ilin data tuna sassanyar muryarsa a lokacin da yake rarrashinta idan wata masifa ta sameta,
lumshe idonta tayi na minti biyu ta bude still hoton ta cigaba da kallo gabanta na wani irin
fad'uwa!.

Har Hamra'u ta shigo falon tana can gurin kallon hotonsa, gaisheta take amma inaa! hankalinta
gabadaya na can wani guri, Hamra'u ranta ya b'aci wata kibiyar kishi mai mugun tsini tazo ta
tsaya mata a wuya!! kusa da Uwale ta zauna tana jin takaicin abun a ranta.

Maganar Uwale ce ta dawo da hankalinta, da sauri ta janye idonta daga kan hoton tana kokarin
saisaita tunaninta ta kalleta da fadin" Kowa lafiya insha Allah gobe nake sa ran had'uwa dasu."

Cikin kulawa tace."To masha Allah, don Allah idan kin isa gidan lafiya ki mika gaisuwarmu gare
su, Allah ya kiyaye gaba."

Ciki-ciki ta amsa da "Ameen." Ta dora idonta kan Hamra'u dake ciccin magani! kallon 'yar
'kauye tayi mata kafin taja tsaki a fili tace." Stupid girl!." Uwale ce kawai bata fahimci komai ba,
Nabila da Hamra'u sunji lokacin da tayi zagin sai suka rasa da wanda take a cikinsu! Hamra'u
tafi tsarguwa cewa da ita take, ba tace komai ba ta tashi domin barin gurin, ta kalleta a yatsine
kafin tace." Ugly!!." (Mummuna!) da yake ta danyi karatu ta fahimci maganar, amma bata tanka
ba, tayi saurin bude dakinta ta shige tana mugun mamakin al'amarin!
Ita kuwa Nabila duk wannan abun dake faruwa ba sabon abu bane a gurinta ta riga ta san hali
shiyasa uffan ba tace mata ba, har ta k'araci iskancinta ta gama, Uwale dai ba jin turanci take
ballanatana ta fahinceta, tas taci musu mutunci cikin turanci ba tare da wata shakka ba!


Yace."Kamar yanda muka tattauna maganar a kwanakin baya yanzu ma zan sake dawo mana
da ita domin samun solution." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Ka san da cewar
duk abunda yake faruwa Commissioner of police baya gari yaje taron k'arawa juna sani dashi
da ta kwarorinsa, sai dai duk abunda yake faruwa yana da labarinsa, ya san labarinka kuma
yana da cikakken labarin irin muhimmiyar rawar da ka taka, sai dai kuma a lokacin da ya samu
labarin cewa ka fara gudanar da aiki, sai ya nuna rashin goyon bayansa akan hakan, A cewarsa
lallai sai kaje kayi training domin haka dokar aiki take, banyi masa gaddamar hakan ba saboda
na san yana da hujjah mai kyau! amma na sheda masa cewa umarnin mai girma governor ne
hakan, duk da hakan ya nuna rashin goyon bayansa da fadin shi zai zauna da governor din
domin su tattauna maganar, shine nayi maka maganar a cikin kwana biyar da suka wuce, yanzu
ma ina maimaita maka, gobe insha Allah muke sanya ran zai sauka, babu shakka na san cewa
zai nemi zama da kai, ina so ka kula dashi da kyau!domin shi din wani irin bahagon mutum ne
mai raina tunanin mutane, a tsarinsa bai yarda da cewa wani ya fishi ta kowanne fanni ba,
kullum shine wanda ya iya, sannan baya kar'bar kuskure a tsarinsa, wannan kadan kenan daga
cikin halinsa, ina so ka kiyayi mu'amula dashi."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Asp tun lokacin da kayi min maganarsa ban ji wani tsoro! ko
fargaba! ba (bahaushe yace fad'uwar gaba asarar namiji!!) Ni na fi so ma naje nayi training din
domin nagoge! maganar halinsa kuma wannan bai dameni ba, abinda na sani shine ba zan
yarda da rashin gaskiya ba! ba zan aminci a hada baki dani a cuci 'kasata ba! ba zan yarda a
cutar da wani ba! ba kuma zan yarda da cin hanci da rashawa ba."! Cikin jaddada gaskiyarsa
yake maganar.

Asp yaji dadin furucinsa Yace."Naji dadi sosai da wannan alkawarin naka, ina rokon Allah ya
tabbatar damu akan hanya ma daidaiciya." Ya amsa da "Ameeen ya Allah."

Tare suka mike tsaye, Asp din yace." Idan babu damuwa inaso mu gaisa da Hajiyan." Cike da
jin dadi yace." A haba babu damuwa mutumina muje kawai." Tare suka jera domin shiga gidan
suna sake tattauna maganar.

*Free pege zai kare a pege 40 kuyi payment domin karanta labarin cikin nutsuwa da kwanciyar
hankali, idan da akwai bukata Sadauki Omar 1k za'a tura domin samun damar karanta littafi
biyu wato Goje (Sadauki Omar return) mu nesanta kanmu da haram! duk kankantarta! hakkin
wani bala'i ne! kada ganin 'kyashi- hassada mugunta ya hanaki biyan kudin littafi ki jira na sata
ki karanta! ki dauki nauyi kin dorawa kanki! abunda ba zai zama dole ba, idan baki da ikon biya
babu lallai babu dole akan ki dauki hakkin wani gwara ki hakura!!!!*

*Wa'inda zasu sayi littafin nake da bukata, idan kin san ba siya zaki ba don Allah kada ki dauki
number ta kiyi min maganaí ½í¹í ¼í¿»*




*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number....
22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!!🏹*
🐕â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITER'S*
*ASSOCIATION📚🖊ï¸*
____________________

_Mijina kazami! ne! to ni kam sai dai nace kiyi hakuri 'yar uwa domin akwai su a cikin maza
amma ba duka ba, kuma bake kadai kike da matsala irin wannan ba, amma ki sani ke da kanki
kina iya gyara abinki, da wayo da dabara, zahirin gaskiya kazamin namiji nada wuyar sha'ani!
duk macan da take fuskantar wannan matsalar daga gurin mijinta akwai hanyoyi masu sauki da
zata bi domin gyara masa dab'iu kamar yanda takeso ya kasance!_



FREE PEGE
*33&34*
Police barrack nan ne mafi akasarin ma'aikatan tsaro suke zaune da iyalansu, a nan gidan Asp
yake, haka zalika ma anan ne mai girma Governor ya mallakawa UMARU gida tazarar su da
Asp din babu yawa gida biyar ne a tsakaninsu, tsarin ginin gidan mai kyau ne, plate ne mai
dauke da bangare uku, kowanne 'bangare a shirye yake tsaf da dukkan abinda za'a bukata na
yau da gobe, abinda kawai ya rage a gidan mace, don a ranar da ya tare a gidan ma 'yan uwa
da abokan arziki surutun da suke masa kenan, cewa a yanzu Allah yayi masa komai na rayuwa,

abinda ya rage masa mace domin duk cikar mutum da kamalarsa mutukar bashi da aure to
darajarsa dole tayi 'kasa..........'Kwarai hakane a yanzu ya san cewa cikar mutumcinsa shine
aure, wannan dalilin ya sanya yaji sha'awar auran a cikin zuciyarsa, sai dai kuma babu wanda
ya amsawa cewa zai auri 'yarsa a cikin wa'inda suke kawo masa tallan 'ya'yansu, da kansa zai
duba wacce ta kwanta masa a ransa ya aura.

B'angare d'aya ya dauka Uwale da Hamra'u sai suke amfani da daya, Uwale ganin ba zata iya
zama a gidan ita kadai ba yasa tace Hamrau ta ta zauna domin ta taya ta zama, hakan yayi
mata dadi mutuka domin dama tana neman hanyar da zata kusanta kanta dashi.

Itace ta d'auki ragamar kula da gidan, ta tsaftacce ko'ina har sashensa idan zai fita take 'karbar
key a gurinsa ta shiga ta gyara masa ko'ina tasa turare idan taga ya cire k'ananun kayanshi a
toilet ta wanke masa tas ta shanya idan sun bushe ta ninnke tasa masa a wardrobe, kullum
idan ya dawo daga gurin aiki tsaf-tsaf yake samun gurinsa yana kamshin turare na mussaman,
kafin yayi wanka ya fito ta shirya masa abinci da duk wani abinda zai bukata, k'wazon yarinyar
da yanda take kulawa dashi da kakarsa yana burgeshi! ba tun yau ba ya gane inda ta dosa a
kansa, zai iya auranta saboda kyawawan dabi'unta dama wannan shine abin dubawa a cikin
lamarin aure.

'Bangaranta kuwa shawarwari take da zuciyarta kan cewa ta sheda masa tana sonsa ko kuwa
ta bari ya furta mata da bakinsa, a ganinta yanzu tunda yayi kudi yafi k'arfinta shiyasa kullum
take jin tsoron tunkararsa da maganar gudun wulakanci, sai dai duk sanda masifar sonsa ta
isheta daki take shiga taci kukanta ta koshi, kafin ta roki Allah ya za'ba mata abinda yafi alkairi
a rayuwarta, amma tayi mamakin yanda akayi Uwale tayi shakulatun 'bangaro da maganar
wanda ada can baya har kayan lefe take tarawa burinta bai wuce tabbatuwar auran ba, amma
yanzu kwata-kwata bata maganar, ballanatana ta bashi umarnin auranta kamar yanda tayi
alkawari a can baya.

Kamar yanda gwamnati ta mutuntashi ta kuma karramashi, shima haka ya mutunta yaransa ya
karramasu yayi musu alheri sosai, domin duk rabin alherin da ya samu ya sadaukar musu, a
cewarsa suma suna da hakki duba da irin muhimmiyar rawar da suka taka, hakan ya sake
janyo masa kwarjini da farin jini a gurinsu da sauran jama'ar gari.
*******
Yau satin sa guda kenan da fara gudanar da aiki a ofis dinsa na mussaman, Uniform dinshi ma
na mussaman ne, amma yayi kamanceceniya dana Asp amma kuma akwai bambanci sosai!

Da yake yana da hikima da nazari babu wani abu da ya shige masa duhu, aikin yake kamar
wanda ya shekara yana aikin tsaron lafiyar al'umma!

Wasu takardu yake dubawa kira ya shigo wayarsa dake saman tevur din dake gabansa.

Ya ajiye takardun cikin nutsuwa ya daga wayar da fadin.'' Ranka ya dade barka da aiki."

Daga daya bangaran Asp ya amsa da "Barka dai *Jan wuya!* da yake sunan da yake kiransa
dashi kenan, ya cigaba da cewa." Gobe ne fa tafiyar nan."

Yayi jim! yana tunanin maganar kafin ya dan ja siririn tsaki! ya manta shaf da maganarsu ta
zuwa garin kano domin kai marakunyar yarinyar nan gaban iyayenta........Yace."Ogah me zai
hana ka sata a mota ta tafi ai ita din ba yarinya bace zata kai kanta gida."

Ya girgiza kai da fadin." A'a mutumina ba za'ayi haka ba, ni nayi wa mahaifinta alkawarin cewa
dani da kai zamu kai masa ita, sannan kuma ba haka dokar aikin take ba, dalilin da yasa ma
tuntuni ban shirya tafiyar ba, saboda na fi bukatar yarinyar ta murmure na 'yan kwanaki hakan
zai farantawa iyayenta rai su kuma ji dadin ganinta cikin koshin lafiya, to alhamdullihi yanzu
naga tayi kyau sosai babu rama ko wani abu wanda ya danganci haka daga gareta."

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin.'' Ranka ya dade don dai kawai ka shirya tafiyar nan dani ne
amma da sai dai nace kaje kai kad'ai kawai dalili bana bukatar abinda zai sake danganta ni da
yarinyar nan wallahi.''! Cike da takaici ya 'karashe maganar.

Asp na 'yar dariya yace." UMARU ban san me yasa kai da yarinyar nan bakwai jituwa ba, itama
yanda kake jin haushinta haka take jin haushinka kullum bata da magana sai taka."

Da sauri yace." Tana zagi! na ko."? Asp din yasa dariya da fadin." In kaji zagi! ma d'aya kenan!
shin ka san kuwa maganar da mukayi da ita kwanaki a kanka."?

Kai ya girgiza a k'untace yace." Sai ka fad'a." Jim yayi kafin yace." Na san sharri kawai tayi
maka ba zaka aikata hakan ba, duk da dai zuciya bata da 'kashi kuma a lokacin hakan na iya
faruwa saboda kusancinku da juna wanda dama shi shed'an burinsa kenan mace da namiji su
kad'aice shi sai ya zama na ukunsu."
Tsaf ya fahimci inda maganar ta dosa, murmushin takaici yayi kafin yace." Banyi mamakin jin
wannan maganar ba domin duk mutumin da yake 'kin ka, to babu irin k'azafin da ba zai yi a
kanka ba, Asp wallahi tallahi! da naso keta haddin yarinyar nan da ba zata kai labari a hannuna
ba, saboda na samu dama iri-iri a kanta amma sam ba wannan ne a gabana ba, burina shine
na kubtar da ita, sai kuma sharri! ya biyo bayan alkairi."

Yace." Kwarai kuwa shiyasa a lokacin da take maganar na 'karyata ta domin na san ba za ka
aikata hakan ba, kawai dai tana neman hanyar da zata tozartaka ne."

Yace."Shiyasa ai nace kayi tafiyarka kawai Asp wallahi kaji rantsuwar musulmi ba naso na sake
ganin fuskar yarinyar nan."

Yace." A haba dai kada ka tsananta da yawa abu ne mai sauki wannan ki
'kiyayyar da kukewa junanku ta rikide ta zama soyayya irin wacce take da wuyar samu hakan

na iya faruwa.

Ranshi ya 'baci da jin haka tevur din dake gabansa ya buga! murya a sama yace." Allah ya
kiyaye Asp bana fatan Allah ya jarrabeni da soyayyar wannan yarinyar, kawai kayi min fatan
alkairi ba irin wannan ba."

Asp din yayi mamakin yanda maganar ta fusata shi, sai ya sassauta murya da fadin." Colm
dwon mana ka samu nutsuwa, wannan maganar dana nake maka a yanzu ba wai nace lallai
hakan ya tabbata ba, kawai a jikina nake jin kamar akwai wani abu da zai ratsa tsakaninka da
yarinyar domin anyi irin haka ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, kiyayya ce ake wacce tafi
wannan daga karshe kuma sai ta rikide ta juya matsananciyar soyayya."

"Mtsssssw!!!! Yaja wani dogon tsaki kafin ya kashe wayar ya jefar saman tevur tunda ya had'u
da Asp bai ta'ba 'bata masa rai irin yau ba........Shi kuwa Asp din sakin baki yayi da wayar a
hannunsa yana mamakin al'amarin.


Da takaicin maganganun Asp ya isa gida, takalmanshi kawai ya iya kwancewa ya kwanta
saman kujera ba tare da ya cire inform din dake jikinsa ba, rungume hannunsa yayi a kirji ya
rufe idanuwansa yana hasaso kammanin yarinyar............. 'baka ce ba sosai ba, idan be manta
ba tana da tsayi gami da cikar kirji da fadin kwankwanso, 'kirar jikinta kenan, tana da manyan
idanu da d'an k'arami hanci wanda ke tsatstsafo da gumi ako da yaushe, wannan sune kad'ai
abunda zai iya tunawa a game da ita!

Yaja tsaki! tare da gyara kwanciyarsa, har yanzu maganar ce take cin zuciyarsa! shi kam a
rayuwarsa me zai yi da yarinyar da ta nuna masa tsantsar 'kiyayya irin haka, hanyar jirgi daban
ta mota daban.

Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya bude idonshi tare da tsareta dasu, be tashi zaune ba yana
daga kwance ya amsa mata, still idonshi na tsaye kanta, sai tace tunda suke bai ta'ba yi mata
kallon kurrullah irin haka ba, duk sai ta tsargu dama ta shigo ne domin ta duba taga ya dawo ta
kawo masa abinci, jikinta duk sai ya mutu sakamakon kafe ta da yayi da kaifin idanuwansa.
A sanyaye tace." Yayana sannu da zuwa ashe ka dawo."?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yun'kura ya tashi zaune yana kokarin b'alle botiran gaban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login